Showing 12001 words to 15000 words out of 31859 words

Chapter 5 - ABU NAKA Book 1 Complete Document By SODANGI.txt

02 Dec 2024

1509

ai kin ji, dama na gaya miki bani da wayo, ganin da na yi in na zo gida kina tarairayata kina girmamani sai na xauka ko yanda nake jinki a jikina haka kema kike jina, ni in ina kusa dake wani irin kwanciyar hankali da nutsuwa nake samu, na kan kuma barki ne don tsoron kar in gundureki. To amma tunda kin faxi haka, to gaya min tsakanin ni da saurayinki wa kika fi shaquwa da shi?”
“A’a, Yaya ai maganar ‘yan’uwa muke yi”.
Ya yi maza ya ce, “Eh, haka ne maganar ‘yan’uwa ne, to wa kika fi shaquwa da shi a ‘yan’uwan?”
Hankalinta a kwance ta ce mishi, “Anti Hamida, bana iya yin kwana biyu ban je gidanta ba”.
Ya xan yi murmushi saboda jin da ya yi tamkar taya shi son Hamidan take yi.
“To ai ita kun girma xaki xaya ne Aisha, ba shekaru biyu da suka wuce bane ta je gidan auren ta? Ban da ita gaya min wani”.
Ta ce, “Yaya Bilki”. Tsoron kar ya sake tambayarta ta sake faxin “Yaya Kuluwa”.
“Ko wani can ma daban”. Ya sanya shi yi mata maganar.
“To yanzu xin ni dake mun qulla abota a yau, don ki rinqa bani shawara kan neman auren da zan fara in na yi sa’a yarinyar ta soni to nasarar taki ce, in ba ayi ba ma na san ke ce, don haka mu fara daga yau. Mene ne abin yi tunda na riga na bayyana miki komai?”
Ta ce, “Ka fuskanci yarinyar kawai ka daina maganar tsoro, ai kana da kwalitis xin da za ka nemi aure a ko’ina ne a baka, don kai kanka ba sai anyi maka jagora ba”.
Ya ce, “Haka kike gani ko Aisha?”
Ta yi maza ta ce, “Eh mana, kana da ilimin addini, kana da na zamani, kana da matsayi irin wanda mutane da yawa suke buri basu samu ba, kana da cikakkiyar halittar da zance ‘yammata da yawa za su yi burin samun miji irinka”.
Kamar ya tambayi Saddiqa har da ke? Sai ya kanne ya ce mata, “Ai inda matsalar take ban tsoro shine wurin iyayen yarinyar, sun riga sunyi min wani irin sani basu bar ‘yarsu ta yi min irin wannan kallon ba, amma tunda kika faxi haka to bari zan gwada in bi shawarar ki na yiwa yarinyar magana ni da ita, zan taho Misau kwanan nan amma zan qara kintsawa. Ke kuma sai ki qara sani a addu’a don yarinyar samari ne da ita”.
Ta yi dariya ta ce, “Baka dai daina tsoronta ba kenan?”
Ya ce, “A’a, na daina……”
Fizge wayar da aka yi shine ya katse zancen nasu. Cikin takaici ya zuba mata ido.
“Who are you talking to?”
Ta yi tambayar cikin takaici.
“You are stupid florence”.
Ya faxa mata. Sannan ya ci gaba da yi mata magana cikin Turanci.
“Kin san da wa nake magana? Daga Misau ne fa”.
Ta ce, “Sai me? Duk Misau ne iyayenka? Wannan hirar kai da budurwa ne tun daga nesa nake hangen nishaxinka, wacce ‘yar iska ka samu a can xin da ta sameka haka?”
Ya ce, “A’a, kar ki zageta”.
“Me za ka yi in an zage tan? Ai dama da cikinka na zo gidan yau ina son jin inda ka samu shegiyar da na ganka da ita jiya”.
Ya yi murmushi ya ce, “Florence kenan, daxina dake akwai ki da bagu”. Ya miqa hannu ya jawota jikinshi.
“Tunda kin bar maganar farko to zauna mu yi wannan a zaune ai zamu sasanta, tun jiya ai na gaya miki ba budurwata ba ce”.
Ta galla mishi hara ta ce, “Ba budurwarka ba ce ka gabatar mata dani a matsyin budurwar abokinka”.
Ya yi maza ya ce, “Ni?” Yana mai nuna qirjinshi da xan yatsanshi.
“Kece na gabatar a matsayin budurwar abokina Florence ba ita ce na gabatar miki a matsayin buduwar abokina ba”.
Ta ce, “Abin da na ji ka faxa kenan nice budurwar abokinka”.
Ya ce, “To baki daidai ba, kuma na gane kina da munafukan kunnuwa waxanda basa jin magana daidai saboda suna son ganin ana faxa ni, ni kuma ba abin da yake gabana ba kenan yanzu”.
Ta buxe mishi baki za ta yi magana ya yi maza ya ce, “Ina jin dai kin samu wani saurayin ne yasa kika matsa sai anyi faxan nan don ki samu hanyar rabuwa dani”.
“Ba haka bane”.
Ya ce, “To in ba haka bane zo ki gani”.
Ya miqe ya kama hannunta ya ja ta zuwa xakin kwanciyar shi.
Ranar litinin a wurin aiki bayan sallar azahar ya fito daga masallaci yana nufin komawa ofis xinshi ya hango Jennifer tana sauri saboda ganin da ta yi mishi, shima ya xan xaga kansa kaxan.
Tana shiga ta yi nufin turo qofar ta rufe ya yi maza ya tare qofar da hannunsa, ya shiga ya turota. Yana shiga ya cafketa ya xora bakinshi a nata tsawon, har sai da ya haxata da jikin bango saboda kici-kicin qwatar kanta da take yi.
“Me na yi miki kike guduna?”
“Fita min daga ofis xina”.
Ta faxi cikin tsananin vacin rai. Bai kula ba ya ce mata, “Ki zo gida yau sai mu yi magana”.
“Never in my life”.
Bai kula ba ya ce, “To shi kenan ni zan zo gidanki hira yau, amma in na zo na samu wani kema kin san sauran”.
“To ka bari sai na neme ka mana ka sa min doka”.
Ya yi murmushi ya ce, “Ai ba haka nake ba, na kan daidaita al’amura ne in zan yi su”.
Idanuwanta suka cicciko. Ya fita ya bar ofis xin ya nufi nashi, yana shiga ya danna lambobinta.
“Kar ki ajiye min waya Jennifer, gaya min kawai za ki zo xin ne ko ni in zo naki gidan?”
Cikin takaici ta sake ce mishi, “Na daina zuwa gidanka”.
“Ai babu damuwa, ni zan zo”.
Ya ajiye wayar. Jennifer ta zubawa wayar dake hannunta ido cikin takaicin al’amarinta, ga samarin dake sonta kamar suyi hauka ta qi basu haxin kai sai Mus’ab, mutumin da kullum sai ranta ya vaci a kanshi, ga shi ko ta yi niyyar xaukar mataki mai tsanani game da shi tana ganinshi sai ta kasa aiwatar da komai a kanshi sai yanda ya yi da ita.
Yana kwance a xakinshi bayan ya dawo daga yawonshi na qa’ida zuwa club, juyi yake yi a kan gadon barci ya qi xaukar shi duk da sai da ya kora barasarshi da ya fi ta’ammali da ita wato ‘Bacchus’ kafin ya iso gidan.
Ya sake wani juyin a hankali kafin ya kira sunanta “Aisha”. Ya buxe idonshi a hankali ya ga tamkar ita ce a gefen nashi a kwance, da sauri ya sake rintsewa ya sake buxe su
“Wato ni kike wa gizo ko? Ja’ira zan kama ki”.
Tunanin kama tan ya shigo cikin ranshi, nan take ya tambayi kanshi anya zai kamata kuwa? Nan take ya kunna fitilar xakin saboda wattsakewa da ya yi, biyu da rabi ne na dare, ya rasa me zai yi ya miqa hannu ya xauko wayarshi da nufin ya tura mata saqon da za ta gani da safe, ya yi rubutu kamar haka.

“Aisha!
I wrote a list of my friends I smile.
I wrote a list of my those I still have.
I still smile I wrote the list of those lam keeping for ever I still smile because your name of still there.

Mamaki ne ya kama shi yanda minti biyu kawai bayan tafiyar saqon ya ji wayarshi ya kama ruri, a hankali ya tambaye ta me kike yi yanzu idonki biyu Aisha?
Ta ce, “Na idar da sallah ne ina istigfari”.
Gabanshi ya ba da ras! Nan take ya qara dawowa cikin nutsuwarshi.
“Kin yi min addu’a?”
Ta ce, “Eh, na yi maka na yiwa Inna ma tare da sauran musulmin da suka rigamu, ai tun ranar da ka ce min in rinqa yi ban tava fasawa ba”.
“To na gode Aisha, na gode da kike xaukar maganata da muhimmanci, ga shi kina yi min addu’a ni ina kwance”.
“A kwance kake?”
Ya ce, “A kwance naka amma na kasa yin bacci saboda damuwa ta min yawa, ina cikin soyayya mai zafi, ina son yarinyar da nake gaya miki xin nan, ina cikin zullumi Aisha, ina cikin fargabar abin da zai biyo bayan fuskantar ta da nake shirin yi”.
“Amma mun yi dai a kan ka daina tsoro”.
Ya ce, “Eh, fargaba nake da zullumi ba tsoro ba, abin da zan tarar wurin iyayenta ne ya fi damuna, kin san ni xin tsohon mai laifi ne, Inna ba ta tava baki labarin laifina ba?”
Ta ce, “Ai na gaya maka ba ta hirarka da wani, kuma ba zai yiwu a ce yanda Inna take kallon ka haka suma iyayen yarinyar za su kalle ka ba, don haka kar ka sake jin zullumi ko faxuwar gaba”.
Ya ce, “To na gode da shawararki Aisha, sai da safe”.
Mus’ab yana kwance tare da Jennifer a xakinshi wunin ranar asabar ne, tausa take mishi saboda kukan kasalar da ya yi mata. Wayarshi ta yi qara yasa hannu ya xauka, Sani ne a kan layin.
“Kana fa da baquwa a nan falon za ka samu fitowa ne ko in ce baka nan?”
“Wace ce?”
Ya ce, “A’a, ba zan faxa ba in dai in sallameta kawai to”.
“Gani nan zuwa”.
Ya yunqura ya tashi daga kan gadon ya xauki shirt xin da ya cire yana mayarwa tare da valla botir xin.
“Ina za ka ne?”
Jennifer ta yi tambaya. Bai kalle ta ba ya ce, “Na yi baqi a falo”.
Da sauri ta ce, “Baqi ko ‘yan iskan ‘yammatan da suka saba biyo ka gida?”
Ya ce, “Ai dukanku xaya”. Ya fita.
Ta yi maza ta wuto shi ta riga shi shiga falon.
“Yi maza ki bar falon tun ban ci mutuncinki ba”.
Ta baiwa yarinyar umarni.
“Yi zaman ki Sarah tunda wurina kika zo”.
Daga bayan Jennifer ya yi maganar.
Ta juya ta kalle shi ta ce, “Amma kai ka ce min in zo gida ka yi tsari mai kyau na wanda ya riga zuwa shine maigida”.
Ya ce, “Eh, amma ai hakan ba yana nufin ba zan ga baqi bane, ina son ganin Sarah”.
Ta qara fusata ta ce, “Ai tunda ka gaya min haka ka sani na zo sai na fidda wannan ‘yar iskar daga gidan nan”.
Ta yunqura za ta cafketa ya yi maza ya kamata ya riqe, ta xago hannu da nufin wanke shi da mari ya yi maza ya kama hannun ya murxe.
Kafin ya sake shi cikin nutsuwa ya ce mata, “Kar ki fara don zai sa ki gane baki da wayo”.
Ya jawota suka fito harabar gidan tana antaka ashar, hankalinshi a kwance ya ce mata, “Haba Jennifer a gaban wannan ‘yar qanqanuwar yarinyar kike wannan haukan, kin kusa ki haife ta fa, wannan ai abin kunya ne”.
Haushin shi ya sake kamata, cikin takaici ta ce mishi, “Tsohon banza kai meye? Kai baka girmeta ba?”
Ya yi murmushi ya ce, “Na girmeta mana amma ke kam ai sai dai mu yi sa’o’i ko in xan baki shekara haka”.
Ta zuba cikin takaici, ta gaji ta ce, “Laifina ne da na zo gidanka”. Ta juya ta kama tafiya.
Shi kuma ya wuce ya shiga cikin falon yana murmushi, ya ce, “Sorry Sarah”.
Ta xan yi murmushin qarfin hali. Ya ce, “Me zan kawo miki?” Ta xan yi shiru. Ya sake tambaya “Bacchus ko Whiskey? Wanne zan kawo miki?”
A hankali ta ce, “Za ta gwammace whiskey”.
Ya yi murmushi ya koma, jimawa kaxan ya shigo da tire mai xauke da kwalbar whiskey tare da kofi guda xaya ya ajiye ya zuba, ya xauka ya miqa mata ya koma kan kujera ya kunna karan sigarinshi na Rothmans.
Ta bishi da kallo alamar tambaya, ya xan yi murmushi ya ce, “Yi haquri ki sha ke kaxai kinga azahar ta yi zan yi sallah”.
Ta yarda da uzurin nashi, ta ci gaba da sha shima yana zuqar sigarinshi cikin nishaxi.
“Amma ai ba kina nufin tun gamuwarmu dake a liyafar Bola sai yau ne kika tuna dani ba ko?’
Ta yi murmushi ta ce, “Tafiye-tafiye ne suka yi min yawa, yanzu ma gani na yi bai kamata in yi Birthday xina ban gayyace ka ba shi yasa na zo”.
Kiran sallar da ya jiyo yasa shi ya miqe.
“Sarah za ki xan jirani kaxan”.
Ta ce, “Babu damuwa”.
Ya fita ya barta ita kaxai a zaune, ita ma ta samu damar da ta yiwa falon kallon kyau, tsarinshi ya kai yanda ya kai, ga kuma hotonshi dake ajiye a can gefe.
Ta yi ajiyar zuciya, komai nashi ya yi, sai dai da alamar manemin mata ne sosai. Yaron gidan ya kawo mata gasasshiyar kaza da abubuwan ci da na sha.
Fiye da wa xaya da rabi tana zaune kafin Mus’ab ya shigo.
“Yi haquri Sarah na tsaya ne a masallaci na yi la’asar. Sun kawo miki abinci kuwa?”
Ta ce, “Eh, sun kawo na ci har na qoshi”.
Ya ce, “A’a, ba ga salad na ga baki tava ba? Me za ki ci a shirya miki?”
Ta ce, “Ai ni yanzu ma zan tafi”.
Ya ce, “A’a, to ai ba ki gayyace ni Birthday xin ba kenan, kina nufin in karvi gayyata a kwali ko a fatar baki?”
Ya tashi ya shiga xakinshi ya fito riqe da dairy da biro a hannunsa ya koma kusa da ita ya zauna.
“Yaushe ne Birthday xin?”
Ta faxa ya rubuta, “Saura kwana biyar kenan?”
Ta ce mishi, “Eh”.
“To ai akwai shirye-shirye kenan”.
Ta sake ce mishi “Eh”.
Ya sake zuba Whiskey a kofi ya sake miqa mata ta karva.
“Nawa kike ganin za a kashe?”
Ta soma magana cikin yanayin rangwaxa ta ambato abin da take ganin ta yi qoqari. Yasa hannu ya karvi kofin dake hannunta ya ajiye.
“To zo daga nan mana”.
Yasa hannu ya kama nata ya ce, “Muje in ga abin da zan iya bayarwa”.
Suna kwance a xakin nashi cikin yanayin gajiya, kowanne a cikinsu mai da numfashin shi yake yi a hankali.
“Sai yaushe za ki sake zuwa?”
“Ai kuma na ji tsoron zuwa gidan naka tunda ga abin da na gani”.
Sai da ya fitar da hayaqin sigarinshi da ya zuqa sannan ya ce, “Da kika ganin me ya same ki? In dai kina da aiyuka da yawa shi kenan babu matsala”.
Ya miqa cek xin dubu hamsin tana daga kwance.
“In kin fita sai ki xauka Acces Bank, bana zaton zan iya zuwa Birthday xin don zan tafi Misau a ranar, in na dawo zan zo in kawo nawa gift xin, in kuma kin rigani samun sararin zuwa gidan to sai ki zo ki karva da kanki”.
Ta yi godiya cikin jin mamakin kyautar da ya yi mata.
Mus’ab ya isa Misau, Saddiqa ce kaxai a tsakar gida tana wanke-wanke lokacin da ya yi sallama ya shiga gidan, ta xago kai ta kalle shi cikin mamakin zuwan nashi.
Suna haxa ido ta kwashe da dariya, ya ja ya tsaya yana kallon ta cikin mamakin dariyar tata, ita kuwa sai qyalqyala dariya take yi.
“Me ya faru?”
A yanayin mamaki ya yi tambayar.
Ta ce mishi, “Haba Yaya, yanzu nan qasunbarka ka aske?” Ta sake fashewa da wata dariyar ta ce, “Ai kuwa dai baka ga yanda fuskarka ta yi ba, sai ta yi sarari”.
Ya ce mata, “Eh, canji-canji zan rinqa yi, in yau an ganni da qasumba wani zuwan sai in aske, saboda in yau ta ganni a dattijo gobe

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login