Showing 1 words to 3000 words out of 31859 words

Chapter 1 - ABU NAKA Book 1 Complete Document By SODANGI.txt

02 Dec 2024

1505


ABU NAKA…


1




























HAFSAT C. SODANGI
Haqqin Mallaka (m) Hafsat C. Sodangi






Shekarar Bugu:
2005






An sake Bugawa A:
2015



A lura
An xan yi gyara a cikinshi kaxan saboda wasu dalilai, sai dai yana nan a kan tsarinshi na farko.
Na gode.
11/8/2006




ABU NAKA-1
M
us’ab ya yi parkin xin motarshi qirar peogoeu 504 sabuwa dal sai xaukar ido take yi a rana tana walqiya, baqin fentinta ya yi matuqar dacewa da ita.
Mus’ab ya fito daga cikin motar yana sava babbar rigarshi ta farin voil da aka yiwa xinkin Ado Bayer. Dogo ne sosai wankan tarwaxa da ya kusa ya zama fari, yana da xan jikin da ya qara bayyanar da kyakkyawar halittarshi saboda qara mishi kwarjini da hakan ya yi.
Qofar gida da ya dosa kewaye yake da darmin zanna wanda aka yiwa turaku da bishiyoyin aduruku. Kai tsaye ya nufi cikin gidan, tun kafin ya yi sallama ya hangeta zaune kan shimfixarta cikin rumfar dake kusa da xakinta.
“Hantsi kike sha ne haka?”
Ta xago kai ta kalle shi cikin yanayi na mamaki.
“Ya ya aka yi ban ji sallamarka ba sai ganinka kawai na yi ka shigo min gida?”
Ya yi murmushi haxe da cewa, “Ban tsaya yin sallamar bane Abu, a ina kika ga maigida yana tsayawa neman izinin shiga gidanshi?”
“To ban yarda ba koma kawai ka yi sallama in amsa tukunna kafin ka shigo min gida”.
Ya sake wani murmushin mai ya ce, “Maigidan kike yiwa haka ke? Xan amsa kawai daga nan. Assalamu Alaikum!”
“Wa alaikumus salam”.
Ta amsa tana murmushi tare da faxin, “Sannu da zuwa, hala a Vauchi ka kwana?”
Ya ce, “Ai a xakina na kwana wai dan kawai na taso tun da sauran dare, don a garin Malewa na yi sallar asuba”.
Abu ta riqe baki nuna alamar mamaki, ta ce, “To mu shiga xaki mana”.
Ya ce, “A’a, mu yi zamanmu a nan kawai don mu sha iska”.
“To bari in qara maka shimfixa”.
Ta miqa hannu ta jawo tabarma a bayanta tana shimfixa mishi.
“Wato ke da tabarmini ma kike zama a kusa dake?”
Ta ce, “To gidan nawa ai na jama’a ne, wannan ya shigo ne, wannan ya fita. Kamar yau xin nan Jum’a, da za ka kai bayan sallar azahar a sauko masallaci, ai in ka soma ganin jama’a sai ka yi zaton xaurin aure za a yi’.
Mus’ab ya yi murmushi ya ce, “Ai na lura in har akwai abin da yake da nishaxi a cikin al’amarin tsufa bai wuce zuwa gaisuwar nan da ake yi ba”.
Abu ta ce, “Ban da wannan zuwan ai na rahama ne, ka gama quruciya ka girma ka bar aikata abubuwa na ganganci ka yi ta istigfari kana neman gafarar Ubagiji bisa ayyuka na baya, ga rangwame da Ubanjiji ke yiwa xan Adam a lokacin da ya soma gajiyawa, matuqar shi xin ya rayu yana aikata alheri a lokacin quruciyarshi, alherin tsufa yana da yawa. Ba ga shi duk na sanku kun sanni ba, ga shi kuma ana tare”.
Mus’ab ya ce, “Haka ne Abu, Ubangiji dai yasa mu dace”.
Ta ce, “Ameen”.
Suka shiga gaisawa tana tambayarshi abin da ya dawo da shi bayan bai daxe da tafiya ba.
“Ka ji Abu, ke ce kika ce ina tafiya can ina daxewa ina mantawa daku, har kina cewa ina da wasu ‘yanmatan ne a can masu shagaltar dani? Ai shine na ce, to tunda abin ya zama haka bari in rinqa zuwa akai-kai don ki san ban da kowa a ko’ina ma ke kaxai ce ki sha kuruminki”.
Ta yi dariya ta ce, “Ka ji da shi”.
Wasu samari su biyu suka shigo suna riqe da kayansu na cin kasuwa dake nan kusa, suka gaisa da Abu cikin barkwancin nuna alamar suma jikokinta ne, sannan suka gai da Mus’ab a yanayin mutuntawa. Ita kuma ta tsaya tana yi mishi kwatancen iyayensu don ya gane asalinsu.
Suka sake gaisawa yana tambayarsu mutanen da ya sani a gidan nasu. Da za su tafi sai suka ce mata, “Mun biyo ne ko za ki yi saqon kaji da manshanu don cin kasuwar qauye zamu”.
Ta ce, “Saqo kai, sai dai yau zan huta bayar da kuxina tunda ga babban maigidan ya zo, dama can kuma a kuxin cefanen da yake ban ne nake cin kajin dasu”.
Mus’ab ya xan karkace ya jawo wata walet daga cikin aljihunshi ya ciro kuxi ya miqa musu, suka karva suka qirga dubu biyar ne ke hannunshi.
Ya ce, “Ku raba kai da xan’uwanka, wannan dubu biyar xin kuma ku sayowa Abu kaji da manshanu”.
Suka yi shiga godiya suna faxin “Ubangiji ya qara girma”.
Ya ce, “Ameen”.
Suka yi sallama suka tafi da alqawarin sai yamma za su dawo su kawo saqon.
Abu ta kalli Mus’ab cikin nutsuwa ta ce, “Wai me ya dawo da kai ne yanzu? Ni dai na san mun yi sallama da kai a kan sai wani watan ba ma wannan mai kamawa ba na gaba, ko kuwa dai aikinka ne ya kawo ka?”
Ya gyara zama sosai kafin ya zuba mata ido cikin nutsuwa ya ce, “Wurinki na zo, ai kinga ko gidanmu ban je ba shigowata garin nan kenan na tsaya qofar gidan nan”.
Ta ce, “To lafiya dai ko?”
Ya ce, “Lafiya qalau, kin dame ni kawai da maganar na tsufa ban yi aure ba”.
Ta harare shi ta ce, “Au damun ka na yi? Waxannan yaran da suka fita a haihuwar akuyoyi baka haifesu ba ko kuwa dame iyayensu suka girmeka?”
Mus’ab ya ce, “Abu kenan, babu halin mutum ya zo gidanki sai kin kashe mishi jiki da maganar tsufa, nifa a gidansu Halliru ne sa’ana”.
Ta yi maza ta ce, “Ahaf! Ba cinya ba kenan qafar baya, shi Halliru yanzu aka ce maka xanshi bai kusa waxannan xin ba?”
Ya yi maza ya ce, “To shi kenan Abu mu bar maganar na yarda ko a haihuwar mutane na haife su shi kenan ko magana ta qare? Sai a zauna lafiya”.
Ta yi dariya ta ce, “To ina jinka”.
Ya ce, “Aure nake so in nema nake kuma so ki wuce min gaba”.
Da sauri ta tava qirjinta tare da faxin “Ni?” Ba ta jira amsarshi ba ta ci gaba da faxin, “Allah ya kiyaye min ni Abu, wanda rashin sanin hali ya sani na yi dai na yi shi na kuma ji kunya dai-dai gwargwado, amma kan gaba ba zan sake shiga wani zancen neman aurenka ba.
In dai aka ce an baka, to zan zo in sanya maka lalle don duk tsufan nan naka in ka samu auren lalle zan sanya maka, ba zan barka haka ba sai in turo ‘yan qannen baya-bayanka su zo su taya ka zaman lallen.
Don ba za a samu sa’o’inka ba a garin nan da za su yi zaman lalle, don waxanda suka fara haihuwar da ‘ya’ya mata ma yanzu surukai ne dasu, to wa zan je in kira cikinsu ya zo ya tayaka zaman lalle, wannan abin kunya?
Mus’ab ya gyara zama ya ce, “Haba Abu, ai tamu dake ba ta vaci, in kika yi haka ai za ki sa na ayi mana dariya”.
Ta yi maza ta ce, “Ai gara ayi mana”.
Ya qara matsawa kusa da ita ya ce, “Da gaske nake yi”.
Ta ce, “Kullum haka kake yi, ka matsa na yi maka magana a kan ‘yar gidan Na’ibi aka ce ka fito zuwa hira ma ya gagareka, ka dawo ka ce min ba ta yi maka ba. Ka sake cewa ka ga ‘yar gidan Malam Nomau, nan ma ka dawo ka ce ba ta yi maka ba, saboda wai maganarta ba ta yi kamar ta mata ba, baka son mace mai yanayin maganarta”.
Ta galla mishi harara nuna alamar har lokacin abin da ya yin yana mata ciwo. Ta qara yin qwafa nuna alamar takaici.
“Ka fi son irin ‘yammatanku na birni masu lanqwasa da karairaya suna qirqirar muryoyin qarya, mu nan ai gaskiya da gaskiya ce”.
Ya yi murmushi kafin ya ce, “Ki yi haquri Abu, in kin tambayar min wannan ban aura ba kar ki sake shiga harkata?”
Ta galla mishi harara ta ce, “To wai ni dole sai na wuce maka gaba ne za ka yi neman aure? Can ‘yammatan ka na bariki ni ke wuce maka gaba kake neman su?”
Ya haxa fuska nuna alamar bai son irin waxannan kalaman da take yi mishi.
“Wai ni me yasa Abu kike yi min haka ne? Wa….”
Bai qarasa yin tambayar da ya yi nufin yin ba ta yi maza ta yi mishi tsawa.
“Kai tafi can”.
Nan take ta bishi da wata lalatacciyar harara kafin ta ja tsaki ta ce mishi, “Mene ne ban sani ba, ko kuma mene ne sabo a wurina lamarinka?’
Maimakon ya qara xaure fuska saboda yanda ta yi mishi, sai ya yi maza ya saki murmushi tare da faxin “Abu kenan ni kam ai ba zan yarda tamu dake ta yi tsami ba balle ta samu ta kai ga vaci, ni dai ki sani cewar ina son yarinya, na kuma daxe ina son nata, na yi ta zagaye-zagayen maganar ‘yammatan ne ko zan yi dace ki ce min to gata, me zai kai ni wani wuri? Sai ba ki yi min hakan ba, don haka na sake dawowa wurin naki ki yi min jagoranci zuwa neman auren nata”.
Kalamanshi suka sanya Abu juyowa gare shi ta kalle shi cikin nutsuwa ta tambaye shi, “Wace ce yarinyar?”
Ya xan sassauta murya kafin ya ce mata, “Aisha!”
Ta zuraa mishi ido nuna alamar nazari.
“Wacce a ciki? Ai ka san Aishan yawa ne dasu, kuma yawancinsu sa’anni ne, akwai ta gidan aminin shi Malam Kallamu, akwai….”
Ya katseta da cewa, “Kina kai wa da nisa Abu, ta gidanmu nake so”.
Ta qara kallon shi ta ce, “Wacce Aisha ce a gidanku?”
Cikin an gyajeran nazari ta sake tambayar, “Ko kuwa dai Saddiqa kake nufi?”
Ya ce, “Eh, ita nake so”.
Ta yi maza ta xaure fuska tare da faxin, “To baka ji irin abin naka ba, ba auren kke so ba, ga ‘yammata nan a dangi musamman ma ‘ya’yan qannen babanka, ko amininshi ba za ka je ka nema ba sai ka yi maganar wata Saddiqa? Kai ma ka san ba za a baka ita ba, ka fi kowa sanin cewar masu riqon Saddiqa ba za su baka ita ba. In ka ji shawarata ka je cikin gidanku wajen qannen babbanka ka zavi ‘yammata ka faxi ranar da kake so a sanya maka su a lalle.
Kai xan gata ma za ka je ka tsoma kanka a neman auren da zai vata maka rai, Saddiqan me kuma?” Ka je gidanku can cikin gida ga kakan ku nan da ya saura Malam Hazo, in ka ce mishi ‘yammata biyu kake so a sanya maka a lalle rana xaya kafin rana ita yau zan sa a kawo maka su har gidanka, ai kai xan dangi ne, nan Misau babu wanda bai san zuriyarkuy ba, ku xin kyawawa ne gaku da asali ga malanta.
Idan cikinku ka zavo matarka, kar ka yarda in ji ka zavi xaya haxa biyu kawai, don ka samu ka fanshe zaman tuzurantakan nan da ka yi ta yi shekara da shekaru babu aure”.
Mus’ab ya gyara zama cikin nutsuwa ya ce, “Abu Saddiqa nake so, ita ma tawa ce ba a fi ta zamowa kusa dani ba a xakin mahaifiryata na soma xanxanar ‘yancin rayuwa, ba kyau ne ya dame ni ba ita nake so, ki taimakeni ki gayawa Inna da Babana cewar ina son Aisha su taimake ni su bani izinin neman aurenta, tunda na samu labarin Kawuna ya ce ita Inna uwa ce, dama kuma uba ce, don haka al’amarin Aisha yana qarqashin hukuncinta ne ita da mijinta, kowa yake son Aisha yaje wajensu, to nima na zo wajen nasu don su bani izinin nema, ba wai ina nufin a bani bane, a’a’, nima zan shiga cikin manemanta ne nima, a yarda a ba ta damar da za ta yi zavi da kanta”.
Abu ta yi tsaki ta ce, “To ita uwarta za ta yarda ne? Ita wannan yarinyar da za ta yarda kam ai da komai ya kwana gidan sauqi”.
Ta xan yi shiru nuna alamar nazari kafin ta yi maza ta ce, “Kai ba fa zan tsoma baki ba tunda kai ma kafiya ce da kai ga taurin kai in an baka shawara baka xauka, in ka ce kana yi ko an ce ka bari ba za ka bari ba, in kuma ka ce baka yi, to juyin duniyar nan ma babu mai saka ka yi.
Don haka ni babu ruwana ku je ku yi ta yi, don in na ce zan biye ka to vacin rai kawai za ka jawo min. ta babanka ma duk bai sauqi ne, amma ita Innarka”. Ta xan gyaxa kai nuna alamar lamarin ba mai sauqi bane. Ta sake xago kai ta kalli Mus’ab.
“Tun bara fa ta ce min Sadisu za ta bai wa yarinyar nan, ta kuma sa Saddiqa ta sallami duk manemanta shi kaxai ne mai zuwa wurinta, yanzu to zan je in ce mata kar ta baiwa Sadisu auren ne? Tare suka yi wasan qasa da uwarshi, ita ce ma ta yi mata babbar qawa.
Kuma yanda ka bararraje xin nan shima in ya zo nan gidan haka yake zama ya bararraje muyi ta hira da shi, ko wannan kilishin da na kawo maka ai cikin wanda yake kawo min ne na xan tsakuro maka, anjima kaxan nan ma ana saukowa daga sallar Juma’a za ka ganshi ya zo gurina, to ya ya zan yi da shi? Cikinku wane ne ba nawa ba?’
Mus’ab ya sha mur ya ce, “To ai shi kenan dukkanmu naki ne”.
Yasa hannu ya xauki makullin motarshi zai fara tafiya, ta yi maza ta ce, “To baka ci kilishin naka ba?”
Ya ce, “A’a, ai kuma na fasa tunda na gane kilishin toshiyar bakin da ake kawo miki ne, sai ki yi ta ci ke kaxai”.
Ta yi murmushi ta ce, “To ai hirar ba ta isheni ba zo ka ji”.
“Ni ta ishen tunda na yi abin da ya kawo ni kin ce ba za ki taimake ni ba, to me zan ci gaba da yi a gidan naki in dai ba so kike in yi zaman jiran zuwan nashi ba”.
Abu ta yi dariya da qarfi ta ce, “Baka son gaskiya ne Mus’ab, ai na mara maka baya ma a neman auren Saddiqa in ce a baka a hana Sadisu, ai na ji kunya. Haba ai sai in kasa fita gari”.
Ya ce, “To na ji sai anjima zan zo ki yi abincin dare dani”.
Mus’ab ya isa qofar gidansu mahaifinshi yana alwalar tafiya sallar Juma’a, ya fito daga motarshi ya koma can gefe cikin nutsuwa ya tsuguna da nufin gaishe shi.
“Sannu da zuwa, sannu da zuwa”.
Mus’ab yana amsawa a yanayi na girmamawa, cikin ladabi ya ce mishi, “Ko zan shiga ciki ne Inna ta san na zo sai in fito mu tafi masallacin tare?”
Ya yi murmushi ya ce, “Yi sauri ka yi hakan, amma ai mun riga mun ji zuwan ka wurin waxannan yaran da suka zo su karvi kuxin manshanu wurin Habiba”.
Mus’ab ya ce, “To muje kawai Baba in mun dawo sai in shiga”.
Bayan saukowa daga sallar Juma’a, tunda Mus’ab ya shiga ya gai da mahaifiyarshi ya fito yana wurin babanshi Malam Abdullahi suna hirarsu mai daxi irin ta xa da mahaifi.
Malam Abdullahi yana zaune kan kujera ya yin da shi kuma Mus’ab xin yake qasa suna hirar a haka. Kafin zuwa can ya ce mishi, “Yanzu nan kai zamanka a haka ya yi maka dai-dai? A ce mutum ba zai yiwa kanshi faxa ba? ‘Ya’yam qannenka mata ne fa yanzu suka shigo nan suka gaisheka don sun ji zuwan ka, ko wannan bai isheka ka san baka da sauran quruciya a tare da kai ba?’
Ya qara sunkuyar da kanshi qasa cikin ladabi ya ce mishi, “Da yardar Ubangiji wannan karon zan yi, kusan ma abin da ya kawoni garin kenan a yanzu, na ma riga na je na yiwa Abu bayani”.
Mahaifin nashi ya zuba mishi ido yana kallon shi.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login