Showing 15001 words to 18000 words out of 130495 words
Chapter 6 - Wa Yasan Gobe Compelet Book by Safiya Abdullahi musa huguma
ya karade da waqoqin da irin nasu mamman shata sani sabulu dan qwairo dan indo audu wazirin dan duna da sauransu suma iyaye aka tuno musu da da tunda dama ranar ta iyaye ce,
Washegarin ranar sukayi kuma wuni a gida,wata Washegarin kuma ta zamto ranar daurin aure,daurin auren da ya tara jama'a na ban mamaki garin ranar unguwar ba masaka tsinke,jama'a ne tako ina na nan qasar dama maqwaftan qasashe har da na qetare
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
Misalin takwas na daren ranar daurin auren fadila da farida na durqushe gaban umminsu sanye cikin atamfa super England lemon grean ce da pink sai adon fari dinkin riga da zani an nannade masu jikinsu da wata danyar lafaya fara tas mai dige digen pink a jiki,dan kunne da sarqa sai banguls duk na azurfa ne ,babu abinda ke tashi jikinsu sai wani rantsatstsan qamshin turaren humra yar gasken ta bare barin usuli
Da fari ummi kasa magana tayi saboda tausayi da qaunar yaran nata sai jimamin rabuwa da zatayi da su,daga baya ta daurw ta musu yar tunatarwa saboda ita damacan koda yaushe mai dora yayanta ce kan tarbiyyar zaman gidan aure ce,ta kammala nasihar tata da addu'a da fatan alkhairi a garesu,umma A'i yayar ummi ta leqo tana cewa su fito angwaye nata jira fa,wani kukan suka sake saki suka ruqunqume ummin suna neman yafiyarta,tace ta yafemusu burinta kawai su zauna da mazajanasu lafiya kada taji kada ta gani shine farincikinta,ana riqe dasu amma suna waiwayowa suna kuka idanunsu a kanta kamar zasu qwace su dawo,itama sai ta kasa jurewa suka sata qwalla duk sai suka karyar da zuciyar kowa sai muhammad shima ya dauki masa kukan da ya bawa mutane tausayi kasa zama yayi yabi yan uwan nasa yana ta kuka kowa ya tausaya mai saboda tunda ya taso suna tare da su ya saba su ya saba gani gashi yau an dauke masa su duka biyun
Cikin wata arniyar mota qirar sail akace a shiga da fadila suna qoqarin sa farida a dayar ta riqeta gam tace bata yarda ba saidai a hadasu a mota daya,ganin da gaske take yasa suka sasu a mota gudan,lokaci guda motocin suka tashi suka kuma jeru reras bisa titi tamkar motocin rakiyar shugaban qasa,duk da cewar darene amma duk inda suka bi sai sunja hankalin mutane saboda kyawun motocin,kai tsaye yahaya gusau suka fara nufa inda anan gidan farida yake,a nutse suke shiga gidan saboda ba yara ko daya sai manya da yammata tun la'asar aka kai yara suka gama gani aka dawo da su gida tsarin gidan farida gwanin sha'awa ya burge jama'a da dama atsare ginin yake kana kallonsa kasan sai da aka sa nutsuwa aka fidda masa fasali
Sai da suka ajiyeta a bedroom dinta su umman abuja(itama qanwar abba ce)suka sata tayi addu'o'i sannan sukayi haramar tafiya,fadila na nanuqe da farida har yanzu kukan suke sunqi sakin juna harsai da umma a'i tq fusata dama akwai lafiyar fada ta hau sababi tace"ku kunga bamason isknci,kanku aka fara aure ai kowa da haka ya sabatun dazun ake fama da ku ki fito kin noqe to kada ki sake na qaraso dakinann baki fito mun tafi ba"suka sake rushewa da kuka 😩ganin lallai dai rabuwar za suyi,mama sadiya(abokiyar wasan abbansu ce)tazo ta kama fadilan tana rarrashinta tafito da ita tana jiyo kukan faridan kamar yadda itama take jiyo nata
Cikin nasarawa G.R.A motocin suka kutsa qofar wani katafaren gida suka tsaya,kewaye yake da dogayen kuma qawatattun katangu da fitulu masu tsananin kyau makeken get wanda saboda tsananin girmansa sai kayi tsammanin qofar shiga garice suka tsaya,duk yawan motocin sai da kyakkyawar harabar gidan ta lamushe su,sai ma suka tashi yan tsurut harabar wadace ta take da haske tamkar rana sai ka rantse da Allah rana ce ba dare ba
"Kai jama'a yanzu kamar ba za'a mutu ba?,wannan gidan dai.....inda ni kadai na shigo wlh ihu zan sak na ce gidan yankan kai nazo,kamar ba mutuwa a duniya?"kakarsu fadila hajja gana mahaifiyar abbansu ke wannan santin,su kam me za suyi idan ba dariya ba😂,sai da suka nufi sashen fadilan masu yaba kyau da tsaruwar gidan suka dadu,ginine wanda kaf garin kano baifi ka qirga masu irinsa da hannu ba,ginin part hudu ne sai boys quarters makeken lambu swimming pool gun wasanni kala kala,basketball table tennis,football boxing,tokwand da sauransu baya ga haraba biyu da gidan ke dauke da shi harabar farko dakin mai gadi da parking space take dauke da shi,sun dan tarad da jama'a a gidan acan part din samira suna jira a kawota,ba abinda ke tashi sai kida da yan uwanta suka ware mai barazanar fasa kunnuwa ganin haka hajja gana ta hana su koda guda suyi ta shiga gidanta da addu'o'i bakinta
"🤔wai ni Allah wannan gida naki fadila idan baka da qarfin imani zai iya saka ka manta Allah "gaba dayasai da hajja gana ta sake sa kowa dariya a gun😂 duk da suma sun lalace ne gun kallon tsaruwar gurin nata falone two in one wanda kan ka shigo main falo akwai varender a farkon sashin sannan ka tadda falon,dukka falukan sun qawatu da kayan qyale qyale na falo babba da qaramim falon kowanne ansa masa abinda falo ke buqata ba abinda aka rage masa,acikin main falon anan daga hannun damanka matattakala ce masu fadi guda hudu zaka taka ka haye gun dining wanda ke daume da wasu hadaddun labulaye masu kacar kacar anan qofar kitchen s dinta take wanda duk wayewarka sai quyancinka ya fito,gaban gun dainin kadan wata yar qoface mai kyau ta glass wadda ke dauke da corridor shimfide da lallausan carfet da hadaddun labulaye dakunan bacci ne guda uku daya furniture ne yan Saudi pink da purple daya dakin kuma yan italia ne ash da pinch yayin da daya dakin kuma aka malaleshi da carfet da manyan tuntuna aka zagayeshi da labulaye masu shegen kyau aka rarrataye mata kayan kaba da kumbuna tamkar jeran qauye sai wani dan gado irin na qauye mai rumfa amma wannan an zamanantar da shi kowanne daki da toilet dinsa sai public toilet dake varender da kuma wani a falo,daga kitchen akwai qofa da zaka zagaua bayan part dinka(ventilation)wanda akayi dan qaramin lambu da wata rumfar bunu sai yar qaramar qorama da aka qirqira da doguwar kujera ta siminti qwaya daya,a falo aka ajiyeta,ido kam ya raja'a da kallom kyawun gidan,sanyi a c da qamshin freshener ya game ko ina ga qamshin sabunta,gidan ya kaure da hayaniyar yammata dake ta zuba santi da yiwa kansu fatan samun koda makamancin wannan gidan ne,
Wata hayaniya da suka ji ta kunno kai gidan ya saka su yin shiru suna sauraron daga ina take?,guda ce da aka cakudata da kirari iri iri hafe da habaice habaice"taka lpy uwar gida sarautar mata,isaahshiyar mace a gidan aliyu maitama ,eh anqi Allah yaso,qaryar mahassada ba zasu iya da ke ba wallahi sama ta yiwa yaro nisa saidai ya tada kai yayi kallo,an buga da ke an barki wlh yarinya ko yar sankin santanbul ce kinfi qarfin ta kara da ke saidai tayi iya nata salon ta haqura,"
hakane ya tabbatar musu masu rakiyar samira ne mama sadiya suka hana kowa fita har suka qaraci ahewarau da shegantakarsu suka shige da ita,zuwa wani lokaci kuma sautin sabon kida na kujerar tsakar gida ya karade gidan tamkar wani club,Allah ya kayuta abinda suka ce kenan
Qarfe tara aka soma kwashe yammatan ana maida su kafin tara da rabi gidanta babu kowa,kadaici ya kama fadila,tsoro ya cikata,bata jin sautin komai sai hayaniya da kidan yan uwan samirah,zuciyarta tayi rauni sosai tunanin irin zaman da zatayi a gidan take,Aliyunta bai sonta,kishiyarta kuwa salon da ka rakota da ahi ya tabbatqr mata ba zaman lafiya tazo ayi da ita ba,hawaye ya balle mata😭 zuciyarta kaar tayi tsalle ta fito saboda zullumi da radadin da take mata
Horn din motoci ya sake cika gidan,ta daga kanta ta kalli agogon bangon dake falon sha daya na dare ya nuna mata🕚 ba shakka angone da abokansa suka shigo zuciyarta ke gaya mata haka,sannu taji hayaniyar jama'ar na raguwa hakan ya tabbatar mata ana debe su ne tafiya suke,ga tarin mamakinta sai ta jiyo muryar samira na cewa"ku gaida gida na gode Allah ya huta gajiya,ina jiranku gobe da safe,kuma wlh kada ku yarda sai sun vika muku kudin siyan bakin"fadila ta jinjina kai tana cewa cikin zuciyarta lallai ba shakka kowane tsuntsu kukan gidansu yake
Cikin qanqanin lokaci gidan ya sake zama tsit,ba komai cikinsa sai hasken fitilu daya gauraye da kukan tsintsaye da kuma gyare jefi jefi,haka ya sake assasa tsoron dake zuciyar fadila ta runtse idanunta gam😣tana ambaton sunayan Allah hadi da addu'o'in tsari,sannu a hankali taji idanunta da jikinta sun fara nauyi ,gajiyar kwana da kwanaki suka fara sauko mata,taji bata da buqatar komai illa kashingida,ta zame ta dogara gwiwar hannunta a hannun kujerar,tsananin gajiya yasa bacci har ya dauketa bata sani ba💤
ASUBA TA GARI AMARYAR ALY😊😊
Mrs muhammad bello ce
📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
[10/16, 12:29 PM] 💍🍬🛍Salma🛍🍬💍: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
Wa yasan gobe?
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
Written by safiyya Abdullahi musa huguma
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
▶1⃣1⃣
Firgigit ta farka kamar an tasheta,ya zame mata jiki tun a gida assalatun farko take tashi tayi yan nafilfilu kafin assalatu na biyu daga nan idan ta idar tayi baccin mintuna idan tana da lacture ta shiga kitchen ta shirya breakfast,yauma gajiyar bata hanata tashin ba saidai ta sabawa lkcn da ta saba tashi sai kiran a kiran sallah na biyu ta tashi,cikin kasala ta miqe don har yanzu tanajin nauyin jikinta tayi miqa hadi da salati idanunta suka kai kan wata farar leda babba mai dan duhu guda biyu tsoro ya darsu a zuciyarta ta katse miqar a iya saninta sanda zata kwanta babu ledar a gun to ya akai ta samu?cikin sanda ta isa inda ledar take kamar wadda akace za'a kama,saidai tunkan ta bude ledar qamshin turarensa ya ziyarci hancinta,hakanne ya bata amsar tambayarta lallai aliyu shi ya shigo da ledar tayi mamakin yadda har ya shigo ya fita bata sani ba,
Ta bude ledar gasashshiyar kaza ce wadda akai wrapping dinta guda uku sai ice cream da ya gama narkewa saboda an ciroshi daga ma'ajiyarsa sai fresh milk manyan roba har uku,sai yoghurt shima roba uku tayi ajiuar zuciya ta mayar da kayan,kasala ta sake kamata taja da baya ta koma bisa kujerar ta zauna tana aheqar daddadan turarensa tamkar yanzu yake a gun,ta shiga hasashen fuskan aliyun a cikin wadannan awoyin da yake angon mutum biyu,kishi ya taba zuciyarta,tafan bata waau lukuta a zaune ta kasa tabuka komai sannan ta miqe ta lalubi corridor din nan ta zabi bedroom daya ta shiga,tana alwala tana qarewa tsaruwar toilet din kallo,tabbas dole hajja gana tace kamar ba za'a mutu ba,bayan ta idar sa sallar ma tana lazumi dakin taci gaba da bi da kallo tana yaba irin namijin qoqari da iyayenta da yayansu Ahmad suka yi,bata kammala ba wani daddan bacci ya rinjayi idanunta nan bisa dardumar sallarta
Hasken rana da ya soma shigowa ta window yana taba fuskarta shi ya farkar da ita,da addu'ar tashi daga bacci ta miqe a bakinta ta dubi agogon dake ajjiye kan bedside ya nuna mata goma da minti sha biyar na safe batayi mamakin awanni data shafe ba tana baccin ba,toilet ta shiga ta kunna water heater dake manne a kusurwar bandakin cikin mintina qalilan ruwan ya tafasa ta kunna shower ta daidaita zafinsu ta shige kwamin wankan🛀🏼,tsaf ta shirya cikin atamfa mai zanan manyan ganye mai kalolin pink da ja sai light blue,dinkin da ita atamfar kanta tayi.masifar karabarta duk da ba wani make up tayi ba hoda ce kawai sai man lebe da kwalli,dinkin ya lafe mata sai kayi tsammanin fitted gown ce daurinta yayi das wanda ya awa gashinta damar kwanciya bisa dokin wuyanta
Ta fito falo ta kwashe siyayyar jiya ta kaisu kitchen,tsayawa tayi kallon kitchen din tana jinjina kai da dan guntun murmushi akan fuskarta😊ba shakka ummi tasan tsarinta game da kitchen kuma ta san maitar kitchen irin tata don haka ta cika mata ahi da dukkan wani nau'i na kayan amfanin kitchen babu ce kawai babu,abun nema ya samu nan ta bata lokaci gun tsara da shirya kitchen dinta yadda take muradi,tana tsaka da aikin ta jiyo ringing din wayarta wadda ita sam ma ta mance da ita ta fito galin tana laluben inda take,tsakiyar filalluka ta hangota tasa hannu ta dahota tana duba mai kiran garida ta gani tayi yar dariya sannan ya daga hadi da sallama,muryar farida a qasa ta amsa fadila tace lafiyanki qalau kuwa?"ta masa mata da "hmmmm,ai dole ki ce min lpy qalau tunda ke naji miryarki garau da ke "fadila da bata fuskanceta ba tace"kamar yaya? Wani abu ya faru ne a gida?"farida ta sake ajiyar zuciya tace"mubarak bashi da tausayi Allah sister fadila jiya kada kiso kiga rashin imanin da ya gwadan,anty hafiza tasan haka amma ta dinga dirka mana magani"fadila data dau haske a zancan nata tace"to Allah ya kyauta""wlh kin ga na kasa tashi sister"ta fada cikim karyewar murya,wani yarrr fadila taji tausayinta da tsoro suka kamata tace"ai ke likita ce saiki kula da kanki Allah ya bada lpy"tace"amin na gode ina ya Aliyu"
"Baya nan"
Cikin sauri farida tace "kada dai ace samira kika miqawa uwargidan bayan ke aka fara daurawa aure kuma ke aka fara kaiwa?"
Fadila cikin son abar zancan tace"ban sani ba 'yar jarida kije ki fara jinyar kanki tukun idan kin warke sai kiji amsa"ta katse wayar,jikinta yayi sanyi sosai a salube ta zauna agefan kujerar,ashe har faahin matsayinta ma sai da aka mata?ita idan banda yanzun ma bata san itace gaba da samiran ba tasa hannayanta biyu ta dafe kanta cikin wani irin yanayi da ta kasa tantance ame take?,ganin ba mafita yasa ta koma kitchen taci gana da gyare gyarenta zuciyarta cike fak da tunani,
Da azahar baqi suka soma zuwa mata sallama din komawa gidajensu yan maiduguri ne da yan gwambe,zuwa qarfe uku suka tafi sai su rumasa'u sa'adah minah rahama da hafsah duk cousins dinta ne rumaisa tace'?"wai ke ya ne?"fadila ta kalleta da alamun tambaya ,sa'adah ta karbi zancan "gidan farida muka fara zuwa tana can kwance mubarak nata hidima amma ke gaki dungur gur a zaune"fadila ta juya idanunta🙄tace"lallai yarannan"da yake ta basu tazarar yan kwanaki ta Dora"kuce kawai uawon sa'ido yau kuka fito ko"dukkansu suka sheqe da dariya😄,suka ce"to ai gwara kafin mu wuce muga lamira sun daidaita " tace"to Allah ya qara muku himmar sa'ido"ta fada tana shirin shigewa toilet rahama tace"to ai sai ki kira mana angon mana mu gani ko shi aka dorawa jinyar"ta jiyo ta harareta tace"baki isa ba kuma kwa qaraci zaman gulmarku ku tattara yammatan qafafunku ku koma inda kuka fito"suka sake aheqe mata da dariya😂,ita kuwa ta shige toilet din tana fadi a ranta"koni bancin arziqin samun ganinshi ba rabonku da ganinsa tun a dinner to nima hakan take"
La'asar gidan ba kowa duk sun yoye sun mata yan gyare gyaren da suka ga ya dace na game da jere da yan goge goge sukayi sallama cike da kewa tabi kowaccensu da dan dasheshan turare,turaren wuta ta zuba a bin turare mai amfani da wutar lantarki ta daidaita sanyin a.c falon yayi wani dadi qamshi da sanyi auka hafe guri guda,turare na musamman da hajja gana ta musu da kanta kuma ya tsumu sosai don ya jima a ajjiye ta musu tanadinsa,don haka qamshin har farfajiyar gidan,wajajen biyar ta sake gyara fuskarta ta feshe jikinta da turarurruka don dama babdaga baya ba fadila gun qamshi ta gabatar da la'asar da ta kufce mata,tana linke sallayarta tana ci gaba da jiyo hayaniyar dangin samira don tun farkawarta da safe wajan goma da rabi ta fara jin zuwansu,ta gama ta koma falo ta kama mbc bollywood dan ta samu ta debe mata kewa,kafin takai ga zama kan kujerar taji ana knocking din qofarta,ta nufi qofar tana cewa "waye?"saidai shiru ba'a amsa ba,don haka tasa hannu ta bude idanunta a waje don ganin waye,a subhanallah,ta fadi a zuciyarta saida bugun zuciyarta 💓ya dadu sosai fiye da qima,Aliyu ne tsaye a bakin qofar yana sanye cikin wani lallausan farin yadi qal(tissue),yadin nada shara shara don hakka hatta farar vest dinsa kana iya hangota,dinkin yarbawa aka masa(boda)iya gwiwa da dogon wando yana sanye da baqin takalmi idanunsa saye da farin gilashinsa na qa'ida kansa ba hula sai kwantacciyar sumarsa kamar mai sa mata relaxer saidai natural ce haka sumarsa take,qamshin turarensa ke dukan fuskarta,tsintar muryarsa tayi yana cewa"su bar maka a nan ka dinga daukowa kana ahigowa da su"hakan yasa ta tabbatar bashi kadai bane,tayi niyyar yin sauri ta koma ciki don ba hijabi a jikinta saidai ta kasa moysa qafafunta,sai jan jiki da tayi ta rakube a bayan qofa,nasiru n yake shigowa da kayan abinci duk wani dangin abunci da nasha na har ya kammala shigewa da su tsaf aliyi na tsaye tsakiyar falon hannayansa zube cikin aljihunsa yana facing qofar store yayin da ya juyawa qofar shigowa baya,ta haka fadila ta morewa kallonsa ba tare da ya sani ba,ingarman namiji ne wanda siffar qarfi ta bayyana atare da shi bayansa kawai ka kalla zaka fassara hakan,nasiru ya fito yana kade hannayansa ya dan russauna yace"yallabai na gama"yana qoqarin zaro kudi a aljihunsa yace"yauwa ya miqa masa kudin yace"raguna zaka samo guda biyu ka biyaau su gyara komai su wanke acan ka duba motar zuwa kasuwa ka tafi a ita""to yallabai"ya fada yana shirin wucewa"nasir"aliyu ya kirashi a aladabce ya juyo yana amsawa"ka biya ta gidan gona su gyara kaji ka taho da su""an gama sir"cewar nasiru ya fice da sauri
Ya juyo yayo tattaki har zuwa bakin qofa,fadila ta saci kallonsa sai taga hankalinsa na waje,cikin sanyin jiki da sanyin mutya tace masa"ina wuni"yqdan kalli sashin da take ya kauda kai,cikin wata dakakkiyar murya yace"kada ki qara zama haka bayan kin san cewa ba ni kadai bane,in kunne yaji......"tace"to"har yasa qafarsa awaje yadan dawo da baya ba tare da ya dubeta ba yave"qarfe takwas ki sameni a gefena"to ta sake cewa,"shikenan babu abinda kike da buqata?"ya fada yana duba agogon hannunsa,"babu"tace
"Ok ki duba saman kujerarki"kawai yace yasa kai ya qarasa barin sashin aransa yana cewa"ta wani labe sai kace wadda ake kora"
Hannayansa harde bisa qirjinsa yake bin harabar gidan da kallo ,ko ta ina dangin samirah ne kamar