Showing 27001 words to 30000 words out of 130495 words

Chapter 10 - Wa Yasan Gobe Compelet Book by Safiya Abdullahi musa huguma

din


Wash! Inji farida bayan ta zauna fadila ta kalleta tace kin canza sister fa sosai kinga qibar da kika fara yi?farida tayi murmushi tace ke dai bari ya fadila ina tsammanin ciki ne fa?,fuskarta cike da fara'a 😄tace ke dan Allah,tace wlh da jibi ko gobe mubarak ya matsa sai naje an min test wai kada na jawo masa asara cikin rashin sani ni sai naga kamar ba shi ba,kasala kawai fa nake da yawan bacci,fadila tace,a'ah nima fa ina bayan mubarak sister kije a dubakin meye amfanin zaman haka,kina likita ai kinfi kowa sanin alfanun abin,tace insha Allahu gobe zamu je


Farida ta janyo jakarta ta bude ta miqawa fadila takardunta,cikin zumudi ta buda tana duba result din ba abinda bakinta ke fada sai alhamdulillah,domin kuwa yayi kyau fiye da yadda ta tsammata cikin farinciki tace da farida"burina na gaba farida inga na soma aikin media shine burina tun ina qarama"murmushi ta sakar mata tace"kwantar da hankalinki ya ahmad yana can yana miki wannan aikin don kuwa freedom da express tuni sun karbi takardunki jira yake kawai yaji daga garesu,wani farincikin da qaunar yan uwanta ya sake kamata
Tana toilet tana wanka ta bar farida a afalo tana kallin arewa 24 suna haska maimaicin shirin boyle bitmesin wato kyautata rayuwa da yake jiya tace tayi missing bacci ya dauketa bata kalla ba,ta jiyo hayaniya sama sama ta tsinci dai muryar anty hauwa din haka a gurguje ta gama tana fitowa ta shirya kanta cikin shigar doguwar rigace ta shadda wadda aka mata paint work mai tasadar orange ce akayi mata kwalliyar light blue,body spary kawai ta fesa ta daura dankwalinta ta debo magungunanta wadanda zata sha da rana ta fito falon,rabi'ah ce da sumayya da anty hauwa,cikin fara'a suka gaisa suka mata sannu da jiki"tace ai na samu sauqi ina momy da iftihal mutuniyata,anty hauwa tace suna gida gurin momyn nace ne ba da wanda zanzo duk har su kausar suna gunta muhammad ma tunda ba nono yake sha ba acan na barshi don suna zamu wuce dqga nan wata maqwafciyata ce ta haihu to kuma da yake haihuwar ta danzo da matsala a gidan su take acqn za suyi taron,tace eh Allah ya qara mata lpy,amin inji anty hauwa
Nan suka shiga hira abinsu minti talatin suka miqe suna shirin tafiya fadila dake ta qoqarin zuba musu abincin tace anty ga abinci don Allah ku tsaya kuci,anty hauwa tace bayan lemo da cake da kika cika mana ciki da shi alhamdulillah wlh,rabi'ah tace nikam anti fa na fasa rakiyar nan gidan sunan kuce da maman hidaya ina mata barka na taho anjima farida ta saukeni a hanya,sumayya tace"dama na sani anti ba rakaki zata yi ba ina ji tana cewa yau ana rana da yawa nasan dama daga nan gidan ba inda zata dara"aishikenan muje mu gaisa da samirah sai.mu wuce,inji anty hauwa,sumayya ta coge😒sannan tace a'ah anty nikam zan jiraki cikin mota ki shiga ki fito tayi saurin yin gaba damma kafa antin ta tsayar da ita,fadila tace "baki kyauta ba sumayya idan kika wuce baki gaidata ba"rabi'ah dake zaune tace wlh anty ko nice ba zan je ba,farida dake ta faman cin abincinta abunta tace qyalesu sister mai daki shi yawan inda yake masa yoyo✋🏻,ai kuwa dai sister farida sai.kaje kayi ta bugu taqi budewa gashi fa kana kallo ta tana kalloka qiri qiri,bayan kuma ta bude sai tayi.bake bake a bakin qofa ta tsare ka da ido tana wani ce maka meye?kamar wanda kazo maula gurinta,duk suka kwashe da diyar yadda rabi'ah ta gwada yadda samiran keyi banda fadila da ta dan murmusa gami da girgiza kai tana mamakin halayya irinta samirah
Biyar da rabi farida ta dauki rabi'ah suka tafi suma sashen sai ya dawo sai ita kadai ta so ta yiwa farida zancan dawowar maman iftihal sai kuma taga mai hakan zai dadeta da shi iyaka ta taya ta jimami sai shawara wadda a yanzu ita ma bawa kanta da kanta take,tunanim data fara yin zurfi a ciki ne yasa barin kanta ya soma ciwo bata yada hakan yayi zurfi ba ta tashi ta jona home theatre dinta ta saka cd plate na karatu ya karade falon


Takwas da mu
mintina na dare nasiru ya turo hancin motar ogan nasa cikin gidan,ya samu parking space ya daidaita tsayuwar motar sanna ya kasheta,a hanzarce ya fito ya budewa aliyu shima ya fito sannan ya miqa masa keys din motar yana fadin gashi sir ya amsa yana cewa debo min files din nan na sit din gaba,ya debosu ya bashi sukayi sallama aliyu ya sallameshi,hankalinsa gaba daya ya yi gaba burinsa kawai ya isa sashen nasa ya watsa ruwa a jikinsa ya samu ya kwanta ya huta,ya soma tafiya idanunsa suka kai kan sashen nata babu wadatar haske kamar bangaren samira dake tarwai da haske harda qarar abin kida ya dauke kai ya shige


Yana fitowa daga toilet ya zabi doguwar riga jallabiya fara sol.mai yankakken hannu ya saka ya feshe jikinsa da turarukan baccinsa masu sassanyan qamshi kan sofa ya fada ya miqe qafafunsa sannan ya hardesu ya kansa na kallon sama yasa daya hannun nasa ya shafi cikin sa,yunwa yakeji amma ya rasa inda za shi ya samu abincin da zai gamsar da shi,mutum ne shi.mai tsan tsami ba ko ina yake iya saki jiki ya ci abinscinsu ba sai ya yarda da ingancin tsaftarka hakan ne yasa ya tsani masu aiki hakan yasa tun yana gida ya yi ruwa yayi tsaki ya hana mominsa daukar masu aiki yace meye amfani su sumayya duk da suma bai yarda ko kadan yaci girkinsu sai na mominsa


Ya tashi ya qarasa fridge ya bude ya dauko yoghurt na l&z ya hado da fura ya samu cup ya dama ya sha ,ya sake tashi ya maida cup din kitchen sannan ya qarasa window dinsa yana bude glass din don ya bawa iska daman shigowa duk da iskar a.c da ta mamaye dakin kasancewar mutum ne shi maison natural air,idonsa ya sake fadawa kan bangaren nata duk da yaune ya shigo bashi da niyyar ganin kowa bacci yakeso ya samu isashshe don haka har wayoyinshi ya kashe su gaba daya
Ya saki labulen yana ajiyar zuciya saboda tunawa da yayi haqqine a kansa ya kula da lafiyarta don rabonsa da ita tun jiya da ya batta da magungunan da ya siyo mata ,ya zari keys dinsa ya zura slippers dinsa ya fice


🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
▶1⃣9⃣


Tana kwance a miqe sambal bisa kujera three sitter don tunda tayi sallar isha'i bata tashi ba agun falon tsit yake ba komai sai sanyin na'urar sanyaya daki wanda ta gauraye da qamshin freshner mai dadi idanunta na lumshe ne tamkar mai bacci saidai ba bacci take ba tayi nisa ne a wata duniya mai wuyar fassarawa duk da ciwon da kan yake mata das das das amma hakan bai dameta baqarar bude qofan falon da qamshim mayen turarensa dake rataye da zuciyarta shi ya dawo da ita,ta bude manayan idanunta akansa yayin da shi kuma ke qoqarin tura qofar tayi namijin qoqarin tashi ta zauna kanta na sunkuye a qasa don ba zata iya jurewa kallonsa ba,hannayensa ya goye a bayansa ya qaraso falin yana kallonta da qayatattun idanunsa ya lura kamar ta dan rame duk da ba sanin ainihin kamanninta ya yi ba"ina yini"tace still kanta na qasa,cike da qasaitarsa da izzarsa ya dauke kai ya maida mata gaisuwarta da tambayar jikinta,da sauqi ta fada cikin sassanyar muryarta data sanya yaji wani dan yam ajikinsa


Bata zata ba bata kuma tsammata ba sai jinsa tayi zaune kan kunerar da take kai.kuma dab da ita ya sanya bayan hannunsa a wuyanta da niyyar jin temperatures din jikinta ba komai aransa,sai dai baisan illar da ya sake yiwa fadila ba a zuciya da gangar jikinta ba,kasala mai tsanani tashi guda da kuma wani irin shauqi taji ya saukar mata numfashinta ya tsaya cak na wucin gadi,sam bai kulaa ba yace"still jikinki da ragowar dumi ya kamata ki warke kafin isowar abokiyar zamanku right?ya qare maganar da sigar tambaya,ya.miqe yana cewa babu abinda kike buqata,tamkar ta ce masa"kai nake buqata aliyyu ka qarashe awoyin wannan daren naka tare da ni,maimakon haka sai ta sake gyada masa kai,yace " alright gudnyt"ta bishi da kallo idanunta fal cike da qaunarsa da kewarsa har ya fice daga part din nata ya rufe mata part din,ta koma da baya ta jingina jikinta da kujerar hadi da runtse idanunta hawayen dake maqale a idonta suka gangaro mata wani radadi da zugi zuciyarta ke mata lallai kishi masifa ne


Cikin daren bacci gagararta yayi juyi take kawai akan makeken gadonta cike da sha'awar aliyu tunda take bata taba jin makamanciyar sha'awa arayuwarta irin wannan ba
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
Sannu a hankali ta miqa dukkan lamuranta ga Allah cikin ikon sa kuwa ta fara samun sauqinsu saidai fa har yanzu babu sauqi ta bangaren soyayyar Aliyu dake maqare cikin zuciya ,cikin lokacin sam ta daina bari idanunta suga aliyyu duk da tarin zugi da zullo da zuciyar keyi na son ganin nasa amma ta danneta


Cikin lokacin aikinta ya samu freedom da express din duk suka buqaci yin aiki tare da ita,ya ahmad dinne ya kawo.mata da kansa bayan ya sanar da aliyu da kansa ya kuma amince mata da fara aikin nata,tayi murna tayi tsallae tun a gaban ya ahmad din ya sha godiya sosai har da qwallar farinciki saboda yadda take masifar son aikin jarida shikam dariya yayi yace Allah zata godewa,bayan tafiyarsa ta kira farida dake fama da laulayi suka sha murnarsu tare,nan fa ta zauna ta soma tsarawa kanta yadda zata tafi da rayuwar aikinta
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜


Cikin satin Aliyu ya shirya musu fita wadda ta farko ce agun fadila don bata taba fita ba wani gu da sunan unguwa ba bayan shopping da suke zuwa duka qarshen wata za suje ne gaida hajiyarsa


Tun rana fada ke zumudin fitar tana tunanin mai zata kaiwa momin,akwatunan lefenta dake shaqare da kaya wadanda kamar ba'a taba amfani da komai a ciki ba ta bude ta zabi turarurruka designers guda uku ta warewa abba,ta duba akwatinta da ta adana gift da ta samu na biki ta cirarwa momin atamfofi super Holland da England guda biyu,da kanta ta aiki yaron dake musu gyaran flowers ya samo mata kilishi mai kyau da zuma


Tun magariba ta yi wanka ta shirya kanta cikin atamfa dinkin riga da zani kamar light grean da milk sai ratsin baqi dinkin ya mata cas kamar a jikinta aka qirqireshi yari da sarqa ta saka ma dutse masu kalan milk sai farin agogon hannu tq zuba awarwaro mai 24 farare takalmi da jaka milk sai laffaya data nannade jikinta da ita milk ce mai adon baqi ta debi tsarabarta ta dawo falo ta kunna arewa 24 tana kallon shirin matasa at 360,tayi wani masifar kyau ta fito sosai a babarbariyar ta


Ya qarashe karin hular sa yana daidaita ta a kansa shaddace fara qal a jikinsa dinkin tazarce sai walwali take ta sake fidda sirrin kyawunsa mutum ne shi ma'abocin iya ado ta wannan fannin kam ko mace haka ta ganshi,komai nashi fari ya sanya hatta da agogo,ya sanya glass dinsa sanna fesa turarensa ya rufe sashen


🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺


▶2⃣0⃣


Bangaren samirah ya nufa wanda sai ta kama dole yake shigar sa,ga mamakinsa aai ya taddata sirshan tana zaune abinta zaninta da rigarta daban daban kanta da ta tsefe shi yana tsaitsaye kamar tabarya😜dama ita ba wani tsawon gashi gareta ba sai qarfi da gashin yake da shi,ba abinda falon keyi saiqarnin kifi sardine ta tara gwangwanayen a gabanta ua daurw yadda qarnin ke bugar hancinsa yana tayar masa da zuciya cikin bacin rai yace mata zaman me kikeyi baki shirya ba tun dazun?ta dan yatsina fuska tace qawatace wlh ta kiarani a waya ta kwasheni da jira ya gyara tsaiwarsa cike da qosawa da azababben qarnin kifin yace mata is ok sai ki nemi wanda zaku tafi tare kinsan bana jira yana kaiwa nan ya sanya kai zai fice yana jan tsaki cike da takaici ,ta yi saurin shan gabansa tana cewa haba sweet kayi haquri mana pls ka bani minti uku kaya kawai zan canza,ya kauce ya fice yana cewa wataqila idan kinyi sauri kin tadda ni kafin in ciro mota is ok,ya barta nan baki a sake ta bishi da kallo sai kuma ta zabura tayi cikin daki don ta shirya


Knocking taji anayi don haka ta zira hill shoes dinta fari ta rataya jakarta ta dauki ledarta don jikinta ya bata aliyu ne shi dinne kam idonsa na bisa screen din wayarsa yana danne danne bai dube ta ba ya juya taja part din nata ta kulle tabi bayansa tana qare masa kallo"ya gaji da haduwa"ta zanta hakan a ranta,tana jingine da rumfar ajiyar motoce har ya gyara parking qa'idarsa ne indai tare zasu fita baya neman driver duk da dama nasiru ne kawai.ke driving dinsa,wanni dogon hirn ya ja da sauri ta daidaita nutsuwarta ta nufo motar tun kafin ta qaraso taji an bangaji kafadarta da mamaki ta dago don ganin waye samirah tana ta zuba sauri zani a hannu tana gyara daurinsa,duk saurin da take gidan gaba aahe takewa,abun ma sai ya baiwa fadila dariya ta saki murmushi😊


Cikin mintuna da basu gaza talatin ba suka qaraso gidan,harabar gidan tsaf kuma fetal da haske ba kowa sai mai gadi shi da wasu mutum biyu zaune kan benci suna sauraron duniya tumbin giwa suna cin gyada jefi jefi suna taba hira,cikin girmamawa ya gaida aliyu sannan ya gaida su fadila ta amsa masa fuska a sake tunda dama da yar sanayya tsakaninsu ya samirabko kallo bai isheta ba bare tasan yana yi,ya dage masa get din ya wuce ya yafitoshi yayi masa ihsani kamar yadda ya saba shi da wadanda ke zaune a gun suka hau zuba godiya abinsa shi kuma baiso


Samira da aliyu suka jera suka fara yin gaba zuwan falon gidan fadila bin bayansu tayi ,sumayya da rabi'ah ne zaune a falin da hijabai ajikinsu da alamar sallar isha'i suka idar,suka juyo suna amsa sallamar sannan suka miqe tsaye cikin farin ciki suna gaida su hankalinsu na kan fadila itama su take kallo suna gaisawa sabanin samirah da ta riqe qugu tana qarewa falon kallo tana yaba tsaruwa da dukiya da ya lashe kamar wadda aka bawa kwangila sannan daga bisani ta zabi kujerar da tayi.mata ta zauna akai,cikin dakiya irin ta babban wa yake tambayarsu ina momy sumayya tace tana sama ya nufi benan taku biyu uku sukayi kacibus da iftihal na saukowa kamar yadda ta saba ta tsugunna ta gaidashi sanna ta daneshi ya sabeta a kafada yana tambayarta momi


Tare suka sauko shi da momin yana take mata baya iftihal na hannunshi ganin fadila ya sata ta zille ta diro ta nufeta a guje cikin murmushi fadilan ta tareta ta dora ta bisa vinyarya dukkaninsu suna dariya ta gaisheta,duskar momi washe da fara'a take.musu barka da isowa samira dake zaune dare dare bisa kujera kamar tata tave yauwa fadila dama.na qasa ne kan carpet ta duqar da kanta qasa tana murmushi cike da kunyar momin,gaisuwa aukai da samirah kamar qawa da qawa yayin da fadila ma ta kasa hada ido da ita a haka suka gaisa,ganin taqi sakin jiki ya sa momyn tace su rabi'ah su kaisu dakinsu itama zata gun abbansu yanzu ya shigo gidan,hira suke abinsu da fasika yayin da samirah ta zaro wayarta ta hau danne danne tana ganin duk ta girmesu tafi qarfin zama cikinsu ai,ga takaicin yadda aujewa fadila haba haba itq aunqi mata haka cikin ranta take cewa hmm dangin miji kenan tsinannu(kunji fa?)


A haka bacci ya dauki iftihal akan cinyar fadila aliyu ne ya leqo hukarsa a hannu yace ke sumayya ku taho dining"samrah ce ta fara miqewa tana cewa dama yunwa nake ji ta fice,qememe iftihal taqi kwanciya dole iftihal na nishi ta sabota a kafada suka fito su sumayya nata dariyar yadda ta dauki ifrihal din da qyar,momy ce da abba sai aliyu bisa dining din kusa da abban abba na dariya yaceyau ban dawo da wuri ba bare a murqushen tsohon
qashi na shine aka rama akanki ko?


Duk sukayi dariya kowanne ya samu kujera daya ya ja ya zauna banda fadila dake tsaye sabe dà iftihal wani baccin nason daukarta amma ta qi yarda tayi don kada a sauketa


Mrs muhammad ce


📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻










🌺🌺🌺🌺🌺🌺
Wa yasan gobe?
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
Written by safiyya Abdullahi musa huguma
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
▶2⃣1⃣
Momy ta kalli aliyyu tace alii rabata da rigi mammiyar yarinyar nan don idan ba kai ba ba wanda zata yarda ya sauketa,ya miqe ya nufesu yanayin yadda ya tsaya gab da ita yana yunqurin karbar iftihal ya haifar mata da wani yanayi cikin jikinta,ya sa hannu zai dauketa cikin rashin sani hannunsa ya shafi qirjinta wani abu taji ya tsirga mata tun daga kanta har tafin qafafunta hakanan shima yaji tsigar jikinsa ta tashi wani shocking yaji kamar an jashi da wutar lantarki,ya sabata a kafadarsa ta miqe zata soma rigima suna hada ido da shi tayi gum da bakinta🤐 ta mayar da kanta kafadarsa ta kwantar ya sauka da ita cikin falom ya kwantar da ita bisa doguwar kujera ya karanta mata addu'o'in bacci na tsari ya tofa mata sannan ya koma
Ta tsugunna ta gaida uncle abba ya amsa mata cikin kulawa yana cewa lpy lau diya ta,sannan ta ja kujera itama ta zauna,sumayya tayi serving din kowa🍽🍴 sannan akai bismillah aka fara ci,kwata kwata kasa sakewa fadila tayi ta kasa kai koda loma guda bakinta sai juya cokalin kawai take a cikin abincin ,amma ga tarin mamakimta sai taga samira ta saki jiki tana ta kaiwa uwar hanjinta🍜 harda tsiyaya lemo 🍹🍾da ruwa da kanta,tayi sakewar da ko ita da uncle abba yake kamar uba a gareta ba zata iya irinta ba
Abinka da mata momi na ankare da yanayin nutsuwar kowaccensu tana kuma sake godiya ga sarki Allah da ya qaddara fadila ta zamo daya daga cikin family dinsu,afakaice rabi'ah ta qarewa samirah kallo uadda take lodar abincinta ko aliyyu da yake dan gida baiyi haka ba,ki saki jiki mana fadilan ummi kici abincin ki mu fa iyayenki ne ko babu aliyu baki ga yadda yar uwarki ya saki jikinta ba?,cewar ummi,samirah ta amshe cikin tabe baki tace momi kinsan wani akwai qauyanci da rashin wayewa atare da shi"sai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login