Showing 66001 words to 69000 words out of 130495 words
Chapter 23 - Wa Yasan Gobe Compelet Book by Safiya Abdullahi musa huguma
sake dubanta ba,a dan sace ta harareshi gami da jan dan siririn tsaki ,ya juyo da sauri don tsakin kunnuwansa sukaji kamar tayin da azama ta dauke kanta ta maida window Allah ya taimaketa basu hada ido ba sai ta waske
Tafiya ce ta awa hudu ta saukesu a *ethopia* don musayar jirgi cikin babban birnin na *ethopia* wato *addis ababa*,ba kwana zasuyi ba amma saida aliyyu ya kama one room apartment cikin hotel din dake kusa da airport din,tamakar kazar da qwai ya fashewa a ciki ta nemi gefan kujera qwaya daya dake cikin dakin ta zauna a takure,sallar magariba da isha'in da bata yi bane ke damunta amma duk a takure take bare tayi azamar tashi
Tana kallo ya dora jakarsa💼 kan gado ya tube takalminsa 👞 da socks dinsa ya shige toilet,motsin ruwan da ta ji yasa ta raya alwala yakeyi
Kusan minti arba'in ya fito sanye da rigar towel mai budadden qirji👘,kallo daya ta masa ta dauke kai tsigar jikinta na tashi 😣,gashine kwance luf a qirjinsa baqi sidik tamakar wanda ake sawa relaxer kamar yadda na hannayensa da qafafunsa suka kwanta saboda ruwan da suka sha,ta sake runtse ido gabanta na dan faduwa💔 da alamu ma shi ko ajikinsa don goge sumar kansa yake da dan qaramin towel dake riqe a hannunsa
Ganin ya soma kunce dan zaren da ya taimaka wa rigar ta rufe jikinsa ya sata yin azamar afkawa toilet,ta dade numfashinta na kaiwa da kawowa wani abu na mata yawo a jiki sannan ta iya daura alwalar ta fito,ta cimmasa tuni ya har ya tayar da tasa ta koma gefe ta kalli inda taga ya kalla ta tayar da alama nan ne alqibla har ta kammala tata ta zauna tana lazumi lokaci lokaci tana satar kallonsa har ya sallame
Shirye yake a yanzun cikin jacket masu kalar green da black sabanin dazu da yake sanye da suit baqaqe kullum aliyyu cikin sa kaya yake sabanin wadanda ta sanshi da su,kusan ma zata ce bata taba ganinsa yayi maimaice ba,yana zaune saman qafafunsa ya kammala addu'arsa ya shafa ya miqe tayi saurin yin qasa da kanta don kada su hada ido tana yiwa Allah tasbihi saboda kyawun da taga yayi mata har ya juya ya fice
Fitarsa ba dadewa daya daga cikin ma'aikatan hotel din yayi knocking ya shigo mata da abinci fried spaghetti ce da roosted chicken sai drink da ruwan gora mai sanyi duk da cewa akwai su cikin fridge dake dakin,babu abijda ta iya ci sai lemon da ta sha
Saman kujera ta nade ta janyo wayarta ta kunnata wadda tun shigarsu jirgi ta kashe,babu service da ya hau saboda ya fita daga inda yake da amfani ,ta danna power off ta kashe don bata da wani amfani ta maida kanta ta kwantar a hannun kujerar
A hanzarce ya shigo ya dauki jakarsa 💼 ya juya yana cewa "let's go"ta miqe ita ma ta dauki tata👜 ta bi bayansa
🎊🎊🎊🎊🎊🎊
*_CHINA (SIN)_*
*_guangzhou airport_*
Qarfe hudu ⏰ na yamma da minti ashirin a agogon qasar china qarfe sha daya da minti ashirin agogon Nigeria suka sauka a qasar,iyakar gajiya fadila ta yita,tafiya ce ba kadan ba tamkar ta yada shege zama ne na awanni kimanin goma sha biyar a jirgin wadda bata taba tafiya makamanciyar ta ba
Da qyar take daga qafarta da tayi mata taruwar jini saboda tsabar zama,suka sake bin layin screening immigration suka karbi passport suka kuma duba visa dinsu don tabbatar da cewa sun samu izinin shigowa qasar tasu,bayan sun tabbatar da ingancinta suka buga musu stamp suka wuce
Sauran kadan aliyyun ya bace mata saboda ta lura cike yake da kuzarinsa tafiyarsa yake kamar baiyi wata doguwar tafiya ba bisa dukkan alamu ya saba da irin wannan tafiyar,motar ce mai azqbar kyau da daukan hankali tayi parking gabansu mutum uku ne suka fito dukkaninsu sanye da coart baqaqe baqin space da baqin sau ciki😎,cikin girmamawa suka iso inda aliyyu yake biyu daga ciki suka miqa masa hannu sukayi musabaha,cikin harshen nasara suka fara gaisawa dayan dake gefe ya dauki akwatinansu ya sanya a bayan motar
Bayan ya ruge boot suka dunguna gun motar fadila ta bisu a baya,ita da shi na sit din tsakiya biyun kuma na sit din can bayan driver din kuma ya shiga mazauninsa ya tada motar,hira suke abinsu da aliyyu yayin da hankalin fadila ya kasu biyu,daya ta dora shi ne bisa ga aliyyu yadda yake turanci kai sai ka ranyse
[10/16, 1:52 PM] 💍🍬🛍Salma🛍🍬💍: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?..*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*written by safiyya Abdullahi musa huguma*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*part 2*
2⃣9⃣&3⃣0⃣
Yayin da hankalin fadila ya rabu gida,daya ta dorashi ne kan yadda aliyyu ke turanci kai ka rantse da Allah cikakken buture ne gaba da baya,babu tuntuben harshe ko kuskure ko qanqani,daya kuma ya tafine kan kyawu tsari gami da tsaftar garin ,garine mai azabar kyau da tsari,yanayin gine ginensu sun burgeta matuqa da gaske,saidai abu na farko da ya daga mata hankali dan banzan sanyin da suka tarar ana danawa a garin🌫,taji daya daga cikin yan chinan na sanar da aliyyu yanzu ma aka shiga cikinsa wanda irin wannan sanyin a Nigeria shine wucewar jaurarmu
A hankali motar taci gaba da kutsawa cikin cikin kyakkyawan shimfidedan titin har suka shigo cikin wata kyakkyawar unguwa mai tsafta da tsari wanda tafiyar fadila tsakanin airport da inda suke yanzun ta fuskanci haka unguwanninsu suke,basu yi wani nisa a layukan da suke wucewa ba suka sa signal suka gangara wani layi,sun kusa kaiwa qarshen layin driver ya faka qofar wani dan kyakkyawan gida dake yanyame da shukoki daga gaban gidan kuma grass carfet ne to kusan ko wanne gida dake layin haka yake left to right
Driver din ne ya fito ya bude musu qofa sannan ya bude boot din ya fitar da kayansu,Aliyyu ya ciro keys daga aljihun cikin rigar suit dinsa ya miqa masa ya sa hannu ya karba ya nufi gidan ya bude,ya shigar da kayan sannan daga bisani shima ya shiga
Tun fadila na tsaye har ta gaza jure tsaiwar ta maida bayanta ta jingina jikin wata 'yar bishiya dake dashe a gun,shi kam tsaye suke qyam jikin motar shida lukas da andi suna ci gaba da hirar kasuwancinsu cikin harshen nasara,jifa jifa tana tsintar wani abu wani abun kuma ya kuce mata idan tunani ya rinjayeta,tsayuwar awa guda cif sannan ya fito ya qarasa shigar da ragowar kayan da bai dauka ba ya kaisu ciki,ya dawo cikin girmamawa ya ya miqawa aliyyu maqullan ya karba yana tambayarsa "have you finished?" Ya gyada kai gami da cewa "yes sir everything is ready"ya girgiza kai yana cewa "well done"ya juya gunsu andi da lukas ya basu hannu sukayi musabaha gami da sallama ya juya ya nufi cikin gidan su kuma suka shige motar driver ya jasu suka bar gun a kasalance ta rufa masa baya zuwa cikin gidan
Falone wanda ba za'a kirashi qato can ba hakanan ba zaka kirashi da qarami ba,saidai yadda ya tsaru dole ya qayatar da kai ta yadda zaka iya fin sha'awarsa ma fiye da wani qaton,kujeru ne set guda yan madaidaita masu azabar kyau sai labulaye na alfarma da suka kewaye falon ta yadda baka iya bambance ina qofa take center carfet center table da wasu yan qanana dake maqale tsakanin kujera da kujera tafkekiyar plasma TV da home theater dining area mai dauke da dining table mai kujeru hudu komai na falon fari ne tas sai wasu abubuwan masu sirkin baqi kadan,qofofine hudu cikim falon daya kitchen ne sai store sai public toilet sai bedroom,komai tsaf yake kuma qal qal ta tsammaci hakan dama idan tayi la'akari da dan karen son tsafta irin na aliyyu
Fadila ta zabi daya faga cikin kujerun tayi saurin zama saboda yadda take jin gajiya na nuqurqusarta har cikin qashi ji take tamkar ba zata iya daga koda yatsanta ba,tana nan takure kan kujerar tana satar kallonsa,gaba daya sanyin garin ya soma takura ta tun yanzun,ga bashin sallah dake damunta tunaninta daya ta ina zata soma iya taba ruwa da wannan azababben sanyin?
Key yasa ya bude dukkanin qofofin ya tura daya wadda a samanta aka rubuta da wani dan siririn katako mai kyau *bedroom* ya shige,ta miqe itama a gajiye ta shiga public toilet cikin sa'a ta tadda a kwai heater kunna ta tayi ruwan ya dan yi zafi sannan ta kunna famfo na zafin da na sanyin ta saisaita su yadda zai mata dadin alwala,falon ta dawo saidai bata san ina ne gabas ba don haka ta kintaci inda taji hankalinta ya fi karkata ta tada salla
Minti goma ta kammala magrib da isha'i har ma da shafa'i da wutirinta,batabar kan carfet din ba tana duqunqune cikin hijabinta wanda dama yana cikin jakar hannunta haka al'adarta yake ko ba zata sanya hijabi ba to bata rabo da shi cikin jakar ta,a hankali tana duqunqunen idanunta suka soma mata nauyi da radadin bacci tamkar an watsa mata tsakuyoyi a cikinsu gajiya da bacci suka yi mata tarom dangi suka murqusheta bata san sanda ta bingire da bacci ba agun
Cikin sabon shiri yq fito yana sanye da jibgegiyat rigar sanyi mai gashin dabba daga ciki trouser ne da long sleeve shirt duka baqaqe kansa hular sanyi ce ta gashi mai azabar kyau qafafunsa boot ne mai dan tsawo 👢ya sanyawa hannayensa safofin hannu ya saye idanunsa cikin gilashin nan nasa na ko yaushe👓 cikin hanzari ya fito da niyyar fita don sama musu abinda zasu ci idanunsa ya sauka kanta tsakiyar centre carfet din dake tsakiyar falon ta cure guri guda
Ya san sanyin garin ne ya soma addabarta shi kansa da ya saba zuwa abroad cikin irin wannan yanayin wannan karon sanyin ya dameshi balle ita da bai tsammanin ta yaba zuwa,ya dawo da baya a hankali ya isa ga makunnin na'urar dumama daki ya kunna ta ya sake juyawa ya zuge gami da rufe duk wasu qofofi windows da labulaye dake abude na gidan sannan yasa kansa ya fice hadi da sa key ya kulle gidan
A hankali ya soma bude idanunta tanajin yanayin dakin ya sauya mata,sanyin da ya takura mata dazu da zata kwanta ya ragu sosai da sosai,ta kasa tashi illa idanunta dake bude tayi zuru tana jin yadda cikinta ke qugin yunwa,idan bata manta ba rabonta da abinci tun a nijeria sai drink da take ta sha har acikin jirgi
Wanka a qa'ida take da buqatar yi da ruwa mai zafi don ta samu ragowar gajiyar ko zata sake ta amma rashin ganinsa afalo yasa take tsammatar yana bedroom din,kasa kunnenta tayi sosai bata jo motsin kowa ba don haka ta miqe akasalance,cikin sanda ta tura qofar bedroom din ,babu kowa ciki daki ne babba yalwatacce ba wani tarkace cikinsa cupboard ce sai dressing mirror hadi da dressing chair sai sofa qwaya daya madaidaicin gado ne mai rumfa wanda aka kafashi daga jikin window sai center carfet da center table daga gaban gadon kenan,komai na dakin shima farine kamar dai falon hatta da kalan furniture din zuwa ga bedsheet
Ta sako kanta ciki bayan ta tabbatar babu kowa akwatunansu na saman gadon a ajjiye nashi akwatin ne ta gani a bude kayan sun dan hargitse kadan da alama ya bude ne ya debi wasu abubuwa,gefe ta zauna ta fiddo da duka kayan nasu ta shirya su cikin cupboard,nashi ne auka cinye fiye da rabinta ta tsaya tana kallon yadfa kayan suka tsaru ita kanta sun burgeta ta karkade hannayenta ta rufe qofofin sannan ta shige toilet din bayan ta ciro kaya kala daya da zata sanya
Ta fito daure da towel wanda ya sauko mata qasan gwiwarta yayin da ta yafa qaramin saman kanta tana goge ruwan da ya dan taba mata shi da wanda ya shigar mata kunne,sam bata yi tsammanin ya shigo dakin ba shi din ma haka yana zaune ne kan bedside hannunsa riqe da lemon kwali yana dan zuqa kadan kadan ,gabanta ya fadi sosai don ta tsorata da ganin nasa,da azama ta juya don komawa toilet din garin haka towel din kata ya zame ya fadi qasa kanta zuwa kafafunta suka fito sarari,gashinta ya kwanta luf bisa dan dogon wuyanta zuwa gadon bayanta wanda ruwan da ya tabashi ya sake sashi kwanciya,da sauri ya dauke qwayar idanunsa ita kam ko ta kan towel din bata bi ba ta koma hadi da tura qofar
Ta hudar dan maqulli take leqensa tana gani ya daga lemon maimakon shan ganin dama irin na dazu dai taga ya daga kwalin bai sauke ba saida ya daddake shi tas sannan yayi cilli da kwalin yayi qas da kanshi yafi Minti guda ahaka sannan ya miqe da sauri ya five a dakin,sai da tabbatar ya fita sannan ta fito da sauri ta sawa qofar key sannan ta shirya cikin doguwar riga mai dogon hannu cotton ce sosai ta yane kanta da mayafi ta duba jakarta don dauko turarenta na shamsul imarat da blue lady
Kaf jakar ta lalube da hannunta ta nemi su sama ko qasa ta rasa,cikin shakku ta zazzage jakar gaba daya babu babu blue lady din babu shamsul imarat din sai wani da ta gani cikin kwalba cikin takaici take kallonsa tasan dai ita ta sayeshi amma ta manta a ina?,ta zumbura baki tana maida kayan da ta zazzage din cikin jakar,ta dauko shi shima zata maida saita shanshana"ba laifi shima qamshinsa"ta fadi haka tana ajjiyeshi a gefanta
Kuyi haquri da aliyyu kudai kuci gaba da bina komai daki daki yake a rayuwa😂😂😂
Na gode🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻
Mrs muhammad ce 👑
📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
[10/16, 1:53 PM] 💍🍬🛍Salma🛍🍬💍: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?...*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*written by safiyya Abdullahi musa huguma*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*part 2*
3⃣1⃣&3⃣2⃣
Ta dade a tsaye tana takaicin rashin sako turaren nata da batayi ba don gaba daya tayi tsammanin ta sako su,taja tsaki yafi a qirga ita ba sanin gari tayi ba hasalima yau ta soma shigowa qasar ko da ta sani din ma ai dole sai dai ta yiwa aliyyu magana wadda ita kuma hakanne bata so,to idan kuwa haka ne bata da zabi illa saka wannan turaren tunda sam bata son zama a rayuwarta ba tare da taji jikinta na tashin qamshi ba haka take qamshi a jininta ya ke,ai shima wannan din turarene,sam fadila ta mance aikinsa tama manta a inda ta sayeshi tunda abun bai gabanta tunda ta wulla shi a jaka ta manta da babinsa
Ta kammala shafawa tana lumshe ido gami da cewa "hmmmm" saboda yadda qamshin nasa ya yi mata dadi sosai,qanshi ne mai sanyi ya karade jikinta da ma dakin gaba daya,ta maida shi cikin jakarta ta rataye jakar a abun rataye jakankuna ta jawo qofar dakin ta dawo falo,yana zaune a gaban laptop dinshi 💻(agogo sarkin aiki😏)cewar fadila cikin zuciyarta,aliyyu hardworking person ne komai yasa a gabansa yakan zama serious akai har sai ya kai ga cimma burinsa,yana jin fitowar tata amma bai daga kai daga abinda yake ba bare ya dubi sashenta
Sannu a hankali qamshin ya soma karade falon ya soma kuma fisgar hankalinsa,ya rasa daga inda qamshin ke fitowa,sannu sannu kasala ta soma rufeshi idanunsa suka soma lumshewa,ya daga kansa ahankali ya dubi sashen da take waya ce a hannunta📱 tana danne dannenta saqonni take dubawa da suka shigo mata,ya maida ido runtse sosai yana qaryata kanshi game da feelings din da yake ji,ya sani tun usul haka halittarsa take yana daga cikin mabuqata,gaba daya ya mance da wannan matter din sanda zai taho aiki ne kawai a gabansa da kuma tsaftar inda zai zauna da abincin da zaici
Cikin lokaci kadan mood dinsa ya canza sosai he needs something really, idanunshi sun jima a rufe aikun da yake ya gagareshi saidai still mood din da yake ciki bai canza ba,ya sake kallonta karo na biyu bata san ma me ake ba har yanzu wayarta na hannunta tana latse latsenta,"take dis bags ki samin nawa a plate ki dauki naki
Juyowa tayi don jin muryar tamkar ba tasa ba,amma sai taga latse latse yake bisa laptop idanunsa na bisa screen din,bata ce komai ba ta ajjiye wayar a gefanta ta debi kayan ta shiga kitchen,shawarma ce da Chinese spaghetti sai roasted chicken ta saka kowanne a aplate din ta hada masa da ruwa da lemo ta jawo dan side table gabansa ta dora masa akai,zuwanta gabansa ya sake sa qamshin ya cika masa hanci,ya sake runtse idonsa hadi da qanqame hannayensa gu guda cikin wani irin lust moode,sam bata lura ba ita dai ta kammala hada masa ta dauki tata ledar ta koma mazauninta,duk yadda ya kai ga son cin abincin haka ya dinga tsakurarsa a kasalance girman kai kuma ya hanashi ya sake koda duban sashen da take
🔅🔅🔅🔅🔅
Ta sake duban agogo karo na uku kenan sha daya da rabi na dare🕦,tuni bacci ya sake cika mata idanu kamar ma batayi shi dazun ba duk da dama ba wani jimawa tayi ba ta farka,tunaninta daya ko ina makwancinta? Tasan dai ko giyar wake ta sha bata tafiya kai tsaye su hada dakin kwana da aliyyu ba bare ya yarfata
kasa daurewa baccin da take ji tayi saboda haka ta ware mayafinta ta lullube kafadarta zuwa qafafunta ta ja filin kujera qwaya daya ta tada kanta da shi tunda shi kam lura aikinsa yake tuquru hadi da amsa kiran dake ta shigo masa wanda dukka da harshen turanci yake maganar hakan ya tabbatar mata yan qasar ne masu kiran,batasan yayi hakanne bane ko zai samu feeling da yake ji ya sake shi shi uasa ya takura kansa da aiki,ba abunda yake sai faman dirkawa cikinsa coffee flask guda ta hada masa amma ya kusa tafiya abun har yaso bata tsoro
Tsaye yayi a kanta baccinta take sosai,bai taba qarewa fuskarta kallo ba irin yau,gashin gaban goshinta ya sake kwanciya kamar relaxer ta shafa masa komai nata medium mai kyau tamkar ma ba baccin take ba,a hankali abun nan da yake son ya danne ya ci gaba da taso masa,ya tabbatar idan yaci gaba da kallin nata a yanayin da yake ciki din nan zai iya aikata abinda yame ganin ita din ta masa kadan ta iya daukarshi gane yake zai iya nakastata,ya janye ida nunsa daga kan fuskarta yana maida numfashi,yasa hannunsa ya zare filon da take kai kanta ya sauka saman kujerar
Firgigit tayi ta farka don ta dan tsorata ya kalli idanunta wadanda bacci da ta soma da tsoratar da tayi yasa su sukai wani kyau ya dauke kansa gefe guda zuciyarsa na dan bugawa