Showing 42001 words to 45000 words out of 130495 words

Chapter 15 - Wa Yasan Gobe Compelet Book by Safiya Abdullahi musa huguma

duk da bata nuna mata hakan ba,ai kuwa da ta karanta kwalin sai taga tabbas sun fi nata kyau to tun daga ranar bata sake bari ba


samira nata rashin mutuncin yafi ysakanin falo da kitchen parlour zuwa kitchen,zata dauko plates ne🍽 kofuna ne🍶 da su spoon tayi ta batawa wani abun plate din ma leda ce ta chewing gum ko biscuit zata dora akai kuma ta barshi a nan tunda ta sani cewa babu mai aikin gyara gun sai fadilan,duk da wannan neman masifa da suke ba wadda ta isheta kallo a cikinsu


Su kansun so suke ta kulasun amma ta qi basu wannan dama


Mrs muhammad


📚📚✍🏻✍🏻✍🏻


01:18 pm 05/11/1437


🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*wa yasan gobe?*


▶3⃣3⃣


Lahadi daya daga cikin ranakun qarshen mako ne wanda yake zama ranar hutu ga ma'aikata to haka ne ya zama ga fadila hutun ya zame mata double babu zuwa office kuma bata da girki,la'asar sakaliya ta ranar ta shirya tsaf cikin doguwar riga shigar da tafi so kenan ta material ce ruwan qwaiduwar qwai dinkin rigar ya bude sosai dga qasa an mata dogon hannu tayi rolling dinta kamar yadda ta saba da jan mayafi,takddunta ta diba 📄📉📈 na aikin office da takeson dubawa zata yi wani aiki a kansu ta dauki yar madaidaiciyar dadduma da daya daga cikin matashin kujerarta ta zira takalminta ta firo harabar gidan,sai ta tarar da saluma da samira zaune kowacce a harabar sashenta bisa farar kujera plastic,novel a hannun salima📖 samira kuma na riqe da wayarta📱 tana tana ta faman danne danne,tun kafin fadila ta kai ga zama ta fuskanci zaman nasu ba na Allah da annabi bane don kuwa taba fitowa ta fara cin karo da baqaqen maganganun da auke jifan juna da shi a fakaice ba tare da kowa ya kalli dan uwansa ba


kamar ta koma ciki sai kuma ta duba agogon wayarta📱taga biyar harda rabi da minti uku bata da wani lokaci na duba takadddun idan ba yanzu ba cikin gidan kuma zafi yayi yawa sanadiyyar hadarin da keta hadowa ana yin yayyafi dan kadan wanda ke qara tada zafin garin,ga injinsu yayi tsiya yaqi tashi tun wajen uku bakaniken ke kansa yana fama da shi kasancewar ba dan qarami bane yana daukar dukka freezers dinsu heater a.c da sauransu sun riga sun saba da wuta ko yaushe 24 hours,sai kuma ta ahimfida dardumarta cikin ranta tana fadin _ina ruwan biri da gada?_,tayi bismillah ta zauna ta soma aikinta,ashe duk suna ankare da ita,minti goma bai cika ba da zaman nata samira ta soma receiving call "shegiya kina duniya?......heeeee wlh gamu a cikinsa muna gogawa.......hahahahahaha aike kinsan fa hali tun ba yau ba"ta danyi shiru sanna ta sake kecewa da dariya kamar wani gardi tace"a haba haba ke sai kace ba nice samira ba?.....k kinsan saidai a gaji aqyale mana,kowacce qaramar shegiya sai ta kama gabanta da qafafunta🏃🏽 ,salima ta bude shafin gaba na littafin dake hannunta tamkar da gsken karatun take tace"qaramin dan iska ma yaci uwatar ai yasan kansa,samira ta sake kecewa da dariya "wlh har mai share share da goge goge ita wannan ai ba wahala zata bani ba.....yo hannatu yar anacen ma ba komai bace a guna wallahi duk hasashen da take na ita wata ce a gunsa


Sarai fadila ta san da ita take amma sai taga ba mutuncinta bane tsayawa tana cece kuce da wadda batasan ciwo mutunci da kuma darajar kanta ba ,kan ta qare wannan tunani sai ji tayi tas!


Da sauri ta dago idanunta don ganewa kanta wanda ka zubawa wannan lafiyayyen marin,aikin salima ne tana tsaye a gaban samiran bayan ta kwasheta da marin tana huci,tuni samira ta katse wayar hannunta na kan kumatunta ta miqe tsaye salima ta dora mata da bayani👉shiru shirun da kike ganin ina miki ba fa tsoronki nake ba ki bar ganin kina min kina samun nasara wallahi kin kaini bango nifa ba sa'ar yinki bace don uwarki"tasa yatsanta tan nuna qirjinta👆🏼 tana cewa"ni kika mara?"😁an marekin kadan ma kika gani wata rana zaki ga abinda yafi marin ma,kina tsammaninke kaďaice tantiriyar karuwa ko?💁🏽to 👆🏼nima karuwace nayi nayi kuma yaqon duniya fiye da naki ke da kika local ma


😳😳mamaki da tsoro suka kama fadiladama har akwai abun tutiya gun mace don tayi yawon karuwanci?wannan wane irin zama nine da Allah ya kwomù da har karuwanci ya zama abun ado?ita takaici ma sai ya sata ta maida kanta kanrubuce rubucenta📝taqi kola kowaccensu tana jinsu cacar baki mai zafi ta barke tsakaninsu tamkar zasu cinye junansu 🎭


Duf taji gun yayi shiru kamar an sanya musu kwado a baki🔐,ta dago da hazari don ganin mai ya sanya su yin shirun ba tare da kowa ya raba su ba?,aliyyu ne ashe ya ahigo kuma baau ankara da shigowar tasa ba sai da ssuka soma daga hannu da niyyar kaiwa juna duka👊🏻,kowaccensu tayi sak saluma ce ta fara cewa 😢wallahi tallahi ban kulata ba itace ta fara takalatakuma ka tambayi fadila"jin sun sanyo sunanta cikin sha'aninsu ya sanyata azamar taahi ta soma linke sallayarta,daidai lokacin da ya kai dubansa😒 gun da fadilan take da salimar ke nuna masa,ga mamakinsa tana gama ninke sallayar a nutse ta duqa ta mwaahe takardunta ta juya ta shige sashen nata ba tare da ta kalli ko da daya daga cikinsu ba cikinsu ba sai aliyyu ya bita da.kallo👀 karon farko wani abu daga garetà ya fara burgeshi nutsuwarta ,sai da ta shige ta kulle qofarta sannan ya dawo da idonsa kansu tuni samira har ta gudu🏃🏽ta rufe itama qocarta cike da fargaba da tsoron fushin Aliyyu😡 a akanta don ta tabbatar In dai ya bincika ya tarar bata da gaskiya to la shakka fa kashinta ya bushe,ta ruwan sanyi yake ma hukuncin da zaka raina kankà babu duka ba zàgi bà baqar magana,ya juyo ya dubi saluma da jikinta ke rawa sai kawai shima ya gewayeta ya shige nasa part din


⚜⚜⚜⚜⚜


Kwana uku tsakaniya kamaqarshen wata ne,kamar yadda ya zama al'adar gidan fita aiyàyya a iřin lokacin don sabunta abu uwan buqata na amfanin yau da kullum
Yaune za auyi fitar farko tun bayan dawowar salima gidan gidan


Fadila ta shiryq cikin shigarta ta bare bari tana nannade cikin lafayarta ,ta kammalà komai ta kira umminta don su gaisa,hira suke sosai ta jiýo tashin horn ta tabbatar aliyyu ne don bai son jira kuma baya jira saboda haka shima bai bari a jirashi tayi saurin maqale wayar a kafada tan ci gaba da hirarta da ummin tasa daya hannunta dauki jakarta🎒ta sa mèy ta kulle sashin,ta qarasa jikin motar tana sallama da ummin ta ciro wayar daga kafadarta tana kashewa sai ga salima da samira tamakar an jehosu kowacce na qoqarin bude gidan gana ta shige don badon fadila tayi azamar matsawa ba da daita zasu yi awon gaba,ta rufe bakinta da tafin hannunta🙊 dariya na shirin subuce mata😂,cikin zuciyarta tana cewa sunan wani film *qauyawa* Allah kayi mana magani wannan ai kishin jahiliyya ne


😂😂😂😂😂


Ku biyo *mrs muhammad*


📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻






[10/16, 12:41 PM] 💍🍬🛍Salma🛍🍬💍: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*wa yasan gobe?*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*written by safiyya Abdullahi musa huguma*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺


▶3⃣4⃣


Allah ya sawwaqe tace,ta bude gidan baya ta shiga tana kallon drama,aliyu ne ya juyo don ganin meke faruwa haka ake shirin cire masa hannun mota?cikin tsawa musu su matsa masa daga jikin mota,bai wata wata ba ya figi motarsa ya barsu a gun sake da baki😦,gudu yake zubawa abinsa bisa dukkan alamu ransa ya baci,duk sai fadila tayi tsuru-tsuru don da irin wannan gudu da yake zabgawa gwara ya sauketa salun alun ,


Qiiiii...taji ya taka burki,ya gangara gefan titi ya faka motar cikin shaqaqqiyar murya taji yace"fito ki dawo gaba don ni ba driver din gidanku bane😠"bata ce kanzil ba ta dawo gaban


Yanayin zaman yayi wa fadila kusa sosai,mayen turarensa ya soma raba mata hankali,lissafinta ya soma qwacewa take kasala ta saukar mata,wani shauqin aliyyun ya mamayeta duk da azahiri idan ka kalleta zaka yi tsammanin ko inuwar sa bata gabanta


Sun isa shoprite inda suka saba siyayyar duk qarshen watan,ta san tsarinsa bai shiga yana tsayawa ne a waje yayi zamansa cikin mota,da sun gama siyayyar ayi masa total a turo masa list da amount,da yake yana harka da su akwai kamfaninsa dake india wanda akwai hurdar kasuwanci tsakaninsu,"u have twenty minutes idan kima gota haka so sai ki nemi motar mai da ke gida"ta jinjina masa kai duk da idan da sabo yaci ace ta saba don duk sanda ya kawosu mintina ashirin din yake basu basa kuwa darawar domin dukkaninsu sun san halinsa yana iya tafiyarshi


A nutse ta shiga ta duba muhimman abubuwan da take buqata don tana lisaafin jibi ita zata karbi girki duk da ba wani tsiya bane a ciki banda tsabar bauta ta gyare gyare da dafa masa abinci wanda sau da yawa tare suke cinyewa da samira da salima ,sukan daidaici lokacin cin abincinsa ne su shigo da nufin sun zo taya shi hira sai kuma su taya shi lamushe abincin


A gurguje ta kammala zabar duk abinda tasan bata da shi ba wani kaya ne mai yawa ba tunda bata iya gama amfani da siyayyar tsohon wata suke sake sabuwa saidai ma wani abun ta bada shi,sai ta soma dibarwa salima da samira abinda ta lura sunfi siya yawancin lokuta idan suka zo,Allah ya taimaketa minti goma sha takwas ta gama komai,ta riqe leda daya ragowar aka biyo ta da su
Tana fitowa suka yi kacibus da shi yana tsaye a hanyar wucewar tata,shi da wata matashiya ce wadda a qalla shekarunta ba zasu gaza ashirin da shida ba,abunda ya bata mamaki shine ganin hawaye bibbiyu bisa fuskarta😭,ta maida dubanta garesu a karo na biyu daidai lokacin da aliyyun ya nuna ta da yatsansa yana cewa "👉 this is d last warnings da zaki sake bina wani guri ki kama kanki tun kafin ya gudu ya barki and respect ur self"


😳Sai taga kawai ya sa hannu ya rungumota kafadarsa sassanyan qamshinsa ya buwayi hancinta suka bi ta gabanta suka wuce,cikin mamaki fadila ta waiwayo still tana tsaye tana binsu da kallo hawayen na bin fuskarta😭,ta sake fashewa da kuka a guje ta nufi motarta ta fada ciki🚗🏃🏽,


Daf da zasu qarasa cikin motar wadda tuni an kammala zuba kayan taji ya tureta daga jikinsa ,ta tsaya a baya sai da ta bari yayi gaba sannan ta biyoshi,zaman kurame suka sakeyi cikin motar har suka isa gida


Ta kammala shirin baccinta ya sanya night gown sannan ta dora dogon hijabinta mai hannu da ya sauka har saman qafafunta ta sanya sannan ta kwashi ledojin da ta yima su salima ta su siyayyar ta nufi sashensu,saidai ta tarar dukkaninsu basa nan don haka zuciyarta ta bata amsar ba zasu wuce sashen aliyu ba


Can kuwa ta tarar da su kowacce ta debi fushinta akan ya wulaqantata ya tafi ya barta taje masa da shi ,basu san ya fisu fushin ba don haka ci kanki ba wadda ya gaya mawa a cikinsu ya watsar da su a falo ya shige dakin barcinsa ya shiga wanka,sun sani ba wadda tayi gigin binsa ciki tunda suka ga ya musu banza to da tashi da su nan suka jibge a parlour zaman jiran sa,har ya fito ba wadda ya kalla ya haye dining yana fama da girkin salima wanda,farar shi kafa ce tsura babu salad ko cabbage bare akai ga batun nama,cikin qufula ya kira sunan salima da suke zaune suna fama da 'yar harare harare,bisa kansa ta tsaya ita dole wadda akayiwa laifi ce tace gani😼,ya dora gwiwar hannunsa saman table din ya hade yatsunsa cikin juna ya dora habarsa a tsakiya sannan ya kalleta yace"😒 sau nawa nake gaya miki I don't like such cooking?,ko kayan cefanenki sun qare ne?ko sun qare ba zaki iya sanarmun ba kenan?,ta tabe baki ta kawar da kai tace "kayi haquri "ya danyi shiru ya dafe kansa kamar ba zaice komai ba,har ga Allah ba don yunwa ba baiga dalilin da zai sanya shi cin wannan abincin ba,ya shiga tuna irin dandano mai gansarwa da yake samu duk ranar girkinta,ya dago kai yace bude fridge dina ke debi cabbage da cucumber ki yankamin ki hada min da dafaffen qwai tunda yau ban isa naci nama ba"ba tare da ta amsa ba ta juya


Mrs muhammad👑👑


📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻


5:44 pm 5/11/1437


🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*wa yasan gobe?......*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺




▶3⃣5⃣


Da sallamarta ta shigo falon sam bata ma lura da shi ba bisa dining,ta dan dora murmushi bisa fuskarta🙂,salima ce ta masa sallamar itama ciki ciki kamar wadda aka cusawa tsumma a baki,ta qaraso gabansu ta direwa ko wacce ledarta🛍 a gabanta tana cewa"sannunku,ga siyayyarku nan Allah yasa na haso muku da abubuwan da kuke buqata " salima shiru tayi saboda tafasa da zuciyarta keyi,yayin da salima yar takife tace" waye ya saki sarauniyar masu shishshigi ,kina murna kina rawar kai an koro mu ke an tafi da ke,shine don digimi da neman gindin zama harda wani yi mana siyayyar kaya ko?to ahir dinki wlh ni ba'a shiga gonata don kiji na gaya miki,har wata fada ce dake a gunsa banda ta shara da zaki mana rawar kai?ko an gaya miki sonki yake?"


"Hmmmm matar cushe kenan"cewar saluma da bata tofa ba sai yanzun,cikin wani irin mamaki da al'ajabi ta dago tana dubansu,meke faruwa?a ina suka san wannan ?haka aliyyu ya gaya musu cewar ba aonta yake ba?,wannan wane irin kwance zani a akasuwa ne?,wanne irin cin kashi ne haka yayi mata?"take idanunta suka sauya launi,wani irin fushi da bata tsammaci tana da shi ba ua sauko mata😡😣,kamar hadin baki suka miqe suna shirin barin dakim don dama haushin kaza ne huce kan dami,tunda sunsan ko giyar wake suka sha basu isa su juye haushinsu ba kan wanda ya musu laifin sai suka juyeshi kanta,suna shirin ficewa suka jiyoshi cikin lion voice dinsa yana kiransu "😠ku kwashe kayan nan daga gun nan ku bace min da gani"kunnen uwar ahegu sukayi niyyar yi a zafafe yace da su"👉�billahil azim duk wadda tabar ledarta a nan tamu ce ni da ita"tilas kowacce ta waiwayo ta dauki tata tabar sashen


Cikin matsanancin bacin rai ta dago kantasai suka hada ido,wani baqinsa ta gani wanda bata taba ganin yayi makamancin haka a idanunta ba,kafin ya janye idanunsa ta fara janye nata tayi azamar juyawa ta bar sashen


Kusan kwanan zaune tayi ,babu abinda ranta bai gaya mata ba,abunda take ta qoqari da fadi tashin bunneshi ashe ya dade da yin tsiro har yqyi yabanya?tabbasa aliyyu ya cutar da zuciyarta ya cutar da zuciya da ke cike da qauna gami da begensa cikin kowanne fitar numfashi na dan adam,tabbas a ayu badon mutum bai da ikon cire son wani daga zuciyarsa ba da itakam ta ciro har zuciyar ta wurgar ta huta ma gaba daya,ranar idanunta basu ga bacci ba sai tunani data takurawa.kanta da shi wanda ya haifar mata da da ciwon kai da zazzafan zazzabi,ba ita ta samu kanta ba sai washegari da la'asar bayan ta takurawa kanta ta cire damuwar ta ajjiyeta gefe


⚜⚜⚜⚜⚜


Cikin qyanqyami yake shiryawa,gaba daya dakin ya hargitse sun kuma barshi kamar yadfa suka saba,sai dan yakanji relief idan ya tuna zaije ya dawo ya tarar da komai ya zama neat,da hanzari ya kammala ya dauki jakarsa💼 ya fice ba tare da ya saurari breakfast da salima ta hada ba ruwan tea ne fari sol babu citta bare kanunfari sai soyayyen qwai wanda qarninsa ke hanashi hadiyarsa,shi kuma akwai qyanqyami yayin da su kuma basu maida tsafta 💄👠👒💅🏽da gyara wani abu mai muhimmanci ba


Sanda ya dawo ya tarar da sashen nasa yadda ya barshi yayi matuqar mamakin hakan,don bai saba ganin haka ba,yasan ranakun girkinta zai tadda komai a kintse hakanan yaji ransa ya baci da ganin haka,ya zube anan saman kujera yana fitar da iska mai zafi daga bakinsa,ya dubi agogon hannunsa qarfe shida da arba'in har da hudu,mintina qalilan suka rage a shiga masallaci sallar magarib,a kasalance ya duqa yana zare sau cikin qafarsa👞hadi da sabule safar,wata bahaguwar yunwa ke rarakarsa,yinin yau gaba daya ba abinda yaci banda maltina mai sanyi da ruwa da yake ta dirka,saoda yana da yaqinin zuwa ya tadda abinci mai kayau🍛,


Kai tsaye ya shige toilet ya dauro alwala ya dawo falon yana goge ruwan jikinsa da handkerchief,gidan🏛 tsit sai hasken fitilu da ya gauraya da duhu suhun magariba da ya soma kawo kai ,ya dan lumshe idanunsa kewar qanan yara na shigarsa👫,ya tabbata da yana da su da zai dinga jin koda hayaniyarsu ce da gilmawarsu ,ya riga ya saba da tsabar qwarewar.matan gidan wajen iya rashin kula da miji,ya katse tunaninsa sanda ya jiyo kiran salla a masallacin dake can farkon layinsu ya sanya silifas ya fice yana maìmaita abinda liman ke cewa kamar yadda annnabi ya horemu idan munji kiran salla


A can ya zauna ya jira sallar isha'i sannan ya dawo gidan,still gidan dai na nan kamar yadda ya barshi kowa na kulle a sashensa,ya dauki wayarsa ya kira nasiru ya gaya masa inda zaije ya samo masa masa da miyar ganye,cikin lokaci kadan saiga nasirun ya dawo ya amsa ya koma ciki yayi wanka ya sauya kayan bacci,ya zuba masar ya ci sai da ya qoshi sannan ya jawo computer💻 dinsa ya soma shigar da lissafinsa na yau,hankalinsa ya kasu kashi biyu,ko alama zaman gun ya gundireshi sabo da tsaftar gun bata masa ba,shigowar saluma ce ta saka shi tsai da abinda yake ,ba laifi salima indai ta bangaren qalqale jiki ne salima ta iya wannnan kam,yanzun ma ashirye take cikin dinkin lace baqine mai adon ja,ya sauke biron dake hannunsa


Mrs muhammad ce👑


📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻
[10/16, 12:42 PM] 💍🍬🛍Salma🛍🍬💍: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*wa yasan gobe?*.......
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*written by safiyya Abdullahi musa huguma*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺


▶3⃣6⃣


Ya sauke biron dake hannunsa🖍yana dan binta da kallo,tayi masa kyau sosai,fuskar sa ta dan sassauta daga dauretan da yayi ganin yadda take masa murmushi😃,gefansa ta zauna cikin salon kissa take cewa"barkanka da warhaka ranka ya dade"yadan janyota jikinsa yana cewa "barka kadai......sai yanzu aka ga damar zuwa yimin sannu da zuwan?"ta san tabe baki tace"girki na ne da zan taho daga dawowarka?" "Ko ba girkin ki bane ni ba mijinki bane?" "To ayi haquri ko" yace "ya wuce"ya maida kansa kan aikinsa tana tayashi da hira jifa jifa yana amsa mata


Samira ce ta shigo wannan karan harda sallama,abun arziqin nata yau yana da yawa🤔 don ba'ayi wari da.wari ba riga da zani ta saka na atamfa,kanta tsaye ta zauna daf da shi tana mata sannu da zuwa ba tare da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login