Showing 30001 words to 33000 words out of 130495 words
Chapter 11 - Wa Yasan Gobe Compelet Book by Safiya Abdullahi musa huguma
kowa yayi dif rabi'ah da takaici ya cikata tace ba rashin wayewa bane kowa dai da irin yanayinsa,ta sake tabe baki tace uhmm,ita kuwa fadila dariya ma ta bata sai daga qarshe ne taga kada suji ba dadi ta kurbi lemon da rabi'ah ta zuba mata
Bayan sun kammala momi tasa rabi'ah da sumayya suka gyare gurin suka kwashe kwanukan,suna shirin wucewa don su basu guri momi tace su dau iftihal su wuce da ita,falon yarage daga fadila aliyu samirah sai momi da uncle abba
Abba yayi gyaran murya yayi bismillah sannan ya kirawo sunan aliyu ya amsa masa"naam abba"ya dora "aliyyu girma yanzun ya hau kanka duk da a baya kwatan kwacin wannan girman ya taba hawa kanka kuma kayi namiji qoqari wajen riqeshi yadda ya kamata amma bai kai wannan ba,a yanzu dole na sake jaddada maka saboda zama ne da zaka yishi tsakanin iyalinka har su uku wanda ko ni mahaifinka banyi duk da komai tsarin Allah ne
Daga samirah har fadila babu wadda gabanta bai fadi ba har sai da samiran yabdaga kai ta kalli abban,uncle abba yaci gaba "lamarin mata ali sai da haquri kawaici da kuma jajircewa halitta ce su maau wuyar sha'ani amma idan ka duba Allah sai komai ya zo maka da sauqi ,aliyyu ina horarka da kaji tsoron Allah ka tsaida adalci tsakanin matanka duk wadda ka cuta wlh wlh sai allah ya bi mata haqqinta sai kuma ya tambayeka,kuma ko ni ban lamunci rashin adalci ba acikin gidanka ka riqe Allah ka kuma ji tsoronsa
Ya juyo gunsu fadila da kansu ke qasa kowa da abinda ke cikin zuciyarta yace "dukkaninku ina kallonku ne a matsayin 'ya 'yana na na cikina da na haifa nasihar da zan muku itace kuma ku ji tsoron Allah kuyi zamqn aure a matsayin ibada kuyi biyayya ga mijinku.ku kyautata zamantakewar ku domin kuwa shine muqullinku na shiga aljanna ko wuta idan kuka saba masa Allah ya tsare mu,magana ta biyu kuma na dakatar da shi ne daga gaya muku don inason na gaya muku ni da kaina ta hanyar da ta dace,nasan kowacce mace haka Allah ya halicceta da kishi kuma ba zaku so abokiyar zama ba a yanzu amma ba yanda muka iya da hukuncin ubangiji kuma aure rai ne da shi matuqar bai qare ba komai dadewar zamani sai an dawo anci gaba da yinsa to ina mai baku haquri a madadin aliyyu,mahaifiyar khadija(sunan iftihal na gsky haka abba ke kiranta yawancin lokuta)zata dawo dakun aurenta ina fata zaku hada kanku ku zauna lpy,samirah ta dago kanta a gigice tana fiddo da idanu wajeπ³tace"abba mai kake fada ne?dama da gaske aliyu yake da yafara zancen?" aliyyu ya juyo ya kalleta wani huci ya saki abba ya lura da yadda yanayinsa ya canza ya san yadda fishin aliyyu yake don haka ya danne shi,cikin tausasawa ya kalli samira yace ki kwantar da hankalinki yata insha Allahu ba zaku fuskanci rashin adalci ba daga gun aliyu ni kaina bazan lamunci hakan ba shiru tayi tana muzurai idonta ya kada yayi ja saboda ganin yadda aliyu ke gasa mata hara ra tamkar zai cinyeta danya,itakam fadila gabq daya jikinta ya saki tunaninta daya ta ina zata samu aliyyu bayan ga wasu na farautarshi ? Jin sunyi shiru dukkaninsu abba yace da momi"kina da magana momin yara?" Ta danyi murmushi tace" aikace komai abban yara,saidai nace aliyu kaji tsoron Allah kamar yadda abbanka yace sannan ku kuma Allah yayi muku albarka kuyi haquri kuma kuyi biyayya sai.kuci riba"suka amsa da amin banda samira da ta kasa furta komai sai tafasa da zuciyarta keyi,abban ya sake basu dama akan idan da mai magana ya yi,ba wadaa tace komai sai aliyu da yace"abba da momi na gode muku kuma insha Allah zaku sameni mai amfani da duk nasihar da kuka yimin zan zamo mai adalci da yardar Allah"Allah ya amince suka ce,fadila ta fito da kayan data taho musu da su ta dorawa abba nasa a gabansa sann ta dorawa momi nata
Duk da ranta babu dadi amma ta ji dadin yadda suka nuna jin dadinsu suka sa mata albarka,aliyyu kansa can qasan zuciyarsa yaji dadin hakan don shi mutum ne mai dake qaunar wanda ke kyatatawa iyayensa,haushi ya sake cika samira tayi dana sanin zuwan ta gidan yafi sau cikin carbi bata son taga wani yana yabo ko son fadila kwata kwata
Cikin mota ma kowa da irin zaren da yakr saqawa zuciyarsa shikam ya dake abinsa kamar bashi ya sanar da mata har biyu zai qara musu abokiyar zama ba tuqinsa kawai yake a nutse,fadila tata saqar na yadda zata juyo da hankalin aliyu take bata so kuma bazata so ace kishiyoyi har biyu su fuskanci raahin qauna da jituwa dake gudana tsakaninta da shi ba,samira kuwa wani mahaukacin kishi ne ke taso mata zuciyarta namata saqa da baqin zare,tana shirya mata irin mummunan matakin da ya kamata ta dauka abu guda ke taka mata burki idan ta tuno yadda aliyyu ya birkice mata da yanayin da ya sameta a daren farkonsu tasan har yanzu dafin na sukar zuciyarsa somin kuwa duk wani tanadin soyayya da sukayi wa juna tn daga ranar ya rushe,duk kuma waa qauna tata dake zuciyarsa wadda ta rage tuni ta rushe
Cikin satin komai ya fara kankama abubuwa suka cedewa baiwar Allah fadila ga zirga zirgar shirye shiryen fara zuwa aikinta ga kuma lamarin na dake mintsinin zuciyarta duk da shiryr shiryenta ya tafi da kaso.mafi tsoka daga damuwar dake cin xuciyarta,tuni tayi waya gidan an ma motocinta service daya tsohuwar tata ce tun ta gida aka sake mata fenti da wasu abubuwa sai ta tashi ta dawo sabuwa dal don tana qaunar motar bata son rabuwa da ita yanzu sai kuma wadda aliyyu ya sa musu a lefe wadda ta sam ira tuni ta dade da cin uban tata ta mora qawaye su ara suma su mora
Kira ta dinga samu daga su anty hauwa anty hafiza har da farida kowannan su nasiha ce da jan hankali ne nasa har farida ta so karayar mata da zuciya saidai tayi qoqari matuqa wajen nuna dakiya da mai da komai ba komai ba
πΊπΊπΊπΊπΊπΊπΊ
Wa yasan gobe?
βΆ2β£1β£
Samira kuwa abun nata sai ya zamto tamkar mai qaramin ciwon hauka kamar a kanta aka fara kishiya kasancewar ta samu gudun mawar zuga daga qawaye da yan uwa kala daban daban duk da wasu ba don Allah suke bata basuna baqinciki da rufin asirin kawai da take ciki ne(qalubale a garemu mata sai azo ayita baki shawara akan za'a miki kishiya ko wani harkar wani ahaka kamar mai sonki amma da zaki ga cikin zuciyarsa game da ke tsoronsa ma zaki koma ji,sanin haqiqanin mutum sai Allah,sai ki auna da hankali da Allah ya baki a matsayinki na mutum mai tunani)sai ta sake zama kamar zararriya ita kadai ma abangarenta sai ka jiyota tana bala'i tana zunduma ashariya(wa'iya zu billah)cikin satin baqi ta dinga yi kala daban daban kowanne da tasa guzuri da salon hudubar waccan ta shiga waccar ta fita
Tun Aliyu na zuba mata ido idan tana salon rashin mutuncinta da haukanta har sai da ya zamto idan tazo sai dai ta gajibda bugun sashen nasa ta juya da haukanta ta koma inda ta fito,tuni fadila tabgama tsarawa kanta yadda zata tafiyar da rayuwar aurenta ta gama tanadar komai,tana hango cewar itama fa maca ce tana da duk wani abu da da duk wata ya mave maiji da kanta ke taqamar tana da shi,tana da duk wasu qualities da ake buqatar mace da su kafin ta amsa sunan ta na mace,to me yayi saura banda itama ta shiga fagen a dama da ita?? Me zata jira banda ta shiga ta karbo aliyyunta? Ta gaji kuma lokaci yayi da take ganin ya kamata ace ta kasance da da shi ta gaji da dako da rainon soyayyarsa ita kadai
βββββββ
Biki ya zamto saura kwana uku wanda yayi dai dai da sauran kwanaki bakwai fadila ta soma zuwa aikinta
A ranar ne bayan sallar magariba aka shigo mata da akwatina set shida masu matuqar kyau maqarenda kaya nasiru yace mata inji maigida,ta jinjina kai ta rufe qofar sashen nata ta koma kan kujera ta zauna daya bayan daya ta budesu ta zubawa kayan ido duk budurin da ake sai yanzu zuciyarta ta tsinke hawaye suka soma zarya a kuncinta a hankali take sa yatsunta tana sharesu tabbasa an jarrabci rayuwarta da jarabta mai girma ta sani cewa son aliyu jarabta ce daga ubangiji acikin jininta yake kuma bata fatan Allah ya dandanawa wata mace kwatankwacin yadda take ji a zuciyarta,nan saman kujerar ta lafe tana hawaye a hankali take furta HASBUNALLAHU WA NI'IMAL WAKIL har taji zuciyarya ta soma sanyi
Haya niya da hargowa take jiyo wa maau qarfi suna karade filin gidan hakan ya sanya kukanta katsewa ta tashi kamar mai sanda ta isa window dinta da yake cikin balcony dinta ta yaye labulen ta riqeshi a hannunta,daga nan tana iya hango dukkq sararin gidan samira ce ke wannan hayaniyar cikin hargowa da babat tanajanyo akwatina irin wanda nasiru ya kawo.mata dazu daga part dinta daya bayan daya tana cillarwa anan tsakiyar filin gidan ko nauyinsu bata ji ,aliyyu na tsaye hannayensa harde a qirji ya zuba mata ido bai ko motsa ba
Sai da ta gama lodesu sanna tayi cikin gidan nata a fusace sai gata da gallon da ashana ta daga tana qoqarin bulbula musu fetur din da yake ciki sai a lokacin aliyyu yasa hannu ya fincikota baya a fusace ya nunata da dan yatsa yana cewa kul kada ki soma,ta dubeshi duk da ta tsorata da yanayinsa amma sai ta dake cikin bala'i take cewa" sai na qona aliyu sai na qona wallahi kayan fadar kishiyan wata tsiya ce,sai dai idan na qona idan ka so nima ka qona ni" ta sake zabura tayi kan kayan da nufin idar da niyyarta cikin qaraji da tsawa ya ambaci sunanta wadda sai da hantar cikinta ta kada amma sai ta waiwayo tace"ko kasheni zakayi ba zan fasa ba" tadai sake nufar kayan cikin azama a karo na uku,cikin fusata yasa hannu ya janyota baya harsai da ta zube warwas a gun tamkar ya bita ya tattaka haka yake ji,don da namiji ne ya masa haka to yanajin ba shakka sai ya nuna masa qwarin qwanjinsa
Ta sani cewa idan taci gaba da abunda take hukuncin da zai yanke mata ba mai sauqi bane hakan yasa tana daga zaunan ta hau borin kunya cikin surutai da maganganu marasa kan gado daga baya ma da taga ya qi kulata sai ta fashe da kuka
Ko kallo bata isheshi ba ya dinga siban akwatunan bibbiyu bibbiyu ya shigewa da au bangarensa yana gamawa ya rufe qofarsa ya barta a nan,data waiga ta waiga taga ba kowa ba wanda ya gansu sai ta goge idonta ta miqe tana kade zaninta tana wa allah godiya da ba wanda yaga abinda ya faru tana yi tana tsinewa hannatu qanwarta gashinan ta jawo mata asarar akwatinan ma dungurun gum dan ita ta bata shawarar tayi haka
A falon sa ya zube ya dafe kansa hannu bibbiyu yana tsananin jimanta al'amarin to haka mata suke ne basu da hangen nesa ya jima a haka sannan ya tuno bai ma shiga bangaren dayar ba kamar yadda yake ce mata a ransa"itama idan ka shiga wataqila haukan da zata yi maka kenan"wata zuciyar ke gaya masa,ba yadda ka iya tunda itama aqarqashinka take kuma ka shigarwa 'yar uwarta indai adalcin kake son yin
Da sallama ya shiga ta amsa a sanyaye tana zaune ne kan kujera hijabin da tasa ta budewa masu shigo da kaya har yanzu shine a jikinta saidai sabanin da yanzu akwatinan a rufe suke,a fakaice yake dan nazarin falon komai tsaf yake cike da tsafta da qamshi hakanan komai a killace yake a muhallinsa da kyawunsa kamar yau aka jerashi sabanin falon samira da komai ya fita hayyacinsa saboda rashin kulawa duk da dama tsadar kayan ma ba daya bane don iyayenta basu da qarfin iyayen fadilan,kanta na qasa ta dam zamo daga kan kujerar tace ina wuni? Duk da bata sa ran masawarsa ba don bai taba amsa gaisuwarta ba ga mamakinta wannan karon sai taji yace "lpy ga kaya nan abinda babu ko baiyi ba sai ki yi maga ko ki rubuta ta girgiza kai tana cewaπ komai yayi mun gode Allah ya qara arziqi" ya lumshe idanunsa don har zuciyarsa ya ji dadin addu'ar "madalla" yace ya zaro bandir na dubu dubu guda uku ya dora saman akwatinan ya juya ya fice sai yaji wani sauqi na radadin da zuciyarsa ke masa addu'ar ta faranta ransa don tunda yake bai taba samun kwatan kwacin wannan ba daga bakin wani abu wai iyali ba
Muje zuwa yanzu aka soma
Mrs muhammad
πππβπ»βπ»βπ»βπ»
12:45 pm 03/11/1437
πΊπΊπΊπΊπΊπΊπΊ
WA YASAN GOBE?
πΊπΊπΊπΊπΊπΊπΊ
πΊπΊπΊπΊπΊπΊπΊ
Written by safiyya Abdullahi musa huguma
πΊπΊπΊπΊπΊπΊπΊ
βΆ2β£2β£
Ana ya gobe daurin aure su anty hafiza anty hauwa farida sumayya rabi'ah har da rahama suka zo wa fadila,farida ta zube dinkunan da fadila ta bayar aka mata sunyi matuqar kyau da gaske duk da tana da sababbin din kunan ma da bata taba sa su ba,kala ashirin farida ta zabar mata aka dinko su lace biyar atamfa biyar shadda biyar material ma biyar ne,anty hafiza ce ta taho mata da mai gyaran jiki gashi da lalle takanas sai hade haden magunguna namu irin na mata imgantattun na 'ya'yan itace,anty hauwa sai dariya take tana cewa o'o'o fadila 'yar gata to ai ko kece amaryar sai haka,sai dai tayi dariya ta sunkuyar da kanta qasa cike da kunyarnan ta ta,anty hauwa ta zuge jakarta ya fito da littattafai tace ga saqon momi nan,hannu biyu tasa ta amsa tana godiya litttafai ne kusan goma na addu'o'ine da kuma gyara zamantakewar aure,
Zuwansun ya sake debe mata kewa taji dadi nan suka fara tsara yadda za su gudanar da yinin su na gobe wanda ko wacce mace da za'a qarawa abokiyar zama ke gudanarwa,wuni akai ana qalqale mata jiki yayin da su rabi'ah sumayya da rahama suka zage wajen qal canzawa gidan fasali,sune canza labulaye canza carfet goge goge da ahare share duk da komai na fadila tsaf yake sai abinda ba'a rasa ba,cikin qanqanin lokaci kuwa gidan nata ya canza kamar ba shi ba,hatta qamshinsa sai da aka canza kalarsa ya zama na musamman abinka da diyar bare bari
Rahama ke tambayar fadila samirah fa?fadila tace wlh tun safe dai naji tashin motarta amma ban sani ba ko qunshin itama ta tafi "Allah ya kyauta inji anty hauwa ,bayan isha'i komai ya kammala anty hauwa tace zasu wuce sai gobe kuma idan Allah ya kaimu anty hafiza da yake kwana za suyi ita da farida tace"dama kwanciyar ku muka yi maman kausar wlh ,a'ah hafiza na bar yara su daya a gida daga su sai Abbansu wunin yau fa duka?"anty hafiza tace to don Allah ga laila(mai qunshin da ta dauko)ku sauke min ita a dorayi
Suna kan gado duk su ukun sunyi shirin yin bacci hafiza ta zubawa ido dake qoqarin shafa addu'a tace wai yau wa kuka barwa mijin ne?samira fa bata dawo gidannan ba haka kuke masa?"cikikin son rufe sirrinta da son gyara rayuwar aurenta ba tare da taimakon kowa ba tace "girkin samira ne anty bana son neman rigima da tashin hankali me zani in masa tunda ba girkina bane?salin inje mu raba dai abun fada?"daga haka suka qyale zancan
βββββββ
Washegarin aka zo akawa salima jeranta da yake aikin maza ne nan da nan yayi sauri amma akwai wasu daga cikin yan uwanta mata da suka zo da su,girkinsu su fadila sukayi sosai suka zuzzuba a manyan warmers suka aikawa yan uwan salima da wani wasu kuma suka barshi nan cikin kitchen dinta saboda mutane yan uwa da maqota da keta zuwa Allah ya sanya alkhairi har a lokacin sashin samira na kuelle ne alamar bata dawo ba kenan hakan yasa kowa ya shigo gun fadila yake yowa idan suka tambayeta samira sai tace ta tafi gidan qunshi
Ba qaramin kyau fadila ta zuba ba tamakar ita ce amaryar daga wayewar garin zuwa yanzu ta sanya kaya kusan kala takwas kenan har harabar gidan jama'ace don babu laifi yan taru duk da ba wanda suka gayyata
ππππ
Qarfe sha daya da rabi na rana aka daura auren Aliyyu salim maitama da salima tukur Abubakar,kasancewar gidansu salima na na unguwar dake daura da g.r.a ne yasa yanuwan fadila na jiki da suka halacci daurin auren suka dinga zuwa ana gaisawa suna tafiya ciki kuwa harda abbanta da muhammad da ya ahmad taji dadin zuwan hakan kuma ya faranta mata ranta don tun da aka daura aurenta rabonta da taga abban nata kuma shima yaune zuwansa na farko gidan nata,ya mata nasiha sosai da ta qara mata nutsuwa ta kuma sata kuka ta sake tabbatar da cewa ba qaramin zumunci bane tsakanin abban nata da uncle abba mahaifin aliyyu tabbas babu abinda zata wa abban ta aduniyar nan fiye da ta jure zaman aure da aliyyu,anan suka bar mata muhammad zuwa yamma abban zai turo a daukeshi
Qarfe sha biyu da rabi ta sake wanka ta sanya wani Swiss lace pink ne mai dan turuwa kadan sai kore aka masa da ratsin silver din zare sai manyan dutsina masu walqiya sarqarta abun hannu da dankunne mayafi da takalmi duk silver ne dinkin riga da skert aka mata skert din eight pieces ya bude daga qasa sosai ,yayi matuqar karbarta ya haska chaculet din fatarta gashinta mai tsawo da santsi da baqi ya sha parking da pink and green din ribbom sai ya kwanta a bayanta sai sheqi yake tayi daurinta das wanda ya ta qasansa gashin nata ya fito,ta dauki turare tana fesawa taji ana kiranta maqotanta sun shigo kuma wasu na nemanta a harabar gidan saurin da take yasa ta manta bata dauki mayafi ba,suka gaisa da baqin tasa aka kawo.musu abinci sannan ta qarasa harabar gidan, nasiru ne da wasu mutane suke neman gun jibge abincin da ake ta shigowa da su,ta nuna musu store dinsu dake harabar gidan ta farko kusa da parking space
Tana shirin shigewa ciki motocin suka soma danno kai suna parking daya bayan daya,bata fuskanci su waye a ciki ba sai da suka cika harabar gun dukkaninsu cikin fararen