Showing 54001 words to 57000 words out of 130495 words
Chapter 19 - Wa Yasan Gobe Compelet Book by Safiya Abdullahi musa huguma
gida na kullum dake kan matar aure baya ga wadanda ka iya taso mata wadanda bata tsara da su ba a rana,ku dinga adalci kuna hukunci na gaskiya,mu fahimci juna don Allah wannan shi zaisa ni daku muci gaba da jin dadin alaqar dake tsakaninmu,wlh akwai abubuwa masu yawa da muhimmanci a rayuwata da nake yi kulluma da kafin fara muku rubutu amma a yanzu sun gagareni yi saboda rubutunku,na sani harka ta mutane sai kayi haquri tunda yadda muka banbanta a halitta haka Allah s.w.a ya ban banta mu a halaye da dabi'u,na gode Allah yasa mu dace๐๐ป๐๐ป
Na biyu kuma masu ganin abunda aliyyu yake yayi yawa kada kusa gaggawa a lamarinku kuma kada ku manta shi haquri shine jagoran kafatanin lamuran mu na duniya bare haquri ga 'ya mace kuma acikin gidan aurenta hanyar shiga aljannarta riba ce ba kadan ba,ina so ne yan uwana mata muyi koyi da halinta koda cewa ba irin auren ta kikayi ba amma nasan baza'a rasa matsala daya ko biyu da kike iya fuskanta ba daga mai gida wadda shigen halin da aliyyu ya taba nunawa fadila ne to ga yadda ta shanyeta ga kuma ribar da ta samu,na godewa masoyana gana daya ,Allah yayi mana sakamako agidan aljanna ya hadamu dukkanmu a cikinta in kuma ci gaba da zama marubuciyarku ta gidan aljanna ๐๐๐๐๐๐ป
Mrs muhammad din[truncated by WhatsApp]
4:50 pm 23/8/2016
๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ
*WA YASAN GOBE?..*
๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ
๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ
*written by safiyya Abdullahi musa huguma*
๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ
*part 2*
1โฃ1โฃ&1โฃ2โฃ
Powder kawai ta shafa a fuskarta ta shafawa kyawawan labbanta lip glosses,atamfa ta zaro cikin kayan nata dinkin doguwar riga ne mai umbrella ta bude sosai an mata dogon hannu simple style ne,ta ware dan madaidaicin mayafinta ta yafa shi har saman kanta kamar yadda ta saba yafenta sannan ta fesa turare ta fito
Yana tsaye a wajen motar yana amsar calling yayin da salima ke tsaye kusa da shi hannunta harde a qirjinta tayi kicin kicin da fusaka,sallama fadila tayi mata sai taga ta dauke kai don haka sai ta ja tunga itama tayi banza da ita,ya gama amsar kiran ya kashe wayar hannunsa na kan mabudin motar salima ta kalleshi tace"please dear"kai ya gyada yana cewa"dont mind" ya bude gidan gaba kusa da kujerar mai tuqi ya zauna ta bude baya itama ta shige,nasiru ya gaida ta cikin girmamawa a mutunce ta amsa sannan ya tada motar suka fice
Tafiya ce kamar ta kurame sai ka rantse bata cikin motar sai shi da nasirunne ke hira jefi jefi galibi ma bai wuce zancan kasuwa,idanunta na kan titi yayin da zuciyarta ta lula duniyar tunani
A bakin get suka dakata bayan mai gadin ya dage masu get aliyyu yasa nasiru yayi masa magana ya rufe ba shigowa za suyi ba,fadila ta tabe baki cikin ranta tana gulmar aliyyun,nasiru ya gyara parking din sannan ya fice daga cikin motar,fadila ta sa hannunta a kan mabudi zata fice "twenty minutes"haka ya fada cikin carelessness,ba abunda tace da shi tayi ficewarta "ko baka gaya min ba ai na sani uban masu tsari da qa'ida na duniya๐"tayi zancan cikin zuciyarta
Da yake takwas na dare ma ta dan gota gidan ya samu sararawa daga cincirundon 'yan barka mutum hudu ta tarar Amina da mariya qannan mubarak ne sai maqociyarta guda daya sai kuma wata dattijuwa inna jummai wadda mahaifiyar mubarak ta kawo mata ita saboda kula da mai jegon da kuma jaririyar,alokacin da ta shiga ma tana kitchen tana kwashe tuwon da ta yiwa faridan,fadila nata qyalqyala dariya ganin inna jummai nata loda tuwon a flask tana ce mata"inna zanso naga dambarwar ku kam da farida don ba abincin da taqi jini irin tuwo,dama dai ni kika baiwa"innan da yake macace mai kirki da saurin sabo da jama'a tace"ai duk qinta kuwa da tuwo yanzu ya zama abokinta dole ta cishi tunda jego ya zo"
Tayi sallama ta shiga falon faridan dukkaninsu suka amsa mata cikin fara'a suna dariyar hirar fadilan da inna jummai,farida kam ture kayan jarirai dake gefanta take tana cewa sister taho nan daya hannun nata kuma cup ne cike da tea tana sha sai hada gumi take inna kuma taqi ma a kunna fanka bare a.c saboda wai jego faridan zatayi irin na da,fadilan ta qaraso tana cewa "๐คsister farida mai tsokana da yawon gidan qawaye yau gata dq baby" dariya ta basu dukkaninsu harda faridan,idanu fadila ta baza tana neman baby tace nifa baku nazo gani ba wlh ina 'yata ku bani ita naji duminta"yarinyar na hannun maqociyar ta ta nannade cikin farin shawul mai taushi ta miqe tana miqawa fadila ita hadi da yi misu sallama ta ajjiyewa faridan 1000 kudin barka ta mata godiya ita kuma ta fice
Ta kammala shanye tea din tas ta dire cup din tana kallon fadila tace "sister da fa har nayi fushi kece ta farko da kika fara sanin haihuwarnan baya ga abbanta amma sai yanzu zaki zo mana tun dazu baby ke son ganin mummynta bata zoba sai da aka rigata gane mata ita" "hmmm lallai yarinyarnan kukan dadi fa kike da yaya yanzun ma ya barni tare ma fa muke"cikin zolaya wadda attitude din farida ne tun usulinta tace "wow kice har an fara boyonki lallai soyayya ruwan zuma"fadila ta harareta tace "wlh badan kin mun abun kaiba kin bani baby mai kama da ni ba da sai na bubbuge bakinki"su amina suka qyalqyale da dariya sannan suka miqe suka ce bari dai mu baku guri kada a buge mana anti a gabammu"dariyar suka bawa fadila su kuma suka fice kitchen gun inna jummai
Fadila ta sake zubawa yarinyar ido tubarkallah masha Allah qatotuwa da ita lallai kam wannan photo copy dinsu ce ta kalli farida tace sister sannu"farida ta ya da kai gefe tana tuno wuyar da ta sha"hmmm ke dai bari sister ansha gwagwarmaya ni kam dan ba qara"fadila ta sake rungume yarinyar a qirjinta tana sake jin qaunarta na shigarta bata qi ace tata bace,ta saki dariya tace "yanzun fa aka fara farida me akai da maza daga ihu daya sai kuma murya ta dashe?๐"ta qarashe ta sigar tsokana yau dai ta maida raddin tarin tsokana irin na farida da take mata ko yaushe,ko da can dama fadila Allah ya zuba mata son yara,sanda suka tashi muhammad ne kawai yaro a gidansu to har gidan maqofta take shiga dauko yara duk da yanayin unguwarsu irin unguwan nin nan ne da ba ruwa na da kai kowa na qulle shi da ahalinsa cikin gida amma haka fadila ke shiga ta taho da su,miskila ce ako ina magana bata dada ta da qasa ba amma banda kan yara hakanan zaka ga ta sasu a gaba suna ta wasansu,farida kam dama idan taga dama idan suka zo neman anty fadila sai ta korasu tace bata nan zasu zo su dameta ne
Farida ta girgiza kai da sauri tana juya ido tace "kai sister is hardly in sake ko zan qara sai after five to ten years,nikam na barmiki ki taba kiji"dariya ma ta bata ganin duk yadda tayi laushi duk rashin tsoro da dakiya irin na farida,murmushi fadila tayi tana ci gaba da kallon yarinyar tayi kissing dinta agoshi,"ina aliyyu ne sister?"๐af yana waje " farida ta miqe daga kashingidar da tayi tace "kada dai kice mun kuna tare yaushe ya aliyyu boss ya fara kai matarsa unguwa"fadila tace"saboda ya bata min ya fara ta kaina yau kina gani fa kamar gidqn nan yace min wai twenty minutes?"farida tace "wlh am serious ya aliyyu ko salima matarsa ta farko bai taba kaita wata unguwa ba idan ba monthly shopping naku ba(farida ta fi fadila sanin halinsa ne kasancewar tq fita shiga jama'a hakanan ta fita zuwa gidan uncle abba)kuma shine kika barshi a waje ga sitting room nan"fadila ta tabe baki tace "oho masa har get malam salisu ya bude masa yace a maida arufe ba shigowa za su yi ba" "gashi mubarak yanzu ya fita maida hajiyarshi gida da ya shigo da shi"farida ta fada tana lallatsa wayarta,"zancan kike so ki bar mubarak kada ki taso shi idan da rabon zasu hadu zasu hadun don ko mubarak ya zo idan bai ra'ayi ba bazai shigo din ba"
Minti goma sha biyar ta shude suna ta hirarsu farida na cin tuwonta a sake kasancewar su mariya sun bar masu dakin,dahiru yaron dake wa farida aike aike ne ya shigo karbar abincinsa bayan ya miqawa inna jummai kwanon ya tsaya bakim falon faridan yace"anty wai baquwa ta fito za su tafi"fadila ta bata rai don tasan aliyyu ne yayi aiken kuma aqa'ida tana da sauran minti biyar
Ranta a bace bayan ta bude camera din wayarta ta yiwa baby pic ta sake sumbatarta ta ajjiyeta gefan faridan ta dubeta tace sister zan dawo insha Allah me kikeson na kawo miki"murmushi tayi tace"sister fadila nayi missing din wainar shinkafarkin nan da kike mawa dady,idan zan sameta inaso"dariya fadilan tayi saboda ta tuna mata lokacin da suna gidan idan tayi insha Allahu kan ta gama shiryawa Abban a warmer taci na ci kuma ta bi ta har falon abban suci tare da shi tana hara rarta tana komai amma sai tayi biris,"insha Allah kamar kinci waina ta kin gama"sukayi sallama tamkar kada su rabu
Tana fita taga motar mubarak fake kusa da tasu shi dinne kuwa da alam yanzun ya iso don lokacin suke gaisawa da aliyyun ta qaraso suka gaisa ya juya yayi cikin gida yana cewa bari ya dauko ma aliyyun babyn ,hannu biyu yasa ya dauki babin mubarak na gyara masa riqon don da gani bai iya ba,ya riqe ta sosai yana kallinta hadi da fadin"masha Allahu la quwwata illa billah"(yan uwa gaka annabi ya horemu da fada a duk lokacin da muka ga wani abu da ya qayatar da mu to ko kana da kambun baka bazai kama abun ba domin wasu ma auna da shi amma basu san suna da shi din ba,sai kaga abu kayita kodashi ba tare da ka fadi hakan ba daga qarshe sai wani ibtila'i ya saukarwa abun ya lalace don Allah mu kula da wannan)
Fadila na satar kallonsa kadan kadan tana kallon yadda ya zubawa yarinyar ido ya lumshe idanunsa daga baya ya budesu ya sumbaci goshin yarinyar sannan ya miqawa mubarak ita yana sake cewa Allah yayi mata albarka,ya amsheta sukai sallama ya shige gida da babyn
Aliyyu ya yafito qasimu dake fitowa fitowa daga gidan hannunsa da robar abinci qasimu ya qaraso hadi da rusunawa aliyyu ya amshi bandir din kudin dake hannun nasiru ya miqawa qasimu yace ka kaiwa maman baby ya zaro 1000 daga aljuhun trouser dinsa ya bashi ya shige motar yabar qasimu nata zuba godiya yare da komawa cikin gidan don sada saqon aliyyu ya bawa nasiru umarni ya tada motar suka bar layin fadila nata satar kallonsa don kiwa dubu dari ce ya bayar a kaiwa babyn
Mrs muhammad ce ๐
๐๐๐โ๐ปโ๐ปโ๐ปโ๐ป
2:08 pm. 24/08/2016
๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ
WA YASAN GOBE?..
๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ
๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ
*written by masoyiyar buk din wayasan gone..*
๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ
*Part 2*
1โฃ3โฃ&1โฃ4โฃ
Fadila tacigaba da sake2 azuciyarta bata ankaraba taji ana bude get tana dago kaitaga harsun iso gida ashe,parking space ya nufa ya kashe motar,fadila dakekokarin bude motar setaji ya kulle motan ta waiwayo tadubesa suka hada ido tayi saurin dauke kanta zuwa gefe,shiko gogon sebinta ya ke da kallo can yace wai meye kiketa wani bata rai tamasa banza yacigaba damagana ,inatambayarki,kaikidanayine nayi lefi koso kike danabarki kikwana? nan ma shiru yaharzuka cikin tsawa yace wai badakenake maganaba salan wulakanci,
Se asannan fadila tadago kai da fuska cike da hawaye tace wulakanci? wulakanci yawuce wulakantani dakakeyi Wanda haka har matanka suka sami damar gorantamun,Aliyu nayi nadamar aurenka auren bakinciki Inatabbatarma dabadan mahaifinaba dana dade dabarin gidan nan,cikin kuka takemaganar yayin da Aliyun yatsinci kansa da tausayinta Yakuma kasa cewa kome illa binta da kallo.
Fadila tacigaba kodan matanka da ni ba irin su naso nayi kishi dasuba,naso ahadani da wayanda suka San mesukeyi๐ญ bawadannan da kake kallo amataba nibanga mata anan ba kuma duk ajin naka akan salima da samera yakare ragowar wasu,cikin bacin rai yadakamata tsawa,itako ta dannan motar tabude tafita da gudu tanufi sa shinta,tana shiga tafada kujera setaji ya akayi tayi wadannan magana,setaji kamar bats kyautaba cankuma wani bangaren zuciyarta tacemata garadakika masa haka yasan fa kinsan mekikeyi kuma yasan badan shikike gidanba Dan biyayyar iyayankine,tamike tashiga toilet tayi alwala ta fito ta tada sallar isha dabata samu tayiba.
Can Aliyu kuma kasa futa yayi daga motar jikinsa duk yamutu zuciyarsa ta cunkushe abinda yafi damunsa shine kalmanta datayi kansu samira da salima domin yakaratunawa da yanda yasamu samira adarensu nafarko,sannan Salima bayan rabuwarsu itama ba agida tayi rayuwaba,yadafe kansa karo na farko da naga A S metama na kwalla daya nazurarowa daya bayadaya๐ฐ yace inna lillahi wa inna ilaihirraji un.tabbas jidakai bekama ceniba domin ina tare da wadanda basu cancanci suzama iyayan yayanaba,gashi inakallo se haihuwa ake Wanda akai bikinmu tare duk sun haihu,su naji kowacce tace batashiryaba itakuma wanan yarinyar banashiga harkanta,gashi du k ta gane kome,Aliyu yacigaba da hawaye yana maibakkincikin abubuwa kala kala yadaure ya fita daga mortar jiki akasalance yanufi bangaransa yanashiga ya kulle kofar yabar makullin ajiki sabida bayasan ganin kowa domin koda sunzo sunyi amfani da makullinsu bazebuduba.yashige bedroom yafada gado yacigaba da tunani aranar dai Aliyu beruntsaba Dan maganganun fadila kemasa yawo akwalkwaluwarsa,
Itako fadila cikin nishadi tayi barci domin tafidda wani tabo da kedamun zuciyarta.
*amun afuwa Mrs Muhammad nayi muki shishshigi amma haka mukeson buk yadawo munakara mikamiki godiya dayabawa Allah yakara basira kidora saga inda natsaya domin zansamu goyon bays amma kitambayi friends sunyarda kidora๐*bye nabarki Lfy Wanda sukaji haushi suyafemin kar azagen nima wlh soyayyar buk din yasa nayi๐๐ป
Ba Mrs Muhammad bace๐
๐๐๐โ๐ปโ๐ปโ๐ปโ๐ป
[10/16, 1:46 PM] ๐๐ฌ๐Salma๐๐ฌ๐: ๏ฟผ๐บ๏ฟผ๐บ๏ฟผ๐บ๏ฟผ๐บ๏ฟผ๐บ๏ฟผ๐บ๏ฟผ๐บ
*WA YASAN GOBE?..*
๏ฟผ๐บ๏ฟผ๐บ๏ฟผ๐บ๏ฟผ๐บ๏ฟผ๐บ๏ฟผ๐บ๏ฟผ๐บ
๏ฟผ๐บ๏ฟผ๐บ๏ฟผ๐บ๏ฟผ๐บ๏ฟผ๐บ๏ฟผ๐บ๏ฟผ๐บ
*written by safiyya Abdullahi musa huguma*
๏ฟผ๐บ๏ฟผ๐บ๏ฟผ๐บ๏ฟผ๐บ๏ฟผ๐บ๏ฟผ๐บ๏ฟผ๐บ
*part 2*
1โฃ5โฃ&1โฃ6โฃ
Qarfe tara fadila tayi wa iftihal wanka itama ta shirya cikin riga da skert na atamfa a cikin qana nun kayanta ta cirowa iftihal wasu riga da skert dama sun mata kadan jajayene in and top ta raba mata gashinta gida biyu ta tufke mata da ribbon sosai iftihal tayi kyau suka yi break sannan ta soma gyara part dinta kafin ta isa ga na aliyyu don duty dinta ne duk inda ta shiga yarinyar na biye da ita ita ala dole sai ta taya ta aiki sai da fadila ta bata mopping din kayan kallo sanna ta rabu da ita
Fadila ta fito tana goge hannunta da duster bayan ta gama aikin ta iftihal dake ta fama da chocolate tace "anty ina daddy na?"murmushi fadila tayi ta kama kumatunta tace"kwantar da hankalinki 'yar daddy yanzu zaki ga daddy shiga daki bakin gado ki dauko min hijabina"da gudu kuwa ta shiga sai gata da shi a hannu ruwan madara ne iya qugu wanda ya shiga da atamfar jikinta sosai,ta kama hannun iftihal din bayan sun rufe qofan
Tana sa kai falon taji hayaniyar sama sama muryar salima ke a sama,tana tsaye hannayenta harde saman qirji kan aliyyu shi kuma na zaune kan kujera yana sanye da kayan bacci na maza ruwan madara shima hannun nasa harde a qirjinsa๏ฟผ๐ ,shigowar su yasa salima yin dif daga maganar da take yi din gami da sakin fuskarta daga tsukewar da tayi tana dan binsu da kallo(salima akwai duniyanci)sam bata lura da iftihal ba da suka shigo tare sai da yarinyar ta zame hannunta daga na fadila wadda ta shige kitchen ta ruga a guje tayi gun daddynta tana cewa"daddyyyy daddyyyy...."kamar yadda ta saba ta durqusa a agabansa kafin ta haye cinyarsa tana cewa"morning daddy sabahul khair",murmushi ne sosai dauke a fuskarsa wanda bai bayyanar da haqora๏ฟผ๐yasa hannu ya dagota yana kallonta yace"sabahun nurrrr my lovely khadija"tayi tsalle ta dane cinyarsa abinta tana wasa da maballan gaban rigar baccinsa tana cewa"daddy tunnjiya nazo da daddare kaqi zuwa na ganka" "wonderful,anan kika kwana ke da wa?""ni da anty fadila tare ma yanzu muka taho"ya daga kansa yana nemanta da idanunsa sai dai tuni ta jima a kitchen bata a gun sai salima dake tsaye ta zubawa 'yar tata ido
Kallonta take tana jin wani alfahari na shigarta tana godewa Allah da bai bata damar rasata ba,wani dadi ne ke cikata ganin gudan jininta ita da halitta mafi soyuwa a gareta wato Aliyyu salim Abdallah maitama,tabbas iftihal abar alfaharinta ce yarinyar bata debo kammaninta ba ko kusa babu wani abu nata data dauko illa farar fata wadda aliyun ma na da ita,kowa ya ganta ya san jinin su ce family din alhaji salim Abdallah maitama ce jininsu ce
Ta dawo daga duniyar tunaninta hadi da miqawa iftihal din hannu alamar ta taho sanda suka hada ido fuskar salima dauke da murmushi,da taga kamar yarinyar bata fahimta ba sai tace"come on baby na come on my dear " yarinyar ta noqe kafada tayi luf jikin mahaifinta kamar mai tsoron ta babu sabo ko kusa tsakaninsu,wani kishi ya kama salima don taga yadda suka shigo da fadila yarinyar a sake take kana ganinsu kasan akwai sabo mai yawa tsakaninsu
Ta sake gwada sa'arta ta miqa mata hannunkaro na biyu tana sake cewa"come on mana mai dear kin manta mominki ne iftihal? Me yasa baki zo guna kin kwana ba ina da chocolate da biscuit da yawa da zan baki"ta sake noqe kafada tace "um um nafison na kwana gun anty fadila she's nice like daddy"sai salima ta maida hannunta ta rungume cikin jin haushi
Aliyyu na ankare amma yayi kamar baiga abinda ke faruwa ba,sai da yaji tana jan qwafa sannan ya tanka mata"duk uwar da bata yi showing mercy akan yaronta ba tayi abandoning duk wasu duty nata akansa no need to deceive her self akan shi zai iya jin qanta ya kuma ji tausayinta"idanunta sun kada sunyi ja kadan take jira ta fara malalar da hawaye tace"aliyyu abinda ya wuce ya riga ya wuce please"ta juya cikin zafin nama ta bar part din nasa kamar zata rushe da kuka
๏ฟผ๐ฑ๏ฟผ๐ฑ๏ฟผ๐ฑ๏ฟผ๐ฑ๏ฟผ๐ฑ
*TUNA BAYA*๐๐ผ
๐ฑ๐ฑ๐ฑ๐ฑ๐ฑ
Aliyyu da salima