Showing 45001 words to 48000 words out of 130495 words

Chapter 16 - Wa Yasan Gobe Compelet Book by Safiya Abdullahi musa huguma

ta nuna ma ta san da zaman salima ba agun,ya dan saki fuska bayan ya ja yatsun hannunta da nashi zara zaran yatsun yace"bana amsawa tunda kema sai yanzu" "bana shishshigi ne sweet kuma bana son maiyi shi yasa"ya dade da haddace wannnan kalma daga bakin samiran,don haka ya mele baki gefe sannan yace"lallaikam,da kun bani babies ai da sai nace kusha zamanku ni kuma insha hira da yara na ko?"


"Nikam ai na riga nabada tawa baby din"cewar salima"no she is belongs to momy,u already know...sabuwa nake so"cikin shagwaba ta dan bata rai sannan tace"haihuwa is not easy dear"samira sai ta tabe baki hadi da cewa"mukam ai ba yanzu ba,tunda sauran quruciyata🤔"aliyyu ya jawo ragowar takardunsa yaci gab da rubuce rubucensa ,kowacce yasan inda tasa gaba dama salima d tasu ai tun shekarun baya,shikam idan da abunda ya rage masa yanzu shine tara family babba


Cikin kwanakin fadika ta watsar da duk wata harka data danganci aliyun ta koma rayuwarta irin ta da,idan gari ya waye tayi ayyukanta na gida ta fice office sai ta dawo tan dawowa ta shige to sai washegari idan ta gaji sai fa kira farida ummi ko anty hafiza su sha hirarsu,ko muhammad yazo mata su wuni tare abinsu


Gaba dayan bangaren ya fita daga ran aliyyun saboda tsabar kacamewar da yayi,ko ina ba kyawun gani a hargitse,ranar da salima ta fita daga girki yaga tana shirin kulle sashen ta wuce nata sashen,cikin takaici ya kalleta ganin bata da niyyar kawar da ko cup din da ta hada masa tea bare akai ga batun gyara "jimana!" Yace da ita a zafafe ta dawo tace gani"bai ko kalleta ba ya daga intercom ya kira sashen samira ,sai da ta qara wasu mintina kana ta iso hakan ya sake hassala shi,ya dubesu cikin bacin rai yace


"Anya kuwa ky mata ne cikakku?ba ko wani jinsin bane ku?"a mamakance suka dago suna kallonsa,"kamar ya?"inji samira,da hannunsa ya soma yi musu nuni da falon suna binsa su kuma da kallo,"ku duba....dubi......haka ya kamata ace ya kasance?haka sauran mata suke barin turakar mazajensu?....abun naku ba ya yi yawa na lira ba hankali a ciki,ba tsafta ba iya kula da miji?kuma ni kuna son kyautatawa daga gareni?....it cant abun yayi yawa na gaji da tolerating bad attitude dinku....👉as from today ya zama dole a kanku kowacce kafin ta bar nan ta tabbatar ta gyara duk inda ya kamata ba ruwana da qazantarku ruwanku ne ku gyara naku ko ku barshi haka is not my own business.....


Ya suri briefcase dinsa ya fice,da kanshi yau zaiyi driving kasancewar nasiru baya nan ya tafi ganin gida ,ya juya kan motar ya danne horn yana jira a bude masa,ta kalli gilashin mudubin dake gefansa da niyyar gyara zamansa don ganin wanda kebin bayansa sai yaga wata motan na jira ya fita itama ta fita,ya duba sosai sai ya hangota zaune hannun ta saman sitiyarin fuskarta tayi fresh cikin safiyar,agogon dake daure a tsintsiyar hannunta take kallo da alama ta kusa maka rane don sai yatsina fuskarta take,material ne ajikintan yellow mai adon coffee,ba makeup ko kadan a fuskarta banda powder data shafawa soft chocolate skin dinta,sai lips balm data shafawa lips dinta sirara masu taushi,tayi lullubinta na mutunci har saman ka,ya dan tabe baki ya dauke kai itakam bata san ma yana yi ba,duk da ta ganshin


Ayimin afuwa kasancewar yau ina da uziri irin wanda ke kama ko wanne irin dan adam na turo muku shi late kuma ba yawa amma zamu hadu insha Allah,ina godiya a gareku👏🏻👏🏻


Mrs muhammad ce


📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻
[10/16, 12:42 PM] 💍🍬🛍Salma🛍🍬💍: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*wa yasan gobe?......*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*written by safiyya Abdullahi musa huguma*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺




3⃣7⃣~3⃣8⃣


Fisgar motar yayi ya ficee daga gidan sannu sannu take binsa a baya har suka bar cikin layin suka hau babban titi,yana hangota ta qarawa motar gudu tayi over taking nasa ta wuce shi ba tara da ta dubi koda sashen sa ba,ya daga idanunsa yabi motar da kallo yana dan gyada kai cike da mamaki da jin izza shi zata nuna wa iyawa da qwarewar sarrafa mota?,yaushe ma ta fara kama sitiyarin


Wani girman kai ne ya kamashi,ya qarawa motar shi speed cike da qwarewa da gwaninta shima ya mata over taking,ta lura sarai da shi amma sai ka rantse da Allah batasan da wanzuwarsa akan titin ba,ta dan cije lebenta sannan ta dan daki saman sitiyarinta cikin zuciyarta tana dariyar mugunta,sai da ta barshi ya sakankance sosai ta take motar ta qara maya gudu sai ji yayi fit ta wuceshi ,cikin zafin nama da mazantaka ya qara wa tashi shima wutar don ya nuna mata bata isa ba saidai kafin ya qaraso har ta qaraso kwanar freedom ta sanya signal ta shige,ta morrow din gaba suka hada ido yana wucewa amma sai ya wuni mugun dauke kai kamar ma bata sanshi ba


Ya girgiza kai ya miqe kasancewar b.u.k zai shiga hanyar ta rabu cikin zuciyarsa yana fadin"zan koya miki hankaline kin maida ni abokin wasanki kenan


Qarfe biyu ya baro b.u.k din bayan ya kammala abinda ya kaishi,kai tsaye ya tashi motarsa ya bar makarantar,biyu da rabi ya iso freedom hakanan bai taba zuwanta ba koda hira suke son yi da shi yana basu appointment ne,ahankali ya gangara layin ya qaraso bakin gidan radio din ya yiwa mai tsaron bakin qofa horn ua taso don yaji me ke tafe da shi,da ganinsa ya fara fara'a cikin mutunci suka gaisa ba tare da jiran komai ba ya bude masa qofa yana jira ya shiga,da hannu aliyu yayi kiransa ya qaraso saitin window ya ranqwafo yana saurarensa,"wata sabuwar ma'aikaciyar ku nake nema ina fata bata fita ba"cikin tunani yake kalleshi,aliyu ya gyada masa kai da son tabbatar masa,sai kuma yadan saki murmushi yace "oh ko haj fadila?"aliyu ya gayada kai yace"yes itace"😃 tana nan ciki kuwa bata fita ba mutuniyar arziqi kuwa ranka ya dade.....ko kira maka ita za'ayi"aliyu ya dakatar da shi"✋🏻a'ah barshi zan dan jirata ba matsala"ya tada motar ya shiga security suka nuna masa gun parking"ya daidaita motar qasan bishiyun dake gun ya kasheta,ya miqar da sit din nasa ya kwantar da shi yadda zai masa dadin kwanciya,yayi sama gaba daya da glass din motar kasan cewarsu akwai (tinting)jikinsu,yasa hannu ya qaro qarfin a.c dake jikin motar ta gauraye masa ko ina ya kashe dukkanin wayoyinsa ya watsa su sit din gefansa,ya maida bayansa ya kwantar jikin kujerar yana fuskantar ginn gidan idanunsa akan reception,lokaci lokaci kuma yana bude mujalla yana dubawa


Zaman minti ashirin yayi ya ganta ta fito gefanta wata yar matashiyar ce sabe da baby girl a kafadarta ,ita tayi hanyar waje ita kuma ta nufi inda tayi parking tasa maqullinta ta bude motar tashiga,ya miqe ya gyara zaman kujerarsa ya jawo belt ya daura,ya kunna motar ya biyo bayanta sanda take ficewa daga ginin gidan radiyon


Ko kusa fadila bata lura da shi ba don bata kawowa ranta ba,cikin kwanciyar hankali take tuqinta,wani mahaukacin horn taji ana mata kafin ta ankara motar ta zo daf da ita tana shirin gogarta a gigice tayi gefe da motar tana ci gaba da kallon motar da ta kasa tantance waye a ciki?,kafin ta gama wannan tunanin har ya dawo daya side din data koma ya sake matsowa daf da ita yana shirin gogarta,sai ta tsorata 😳kasancewar titin da ta biyo ba mai yalwar jama'a bane bugu da qari kuma rana ce babu gilmawar mutane sosai a gun


Cikin lokaci qanqani ya gama rudata gaba daya ta tsorata dama da hugunta ya dinga komawa,tuni lissafinta ya qwacr tama manta sitiyarin na hannunta ne,sai ta taji motar ta soma yawo da ita saman titi idanun aliyu na kan motar,ya zubawa motar ido ganin ta soma yawo bisa kwalta a hankali yana nazari,ya saki ajiuat zuciya sanda yaga ta daidaita ta daina tangal tangal din da takeyi,ya qaraso saitin window dinta sai ya sauke glass ta juyo idanunta cike da taf da tsoro suka hada idanu,ya dauke kansa ya qarawa motar speed yayi wucewarsa,wani abu ya daki zuciyarta sai ta kasa tuqin,ta sauka a hankali ta gangara gefan kwalta ta kashe motar ta jingina da makarin motar idanunta a runtse😣 zuciyarta na ci gaba da bugawa💓,sai hawaye ya biyo rufaffun idanunta ta saki kuka silently,sai da taji don kanta ta samu nutsuwa sannan ta kunna moyar taci gaba da tafiya slowly a gefan titi don gaskiya ya dauki haqqinta


Tana isa parking space taga motar tayi tsammani ya shge cikin gidan saidai tana gama kulle motar ta ganshi tsaye jikin motar yana amsa waya,idanunsa suka shiga cikin nata wadanda suka dan kafa alamar tayi kuka takaici yasa ta sakar masa harara🙄 hadi da murguda masa baki😙ta shige jin alamun taku tayi ana bin bayanta,tana juyawa taga kuwa shi din ne,tasan mai yasa ya biyota cikin azama ta qarasa shigewa bangaren nata daidai lokacin da yakai hannunsa zai fincikota,tayi saurin sanya maqulli ta qulle qofar hadi da jingina a jiki,tana kallonsa ya juya ya koma" kawai"ta fada a hankali


Zaune take tana kallon wani Indian film hum dil de chuke sanam tana ganin son maso wani tamkar nata da aliyu,ta bada hankalinta kacokam bisa t.v din sai tsintat qamshinsa tayi yana yawo bisa hancinta,ta dago da sauri yana tsaye bisa kanta hannunsa harde a qirjinsa shima idanunsa na kan t.v din sai a lokacin ta tuna da abinda ta masa dazu da hanzari ta miqe ta jawo hijabinta ta zira tana neman guduwa sai alokacin ya dawo da idonsa kanta fuskarsa a dinke tsaf,da baya da baya ta soma tafiya yana binta har ta dangane fa qofar bedroom dinta ta fafa ciki tana shirin danno qofar,yasa hannu ya kare ta,yaci gana da binta sai da ta dangane da sif dinta ,qwalla ta cika idanunta idonta tuni ya raina fata,girgiza kanta ta soma yi tana cewa cikin tawar murya"donA....Allahh kay......yi...yih.....haquri...."yasa yatsansa ya dalle mata baki,taji zafi sosai ta sanya hannunta ta dafe bakin🙊,ya zare mata ido sosai yace"wa kika harara? Ni sa'anki ne?kin raina ni ko?,still tafin hannunta na dafe da bakinta ta girgiza kai tuni hawaye ya balle mata😭,ya saka hannunsa ya kama gashinta💆🏼 da ta tufke cikin hijabin har sai da tace "wayyo Allah na!......,hadi da wani dan guntun hawaye da ya silmiyo mata,ya saketa yana sake matsota har tana jin hucin numfashinsa,ta runtse idonta gam tana jiran jin hukunci na gaba,ta yarda aliyyun mugu ne,tasan yau Allah ne kawai zai qwaceta


Shirun da taji yayi yawa ya sata bude idonta,ba kowa a dakin hasalima an ja mata qofar dakin sai ita kadai dake tsaye jikinya na kakkarwa,ta sake sakin kukan ta kifa kan gadonta


⚜⚜⚜⚜⚜


Cikin kwanakin gaba daya ya gama tsanar bangaren nasa,bedroom sin da suke cikin corridor din wadanda bai amfani da su duk sai da ya budesu yayi amfani da su ,duk da alokacin su su samira suna ganin suna qure adaka gun gyaran amma shi sam bai masa ba,don ba wani qwarewa sukayi ba kamar na fadilan,yakan daure ne kawai ya nuna yabawarsa,ya tabbatar wa ransa nata yafi wannan kimtsuwa


Kowanne dan adam wani lokacin kakan tsinci kanka cikin rashin jin dadin rai hakanan to haka yau aliyu ya tashi,alhamis ce wadda aka wuni garin lullube da hadari da iska mai cike da qamshin qasa,mutane da yawa yanayin yayi musu amma banda shi,biyar saura yama yi dawowarsa gida,yayi cilli da jakar tasa a falo,gidan dai na nan a yanayinsa na kullum wato shiru,toilet ya shiga ya watsa ruwa ya fitar jallabiya mai sulbi irin ta maza milk colour mai dogon hannu ya saka,ya feshe jikinsa da shamsul imarat ya hada da turaren chastity ya dawo parlour ya fitar da computer dinsa ta tafi da gidanka(laptop)ya jona mata chargy ya jawota har kan kujerar da zai zauna ya dora ta a saman kujerar,ya daddanata ya bude bayan komai ya gama daidaituwa ya soma aikin da ya dawo da shi


Munti biyar goma sha biyar sai aikinbya soma gagararshi saboda yunwa,ya dafe kansa da hannu daya yasa dayan ya lallatsa comouter din ya kasheta,ya zubawa fridge dinsa ido yana nazarin me zaici a ciki?komai dai na nau'in ciye ciye akwai aciki🍏🍎🍐🍊🍋🍌🍉🍇🍓🍈🍒🍑🍍🍅🍆🌶🍠🍤🍟🍔🌭🍕🌮🌯🍕🍘🍦🍧🍨🍺🍷🍾
Saidai gaba daya sun gundireshi babu abinda yagi buqata sai abinci mai nauyi da gishiri,gaba daya taste din girkinsu salima bai gamsar da shi bare yasa su dafa masa wani abun,koda ranar gikinsu ne yana yin kawaici ne kawai yaci don kada suga rashin kyautawarsa


A nutse ya isa gaban freezer din ya bude yana sake kallonta kamar baisan meye da meye a ciki ba,hannunsa yakai kan madarar fresh yo da tayi sanyi sosai tanata fidda tsatstsafar sanyi yasa daya hannun ya maida murfin freezer din ya rufe,ya maida kallonsa kan robà dake riqe a hannunsa yana jujjuyata tamkar mai karanta rubutun dake jikinta


Ya saki tsaki hadi da cillar da robar kana yayi tattakì ya isa bakin window dinsa yajanye labulayen jiki gefe daya ya dora idonsa a harabar gidan,idanunsa suka sake kaiwa kan bangaren nata a karo na barkatai,tarwai yake da haske alamun tana nan,ji yayi yà gaji baAi iya jutewa ba sole ne yazo tayi masa aikin da tasabar masa idan yaci gaba da jurewar yana jin qila yunwa da tsantsami na iya illatashi,ya juya ya zira slipper dinsa ya fito....


Mrs muhammad ce👑


📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
[10/16, 1:41 PM] 💍🍬🛍Salma🛍🍬💍: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*wa yasan gobe?.....*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*written by safiyya Abdullahi musa huguma*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺


3⃣9⃣~4⃣0⃣


Ya juyabya zira slippers dinsa ya fito Gaba daya tana ma gida babu inda ta fita saboda ba ba abinda zatayi a gidan radiyon shi yasa bata shiga ba,zamanta tayi ta dinga bacci abunta sallar azahar kawai ta tashi tayi ta dan sha yoghurt ta koma baccinta


Qarfe hudu da rabi ta farka tayi wanka,tq gabatar da sallar la'asar din da ake binta,riga da skert ta saka hade da mayafinsu sannan tayi kitchen da azama saboda wata hadaddiyar yunwa dake sakadarta


A tsaitsaye ta hada jallop din taliya🍜 da tasha kifi ta watsa mata carrot piece da grean beans,da zaman jiran dahuwar abincin da zata yi sai taga gwara ta hada lemo,cikin lokaci kadan ta hada lemon kwakwa da yasha madara ta bude freezer din kitchen din ta sanya ta a ciki,bayan ta kammala ta juye a plate ta kalli plate din tana murmushi hadi ya tsina fuska don ita kanta tasan ba iya cinyeta zata yi ba ta mata yawa"let me try"ta fada tana gyada kai ta hado da lemonta dake cikin jug din ta taho dashi parlour ta zabi kujerar da zata zauna akai don haka ta jawo centre table ta dora su a samansa


Ta juya ta koma daki don daukar wayarta ta tashi ne ta tarar da missed call din fauziyya colleague dinta ta barshi da niyyar idan ta gama abinda take ta kirata


Ya kama handle din ya murda hadi da tura qofar ta bude ya shiga,qamshin freshner din parlour hadi da qamshin jallop din ya dunqule ya daki hancinsa wanda hakan ya sake haddasa masa yunqurowar wata matsananciyar yunwa,idanunsa suka kai kan plate din dake dauke da jallop din🍝😋dake ta tururi da qamshi,


Fadila ta fito hannunta dauke da wayar tana duba missed calls din data tarar ciki harda na rumasa'u da farida,,sam bata lura da shi ba agun sai da yayi gyaran murya,adan furgice ta dago don bata zaceshi ba,a dinke fuskarsa take kamar kullum ya cillo mata muqullai suka sauka a kusa da qafafunta,yayi gefe da kansa sannan cike da ginshira yace"ki gyara min bangarena sannan ki sama min abinda zanci yanzun nan tunda sai an koya muku abinda ya dace" ya nemi kujera ya zauna hadi da jawo wani dan qaramin table din na glass ya miqe qafarsa akai


A hankali ta sunkuya ta dauki muqullan,cikin zuciyarta tace"ka gama qunbiya qunbiyarka ka ma,mutum sai shegen jin kai ka fito kawai kace kazo neman taimako guna,ki banza dai ina da muhimmanci tunda.duk cikinsu babu mai iya maka haka sai ni duk da dan banzan jin kanka"ta shiga daki ta canza mayafin zuwa hijabi sannan tazo ta wuce shi yana zaune yadda ta barshi


Kamar jira yake ta fita din ya jawo abincin gabansa,ya dauki cokali mai yatsu yana jujjuyata yana qare mata kallo,a zahiri shi taliya bata dameshi ba don haka ya ture plate din gefe sai kuma qamshin ya addabeshi don haka dole ya jawo yakai loma daya bakinsa🍜


Lumshe ido yayi dadin na zagaya kunnensa👂🏻,ya tabbatar wannan ne taste😋 din da yayi missing kwana da yawa kuma shi yake nema wasa wasa saiga gashi ya tashi da plate din gaba daya,ya shafa cikinsa take yaji yana buqatar qari bai qoshi ba, ya miqe ya nufi kitchen kasancewar tsarin ginin nasu daya ne shi yasa ya fahimci inda yake,ya daga tukunyar gaba daya ya juye ta ciki ya cinye ya dawo falon dauke da ruwan roba na faro a hannunsa ,sai yaji ya samu nutsuwa ba shakka yunwa bata da hankali inji dan almajiri


Ya miqe a kan three sitter🛋saboda yanaji har cikin zuciyarsa yanayin qamshi da tsaftar falon sunyi.masa,idanunsa a lumshe yana tunane tunane har aka fara kiraye kirayen sallar magariba sannan ya miqe ya bar sashen,kafin ya qarasa nasa suka ci karo da samirah na shigowa da motarta,ya tsaya qam yana dakon qarasowarta hannunsa zube cikin aljihun wandonsa,tunda ta hangoshi tace da qawarta sa suka shigo tare "na shiga uku kubra mai gidan nan ya dawo"kubra da hankalinta ke kan waya ta ja tsaki tace"mtswee to sai me?ni wlh samira mamaki kike bani tunda.kika yi auren nan duk kin canza komai adarare duba fa dazu da zamu fita fitted gown fa kawai nace ki saka amma kika qi bayan kinsan gun manyan mutane zamu ji,tsoron mutumin nan kike ji kamar wani Allahn ki ke yadda ma kike tsoronsa baki tsoron Allahn naki ma,nidai gwara ma dai yau naga wanne dan mulkin nan ne wannan da.kike masa biyayya haka kamar shi ya tsuguna ya haifoki


Cike da gadara da rashin kunya kubra ta fito yayin da samira keta.rabe rabe don kuwa riga da skert ne a jikinta na shadda kana kallon shaddar kasan an kashe mata naira mai tsada ce saidai anci mutuncinta ta wajen kacalcalata da yi mata matsatstsen dinki,ga mayafin jiki ta sai kace wadda aka yiwa gorin lullubi


Kallo daya ya yiwa kubra da ta tsareshi da ido duk wata rashin.kunya da ta fito da ita tayi nata gun,hakanan aliyu yake Allah ya bashi baiwar kwarjini masifa,ta sake kallonsa karo na biyu"wow"ta fadi a hankali don gaba daya ya tafi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login