Showing 33001 words to 36000 words out of 130495 words
Chapter 12 - Wa Yasan Gobe Compelet Book by Safiya Abdullahi musa huguma
kaya suke,Aliyyu ta hango a tsakiyarsu fuskarsa nata fitar da wani annuri cikin wata rantsatstsaiyar shadda babbar riga da yar ciki sai wando zata iua cewa bata taba ganinsa da irin wanna shigar ba ya qara wani kyau da kwarjini sosai ta shagala da kallonsa har suka hada ido
Haushi ne da takaici suka cika shi ganin yadda tayi kwalliya kuma ta fito har kusa da get a haka na tare da tayi lullubi ba,yayi mata kallon nan nasa data tsana wanda ya saba yi mata hakan yasa ta tuna a uadda ta fito fa tayi saurin shigewa cikin jama'a ta bacewa ganinsa
Tana zaune cikin baqinta sumayya ta shigo tace anty kije inji yaya sai taji maganar banbarakwai gabanta kuma ya fadi tace yana ina?yana cikin garden,dakinta ta shiga ta sake fesa turare sannan ta lulluba mayafinta,tunda ta nufo lambun zuciyarta ke dukan uku uku a haka har ta cimmasa,yana tsaye ya goya hannunsa a baya ya juyawa qofar shigowar baya,batasan yadda akayi ya gane ta shigo ba don gurin gaba daya grass carfet ne bare tace yaji takun tafiyarta ne sai ji tayi yayi gayaran murya gayaran muryan sai ya zamo kamar ya mata luguden guduma a qirjinta๐จ,me ya fito dake harabar gida babu lullubi?shiru tayi muryarta na dan rawa tace ka.....kay......kayi haquri"ya dan dauke wuta na dan lokaci kana ya juyo da azama kar mai shirin waftar wani abu,hakan ya sa tayi tsammanin duka zai kawo mata tayi baya da sauri cikin tsautsayi ta taka wani dutse sai kuwa ta tadeta tayi baya luuu zuciyarta na bugawa da sauri don ta gama saddaqarwa sai ya sha qasa,sai kuma ta jita jikin mutum aliyu ne ya sa singalalin hannunsa ya tallafeta ta bude idonta data lumshe tana jiran ta jita ta sha qasa sai ga idonta cikin nasa,ya tsuke mata fuska ๐ kana yace meye haka tashi" tayi azamar zare jikintata tana cewa kayi haquri,sai ya harde hannunsa aqirji ganin yadda duk tabi ta duburburce yabi gashinta wanda ya bi wuyanta ya dawo kafadar ta ta dama da kallo lace din ya zauanar mata caras cas yabi lafiyayyar fatarta chaculet,ya dan dauke kansa yabi gefansa da kallo yana jan tsaki a fili
๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ
WA YASAN GOBE?
โถ2โฃ3โฃ
Sai da ya gama shan qamshinsa sannan yace ina da baqi dame dame kuke da shi a kitchen?cikin dai rawar muryar tace akwai sinasir masa funkaso da miya fried rice sai white rice da miya,ya danyi shiru sanna yace cikin sweet a bamu sinasir da masa sai a hado da white rice tace to har ta juya yace hey! Tadan waigo idonta na kallon qasa yace idan min kawo kiyi knocking kawai ki barsu a bakin qofa ta gyada kai ta wuce
Bayan isha'i gidan ua dade ba mowa sai anty hafiza da farida suma suna gama kintsa mata ko ina suka turare shi sannan sukai haramar tafiya,godiya ta musu mai yawa su kuma suka cikata da nasiha ta rakosu tana bawa naty saqo don allah ki kawo min yan biyu tunda kika kaisu gida yaye anty minqi karbosu tace yayanku ma mita yake amma shekaran jiya munyi waya da mama sun kusa dawowa insha allah da haka suka rabu ta dawo ta koma bedroom dinta ta hada ruwan wanka wanda ya wadata da turarukan wanka,bayan ta fito ta shirya kanta ckin wani lafiyayyen material kalar qwanduwar qwai wanda aka masa ado da qyalli silver da ratsin fari kadan kadan ,shima yana daya daga ckikim dinkunan da aka kawo mata jiya riga ne da skert amma wadannan sun kamata sun muma fito da shep din ta sosai,tana gyara kayan kwalliyar dake kan madubin nata ne taji gudar yan kawo amarya jikinta ya saki ta zauna bisa dressing chair
Tana kwance bisa kujerar qaramin falonta agogon bango ya kada qararrwar qarfe goma tayi ajiyar zuciya ta gayar kwanciyarta goma da ashirin da biyu qarar intercome ta tada ita daga bangaren aliyu ne hakan yasa ta fahimci hadasu yake sonyi kamar yadda al'ada ta tanadar gabanta ya tsanata faduwarsa๐,cikin nutsuwa ta sake feshe jikinta da turare turare ta lulluba mayafi a lallausan gashin kanta wanda bata daura dankwali ba
Da sallama ta tura qofar falin nasasu biyun ne suka amsa amaryar na tsaye gaban fridge tana ciro ruwan roba da lemo yayin da gogan ke hakimce bisa kujera two sitter shigar jikinsa ta yanzu ta babbanta da ta dazu duk da dai babbar riga ce yanzu ma a jikinsa ta shadda milk colour ya ajiye babbar rigar a hannun kujerar da yake kai,salima ta dan zubawa fadila ido na yan sakanni sannan ta dauke kai ta dauki plate saman fridge din ta dora kayan fadila ta samu one sitter dake gefansu ta zauna ,saluma ta janyi centre table dan madaidaici gaban aliyun ta dora masata tsiyaya ya masa ta jiye ta koma kusa da shi kan kunerar da yake kai ta zauna,fadila ta saukar da idanunta qasa tana cewa cikin ranta "ni kadaice bani da irin wanna damar me yasa why Aliyu?,na kusa samota na kusa da qarfin zuciyata insha Allah" muryarsa ta jiyo yana fadin kefa mume jira ko?,shiru na yan mintina sanna ya qara cewa"yayi miki kyau" ya ajiye wayar ,saluma tace kawai ka qyale ta ni na gaji bacci nake so nayi,fadila ta dago kai suka hada ido sai kuma kowacce ta dan saki fuskarta fadila tace sannu amaryarmu"itama da dan murmushin a fuskarta tace sannu kuna lpy"a taqaice fadila ta amsa mata da" lau"ta dan saci kallonsa shi lemonsa ma yake kurba idonsa na kan qofa
Banko qofar akayi aka shigo samirah ce sanye da baqar doguwar riga babu ko alamar hida bisa fuskarta sai dan kwalun atamfa da ta dauro a kanta wanda tayi masa daurin ture kaga tsiya,ta kama qugu tana cuno baki gaba tace da aliyu "gani" wani banzan kallo ya jefeta da shi sanna yace "ga gurin zama nan ko ina idan kuma bai miki ba.....ya nuna mata qofa da hannu๐๏ฟฝ,sai da ta qarewa ko ina kallo sanna ta nufi kujerar da aliyun ke kai kusa dashi a daya side din ta dora qafa daya kan daya tana girgizata harara salima ta makawa samirah itama kuwa batayi jinkiri gun ramawa ba,taja tsaki sanna taci gaba da jijjiga qafarta,hara rarta aliyu yayi ya kalli qafar da take jijjigawa ta fuskanci abinda yame nufi kuma tasan ba magana zai.mata ba don haka ta sake zumbura bakinta sannan ta sauke qafar tata
Godiya ya far yiwa Allah sanna ya dora dukkaninku a qarqashin iko na kume kuma tsarin Allah ne shi ya tsara hakan kamar yadda yame da ikon tsara rayuwar ko wane bawa nasa to ma gode masa akan duk yadda yayi da tawa rayuwar "daganan ya dora da yi musu gargadi da jan kunne sannan ya tunasar dasu tsarinsa na zama a bangarensa mai girki ta biyoshi"salima ta kanne masa ido tave" dear ani dama na nasan da wanna tsarin naka tuntuni saidai kawai ya zamto kamar tunasarwa a gareni"murmushin shima ya mayar mata yace "yes"
Zuciya ta kawowa samirah iya wuya sai da ta tanka" a banza ai wai talaka ya girmi sarki dolen mutum yanzu shinr qarami ko yaqi ko ya so"cikin fusata salima tace "๐๏ฟฝke nifa ba dake nake ba,ban gayyatar irinku a zancena don ni idan banda qaddara ba ma baki kai matsayin ma ki zama kishiya ta ba wlh don ko yar wanke wanken gidammu ta fiki kwarjini sai kuwa samira ta nuna ta da yatsa tace"๐๏ฟฝdon kutumar uban mutum ya qara gaba mana don ni duwa wuce dole ne a zauna da ni zama daram wlh "sai suka so su kacame
Cikin wata gigitacciyar tsawa aliyu ya dakatar da su sannan yace kowacce ta bace masa agun ba zasu haddasa masa ciwon kai ba haka kawai"salima ta miqe ta shige bedroom dinsa samira kuwa ta fice tana gungunin a qyaleta wlh taci uwar mata,ita kuwa fadila abun nasu tsorata ta yayi don bata taba ganin fadan kishiyoyi ba hasaluma ma ba'a taba yiwa umminta kishiya ba gidansu daga ita sai farida sai muhammad ko a tsakaninsu ba fada suke ba don haka tun ma kafin ya kammala bada umarni su fice din ita tuni ta riga su fita yana juya lamarina ranta
Ransa abace ya shiga dakin duk yadda taso lallashinsa yayi banza da ita ta san halinsa tun ba yau ba kuma bata manta da shi din ba don haka da taga yayi banza da ita yana shirin shiga wankร sai ta qyaleshi sai da ya fito yana shirin kwanciya sanna ta langabe a jikinsa tana bashi haquri,ya dan kalleta ya basar sannan yace matuqar kika ce haka zaki dinga biye mata kunayi a cikin gidana to na rantse babu wadda zan saurarawa acikinku,idan banda raini ma a gabana? Ta sake marairaicewa tana cewa "Allah na lura ita wannan kanta na hayaqi ne da kamar dayar ce da babu ruwana da ita,su auremin mijin kuma suce bazanyi kishi ba" shi sai a lokacinne ma ya tuna da fadila baima san sanda ta fice a dakin ba donsanda yake musu jawabin ka ta na sunkuye ne sai ya tuna rana shigen irin wanna da ya hadasu ita da samirah ba wanda ta kula a ranar ma ahi ko samiran harta wuce" ya kauda wannan yace mata" am telling uh indai kina son zama da ni cikin kwanciyar hankali" "baza'a qara ba dear"
Ganin yadda yaqi sakin jiki da ita yasa ta dinga masa wasu abubuwa wanda suka sa ala dole ya ajjiye fushinsa abinka da dama wanda yake cikin wani hali nan ya bada kai bori ya hau aka tuno da tsohuwar zuma don salima dama idanunta a goge take ta wannnan bangaren to haka shima aliyyun yake dalilin da yasa saliman ma ta kasa auren kowa kenan tayita naci har sai data dawo masa
Mrs muhammad
๐๐๐โ๐ปโ๐ปโ๐ป
๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ
WA YASAN GOBE?.......
๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ
๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ
Written by safiyya Abdullahi musa huguma
๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ
โถ2โฃ4โฃ
Cikin kwanakin amarci kawai ake ta ballewa a gidan ,salima wayayyar gaske ce ko da wani lokaci tana manne da A.s maitama samira kuwa ta kasa tsaida hankalinta gu guda,yiwa salima itada da aliyyu labe kuwa ya zamo.mata kamar ibada mintina kadan sai ka hangota tana ta safa da marwa tsakanin sashenta da na Aliyu,fadila baiwar Allah lissafinta yafi ga kwanakin da zata soma shiga office da kuma ranar da zata zamo itace ranar girki a gareta
Kwana uku kenan da tarewar salima fadila ta soma zuwa aikinta ya kama ranar laraba,shiga tayi ta hausawa atamfa ce dinkin riga da zani wadatattu yayin da tayi lullubi har kanta cikin yalwataccen mayafi komai nata cikin kamala yake da nutsuwa haka nan halittarta take kamar wata babbar mace duk da shekarun nata qana na ne,ta bude sabuwar motarta fara qal wadda bata taba shigarta ba saiyau,ta zauna a sit din zaman driver ta kunnata ta wana ta sosai sanna ta sauke hannunta daga kan key din ta hada tafukanta ta soma addu'a๐๐ป,sai da ta gama tana shirin tasar motar ta tuna da hand bag dinta data manto kan gadon ta da sauri ta bude motar ta koma ciki
A hanyar dawowa ne sukayi kacibus da shi kasancewar ta gefansa ne zata wuce din sai tayi tsammanim bai ganta ba don haka ta dauke kanta cikin sauri ta wuce don ta kusa makara ta ajjiye jakar a asit din baya tasa hannu zata kunna motar taji an janye hannun gami da zare key din ta daga kai tq bishi da kallo bai ko kalleta ba ya zagayo sit din mai zaman banza dake kusa da ita ya zauna sosai sannan ya maida qofar ya rufe,ta dan sunkui da kanta๐ ya dan kalleta sannan ya basar don ya lura kamar al'adarta ce hakan,ya tabe baki cikin muryar nan tasa ta isassun maza mai cike da izza ya soma ce mata"ko banza a qarqashin mulki da ikona kike saboda haka u must obeying my statute and order if kina son aikinki,ya dan qara tsuke fuska ๐ duk da yawancin lokuta haka fuskar take ya dage kafadunsa sannan yace" I don't know why aka wani tsiri yin aikin bayan ban gaza komai a gidana ba......
Ya dan sha qamshi sannan ya dora firstly ya zama dole kanki shiga ta kamala idan kin tashi fita,sannan ban lamunce da yawace yawace abu na gaba kada ki kuskura na ganki da number din wani qato a waya ko receiving calls ba and d last one kuma mafi girma wanda zai iya causing loosing din aikinki mu'amala da maza,kada ki dauki damar da na baki na fita aiki lasisi ne da na baki da zaki dinga ganin kina da right na yin duk abunda kika ga dama,take note๐,yana qoqarin ficewa tace insha Allahu zan kiyaye"duk da ranta a abace yake da irun dokokim da yake kafa mata da ita a karan kanta ai tasan ya kamata,baice komai ba ya cilla mata key din yaja qofar ya fice ya tafi abunsa,ta miqa hannunta ta rufo qofar sannan tabi bayansa da kallo yanayin yadda yake taku kamar zabar masa inda zai taka ake,ranta babu dadi ta ja motar ta fice a gidan ,yanayin motar yana da dadin tuqi hakan ya taimaka mata wajan dawo mata da walwalarta,a hankali temper dinta take sauka sai ta dora da fadin la'ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalim cikim zuciyarta,da haka har ta qarasa gidan radiyon freedom don can ta tafi sha'awa amma duk da haka akwai wasu privet ayyuka da zata dinga yi da express radio din
Yanayin yadda ta samu karbuwa ya sake sa mata interest akan aikin sosai,su biyu ne kawai a office din ita da wata fauziyya kusan za tayi sa'a da fadilan amma ita nada yarinya daya iman,fauziyya shekararta uku da soma aiki da tashar,sosai fadila taji dadin samun fauziyya da tayi wayayya mai faran faran da son jama'a duk da ita miskila ce,wunin ranar tayi shine tare da managing director da wasu ma'aikatan tana arranging din ayyukanta ciki harda tsara sabin shirin da suka qirqiro wanda za'a fara gabatar da shi a asabuwar shekara wanda itace mai gabatar da shirin da taimakon fauziyya ta sake fuskantar yadda abubuwa suke duk da dama tasan da wasu lokacin attachment dinta
Kwana biyu tayi tana tsara komai ta mai da kanta busy sosai ta hana kanta sukuni hakan yasa bata da wani lokaci na tunani ,da ta koma gida tayi wanka tayi sallah sai ta samarwa kanta abunci simple ta ci sai kwanciya idan da wuri ta dawo kuma takan yi tilawar alqur'ani tunda dama ta jima da kammala haddarsa tun lokacin da tayi candy,idan ta gama taga tana da wani lokcin sai ta dauki wani aiki da zai taimaketa a office ta yi ko tayi amfani da laptop dinta tayi research na wasu abubuwan masu muhimmanci,a rana ta uku ne da taga komai ya kammala ta nemi hutu na kwana biyu ba wani matsala suka bata tunda dama bata soma gabatar da ayyukan ba cikin shirye shirye dai take,tayi hakanne don a lissafinta ya bata yau itace zata karbi girki ,kuma dama tuni ta shiryawa zuwan ranar
Da wuri ta koma gida ruwa kawai ta watsa ta zura doguwar riga har qasa mai hannun shimi ruwan hoda ta saka,ta taje dogon gashinta ta daureshi da ribbom shima ruwan hodar ne,farin hijabi ta saka wanda iyakacin qirjinta kawai ya rufe,ta wuce locker dinta ta lalubi inda ta adana muqullan da bata amfani da su ta debesu gaba daya ta zira farin silifas na fata ta fito,a falonta ta soma tsayawa ta bude fridge ta dauki lemon chi exotic nectar na pineapple da yayi sanyi sosai ta sha ta maida sauran ta rufe sashen nata,
TO FADILA SAI INA?๐ค
๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ
๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ
โถ2โฃ5โฃ
Kai tsaye sashen Aliyyu ta nufa gabanta na dan faduwa kadan kadan har ta isa qofan,addu'a fal bakinta ta ke sanya muqullan daya bayan daya take gwadasu har ta dace da na qofar,ta tura babbar qofar ta shiga sanyin a.c ne da daddadan turaren aliyyu ne yayi mata maraba,ta dan lumshe ido kadan sannan ta waresu sosai kamar mai neman wani abu,a hankali take bin kowane sashi na falon da kallo tabbas yana buqatar gyara,bata shakka cewa har bedroom dinsa ma na buqatar a kintsashi,ba tare da tsayawa wani dogon nazari ba ta dauko dust bin dake falon ta ajjiye a tsakiyar falon ta zare dan hijabin nata ta jefashi kan kujera ta fara tattare ta fara tattare leda takarda gwangwani da duk wani abu da ya zama datti ne tana jefashi cikin kwandon sharan
Tana tsaka da aikin ne taji ana taba qofar alamar an shigo a tsorace ta dago tana tsammanin aliyu ne sai dai kuma maimakon haka sai taga ashe salima ce tayi tsaye a abayanta tana qare mata kallo ,fadila ta tsani yadda matar me mata naci nkallo haka,dama ita tun da can ta tsani mutum mai azabar kallo,to haka saluma ke mata a duk sanda hanya zata hada su ,abinda ita fadila bata sani ba shine kishine taf cike a zuciyar saliman don so tayi ta samesu gaba daya babu mamora kamar yadda taga samira bata da qira sam,saidai ance gwano baijin warin jikinsa ne ita dinma da tayi dogon nazari da tsinkaye da ta fahimci yadda tata qirar take irin matan nan ne masu azabar tsawo da sirantaka sai wani azababben fari da take da shi irin me gauu din nan to duk da babu laifi tafi samirah amma ko kusa bata kamo qafar fadila ba,tsawonta da azabar sirantaka su suka sata take a miqe kamar number 1 ba wani shape sai tsabar iyayi da yauqi
Ta kau da kai.daga kallon fadilan ta tabe baki sannan tace"oh nayi tsammanin mai gidan ne ya dawo da naga gun a bude" a taqaice fadila ta amsa mata da"A'a" taci gaba da aikinta,sai kawai salima ta bude fridge ta dau maltina hadi da kunna t.v ta nemi gu ta hakimce,sarai ta gano ba abinda yasa saluma zama a gun banda bin qwaqawafin taga me take yi hakan yasa ta sa key ta bude bedroom dinsa ta shige tare da rufe qofar da muqullin ta ciki,salima tabi qofar da kallo cikin takaici don ba haka ta so ba,nan ta zauna tana ci gaba da shan maltinan tana dakon fitowar fadila wadda batasan ma tana jiran ba
Ta qarewa shima bedroom din kallo sannan cikin nutsuwar nan tata ta fare