Showing 15001 words to 18000 words out of 37665 words
Chapter 6 - ANGULU DA KAN ZABO Complete by BADI'AT IBRAHIM .txt
ya yanke hukuncin fita cirani. Bai yada zango a ko ina ba sai a maiduguri cikin k'auyen Mafa, mai gari shine mai masaukin bak'i, a gidanshi Sada ya sauke a d'akin samarin da suka fito cirani. Suna shiga kasuwar cikin garin Borno ne ranar cin kasuwa, mahaifina ya samu ubangida wanda yake bashi kayan itatuwan turaren wuta, da turarukan binta sudan, da su kafin_ kafin, suna kaiwa kasuwa. Kamar kullum.
Sada na cikin zauren mai gari yana ta zuba kayan itatuwa a cikin buhu, su kuma turarukan mai a cikin k'atuwar robar fenti ya jerasu, abokin fita cin kasuwarshi Sani yace.
"Sada kayi sauri kasanfa in ba duku duku muka fice ba baza mu samu inda ya dace mu baza kayanmu ba, kai sauri. Sada ya d'ago yace."
"Kama mun buhunnan kaji Sani izamun a ka, saimu kama hanya. Sani ya iza mai buhunnan a ka ga nauyi, haka kuma ya d'auki robar fentin turarukanshi a hannu. Suka soma tafiya da duku dukun asuba.
"Sani wannan karon kuma mai ka d'auka zaka siyar ne?" Sani yace.
"Dilka, da kurkum na d'auko wannan karon nifa riba nake bi, shi yasa ban yarda na nace ma d'aukar itace kamarka ba, ko wacce kasuwa da abunda zan d'auka. Dariya Sada kawai yayi ma Sani, suna tafe suna hirarrakinsu, a hanya su kaita had'uwa da abokan ciraninsu, ko wanne cikinsu da buhun abunda zai kai kasuwa a kanshi. Sunyi tafiya mai nisa kafin suka iso titi, motar zuwa kasuwa suka samu suka shiga, dasu da kayan nasu duk a waje d'aya, harda awakai, suna tafe anata hira, Sani ya lura Sada baya magana sam.
"Sada kaddai tunanin wannan yarinyar da kunya ya hana ka tambayi sunanta kake yi, 'yar fara?" Murmushi Sada yayi yace.
"Sani ai da ita nake kwana nake tashi, tayi nisan da banyi zatoba a tunanina, gashi gwarjininta ya hanani tunkararta. Dariya Sani ya kwashe ma Sada dashi, yace."
"Ni kuma yau na yi ma alk'awarin zan tambaya ma sunanta da k'auyansu, tunda kullum a wajanka take siyan itacen Dorot. Baki Sada ya washe yace.
"Da kuwa na gode Sani, dan ina sonta duk da ba lallai ta auri d'an cirani kamata ba. Sani yace.
"Duk matan dake cikin k'auye burinsu guda d'ayane. Su samu saurayin da zai auresu ya fitar dasu daga k'auyansu zuwa birni, abunda ke cikin birnin ne basa sani, balle kai taji a kanon dabo zaku zauna, Kano ai babban garine mai cike da masu arziki 'yan kasuwa dama masu ci a gwamnatin. Ajjiyar zuchiya Sada ya sauke domin abokinshi ya k'arfafa mishi guiwa sosai akan kyakkyawar 'yar shuwan da yake mafarkin mallaka. Da wannan tunane tunanen suka isa kasuwa. Nan kowa ya shiga hada hadar baza kayanshi a inda ya dace. Sani da Sada tare suke zama a gefen wata rumfar mai siyar da su lubban da farce da misik, kayayyakin humra dai. Sun baza kolinsu, kasuwa ta soma d'aukar jama'a sai saye da sayarwa akeyi, 'yan mata kuwa gasunan gungu_ gungu, sunata fitowa cin kasuwa. ansha kwalliyar janbaki da hoda da gazal, sai rawar kai suke yi a kasuwa, su ne can, sune nan, su sayi wannan su taya wancan. Sada kuwa matane suka rufeshi sai awun itatuwan turaren wuta suke yi, Sani ma sai ciniki yake tayi, dama duk ranar kasuwa duk abinda suka kasa k'arewa yake yi tas, sabida jama'ar dake zuwa yawa garesu.
Koshab'b'e
Marne tana gaban madubi tana gyara gashinta wanda ta shurb'uneshi da kulacca sai k'amshi yake yi. Mayafi ta yane kanta dashi tsab, kayan jikinta a kod'e suke amma kuma tsab dasu babu k'azanta a jiki, kuma an turare tsunman kayan da turaren kaya, sannan tabi jikinta ta shafe da humra sai k'amshi take bazawa. Haka ma k'annenta Ajjide, da Latifo, duk suna cikin kwalliya. Fararene su sol sabida mahaifiyarsu farace fat, mahaifinsu kuma bak'ine sosai shi. K'awayan su marne ne suka shigo da Sallama a bakinsu, ko wacce a cikin k'amshi take. Nan suka rankaya zuwa cin kasuwa, suna tafe suna wak'e wak'ensu da yaren shuwa. A bakin titin k'auyensu suka samu motar kaya da zata kai mutane ciyo kasuwa, suma suka shiga.
Sada yana zaune jama'a sun ragu a kanshi sai tunanin Marne yake yi yana murmushi. Sani ne ya dafashi yace.
"Gasu can fa sun shigo kasuwar Sada, ga mutuniyar taka, Sada in dai ta aureka ka more mace, yaranku zasu yi kyau sosai Sada. Bakin Sada ya kasa rufuwa sam sai washewa kawai yake yi. Dubanta yake yi tayi daban a cikin k'awayenta ta fisu kyau da bud'ewar idanu, fatarta sai shek'i take yi a rana. Gabanshine ya shiga dokawa da k'arfi, saurim kawar da kanshi yayi gefe. Cikin harshen fullanci tace.
"Inason itacen dorot, da turaren sasaboriya, da d'an duwala." Zak'in muryarta ya shigeshi sosai, ji yayi kamar tafi kowa iya fullanci.
"Kwano nawa kike buk'ata 'yan mata?" Sani ne ya tambayeta, kallon Sada tayi tace.
"Shi baya maganane me kayan? Sani yace.
"Yanayi sosai ma, nauyinki kawai yake ji, kinsan 'yan mata irinku kwai kwarjini." murmushi kawai tayi ta mik'a mishi kud'in hannunta tace.
"wannan na itacen, wannan kuma na turaren." Had'a mata kayan yayi a leda guda ya bata, saida suka gama siyayyarsu suka kama hanya, sai Sani ya bisu da sauri.
" 'yan mata ji mana." Dukkansu suka juyo, Isowa yayi garesu sai ya nuna Marne.
"Dake nake yi dan Allah." Nan k'awayen Marne da k'annenta suka shiga yi mata dariyar tayi saurayi, gefe guda suka koma."
"Dan Allah zan soma da tambayarki sunanki tukunna. Far Marne tayi da ido tace.
"Sunana Marne.
"A wanne k'auyan kike da zama?
"Ina cikin koshob'b'e da zama, gidan Ammi mai turare, in ka je babu wanda baisan gidanmu ba." Murmushi Sani yayi yace.
"Dama abokinane ya gani kuma yake so, amma kunya irinta fulani yasa ya kasa taranki kai tsaye. Sai dai ya jima da sonki a zuchiyarshi. Ki bashi dama. Murmushi Marne ta yi tace.
"Na bashi dama gobe zai iya zuwa da yamma sai mu yi magana. Tana kaiwa nan ta wuce suka kama hanya.
Sani ya ba Sada labarin yanda suka yi da Marne. A daren ranar bacci gagaran idanun Sada yayi, ko a k'aramar kasuwa inda anan suke gudanar da kasuwancinsu. kasa sukuni sam Sada yayi. Da yamma kuwa suka shirya sai koshob'b'e shi da Sani.
Sun samu tarba mai kyau a wajan Marne dama iyayenta, harma mahaifinta yace ya ba ma Sada nanda shekara mai zuwa ya turo magabatanshi.
Tun daga nan soyayya mai k'arfi ya shiga tsakanin Marne da Sada. mahaifiyar Sada ma tasan da maganar Marne, taso tak'i amincewa amma Sada ya tusata a gaba da rok'o har ta amince mishi yaci gaba da zuwa wajan Marne. Wasa_wasa lokaci sai tafiya yake yi, soyayyar masoyannan biyu sai nisa take yi, wata rana da yamma Sada na wajan Marne yaxo yi mata Sallama za shi ganin gida. Suna zaune a kan wasu duwatsu dake k'ark'ashin bishiyar gefen gidansu Marne suna Sallama.
"Sada me kake tanadi game da aurenmu ne, kasanfa auranmu akwai kashe kud'i gashi yanzu wata biyu ya rage ayi bikinmu, dan tare da k'annena za'a had'a." Sada yace.
"Ai duk wani tanadi yanzu da nake yi baya wuce na bikinmu Marne, zan fito dake a cikin wannan k'auyan, zan yi miki kaya na gani na fad'e. Dariya suka saka baki d'aya tace.
"Ai nasan Sada bazaka bani kunya ba, amma yanzu Sada sai yaushe zaka dawo kuma?" Gyara zama yayi yana fuskantarta.
"Marne magana ta gaskiya, in dai na tafi bazan dawo ba sai dai in zo bikin d'aurin auranmu, akwai shirye shirye da zan gabatar a gida, kuma nima tare zamu yi aure da k'anina Junaidu. Ki yi hak'uri kinji?" Kud'i masu yawa ya ba ma Marne yace in zata yi buk'ata tayi a cikin su. Sunyi sallama Marne tana kuka a haka suka rabu.
Kano
"Baba Toh ni dai kinga iya abunda na tara, su kenan iyakar abunda nake da shi, amma cewa na yi, mu je k'auye ayi maganar Gadonmu. A siyar da gonakan a bamu, in yaso sai mu nemi gida mu siya, Ko Baba?" Junaidu yace.
"A'a Yaya Sada ni dai kar a siyar da nawa, gaba za su yi mun amfani sosai, d'an abunda na tara, sun isheni in yima Harira komai. Baba tace.
"Nima ina ganin kamar a barshin zaifi ko, sabida gaba ake ji, da kunyi aurannan zaku soma tara yara ne, ga ciyarwa fa, kuma babu mai k'wak'k'warar sana'a ta dogaro da kai. Sada yace.
"Ni matsalar shine. auran shuwa akwai kashe kashen kud'i, su basa yar da al'adarsu sam, kuma kinga da sisin gwal zan biya sadaki shiyasa."
"Sisin gwal kuma wannan yaron?".Sunan da Mahaifiyarshi ke kiranshi dashi kenan. kasancewarshi na babban d'anta.
"Eh Baba sisin gwal, toh kinga 'yan kud'ad'en dana tara ba za su isaba." Baba tace.
"Tun farko yarinyarnan tafi k'arfinka. Nifa shi yasa sam bansota ba sam, sabida matan shuwa ba kirki bane da su, aikinsu shine mallaka da nuna kowa zasu iya mulkarshi. Amma tunda kai zaka iya, sai mu je mayo a siyar da gona d'aya azo a sayi gida, sauran a gangand'a a gama komai.
Hakan ko akayi, sun je k'auye an siyar da gonarsu Babba ta gado. A Jacara suka sai gida mai d'auke da d'akuna hud'u, ciki da falo falo, guda uku, sai d'add'aya guda biyu, da kitchen da band'aki a tsakar gida. Tsakar gidan babu laifi da girma.
Sannu_ sannu lokacin biki nata k'aratowa, shiri ya kankama daga ko wanne b'angare. 'yan uwa da abokan arziki sun soma zuwa daga gari_ gari, k'auye_ k'auye, Shagulgula na al'adar fulani da ma na shuwa babu wanda aka zubar. Rana d'aya aka d'aura Auren, 'yan d'aurin aurene suka tawo da Amarya Marne da gandinta. Haka ma Junaidu. 'yan d'aurin aurenne suka tawo tare da zugar dangi da ƙawayen Amarya Harira. Da Yamma lis 'yan mayobelwa suka iso, nan kuma aka shiga yin dank'in d'akin amarya.
Gadone mai rumfa, da doguwar kujera guda d'aya, sai tarkacen kayan k'ore, da kayan aikin gida akaima Harira. Basu jima ba aka kammala komai, har amarya ta samu ta shiga d'akinta. Mutanen maiduguri kuma sai cikin dare suka iso. Dole aka jibge tulin kayan Amarya a tsakar gida, sannan aka cire kayan uwa da suke yi bisa al'ada aka mik'ama mahaifiyar Sada. 'yan uwanta ne suka amsa su kai godiya.
Santin gidan dangin Marne suka shiga yi sosai da sosai, sun yaba da karamcin dangin Sada matuk'a gaya. Washe gari aka yi jeren d'akin Amarya wanda yasha kaya sosai. Gado har biyu aka kafa a uwar d'akin da mai rumfa da kuma bono 😉. Ga daddumai da aka shinf'ida a ciki da falo, dadduma har a bango aka kafa ta, gashi an zagaye bangon d'akin da cotin jajaye masu kyau sosai. Kwanansu biyu a gidan sannan suka tattare yana su ya nasu.
Amarya Marne tana zaune a d'aki ita kad'ai sai tunane_tunane take ta faman yi. A haka ta jiyo sallamar Mahaifiyar Sada da Harira. Gidan kowa ya watse. a yatsine ta amsa musu tana daga uwar d'aki. sun jima a falon a zaune kafin ta fito cikin isa.
"Lafiya daga ina haka?" Da harshen fulatanci tayi magana. Cikin Fara'a Harira tace.
"Mahaifiyar Yaya Sada ce." D'an sakin fuska tayi tana tsaye ta gaisheta ta yi komawarta d'aki ta yi zamanta.
Suna zaune sunyi tunanin ko wani abun taje d'akkowa amma sai suka ji shirun yayi yawa. Baba ta girgiza kanta, ta yafici Harira suka fice.
"Koma d'akinki Harira mak'ota zaki gansu zuwa anjima sunzo ganin d'akunanku, ki gyara ko'ina." Harira cikin ladabi ta amsa mata ta wuce.
Tsaki Marne ta saki tana maganganu k'us_k'us.
"Kawai zai wani had'ani da k'azamar uwarshi gida d'aya. Da ya fad'amun hakan ni mai zai sa ma in aureshi? Na yi zaton gidansu yama fi haka, wannan dame yafi k'auyenmu?" Tana dai zaune ta gama k'umewa da Sada.
Baba ce ta fito tsakar gidan ta kunna itace a murhu, sai ta d'auki tsintsiya tana sharar tsakar gidan da yai kaca_kaca. Harira ce ta fito da sauri ta amshe tsintsiyar. Nan kuwa ta shiga aikin shara. Baba tana zaune a dokin k'ofarta tana tsintar shinkafa. Sai ga Marne ta fito rik'e da kaskon turare a hannunta. Baki Baba ta washe tace.
"Masha Allah Marne kin fito ne?" D'an yak'e Marne ta yi tace.
"Eh na fito zan d'ebi wuta ne." Da fara'a Baba tace.
"D'iba gashi nan, yanzu na kunna ma. Marne bata kuma kallon Inda Baba take ba balle ta tanka mata. Wuta ta d'iba ta yi shigewarta d'aki. Can gidan ya kaure da hayak'i. Harira da Baba ne su ka yi girki. Har d'aki Baba ta sa Harira ta kai ma Marne. Tana zaune a falo wannan karon.
"Amarya ga Abikinci." Ajjiye kwanon ta yi, Marne tace.
"Nagode" Su Sada ba su suka shigoba sai dare, bayan sun shiga d'akin Baba, daga nan kuma kowa ya shige d'akin Amaryarshi.
A daren Marne ta dinga yi ma Sada k'orafe _k'orafe mara sa kai da gindi. Shi dai sai lallab'ata yake yi. A daren ya mantar da'ita komai, ya samu budurcinta cikakke. Satin su guda suna cin Amarci, a kwanakin amarcinnan Marne bata cin abinci daga nama sai shayin wajan mai tsayi da Sada ke siyo mata. Yau ta kasance Sada zai soma fita kasuwar Kurmi dan ci gaba da sana'arshi dai ta siyar da itacen turaruka.
"Sada yanzu zaka fita ni me zanci da rana, tunda yanxu naci ragowar balangun jiya da daddare?"
"Haba gimbiyar Mata, ki yi hak'uri ki daure inzan dawo zan tawo miki da balango. Harararshi tayi tace.
"Harda tsirenma inaso ka siyo mini, sai shayi Sada sai gurasar kano yau dai zanci. Dariya yai mata kawai yace.
"uwar rigima, yau dai sai dai in Baba zaki yi ma." Had'e rai ta yi data ji ya ambaci Baba. Sallama yai mata ya fice. D'akin Baba ya shiga.
"Baba barka da safiya, ina kwana?"
"Lafiya lau, yau zaka soma fita ko? Toh ka rik'ema wannan bawan Allah dukiya da amana. Tunda ya amince ya baka kayanshi ka tawo dashi, ka daure ka rik'e amana har Allah ya baka naka jarin. Kai ya sauke yace.
"Ameen Baba, ni zan wuce." Har ya mik'e tace.
"Abb dawo ka zauna ina da magana." Dawowa yayi ya zauna.
"Matarka bata tab'a zuwa ta gaisheni ba. tunda aka kawota. Tana d'aki zata jiyomu a tsakar gida ni da Harira, amma yarinyarnan in ka ga ta fito, toh band'aki zata shiga, ko ta fito ta tone mana itace ta d'ibi wuta. Irinfa hali da d'abi'un shuwa kenan. shi yasa mazan yarensu ne kad'ai ke iya aurensu, ko hamshak'an masu kud'i, mugun kwad'ayin abun duniya ne dasu sosai, basu cika yarda da talakaba. Dan daga k'auye ma ta fito kenan. Sada dai yayi shiru baice komaiba Har sai da Baba ta gama sannan yace.
"Ki yi hak'uri Baba, zan yi mata magana zata gyara." Sallama yayi mata ya tafi.
Haka dai zaman nasu yaci gaba da gudana, kullum sai Sada ya shigo da tsire ma'ishi ya ba Marne, dan sam bata cin abincin gidan. Gashi ta raina kowa, har fad'i in fad'e Marne ta ke yi da Baba. Sada kuma tsabar son da yake ma Marne baya iya tsawatar mata. Sai dai yaita lallab'ata, dan wani tsoro tsoronta yake ji. Da asuba Sada ya tashi Marne a bacci.
"Marne ki tashi kije ki tsarkake jikinki sai ki yi sallah ko?"
"Toh" Kawai tace mishi, shi kuma ya fita zuwa masallaci. Ya shigo ya sameta a tsaye tana goge jikinta. Kanta ya kalla yaga babu ruwa.
"Marne kinyi wankan tsarkin kuwa?" Dariya tayi tace.
"Ji wani tambayan renin hankali. Sada tuwo ka manna a idanunka ne?"
"Marne naga banga kanki na d'igar ruwa bane"Dubanshi ta yi tace.
"Ana wanke kaine dole Sada?" Hankalinshi ne ya tashi. hannunta ya rik'o suka zauna yace.
"Marne wanne irin wanka kikeyi in munyi mu'amalar Aure dake ne?"
"Wankan da kowa yake yi na soso da sabulu. Ya jinjina yarinta da wautar Marne sosai. Tambayoyi ya soma yi mata a addinance. Abun mamaki bata iya komai ba, dai_dai da sallah dungurawa kawai take yi, babu abunda take cewa. Ai a ranar Sada ya sa Marne a makarantar Addini ta matan aure wacce take can k'asan layinsu. Ringid'i_ringid'i Marne ta soma zuwa makaranta tana d'aukar darasi, cikin wata biyu ta haddace ixu biyu, sannan ta iya wankan tsarki dana haida. wannan zuwa makaranta da cud'anya da mata da Marne ta soma yi, harta soma jin hausa jifa jifa, dan ta yi k'awaye da dama, tama dena zama a gida sam Sada nasa k'afa ya fita zata fice a gidan itama. Harira kuwa cikinta ya tsufa zama da kyar tashi da kyar, Marne ta sake gogewa sosai, ta d'anyi k'iba da hasken sabon jinjirin ciki, irin wanda masu juna biyu ke yi. Ta d'anyace sosai. Tana jin Hausa daidai gwargwado. Kullum Marne a cikin yawo take.
Mrs Bukhari ce
*TALLAH*
Ina kuke amare uwayen gida kai har ma da ƴan mata? Ko kun san Mrs Bukhari mai kayan ƙamshi, ai in dai batu na kayan ƙamshi gyaran jiki da na ɗaki to kai tsaye ku ne mi Badi'at domin gwana ce ta ko wanne fanni a ciki. "Wai ƙamshi kina nufin Badi'at dai marubuciyar nan tamu mai nishaɗantar da mu?"
"Tabbas Fati ita take magana, ai kin dai ji yadda ake magana a kai na, hatta me gidana ya jinjinawa Badi'at domin duk wani ƙamshi da zaki ji a jikina tare da gidana to daga ita ne, ke me kankat ma har gyara na nake yi domin gyaran aurena daga gareta ne, shi ya sa bana wasa da gyaran jikina da na gidana har kuke kirana da ƙamshi."
"Eh tabbas nima na jinjina mata, kuma zaki bani addireshinta domin nima na kwankwati wannan garaɓasa. Ko zaki iya faɗa mini abubuwan da take sayarwa.?"
"Bari na faÉ—a miki akwai...
Humra
Kulacca
Sudanese Humra
Kulacca ta gashi.
Turaren wuta É—an gaske, iri daban daban.
Turaren mopping
Room freshner
Turaren turara kaya.
Turaren wuta na toilet
Sannan akwai ingantaccen maganin infection
Ina da magungunan mata, wanda zai gyara amarya da uwar gida.
Wanda zasu shiga daga ciki kuma
Akwai sabulun amare, da dilka ta amare, wanda zaisa amarya ta fito ta haska tas
Kabbasa
Setin kujerar tsugunno
Sannan inayin turaren wuta da kasko, da ashana wanda ake rabawa a taron biki ko suna.
Ina bayar da sari.
Ma sha Allahu to taya zan sameta domin mallakar nawa?
"Kai tsaye zaki mata magana ta whatsApp ko kiranta ta wannan number.
08179523215
*TALLAH*
A yau nazo muku da manya manyan magunguna domin gyaran Auranmu! Saboda yadda