Showing 30001 words to 33000 words out of 37665 words

Chapter 11 - ANGULU DA KAN ZABO Complete by BADI'AT IBRAHIM .txt

BUKHARI (B4B)


*ANGULU*
*DA*
*KAN ZABO*
17/18












"Assalamu Alaikum, maman Hewa kina ciki?" Maman Hewa tana daga d'aki tana turare d'akinta da turarukan k'amshi tace.
"waye shigo" Dada ta bud'e labulen da sallama ta shiga. Bata tab'a shigowa gidan ba, dan ba dad'ewa su ka yi da dawowa ba, 'yarta d'aya ce mace me suna Hewa. D'akin yaji kayan alatu sosai. Dada ta nemi kuri ta zauna a ranta tace.
"Shuwa gidan k'amshi kenan. Kaima Allah ya baka Aminu" Maman Hewa ce ta fito daga d'aki da fara'a suka gaisa da Dada. Ta tsaɓa ado tamkar zata je gidan biki ko suna. Dada tace mata.
"Dama nazo ne in miki wasu 'yan tambayoyi a game da al'adun auren shuwa. Da farko dai bari in soma da sadakinsu. Yana kaiwa nawa?" Maman Hewa tace.
"Toh Dada k'arfi k'arfine abun, kamar dai mu talakawa haka, sadakin daga dubu d'ari uku, d'ari hud'u har zuwa bakwai. Kuma da sisin gwal ake biya, wannan wajibine, duk cikakken shuwa da sisin gwal ake biyan sadakinsu. Daga sisin gwal uku, huɗu, biyar, goma sha biyu ne ƙarshe. Masu sukuni kuwa har million hudu, million goma ana biya sadaki, Dada har Million ashirin ana biya ya danganta da ƙarfi. Dangin amarya kuma gaskiya zasu narka mata kaya sosai. Akwai kayan uwar miji da akeyi har da katifa, da kafet na ɗaki, su kulolin cin abinci, abubbuwa da dama, shi kanshi kayan uwa kuɗi ake narkawa sosai. Al'adun da yawa gaskiya. Wannan dalilinne shuwa basa auren talaka, sai ake fassaramu da kwaɗayi, ba kwaɗayi bane talaka bazai iya bane. Akwai kashe kud'i." Dada ta yi shiru tana nazari, can kuma tace.
"Tom shikenan nagode sosai." Sallama ta yi mata ta fita. shagon k'ofar gidan nasu inda nanne d'akin Aminu. Dada ta shiga da sallama. Aminu ya amsa mata a hankali.
"Ina Saminun?" Dada ta tambaya bayan ta zauna.
"Ya shiga cikin gida, zai kama ruwa."
"Aminu har ga Allah banason wannan 'yar shuwan, ni hankalina bai kwanta da'ita ba. Ka ga mun jima muna wannan maganar dani da ku. Toh amma gudun kar in rasaka, kuma itama yarinyar tana sonka. Toh bazan tauye ku ba. Na Amince Allah yasa albarka." Murna ce ta cika zuchiyar Aminu fal. A haka Saminu ya dawo ya samu aminin nashi.
"Toh Saminu na tambayo mak'ociyarmu 'yar shuwa. Ashe dai haka ake biyan wannan sadaki, wai harda masu bada million ashirin abu kamar hauka. Naga yaronnan yayi zurfi a son yarinyar. dan haka na amince muku. Zan kuma je k'auye, a cikin shanun gado in gani ko guda biyu a siyar, ya samu ya aureta kowa ya huta." Murna su ka yi sosai da sosai. Washe gari Dada ta tafi gida. kwana hud'u tayi suka dawo ita da k'anin mahaifin Aminu, su ka had'u da mahaifin Saminu, ranar da aka yanke musu gobe ne, sun shirya zasu je da yamma."


Hauwa
wayar gari nayi cikin fad'uwar gaba da fargabar rasa Aminuna. Hak'ik'a ina son kud'i, kuma ina son auren mai kud'i. Amma son Aminu yaci k'arfina har nake ganin in zan samu Aminu zan zubar da makaman yak'i, in aureshi in ci duniyata da tsinke. na kasa walwala sam. Ammi ta yi mun tambayar duniya kan meke damuna. Ni dai da Ba komai nake amsa ta.
Tunda Aminu ya tafi bai d'aga waya ya kirani ba. Koda na kira wayarshi da safe dan in jaddada mishi yaune fa. Sai naji wayar a kashe. Hakan ya tsurad dani sosai."
Da daddare muna zaune a tsakar gida, sai ga sallamar Baffa Junaidu. Sannu da zuwa mu ka yi mishi, duk muka tarwatse.
"Marne na zo ne akan iyayen samarin yarannan da kika turosu maganar sadaki da tsaida rana. Sisin gwal biyar kamar yanda kika yanke. Gasu sun samu, Alh Auwal kuma guda sha biyu ya kawo. Marne kiji tsoron Allah yarannan siyar dasu zaki yi ne da irin wannan dukiya. Albarka ai itace kan gaba a aure ba tulin sadaki ba. Sannan kinsa musu wata d'aya ca su kai dake duk sun gama shiryawa koko yaya nine dai uban yarannan duniya da lahira. Kwatsam sai jin sallama na dinga yi a zauren gidana, wannan wanne irin ɗumasariya ne?"
"Hmm jibeka Junaidu me jiya ta yi ma bare yau. Dan kaga na baka girma anje kai sadaki gidanka har shine ka samu zarafin ci mun fuska?. Tunda wan naka ya mutu mai ka tab'a yi mana daga ni har yaran da kake ikrarin kai ubansune? Ko Sada bai isa nunan yatsa ba kai ka sani."
"Yaran da baki nuna musu girmana ba balle su san mutuncina. Ubansuma baki nuna musu su dinga yi mishi adda'a ba. Ranar fa Sada yazo yana faɗamun a titi ya haɗu da Hafsa amma kawar da kai tayi tamkar ba ɗan uwanta ba. Yanzu dacewa kenan, in yarannan basu yi zumunci dasu Sada ba dawa kike so suyi zumuncin to? Mu biyu rak iyayenmu suka haifa.To Ayi dai mu gani in tusa zata hura wuta Marne. Sisinan gwal d'in ya zube mata a gabanta ya fice. Yana magana"
"In banda fitina ina Sada ina wannan mata, gata kamar basamudiya, ga rashin tarbiyya, sanda aka kawota ko sallah bata yi. Itace aka auro a matsayin uwar ƴaƴa. Ba dole aga aikin jahilci ba.
Gud'a ta shiga yi.
"Aiyiririiiiii Yarana sunyi kasuwa, Junaidu sai dai ka mutu. Irina sunfi ƙarfin aurenka sai dai irinsu Harira ai. Jin guɗarnanne yasa muka fito a guje dukkanmu.
"Ammi sun biya sadakinne?" na tambayeta a ɗarare.
"Sun biya sadaki, sun yi rabin aiki, inaga aje dasu d'in kawai ku auresu. Amma in ina raye babu wacce zatai kuka a gidan aure, zan shiga in fita a tsumaku, da sihirtattun itatuwan mata, ta yanda tasirinku zai baku damar mallakar mazajenku. Dan haka nan da sati biyu zamu tafi koshob'b'e duk wani gyara acan za'ai muku shi. Ku sanar da su kud'in gyaran jiki nera dubu d'ari d'ari, ke kuma Hafsa sai abunda Alh ya bayar."
Kwanan farin ciki nayi, inata kiran wayar Aminu a kashe, sai washe gari da daddare kawai yaro ya shigo kirana wai inji Aminu.
A jingine a bangon gidanmu ya tsaya.
"Aminu ka sanyani a cikin damuwa, tun ranar daka tafi ka barni a mawuyacin hali ban kuma ji daga gareka ba. Murmushi yayi mun. Sai naga Aminu ya sake yi mun mugun kyau a cikin darennan. Har nake jin lallai nayi dace. A lokacin Aminu bai wuce shekara Ashirin da biyar ba, ni kuma shekaruna duka duka Ashirinne . Amma Aminu yana da nutsuwa da kamala, gashi da tunani irinna manya.
"Hauwa ki yi hak'uri wayarce aka sace, kuma na kwanta jinya shi yasa baki jini ba."
Subuhanallah, jinya kuma? Muje dakali mu zauna Aminu.
Ina gaba Aminu na bina a baya har zuwa kan dakalin.
"Ciwon sonki ne ya kwantar dani a daren da muka bar gidanku da Saminu. Hauwa ina sonki fiye da tunaninki fa. Ina jira lokacine in nuna miki tsantsar son da nake yi miki. Na shinfid'a miki wata rayuwa mai kyau a gidana. Murmushi nayi ina kallonshi, Sonshi na k'aruwa a xuchiyaya.
"Aminu, nima ina sonka sosai. Kuma ina farin cikin mallakar juna da muka kusan yi. Amma dai bazaka had'a sonda kake mun da wata mace ba dai ko?" Dariya yayi kawai yace.
"Cikakken namijin da ya san kanshi, da irin halittar da Allah subuhanahu wata ala yai mishi. Bazai ma budurwar da zai aura romon baka irin wannan ba. Ni a ganina masu amsa tambayarnan da cewa eh bazasu yi ba. Ni na d'aukesu mak'aryata, mayaudara kuma Hauwa. Ni a tsarina bana yaudara." Rai na b'ata bance dashi komai ba. Shima shiru yayi yana kallona yana sake mun murmushi.
"Aminu zaka ba da kud'in gyaran jiki bisa al'ada, domun nanda sati biyu zamu tafi k'auyanmu, sai satin bikin zamu dawo."
"Toh nawa ne Hauwa? Ai mun gyara da kyau Hauwa."
Dubu d'ari ne kacal ba yawa."
"Dubu d'arinne ba yawa Hauwa, wannan wanne irin gyaran jiki za'ai miki haka Hauwa, a injin za'a saki?.
Haba Aminu dad'ina da kai ka fiye mammak'o da yawa akan komai sai ka nuna gazawarka. Kallonta kawai yayi yace.
"zan bayar. Zan nemi gidan haya kafin lokacin, sabida in kai ki kije ki ga gidan ki? Dariya na sakar mishi, shima ya mayarmun da martani.
Hakan yayi Aminu gaskiya.
Sallama Aminu yai mun dan baya doguwar hira.


Aminu
Ta b'angarensu sai shirye shiryen akwatuna suke ta faman yi. Akwati biyar da k'yar suka cika da karo karon dangi suka samu aka kammala komai. Tahira k'anwarshi ita aka wakilta ta sai komai. Aminu ya kai Hauwa gidajen haya da dama. Amma ko wanne sai ta ce bai yi mata ba.


HAUWA
Aminu nifa bari in fito maka a mutum irin gidajen da fa kake kaini ba su yi mun ba.
Ni gida mai get nake so, mai d'akuna biyu da falo, kuma ya zamana akwai bayan gida da kitchen a ciki, anguwa me kyau kuma."
"Haba Hauwa waike baki da tausayine? Gidan da kike magana a kai fa, hayarshi sai ya haure dubu hamsin. Haba ina zan dinga samun dubu hamsin ina biyan haya ga ciyarwa."
Dakata Aminu nifa sai a fasa aurennan fa. In dai bazaka iya kama mun irin hayar da nake so ba."
"Saime Hauwa a fasa d'in. Ku dawo mun da kud'ina mana kiga in bazan samu wata matar ba." Fuuu ya tashi ya barni a dakalin gidanmu. Fuu nima na shige gida. washe gari kuwa muka d'au hanyar Borno, kuɗin gyaran jikin da bai bayar ba kenan. Ammi kamar zata ari baki dan masifa."
"Ai wallahi bai isaba dan uwatar, dole zai biya kuɗinnan ranta mishi zanyi. Wa zai more gyaran inba shi ba?"
Haka Ammi ta dinga sababi daren ranar.


KOSHOB'B'E
mun isa k'auyan su Ammi. Jama'ar k'auyen sai zuwa yi mana maraba su ke yi. Ammin Ammi kuwa ta takwarkwashe sosai, amma tana yawonta ko ina. Kuma tana gane kowa.
Kwana biyu muka yi muna gaisuwar dangi Kafin kuma muka nutsu waje guda.
Nan fa aka shiga tsumamu da magungunan sha da na ci. Kala kala, turarukan jiki da na tsugunno gasu nan barkatai. Gyaran gashi ma sai yi mana shi ake yi. Muci wannan mu sha wancan abun sai dai son barka.
"Marne ina fatan dai fatar da akai ma yarannan kaciya suna adane a wajanki ko?" Kinsan fa dashi za su yi tutiya, duk wata mallaka ta biyo bayan wannan ne. Shi yasa macen da akai mata kaciya a cikin shuwa darajarta ma dabanne kamar yanda sadakin auranta ma daban yake." Ammi ta jinjina ma Amminta kanta tace.
"Duk na adanasu, kin gansu nan na tawo dasu, domun a nad'e musu su a layu a ba ko wacce tata ta d'aure a jikin jigidarta, kota ɗinke a filon kwanciyar mijin nata. "
"Kinyi kyan kai, su kula dashi sosai iya tsawon rayuwarsu. Mahaifinki da ya rasu har muka tsufa yana kiyayemun duk wata dukiyarshi a kaina da ku ya k'are tas. Ka tsufa da darajarka a wajan miji, ka wuce wulak'anci a wajan dangin miji. Ka zame musu k'adangaren bakin tulu. Ga turaren kwanciya da kwalli na had'a musu na mallaka."
Haka dai lamuran su kai ta gudana babu sassauci. Ni kuwa duk kewar Aminu ta dameni sosai, gashi mun rabu cikin fad'a da fishi.
"Hauwa ku xo fa ku cinye kajinnan a samu a baza k'asusuwan, ku zare dunkulen maganin da zaku cire a cikin kazar. In kun gama za'a had'a da kashin da dunkulen maganin a dake shi a xuba muku a yaji ku dinga ci. Sannan ku dage da tsarki da ruwan dorot d'innan." Ammi ke magana da mu.
Nan muka rufarma kajinnan kowacce da nata. Da kyar muka cinye. Shanya k'asusuwan akayi cikin kwana biyu suka bushe, aka dake tare da wasu itatuwan ana xuba mana akan abinci muna ci.
note
shuwa ba wai 'yan asiri bane dukkansu ba a'a, Allah ya basu ilimin sanin itatuwa ne da amfanoninsu, kamar yanxu misali tarihin itacen dorot.
shi itacen dorot itacene mai dogon tarihi sosai. kuma a maiduguri yake fitowa wannan itacen. Ana amfani da itacen wajan yin tsarki dan matsi da k'amshin gaba. Itacen zaki jik'a tsurarshi ki dinga kama ruwa, yana sauke ni'ima. Yana matse mace, yana sanya gaban mace k'amshi sosai. Kuma yana saukar da nutsuwa a xuchiyar mai gida.
Sannan ana daka itacen dorot a yi gyaran fata dashi a maiduguri musamman na amare. Dan yana sa fata taushi da k'amshi.
Yana sawa mace ta zama mowa ta fannin saduwa badai namiji ya wulak'antaki ba. Sannan ana turaren wuta da itacen dorot, na mallake zuchiyar namiji, ta yanda duk inda ya fita Allah_Allah yake yi ya dawo gida.
Akwai itatuwa jingin ma mallakar miji bata hanyar kaucema Allah ba.sanna akwai humrori masu tarin yawa na mallaka, waɗanda akayi su ta tsabtatacciyar hanya. Wannan shine sirrin shuwa, duk da masu asirinma a kwaisu. K'amshi shi wannan bama a maganarshi a wajan shuwa, haka kansu da gashinsu kullum cikin k'amshi yake. Gwanayene wajan iya mu'amular kwanciya, kuma gwanayene wajan iya tsabta da gyaran jiki. Kab matan Arewa da shuwa suke koyi wajan turaren wuta da humra. Humrah iri iri ce akwai humra akwai muna humra. In kina son ingantattun turarukan wuta da humrori masu sirrin k'amshi ki yi magana 'yar uwa (Mrs bukhari) zaki tab'o domun ta gyara miki zamantakewar aure da turaren wuta dana tsugunno da na tsarki, da humra iri iri.


Hauwa
cikin sati guda mun canja sosai, ko ina a jikinmu ya cika yai b'ulb'ul dashi, k'amshin dake jikin fatarmu kuwa da gashinmu sai wanda ya shak'a. Fatarmu ta yi wani taushi da shek'i tamkar ta jariri sabuwar haihuwa. kullum sai an wankemi tas. Abun ba'a cewa komai.
Mun wayi gari da rasuwar mahaifiyar Ammi mutuwar da du d'inmu mun jita sosai da sosai. nan gida ya cika ya batse da maza da mata. Ita dai an sallaceta. Ranar sadakar bakwai aka raba musu gadonsu, sun samu arziki sosai, domun ta tara abun duniya sosai. Washe garin ranar da aka raba musu gado mu ka d'ingumo mu ka dawo Kano, inata d'okin kiran Aminu dan can basu da sarvice na waya sam. Muna isowa gida bayan mun huta na kira Aminu.
Ajjiyar zuchiya ya sauke mun tare da cewa.
"kina da girman matsayi a zuchiyata. Na ji kewar rashin jin k'amshinki da ganin kyakkyawar fuskarki Hauwa. Kun dawo lafiya ko?.
Alhamdulillahi Aminu nima nayi kewarka sosai. ka kusa mallakar k'amshina da ma ni mai k'amshi baki d'aya, har sai ya gundureka ma.
"Kar ki yi sab'o a wajena. In dai zan gundura da jin k'amshinki to ki sani zan gundura da numfashin da nake shak'a da fitarwa. zan xo anjima. Da sauri nace.
"Wanne zuwa kuma, dama ance in sanar da kai ne, zuwa gobe ku kawo lafe, tare da toshi. Sannan jibi za'a je jere. Maganar had'uwarmu kam zai yi wuya Aminu, kila sai dai a wajan event in ka ba da kud'in kenan.
"Haba dai, ni babu event d'in dazan yi gaskiya ki yi hak'uri, kuma banda kud'in da zan bayar akan shashancin da zaku yi. In an kawo ki ma had'u."
Aminu karfa in yi zab'in tumin dare. anya sona kake yi kuwa?" Dariya yayi kawai yace.
"Rigimammiya sai anjima Amaryar kwana uku. Meye sunan Amarya da yarenku?
Hararar wayar nake kamar Aminun yana gani, fur nak'i sake cewa komai dole ya kashe wayarshi ya barni" cikin gida na koma wajan dangina."


Aminu
"Dada wai gobe su ke buk'atar kayan lefe dana toshi, Ya kenan, tunda sai gobenne su Innawuro zasu iso ma. Dada tace.
"Kai wannan iyayen mata naka suna da tsurfa wallahi, nifa aurennan ya fice mun a kai, In sun iso da wuri ai sai su kai, in kuma basu iso da wuri ba jibi sa kai. Ya maganar hayan fa?" Ajjiyar zuchiya ya sauke yace.
"An samu haya a wajajan zoo road, dubu tamanin, harmun biya. Gobe Saminu zai mana fenti ma, jibi za su je jere."
"Dubu tamanin fa kace Aminu, ina zaka dinga samun wannan kud'aden a duk shekara? Kar ka ga na sai da shanu dan kayi aure. Dama na jima da ware maka su, nasone in ka tashi aure, sai a siyar a sai d'an muhalli madaidaici ku zauna a ciki, tunda nan d'in namu ne. Toh auren Hauwa 'yar gwal ya lamushe komai, karkayi tunanin zan tallafa maka wajan kula musu da 'ya. Sannan karka yi sake Hauwa ta gano logonka na sanyi da tsananin tausayi. Dan makami zai zame mata." Tahira ce ta shigo tana kuka, a jikin Dada ta xube.
"Dada a kwato mun hakkina bazan iya zama da mashayi ba wallahi.
"Mashayi!?" Su ka had'a baki wajan fad'e.
"Eh mashayi Yaya, sai ya sha giya yazo yaita dukana, matan yayyenshi da mahaifiyarshi duk suna ji babu mai kawo mun d'auki, ga aman giya." Jikinsu yai murus dukkansu Aminu yace.
"Dada bazai yiwu ta zauna da mashayiba, kamata yayi kawai a raba wannan auren, auren mashayi a kwai wuya Dada."
"Aminu hak'uri Tahira zata koma tayi, ki sa shi a adda'a, Allah sai ki ga ya shiryeshi. Tasi'u yaban mamaki shan giya a matsayinshi na d'an musulmi" Tahira ta kuma fashewa da kuka.
"Dada nifa na gaji.
"Kul na kuma ji Tahira, aure hak'urine. Ashe da zaki shiga ki dubi rayuwar da wasu matan suke ciki a gidajensu Toh cewa zaki yi ke da auren har abada. Aminu zai yi magana Dada ta hana shi furta komai. Mayar da Tahira ta yi, haka tana ji tana gani kuma ta koma."




mrs Bukhari ce


*TALLAH*
Ina kuke amare uwayen gida kai har ma da ƴan mata? Ko kun san Mrs Bukhari mai kayan ƙamshi, ai in dai batu na kayan ƙamshi gyaran jiki da na ɗaki to kai tsaye ku ne mi Badi'at domin gwana ce ta ko wanne fanni a ciki. "Wai ƙamshi kina nufin Badi'at dai marubuciyar nan tamu mai nishaɗantar da mu?"
"Tabbas Fati ita take magana, ai kin dai ji yadda ake magana a kai na, hatta me gidana ya jinjinawa Badi'at domin duk wani ƙamshi da zaki ji a jikina tare da gidana to daga ita ne, ke me kankat ma har gyara na nake yi domin gyaran aurena daga gareta ne, shi ya sa bana wasa da gyaran jikina da na gidana har kuke kirana da ƙamshi."
"Eh tabbas nima na jinjina mata, kuma zaki bani addireshinta domin nima na kwankwati wannan garaɓasa. Ko zaki iya faɗa mini

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login