Showing 6001 words to 9000 words out of 37665 words

Chapter 3 - ANGULU DA KAN ZABO Complete by BADI'AT IBRAHIM .txt

ce ta zubo ta bani na sha. a hankali na sakko gandirobobinnan su sukai mun garkuwa. Jamila na biye damu har zuwa bakin motar gidan firzin. Hafsa ce ta iso, gabana sai da ya fad'i dana kalli tashin hankalin dake shinfid'e akan farar fuskarta. Amma bani da damar tsaiwa in saurari 'yar uwata. Inaji ina gani aka shiga dani cikin mota da ledar magungunana. Jamila ta yi carab ta rik'e hannun Hafsa dake k'ok'arin zubewa. Ni dai ina kallonsu har muka fice a cikin Asibitin.


"Lafiya Hafsa meke faruwa dake haka? Dr ne ya katse zancan nasu da cewa.
"Kud'in gado kune zaku biya ko yayanku ne?" Jamila ta nemi waje ta zaunar da Hafsa tukunna tare da ajjiye basket d'in da tazo dashi gefe. Aminu ta hango yana shigowa. Ajjiyar zuchiya ta sauke.
Hannu ya ba Dr su ka gaisa, sannan Jamila ta gaisheshi, Hafsa na zaune sai haki take fama dashi.
"Sallamarta aka yi ne Dr? Aminu ya tambaya a kid'ime.
"Eh Aminu jikin nata yayi sauk'i babu laifi, anyi mata allurai kuma an had'a magunguna zuwa dai wani watan zasu kawota a kuma dubata. Yanzu nake musu maganar biyan kud'ima." Aminu ya dafe kanshi kawai shi abunda ya so shine a barta a asibitin har sai ta warware. Amma ya zaiyi bashi da ta cewa. Bayan likita yabi zuwa ciki, ya biya duk abunda ya kamata ya fito."
"Hafsa karki jefa kanki a masifa meke faruwane?" Cikin nunfarfashi Hafsa tace.
"Na riga na jefa kaina a masifa ai Jamila, wallah sai naji Yaya Hauwa ta bani sha'awa dama nice ita, in tafi can in k'arke rayuwata hankali kwance. Kuka ta fashe dashi mara hawaye sai dai gunji, a haka Aminu ya fito ya samesu a wajan Jamila na rarrashin Hafsa kamar wata yarinya k'arama. A tunaninshi sabida Hauwa suka shiga wannan halin, shima taya Jamila rarrashin Hafsa yayi. A tare suka fito kowa ya kama gabanshi.
A kasuwar 'yan kaba Aminu ya had'u da Saminu, nanne kasuwar da yake yin dakon kayan gwari da kayan lambu."
"Yaya harka fito daga asibitin? Saminu ke tambayarshi
"Na fito, kafin inje har ma'aikatan gidan yarin sun nemi sallama an basu, banma samu damar ganinta ba."
"Ah ke duniya, yanxu Hauwa zata k'arashe rayuwarta a gidan kurkuku,? Duniya abun tsoro ce Aminu." Murmushi kawai Aminu yayi yace.
"Saminu Dada ta bani shawarar yin sana'ar saida kayan gwari a tebur kamar yanda nayi a shekarun baya, abunda yasa nace zanzo wajanka kenan tunda anan wajan kake aiki, kai kasan yanayin kayan." Murna ce ta bayyana k'arara a fuskar Saminu yace.
"Kai masha Allah da jin wannan daddad'an labarin, wallahi ni kaina da zan samu jari zan bar wannan aikin wahalar, ko tallar kwakwa ni sai in yi. Aminu ya dubi Aminin nashi wanda yai mai dukkan alkhairai a rayuwarshi, tun suna yara in zai fad'i Saminu ke tayar dashi da ikon Allah, Har Ragon sunan d'anshi ya tab'a shiyarwa ya ba Aminu kud'in. A lokacin yana cikin tsananin buk'atar kud'in, Ragon da ba'a yanka ma yaronnan ba kenan, sannan ya taɓa bashi ragon sunan daya siya, yana jiran haihuwar Farida matarshi ta farko, shi kuma a lokacin Hauwa ta haifa mai Mardiyya. Ajjiyar Zuchiya ya sauke, yasa hannu a ajjihu ya zaro dubu goma, ya raba ta biyu ya mik'ama Saminu dubu biyar, cikin tuhuma Saminu yace.
"Meye kuma wannan?"
"Kai dai karb'a abokina. Hannu yasa ya amsa yana sauraron me Aminu zai ce mai.
"Dubu biyar ce ka ja jari, shawara ka sari lemo da kankana ka kafa teburi a kusa da nawa, ni ina da teburina a gida, nima zan sari gwari ta dubu biyar." Hawayene suka sulalo a kumatun Saminu yayi yink'urin yima Aminu godiya amma fur ya hana shi."
"Haba Saminu kafa huce haka guna, Amini kake a wajena, k'ila kuma siriki. Dariya suka saka harda tafawa.
"Yanxu abunda za'ayi teburi zamu bazama nema, muje wajan kafintoci muga ya za'ayi, sai mu nemi inda ya dace kuma mu rok'a mu kafa teburin namu, in yaso zuwa gobe da sassafe kai kayi 'yan lemo na'ibawa, ni kuma inyo 'yan kaba, ma had'e a wajan sana'a." Hakan kuwa akayi, gari suka shiga dan neman inda yayi fuskar jama'a dan su nemi alfarma su kafa teburansu. Amma sun wahala gashi ba'a samu ba, sai bakin titin Galadanci dai layin su Aminu anan suka samu aka amince musu gindin wata bishiya. Sannan suka nufi wajan kafintoci nanma aka yi teburi, suka kawo gindin bishiyarnan kowa ya kafa nashi.


Mardiyya kuwa, ta jima a gaban kaskon masarta kafin ta k'are, har mai k'osan kusa da'ita ta kammala kasuwancinta ta tafi gida, ita tana zaune masa bata k'areba, sai wajajen sha d'ayan rana ta k'are. ta tattara inata inata ta tafi gida.




Hauwa
Gidan yarin Kurmawa
motarmu ce ta shiga gidan yarin. Ahankali gandirobobinnan suka taimaka mun na fito, wani irin sanyi da jiri ke damuna. kai tsaya aka wuce dani block d'inmu cikin d'akinmu. Babu kowa a cikin d'akunan baki d'aya, kuma banga kowa a cikin yadin ba. Bayan na zauna a gadona saina dubi gandiroba guda nace.
"Dan Allah ina 'yan uwana suka je, naga babu kowa?" Saida ta mik'amun ledar maganina na amsa sannan tace.
"Yanzu lokacin d'aukar karatune, wad'anda basu da ra'ayin karatun kuma suna d'akin koyon sana'a dan dogaro da kai." Idanuna da suke mun yaji na lumshe, bance mata komai ba.
"Ki daure kisha magungunanki sai ki kwanta." Kai kawai na d'aga mata, kwanciya nayi dan bana buk'atar tsawon rayuwa balle har in samu lafiya, addu'ata da fatana shine Allah ya d'au rayuwata in huta. Nan rayuwarmu ta soma dawomun turyan turyan a kaina. Da tunanin dama hannun agogo zai iya komawa baya da ba haka zan kasance ba, duk da bawa baya wuce k'addarshi a rayuwa.


*Asalin labarina da ahalina*




*TALLAH*
Ina kuke amare uwayen gida kai har ma da ƴan mata? Ko kun san Mrs Bukhari mai kayan ƙamshi, ai in dai batu na kayan ƙamshi gyaran jiki da na ɗaki to kai tsaye ku ne mi Badi'at domin gwana ce ta ko wanne fanni a ciki. "Wai ƙamshi kina nufin Badi'at dai marubuciyar nan tamu mai nishaɗantar da mu?"
"Tabbas Fati ita take magana, ai kin dai ji yadda ake magana a kai na, hatta me gidana ya jinjinawa Badi'at domin duk wani ƙamshi da zaki ji a jikina tare da gidana to daga ita ne, ke me kankat ma har gyara na nake yi domin gyaran aurena daga gareta ne, shi ya sa bana wasa da gyaran jikina da na gidana har kuke kirana da ƙamshi."
"Eh tabbas nima na jinjina mata, kuma zaki bani addireshinta domin nima na kwankwati wannan garaɓasa. Ko zaki iya faɗa mini abubuwan da take sayarwa.?"
"Bari na faɗa miki akwai...


Humra
Kulacca
Sudanese Humra
Kulacca ta gashi.
Turaren wuta ɗan gaske, iri daban daban.
Turaren mopping
Room freshner
Turaren turara kaya.
Turaren wuta na toilet
Sannan akwai ingantaccen maganin infection
Ina da magungunan mata, wanda zai gyara amarya da uwar gida.
Wanda zasu shiga daga ciki kuma
Akwai sabulun amare, da dilka ta amare, wanda zaisa amarya ta fito ta haska tas
Kabbasa
Setin kujerar tsugunno
Sannan inayin turaren wuta da kasko, da ashana wanda ake rabawa a taron biki ko suna.
Ina bayar da sari.


Ma sha Allahu to taya zan sameta domin mallakar nawa?


"Kai tsaye zaki mata magana ta whatsApp ko kiranta ta wannan number.


08179523215




*TALLAH*
A yau nazo muku da manya manyan magunguna domin gyaran Auranmu! Saboda yadda zamantakewarmu ta AURE keta kara tabarbarewa. Mata iyayenmu ku fito ku gyara jikinku , domin wallahi har Abadan macen da bata gyara bata isa ta hada kanta da mace me gyara ba har abadan! Mu gane yaku yan uwana mata, ma’aurata! wallahi gyara shine mace Akwai mata dayawa dasuka san magunguna na, a online Suna siya kuma Alhmdulillahi ba wadda ta siya bata dawo tamin godiya ba, Alhmdulillahi!Alhmdulillahi! Alhmdulillahi! Yawancin mata dayawa na nemana ta dayan sim dina sede nayi losing dinsa sede wannan shi yake Aiki 08104335144, A YAU NAZO MUKU DA MAGUNGUNA INGANCI DA IZININ UBANGIJI, WATO AINIFIN HADI Iri ~iri na MALLAKA D’ANA MIJI ALFARMAR ANNABI SAW, ina tabbatar muku da magunguna na babu shamaki base na tsaya bata lokaci a bayaniba zanso ku gwada dan tantance GASKIYA * Akwai cututtukan dake hana maganin mata aiki idan kinason sani ki tuntubeni ta wannan lambar 08104335144 wadannan cututtukan inhar kinadasu wallahi duk maganin daza kisha bazeyi Aiki ba, kuma bazaki taba fahimtar komiba a harkar dadih na magungunan mata.


*MUNADA MAGUNGUNA AVAILABLE KAMAR HAKA*👇🏽


*ingantaccen maganin infection *


Ingantaccen maganin basir


Ingantaccen maganin gyaran nono


Ingantaccen maganin gyaran hips


Ingantaccen maganin kara kiba kiyi dumur~mur dake


Ingantaccen maganin rage tumbi meyi tsakani da Allah


Ingantaccen maganin matsin farji mesa dadin farji ga azzakarin d’ana miji.


Ingantaccen MALLAKA TA DOMIN ALLAH (Bata harkoki) shine sunansa, hmmmm Wannan magani inada tabbaci a kansa shidin hadine kawai na mallakar d’ana miji akwai komi a cikinsa na mallaka hajiya ki gwada kisha mamaki Alfarmar Annabi SAW.


Se matsin (GAMADIDI) wannan matsi in kikayi amfani dashi har abadan abidina mijinki baze kawo a gaban wata ya mace ba in har ba gabanki bane wannan inada tabbaci a knsa 💯 kuma wadanda suka saya ma sun kara tabbatarmin da kyaunsa na mamaki.


Akwai zallan hadi na amarya


Akwai hadi na uwar gida sarautar mata wannan seat ne akwai komi a cikinsa.


Akwai ingantattun gumba iri iri kamar haka 👇🏽


Akwai gumbar Madara
Akwai gumba me rubutu 🤐
Akwai gumbar kankana
Akwai gumbar giginya (sa megida kuka)
Akwai ingantacciyar gumba me suna (BARIN MAKAUNIYA)
Akwai gumbar hasi
Akwai zallar gumba wadda ita ta rubutuce zallarta zaki ganta baka karki damu Aikin kawai zaki duba 😉
Akwai gumbar gero
Akwai gumbar ridi
Akwai gumbar garin gamadidi ita ta mallaka ce zallarta.🤐


Akwai tsumi iri iri sunansu sha yanzu magani yanzu 💯👇🏽


Akwai tsumin kankana
Akwai tsumin baure
Akwai tsumin rubutun Ayar Allah
Akwai tsumin kwakwa
Akwai tsumin giginya
Akwai tsumin GORON SUDAN (wannan special ne dan kudinsa ma daban yake)
Akwai ingantattun magunguna na tada shaawah kama daga na turawa har zuwa na Islamic wato namu na gangajiya. Akwaifa maganin maza madam na hausa dana turawa 😉 duk basuda side effects 👌


Akwai rubutun mallaka
Akwai zoben mallaka
Akwai hayakin mallaka
Akwai zani na mallaka
Akwai hadin ci da kaza
Akwai hadin yan shillah
(Muna dafa kaji da yan shillar ma dade sauran abubuwa da dama,)
Akwai dambun nama na mata wanda ke dauke da magungunan sirri na mata mesa tsantsi da laushi da ruwa a farjin mace 😉


Akwai magunguna na ban mamaki wadanda base na rubutasu ba saboda SIRRI 😉
Muna aika magungunan mu kasa kasa gari gari *UWAR GIDA KI GARZAYO QUEN SANAF Islamic chemist kise magunguna na ingantattun ne insha Allahu kin wuce takaicin d’ANA MIJI * direct to me 08104335144 muna sauraron masu shawarwari a kan zaman AURE insha Allahu, amma in knsan baki shirya siyan magungunan jima’i ba na mata ko na maza pls karki kirani.


_Ummu Maheer_
*DINYAR MAKAHO*




_Miss Hajo_
*KHADIJATUL SABREEN*




_Mrs Bukhari_
*ANGULU DAKAN ZABO*


_Ummu Affan_
*SANDAR MAKAUNIYA*


_Mom Islam_
*TSAUTSAYIN TAUNA*


*Ga tsarin yanda biyan yake*


_Guda d'aya 300_
_Guda biyu 500_
_Guda Ukku 700_
_Guda hudu 800_
_Guda Biyar 1k_


Kai tsaye zaku iya turo kuɗinku ta wannan hanya.


0037219728
FATIMA RABIU SUNUSI
StanbicIBTC BANK


Shaidar biya ta nan


0810 433 5144


Masu turo kati MTN ta wannan number.


0702 616 6536


Ƴan Niger zaku turo da naku kai tsaye ta wanna number.


0706 860 6171


*Mun gode da kasancewa da gawurtattu biyar taku na biyu* 🤘🏿


mrs Bukhari ce
[09/12, 19:49] Badi at: GAWURTATTU BIYAR
DAGA ALK'ALAMIN
BADI'AT IBRAHIM
MRS BUKHARI (B4B)


*ANGULU*
*DA*
*KAN ZABO*
GAWURTATTU BIYAR ✋🏻


3/4










A daidaita sahun su Mardiyya ne ya sauke su a bakin titin anguwar galadanci, ta ja hannun k'annenta suka soma takawa.
"Anty mardiyya Mami tana gidan su Dada ne itama?" Cewar Fatima k'aramar k'anwarsu mai shekara bakwai Zara'u me shekara goma sha biyu tace."
"Fatin mami, Mami bata nan ta yi tafiya ba yanzu zata dawo ba" Mardiyya me shekara goma sha shida. babbar 'ya a wajan Hauwa da Aminu ta kasa cewa komai, sai had'id'iye kuka take yi."
"Mardiyya" Dam gabanta ya fad'i data jiyo amon muryar Muktar wanda tun sanda abun ya faru take wasan b'uya dashi. Cak ta tsaya, Zara'u kuma ta kama hannun Fatima suka soma gaba, bayan sun gaishe da Muktar.
Gefe guda Mardiyya da Muktar suka samu, a gefen wani d'an dakali suka zauna."
"Ya k'arin hak'urinmu kuma Mardiyya?" A mugun tsarge tace.
"Mungode Allah, ina yini muktar." Idanu ya lumshe ya na jin sonta na nunkuwa a zuchiyarshi. mardiyya yarinyace mai nutsuwa da shegewa rai ta yi daram, sabida kyawawan d'abiunta da su kai mata k'awa.
"Lafiya lau Mardiyya, yaya ake ciki maganar case d'in Mami?" Kai ta sauke ta soma kuka k'asa _k'asa. Kallonta yayi cikin tausayawa yace."
"Ya isa daina kukan Mardiyya kinji ko? Dama wata magana na zo miki da shi, wanda ya dace ace kin ji tun wuri, sai dai bamu samu damar keɓewa ba sai yau. Amma ki mun uziri ba laifina bane." Da sauri ta d'ago idanuwanta sharkab da ruwan hawaye, tace."
"Iyayenka sun janye maganar Aurenmu ko, a sakamakon abunda mami ta aikata ko Muktar? Wani malolo ta had'iye mu'kut. taci gaba da ajjiyar zuchiya.
"Eh Mardiyya hakane, wallahi sun matsa akan lallai sai dai in hak'ura da auranki..." Saurin dakatar dashi tayi, ta hanyar d'aga mishi hannu, shiru yayi ya zuba mata idanu. Hak'ik'a ya gasgata son da Mardiyya take yi mishi, kuma ya gamsu da ita a matsayin uwar 'ya'ya. Amma ya zaiyi iyayenshi, da mahaifiyar Mardiyya sun sa shi a uku."
"Na ji Muktar na fahimta, Muktar bazan mutu ba in ka rabu dani. A halin yanzu nafi son in zauna in kula da k'annena in basu kariya kuma." Mik'ewa tayi ta soma tafiya ta share hawayenta tas.
"Mardiyya ki tsaya kiji dan Allah." Ko waige ta kasa yi, sai sauri take ta zubawa bata ko iya ganin gabanta. Hannunta yayi maza ya rik'e a zafafe ta juyo tare da fisge hannunta.
"Meye Muktar. kafison kaga na sume ko na mutu sabida ka rabu dani ko? Toh bazan mutu ba, hakan ma dama ya bani da zan ci gaba da karatuna, kuma in kama sana'a. Sadakinka ka turo a karb'ama abunka." A marairaice yace.
"Wallahi Mardiyya na bar miki duniya da lahira." Murmushin takaici Mardiyya ta yi mishi tace."
"Nagode" Tafiyarta ta yi ta barshi a wajan.
A guje ta shiga cikin gidan tana isa kan tabarmar da ta ga su Dada a zaune ta hau, ta fashe da wani irin mugun kuka mai shesshek'a. Dada ta bar kwad'on garin rogon da take yi ta ce.
"Menene ya faru Mardiyya, an yanke ma Hauwa hukuncinne? Kallon su Zara'u Dada ta yi tace."
"Zara'u d'auki kwad'onnan ku shiga ciki, ki d'iban muku naku, saiku rufema yayarku sauran. Saida taga su Zara'u sun shiga ciki sannan ta kuma duban mardiyya tace."
"Mardiyya fad'amun menene?" Cikin muryar kuka tace.
"Dama Muktar ne wai iyayenshi su ka ce bazai aure ni ba, sun fasa. Mami kuma an yanke mata hukuncin d'aurin rai da rai." Sallallami Dada ta shiga yi, tare da tafa hannayenta biyu tace.
"Ni haihuwar fulani, Hauwa ta jawo muku abun fad'en da har abada ba'a dena fad'e ba. Gaku yara mata." mardiyya ta dubi Dada tace.
"Ni Dada inaso in ci gaba da karatuna, sannan ki rok'amun Abba ko da waina in dinga toyawa a waje da yamma, domun mu d'an dinga juyawa." Hawaye Dada ta shiga zubarwa na Tausayin Aminu da yaranshi, Hauwa ta cucesu sosai."
"Mardiyya kar ki bari takaici da bak'in cikin d'a namiji da takaicin rayuwa ya durk'usar dake, ni inaso ki bar batun karatu ki fad'a koyan sana'ar hannu, ko dan ki dinga taimakama k'annenki tunda kinga Abban ku bashi da hali sam, ni abunda nake so kenan amma sai abunda kika ce." Mardiyya ta share hawayenta. bakinta na yi mata d'aci tace."
"Dada na d'auki shawararki wallahi, kinga su Zara'u sa samu su ci gaba da karatu in Allah ya so, amma wainar ma inaso in soma toyata zuwa gobe." Dada sai lokacin ta d'anji sanyi a ranta tace."
"Gobe kuma? Ai dole sai da jari Mardiyya. a k'alla kina buk'atar nera dubu uku kafin ki soma toya waina, tunda kinga za'a sai shinkafar tuwo ga cefanen kayan miya, ga kuma su itace da man suya, ai sai mun had'a kud'in mardiyya."
"Dada Muktar yace ya bar mun sadaki halak malak harma na yi mishi godiya, ki bani dubu uku zuwa yanma inyo cefanen komai da komai sauran ki ba Abba yayi amfani dashi." Dada tace.
"wayyo Allah Mardiyya Allah yayi albarka kinji, Allah ya sanya muku salama da juriyar rashin Hauwa. Wancan d'akin saiku gyara ke da k'annenki kuma saiku dinga kwana. Abbanku kuma zai koma shagon waje da kwana, Allah ya k'ara rufa asiri, kece babba mardiyya ki duba k'annenki domun yanzu kallon uwa zasu dinga yi miki , duk da dama kece ke ɗawainiya dasu, tun ƙarfinki baima kaiba. Amma yanzu dai ba Hauwa, tunda a kurkuku zata ƙarashe shingin rayuwarta, sai kin cire damuwa a ranki tukunna. Gashi 'yan uwan gyatumar taki suma fama suke yi da kansu wannan rayuwa sai dai godiya kawai, taso muje in taya ki gyaran d'akin. Dada da mardiyya suka gyare d'akin tas su ka sanya wani cinyayyen labule da wata guntuwar tabarma. mardiyya ta fice zuwa shagon waje dan gyara ma Abbansu nashi d'akin, cikin awa guda ta tsabtace ko ina ta shinfid'a mishi zanen gado a katifarshi mai kamar tabarma. Kullo shagon ta yi ta shiga ciki. Alwala ta yi sannan ta shiga d'akin Dada, tarad dasu ta yi duk suna Allah. itama tada tata sallar tayi. Bayan sun idar Dada tace.
"Mardiyya ki ci kwad'on naki ni zan fita zamu je barkar haihuwar shatu ni da gwamma, in yaso na ari kud'i a wajan gwamma in yo miki cefane ko tunda ta cikin kasuwa zamu ratsa. Mardiyya tace.
"Yauwa Dada kinga na huta shikenan. Sai kun dawo." mai Dada ta shafa ta sake saka kwalli ta d'auki mayafinta ta fice."
"Anty Mardiyya anan gidan zamu zauna kenan har da Abba?" Zara'u ce ta yi mata tambaya, Fatima kuwa tsakar gida ta fice ta na ta wasanta abunka da yaro.
"Eh Zara'u kinga Abba ya samu damar sanya matar da zai aura acan kinga ya samu sauk'i."
"Toh yaushe zai kaimu wajan Mami kuma?"
"Toh Zara'u Mami yau aka tafi da'ita, kuma kinga sun je dubata yau, sai dai in zai kuma zuwa sai ku bishi kuje tunda kunason ganinta." Hawayen bak'in ciki da takaici mardiyya take

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login