Showing 21001 words to 24000 words out of 49794 words
Chapter 8 - GOJE SADAUKI UMAR RETURN NA BINTA UMAR ABBALE .txt
mata hudu suka cancanta da kai amma ace ma ko daya babu." cike da alhini ya kare maganar.
Sai abun ya bashi dariya ya dan dara kafin yace." Asp matsalar mata nada yawa shiyasa nayi zamana a haka ba wai don bani da bukata ba, kawai nafi bukatar kwanciyar hankalina nayi duk abinda nake so ba tare da wani ya caza min kai ba.''
Yace." To ai hakan nan ake hakuri dasu da matsalarsu Umaru kowane maigida yana da matsalar iyali mussaman idan mace fiye da d'aya yake da ita, dole ba zaka rasa shi da matsala ba, nima matana biyu sai dai kowacce da gidanta kuma yanzu haka ina shirin yin ta uku da yardar Allah sai na cike domin ina da ra'ayin hakan."
Ya girgiza kai da fadin." Kayi kokari sosai kuma ka aikata sunnah Allah ya baka ikon yim adalci a tsakaninsu."
Ya amsa da "Ameen ya Allah ina fatan kai ma kayi koyi dani."
Girgiza kai kawai yai baya tsammanin hakan domin baya san damuwa ba lallai sai ka tara mata a gidanka za'a tabbatar da jarumtarka ba, shi a ra'ayinsa zai iya 'kare rayuwarsa da mace daya, sai dai kuma duk yanda Allah ya shirya masa rayuwa to zai kar'ba hannu biyu tare da godiya a gareshi.
****
Ke'bantacen guri aka ajiyeshi shi kad'ai ba tare da da sauran yaran sa ba, sai dai su an tattarasu guri guda da sauran masu laifi gama gari. wannan karamcin da Asp din yayi masa ya tsaya masa mutuka a rai yayi ta tunanin irin alkairin da zai saka masa.
***
Uwale duk atamfofin da take k'uzu tana tarawa a cikin adaka fito dasu tayi ta siyar. ta dinga bin tsangaya-tsangaya tana bayar da sadaka domin almajiran suyi mata saukar al'kur'ani akan bukatarta, Allah maji rokon bawansa addua ta kar'bu.
Washe garin ranar da ita da Mahaifin Hamra'u da ita Hamra'un suka yanke shawarar zuwa headquarter 'yan sandan domin samun cikkenan bayani.
Sun jima a tsaye kafin wani jami'i ya sauraresu, Malam Hafi'i mahaifin Hamra'u shine yayi masa bayanin abinda yake tafe dasu.
Yayi jim! yana kallonsu kafin yaja tsaki ya barsu a gurin......Uwale da sauri taje tari gabansa kuka ta fashe dashi ta zube gwiwa biyu a gabansa tana rokonsa, hakan ya janyo hankalin ma'aikatan dake gurin suka fara tambayar ba'asi.
Cikin kuka tace." Me yasa dukkaninku baku da imani ne? tunda muka zo gurin nan babu wanda yayi mana kallon mutunci Allah da Annabi sunfi karfin wasa amma gabadayanku bakwa tsoron Allah."!
Daya daga cikin musulman dake tsaye gurin ne yace." Tayi masa bayani abinda yake tafe da ita.
Hanci ta fyace kafin." Tace "Mun zo gurin UMARU wanda ku ka d'aure kuna zarginsa da ta'addanci bayan ba haka gaskiya take ba."
Yace." Yi shuru ki kwantar da hankalinki ki daina kuka zanyi miki kokari yanzu." Ta mike tsaye tana gyara yafan mayafinta, tace."Nagode sosai Allah yayi maka albarka." Ya amsa da 'ameen kafin ya umarcesu da suje su zauna a wata rumfa.
Sai da yaga zamansu sannan ya bar gurin, kai tsaye ofis din Asp ya nufa domin sheda masa abinda ke faruwa.
Ya k'ame da sarawa kafin ya sheda masa abinda ke da akwai, kai tsaye ya bashi umarnin shigowa dasu.
Da kanshi ya nuna musu gurin zama yana musu sannu, Malam Shafi'i da 'yarsa suka zauna kamar yanda ya umarcesu Uwale kuwa kai tsaye kujerarsa ta nufa, ya dinga kallonta har ta iso inda yake ta zube gabansa kawai sai ta fashe da kuka tare da rirrike masa kafafu! kuka take sosai tana bashi hakuri.
Tausayi ya rufeshi da kyar ya iya mik'ewa tsaye sakamakon rikon da tayi masa, ya sunkuya tare da sanya hannu ya dago ta ta mike tsaye, rungumeta yayi yana rarrashin gami da bata hakuri.
Ita kuma fadi take." Ku za'a bawa hakuri ku dubi girman Allah kuyi adalci kada ku yanke hukunci akan wanda bashi laifi bashi ne wanda kuke zargi ba.
Hankici ya ciro daga jikinshi, ya goge mata hawaye yana sake kwantar mata da hankali, sai da ya tabbatar da cewa ta samu nutsuwa sannan ya umarcesu da cewa subi bayan shi.
Kai tsaye ke'bantaccan gurin da aka ajiye shi suka nufa...........Aps din a gaba suna bayansa, yana shiga sai ya basu hanya. gabadaya suka hada ido dashi yana zaune kasan kafet da tire din abinci a gabansa tsaf dashi da nutuswa a tare dashi bashi da wata matsala bayan sararin! dake daure da kafafunsa
Hamra'u da gudu ta iske inda yake, kawai sai ta fad'a kansa tana wani irin kuka! wanda yake nuna tsantsar tashin hankalinta, itama Uwalen da kuka ta karasa gurin duk da ganin da sukayi masa cikin nutsuwa hakan be gamsar dasu ba.
Asp ya juya ya fita yana jimamin al'amarin.
Tun bayan data fad'i jikinsa yasa hannu a bayanta yana dan bubbugawa, a Hankali cikin taushin murya yake rarrashinta, ta dago kai tana kallonsa hawaye sai ambaliya yake a saman fuskarta, kai yake girgizawa alamun ta daina kukan, yasa hannu ya goge mata fuskar sosai yake mamakin irin k'aunar da yarinyar take masa, shiru tayi tana sauke ajiyar zuciya sai dai har yanzu bata saki hannunsa ba ta rike tsam a hannunta.
Ya d'ora idonshi kan Uwale da ta dage tana kuka sai kace wacce aka nuna mata gawarsa.
Murmushi yayi tare da mika hannunshi kan fuskarta hawayen ya share mata da fad'in." Kukan bashi da Fa'idah Uwale addua zaki min."
Tace."UMARU kukan shi yake kansa yin kuma shine samun salama, amma a zahirin gaskiya muna cikin tashin hankali bamu da kowa sai Allah shine kuma zai fitar damu."
Yace."Kin gama magana tunda ki kace Allah, kuma gaskiya tayi halinta tun kafin tafiya tai nisa gaskiya ta bayyana cewa wanda suke zargi bani bane nima kuma na san da hakan saboda haka ku kwantar da hankalinku insha Allah zan fito lafiya na cigaba da rayuwa da ikon Allah."
Tace."Idan hakane mai yasa basu kwance maka wannan d'aurin ba, duba fa yanda kafafunka suke daure.
Yace."Akwai dalilin da ya sanya hakan wannan ba matsala bace kada hakan ya daga muku hankali."
Kusan a tare suka sauke zuciya da jin furucinsa suka shiga godewa Allah da abinda yayi musu.
Har yamma suna tare ya saki jikinsa sosai yana basu labarin irin gwagwarmar suka sha a dajin! tace."Kaga Umaru shiyasa kwata-kwata hankalina bai kwanta da wannan harkar ba mahaifinka har ya mutu da abun a cikin ransa saboda haka idan Allah yasa ka kubta to dole ka ajiye wannan sana'ar ka nemi wata domin hakan shine samun nutsuwarmu baki daya.
Domin ya kwantar mata da hankali sai ya amsa mata akan abinda take so, taji dadin hakan kuwa tay tai masa addua da fatan samun nasara akan dukkan abinda ya sanya a gaba.
*****
Ta jima a toilet din tana durje jikinta da sabulai iri-iri kafin ta dauro towel ta fito. idonta ya sauka kan tufafi wanda aka ajiye mata su kan gado komai sabo underwears sai riga da siket na wani material mai taushi, goge jikinta tayi kafin ta zauna gaban mudubi tana kokarin duba man da zata shafa a jikinta, tsaki taja tana hararar tarin kayan kwalliyan dake dressing mirror din duk ciki babu kalar man da yayi mata ballantana ta shafa a jikinta........wani lotoin ta dauka tana jujjuyashi a hannunta sai ya mutse fuska.
Ta turo kofar dakin ta shigo da sallama a bakinta kallo guda kayi mata zaka fahimci cewa tana daga cikin jerin mutane masu sauki kai da daukar rayuwa a sannu, tana da fara'a sosai domin da wuya kaga bacin ranta sai in tura ta kai bango.
Fuskarta yalwace da fara'a ta 'karasa shiga dakin da fadin." Yawwa kin fito ko ga kaya nan na ajiye miki na san za suyi miki dadin sawa.''
Shuru tayi bata tanka ba. Ta kalleta da fadin." Ko dai na sauya miki wasu wannan ba suyi miki ba."?
Tsaki taja da fadin." Don Allah kin cikani da surutu haka na duba na gani okey nagode."
Ranta ya 'baci da abinda tayi mata amma sai ta danne ko alama bata nuna a fuska ba tace." Okey to shikkenan idan kin shirya sai ki fito muci abinci ."
Ta'be bakinta tayi ba tace komai ba ta cigaba da jujjuya abinda ke hannunta.
Juyawa tayi da niyyar fita daga dakin. sai ta dakatar da ita, ta tsaya tana sauraranta.
A yatsine tace." Wannan tarkacen mayukan shafawar taki ba zan iya shafawa ko daya a jikina ba domin ni ba irinsu nake shafawa ba.
Cike da mamaki take kallonta tana mamakin furucinta, tarkace!!! duk man da take shafawa babu na kasa da dubu biyar sai sama amma shine har take magana cewa ita tafi karfin ta shafa a jikinta.
Jinjina al'amarin tayi kafin tayi 'yar dariya da fadin." Lallai 'kawata kina ji da gayu amma idan ba haka ba meye laifin mayuka na ko wannan na hannunki kika shafa ya isheki." Cike da wasa ta karashe maganar..........Sai ta fusata! ta mike tsaye tare da buga mata tsawa! da fadin." Ke kin san wacece ni kuwa? da har kike min wannan banzar maganar."? Ta'be bakinta tayi tace." Ina zan sani hajiya ni dai Daddy ya kira ni a waya ya sheda min cewa zanyi b'akuwa shiyasa nake karramaki bahaushe yace." bakon ka Annabin ka."
Dogon tsaki! taja kafin ta koma ta zauna..........Ita kuma da sauri ta bude kofar dakin ta fita tana mamakin al'amarin.
Zama tayi tare da sauke ajiyar zuciya, ta kalleta da fadin.'' Ya akayi ne? bata gama shiryawa bane."?
Baki ta dan ta'be kafin tayi 'yar dariya da fadin." Na isketa ta fito daga wanka tana nazari man da zata shafa."
Cike da mamaki tace." Kamar yaya nazari duk cikin mayukan shafawar taki babu wanda yayi mata."?
Tace."Hakan take nufi."
Tana kokarin magana motsin fitowarta ya katseta duk sai suka juya suna kallonta tayi kyau sosai a cikin material din sai dai siket din ya matseta dalili tana da kwankwaso mai fadi da cika sakamakon mai kayan da nata bai kai hakan ba.
Da murmushi a fuskar matar gidan tace." Kin fito."? "Umm." tace kawai ta nemi kujera ta zauna sai wani basarwa take.
Ta kalleta da fadin." Nabila mai yasa ki ka bata wannan kayan kamar sun matseta ki tashi ki dauko mata wasu."
Tace."Mommy kin san duk kayana riga da siket ne kuma bai zama dole suyi mata yanda takeso ba tunda ta fini kiba."
Ta kalleta da fadin." Zinatu baki takura ba dai ko."?
Girgiza kai tayi da fadin." Kada ki damu hakan yayi min daidai domin yawancin kayana haka suke." Tace." To masha Allah ku tashi muje muci abinci." kusan a tare suka mike kai tsaye gurin cin abincin suka nufa.
To duk wasu bayanai da ya kamata ace gwamnati ta san dasu Asp ya harhad'a komai ya turawa maigirma governor domin ya saurara dashi da wa'inda da ke da alhakin hakan, sai dai ya sheda masa cewa ranar asabar shi da wanda ake zargi da aikata ta'addancin zasu shiga sansanin domin binkice akan sassan sannun da zai tabbatar da gaskiyar magana. maigirma governor yayi na'am da maganar ya kuma bada goyon baya akan tafiyar.
*'Yan jarida mane ma labarai suka samu abun yayatawa a gari! gidajen redio da television gami da jaridu labarin abinda suke nunawa kenan cewa ashe wanda ake zargi da *UBAN DABA!* *bashi da ala'ka da zargin da ake masa asali ma shine mutum na farko wanda ya fara karya alkadarin d'an ta'addan da ya addabi kasa da al'ummar dake cikinta, domin tabbatar da gaskiyar magana kakakin rundunar 'yan sanda wato Asp Musa Baharu zai jagoranci shi wanda ake zargi domin gudanar da binkicen sassan hannun wanda ake nema ruwa a jallo...........Sannan kakakin rundunar 'yan sandan ya shedawa mane ma labarai cewa yanzu haka akwai d'iyar Sarkin Kano mai suna Zinatu wanda ake zargin cewa wasu 'bata gari sunyi kidnapping d'inta domin samun kudi daga gurin mahaifinta, amma ha'kan su bai cimma ruwa ba sakamakon zuwan shi wanda ake zargi da ta'addanci mai suna UMARU wanda jama'a suka fi sanin sa da GOJE!* *shine wanda ya zama garkuwa a gareta har yayi nasarar tallafar rayuwarta bayan ya samu nasara akan wa'inda sukayi garkuwa da ita............Wannan shine cikakken rahoton da ya cika garin Katsina dama kewayanta.*
Duk wanda ya danganci masarautar yana cikin farin ciki sakamakon samun cikkaken labarin bayyanuwar ta............Fada ta cika da jama'a masu zuwa taya murna da fatan alkairi maimarta da 'yan uwansa fuskokinsu tamkar gonar auduga saboda tsantsar farin cikin da suke ciki a ranar yini cir masarautar babu masaka tsinke mata da maza wannan ya fita wannan ya shiga.
Gimbiya Aysha da 'yar uwata tare da 'ya'yansu su ka kasance cikin farin ciki mara misaltuwa, Maijidda ma tayi nata murnar daidai gwargwado amma ta ciki na ciki domin kasa zama tayi cikin 'yan uwanta ta nufi b'angaranta jikinta duk a sanyaye yanzu babbar damuwarta kada asiri ya tonu sunanta ya fito shine abinda yafi tsaya mata a rai....
*Hello my fans A hanzarta biyan kudi domin yanzu zamu shiga cikin labarin akwai kuraa!! 😄 kada ki sake ayi bbu ke 'yar uwata kada ganin k'yashi ya hanaki biya ki zauna jiran na sata wallahi tallahi! hakkin wani masifa ne!! mai girman gaske!! yi kokarin gudun haram! komai kankantarta!!!*
*#500 via 0542382124...Binta umar gtbank, idan kati zaki tura ki min magana ta WhatsApp da wannan number... 07084653262........Mutanan Nijar ku tuntunbi wannan number....*
*22796074090* dala dari katin mov ko airtal
*GOJE!*🏹
🐕🦺🐕🦺🐕🦺
_(SADAUKI OMAR RETURN👑💫_)
*BINTA UMAR ABBALE🍒*
*_MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION🖊️📚_*
_____________________
FREE PEGE
*23&24*
*Biyu da rabi na sulusin dare!*
Cikin firgitaccan yanayi ta tashi zaune tana kiran sunan Allah! hakan ya janyo farkawarsa dama can bashi da nauyin bacci, zaune ya tashi kafin ya rike hannunta dake wani irin rawa, yace."Menene Aysha."? Sai kawai ta fashe da wani irin kuka ta rungumeshi tana girgiza kai da fadin." Zinat ce ranka ya dade yarinyar nan na cikin mugun yanayi Allah ya nunan hakan a mafarkina."
Sake rungumeta yayi a jikinsa cikin sigar rarrashi yace."Aysha mafarki ba gaskiya bane kada ki gazgata abinda ki ka gani, bana tsammanin cewa mafarkinki zai tabbata, jikina yafi bani cewa yarinyar nan tana a raye kuma daf take da ta dawo garemu da ikon Allah."
Kallonshi tayi hawaye na tsere a saman fuskarta tace.''Ranka ya dade koda Allah ya nufa yarinyar nan ta dawo gida bai zama lallai a sameta da cikakkiyar lafiya ba ka san dai yanda duniyar nan ta lalace da rashin gaskiya wannan shine babban tashin hankalina."
Ya sauke ajiyar zuciya da fadin." Kada ki fadi haka Aysha! zuciyarki ta dinga halarto miki alkairi akan yarinyar nan! adduarki a gareta karbabbiya ce a gurin Allah, kada ki yarda zuciyarki ta yarda da wannan mafarki ki dauka cewa k'anzon kurege ne, a yanzu abinda zakiyi ki faranta min shine ki tashi kije ki dauro alwala ki gabatar da nafila a gaban ubangiji kana ki mika masa kukanki."
Ta sauke ajiyar zuciya da jin sassauci acikin zuciyarta, a hankali ta zame jikinta daga nasa ta sauka daga gadon ta nufi toilet domin daura alwala.
Tana fitowa shima ya tashi ya shiga ya daura alwalar ya fito, lokacin har ta tayar da sallar, jallabiya da gajeran wando ya sanja kana ya gyara dadduma shima ya tayar da tashi sallar.
******
Tun bayan daya sa'ba ta a kafad'a suke buga artabu a tsakanisu, rikon tsauri! yayi mata yana gudu tare da tsallake manya-manyan dutsina da ita a kafadarsa! tayi duk wani kokari gurin ganin ta ceci kanta abun yaci tura! domin mutumin mugun basamude! ne wanda cizo da yakushi basa shigarsa! dukansa take tana cizo duk ta dauke masa fata amma ko ajikinsa, ya riketa katamau! yana gudu! burinsa kawai ya kaita gaban ogansa ya san hakan zai faranta masa rai.
Hakan ne ya kasance kuwa, Ogan nasu yana cikin bacin rai! mai tsanani sakamakon rashin samun nasara! bai ta'ba fuskantar irin hakan ba sai a wannan lokacin, kai kawo kawai yake gurin ya rasa abinda yake masa dadi! ............Amma zuwan babban yaron sa da yarinyar ya faranta masa rai! mutuka, sai kawai ya kwashe da wata 'yar iskar dariya kafin yayi wani irin tsalle! da juyi na jin dadi, ya zuba mata kwala-kwalan idanuwansa!
Bakinsa kawai yake lasa, jikinsa na wani irin tsuma! komai na yarinyar yayi cif da cif! bata da makusa, cikakkiyar mace irin wacce ya jima bai kwanta da irinta ba!
Gurin ya tsit! gabad'aya yaransa sun zagayeta motsin kirki ta kasa, kanta ne ma yake juyawa a gurin, dishi-dishi! take kallonsa har ya karaso inda take zube!
Ya tsugana kusa da ita, sai tayi saurin janye jikinta, ya sha kunu; tare da matsawa jikinta, ta sake janyewa tana watsa masa mugun kallo!
Mahaukaciyar dariya yayi! ya cigaba da lasar lebansa, yana bin sassan jikinta da wani irin kallo na tsantsar sha'awa! Hannu ya kai jikinta, a zabure! ta fitar da hannu ta bashi kyakykyawan mari a fuskarsa! ko gezau! beyi ba sai dai yaransa da suka zabura! sukayi kanta!
Ya daga musu hannu da basu umarnin matsawa baya.
Suka matsa can nesa suka bar shi da ita, zaman dirshan yayi a gabanta ya mika mata tafkekiyar fuskarsa dake cike da kasumba! yace. " Idan hakan yana miki dadi ki sake aikatawa." Ya fada yana sake tura mata fuskar.
Tsaki mai tsayi taja! ta matsa nesa dashi! ya rarrafa kan gwiwarsa ya cimma inda take! kafafunta dake daure da takalmi ya tsirawa ido, babu abunda yafi tafiya dashi irin shara'ban kafafunta, ya kai hannunsa gurin yana shafawa da lumshe ido, janye kafarta tayi da fadin." Allah ya isa!!
Ya bude idanuwansa da suka rikice! da zazzafar sha'awarta!
"Ni kikewa Allah ya isa."? yafada yana nuna kirjinsa.
Ba ta amsa ba, wani irin kallon banza take mai,