Showing 27001 words to 30000 words out of 49794 words

Chapter 10 - GOJE SADAUKI UMAR RETURN NA BINTA UMAR ABBALE .txt

wani abun.
Hannu ya daga mata da ido! ya gargade ta, sai ta sunkuyar da kai! amma har yanzu bata dawo daidai ba.




Ya kalli Alba da fadin." Bani abun rubutu."


Da sauri ya fito da takarda da biro! ya mika masa.
A takaice ya rubuta."




_*(KA SHIRYA YAKI DA MAKASHINKA!!!)*_



Wanda yake da d'an sauran kuzari ya mikawa takardar da fadin." Sa'kona ne wannan kana isa ka bashi, cewa daga ni *MAKASHIN MAZA!*


Da kyar! ya mike ya kama hanya yana tafiya tare da waiwayen d'an uwanshi dake kwance cikin halin rai da rayuwa!




Koda ya karanta wasikar sai kawai ya fashe! da wata mahaukaciyar dariya! da mike tsaye tare da dukan! girkakken dutsen dake gabansa!


Hannuwansa yasa ya tallefe 'keyarsa! tare da sunkuyar da kanshi kasa!


Ya jima a haka kafin ya d'ago yana kallon yaranshi dake kewaye dashi, gabad'ayansu suma jikinsu yayi sanyi da wannan al'amarin.


Ya kalli Nuhu dake rakube! gabadaya kammaninsa sun sauya saboda wuyar da yasha, ranshi ya sake 'baci! kawai ba tare da kowa ya ankara ba, ya fille wuka! tana! walwali a wuya ya burma masa! a take ya fara shure-shure a gurin jini sai tsartuwa yake, kafin wani lokaci rai yayi halinsa!


Ya juyo kansu a sukwane! yana kallonsu da kwala-kwalan idanuwansa! Sun tsorata mutuka gaya da ganin tashin hankalin maigidansu.


*"Cike da cin laya yace."Kamar yanda na soke! wuyan wannan shashashan! to haka zan soke! wuyan wannan marakunyar yaron daya tunkari inda nake! Ni! nayiwa kaina wannan alkawari!! saboda haka zamuyi kwankwance! kafin mu afka inda suke da yak'i."*


Suka hada baki gurin fadin."Yanda kayi shine daidai maigida muna goyon bayanka ako wane yanayi."


****
Tun bayan tafiyar Nuhu! babu wani abu daya gilma, hakan besa sun saki jikinsu a gurin ba, sai da duhun dare ya shiga sannan suka fara neman abinda za su ci.


Ita dai 'ya'yan itacuwa kad'ai ta iyaci, tana zaune tana kallonsu sun tada wuta sai gashe-gashe sukeyi da kallon ikon Allah! da kudirarsa, ace wai mutum ya gasa majici gafiya da sauran dabbobi marasa kyau yana ci a cikinsa.


K'auri da karni! duk ya cika gurin! dole ta tashi domin sauya gurin zama, domin mutukar tana shak'ar hayaki da kaurin dake tashi agurin zata iya amayar da abinda taci.


Ido ya bita dashi! be dauke ba har sai da ta samu guri ta zauna can nesa dasu, inda Allah ya takaita akwai hasken farin wata a gurin.


Ta jima a zaune a gurin tana sakawa da kwancewa! sai yanzu ta san ya rayuwa take, ta taso cikin kulawa da gata da komai na jin dadin rayuwa, tunda take bata ta'ba tsammanin cewa akwai ranar da za tayi rayuwa mai muni irin wannan ba! babban tashin hankalinta rayuwa da d'an ta'addah! irin wannan, duk abinda yake a kanta bai janyo masa 'kima da mutunci ba, domin kuwa shine mutum na farko wanda yayi sanadiyar tagayyara rayuwarta, hakika ta tsorota da rayuwa da duniyar ma gabad'aya, A yanzu babban burinta ta samu ku'bta daga cikin wannan dajin, sannan tayi wa kanta al'kawarin ganin ta jefa rayuwarsa cikin kunci da tashin hankali kwantankwacin yanda yayi mata.




Saukar wani abu taji saman wuyanta, da sauri tasa hannu ta buge! ta mike tsaye! wata lafceciyar tsutsa ce ta fado daga saman bishiya.


Rintse ido! tayi tana kiran sunan Allah! kafin taji zirrrrrr a kan kafarta, tayi tsalle ta matsa gefe tana kallon gurin, ashe gabadaya gurin tsutsutsine suke yawo.


Jiki na wani irin rawa ta bar gurin, tana isa inda suke ta iske sunyi shimfida sun gatange gurin da itacuwa tare da rufe gurin da Net!


Tsayawa tayi a gurin ta kasa shiga, domin gabad'ayansu mugun haushinsu takeji! daga nesa ta hangoshi ya nufo gurin, d'auke kanta tayi tare da jan tsaki a cikin zuciyarta.




Koda ya iso gurin bece mata komai ba, ya kama hannunta! kallonshi tayi kamar za tayi magana sai dai tayi shuru, jan hannunta yayi suka shiga gurin.


Guri guda ya zaunar da ita, muryar rarrashi da kwantar da hankali ya aro yace." Ki kwanta anan gurin nayi miki alkawai cewa babu abinda zan bari ya sami rayuwarki."


A maimakon hakan ya faranta mata sai kawai taja masa tsaki! ta kawar da kanta tana zumbura baki!


Hakan da tayi ya bata masa rai amma sai ya danne! be dauki mataki ba ya fara kokarin barin gurin, ta bude baki da fadin." Mamugunci! insha Allah sai naga karshenka."


Maganar ta bashi mamaki mutuka! sai ya juyo da wani irin murmushi a fuskarsa ya nuna kirjinsa da fadin." Me yasa kike so ki kaga bayana."?


Ta zabura! da fadin." Saboda kai din azzalimi ne macuci.!!


Ya jima yana kallonta da mamakin furucinta" Saboda kai din azzalimi ne macuci."! to wai shin da take kiransa da wannan sunayen wane irin zalinci yayi mata tun farkon had'uwarsu?


Still murmushin ya sake kafin ya furzar da iskar bakinshi, cikin gaggawa ya fita ya bata guri domin yana ji idan ya kara second a gurun zai iya nakastata.


Ya jima yana fesar da hayaki kafin ya samu sassauci a zuciyarsa, zazzafar ajiyar zuciya ya sauke! yana me sake jin sautin muryarta na amsa kuwwa! a kunnanta a cikin kunnuwansa, tunda ya taso lokacin kuruciya da girma gwargwamaya yake da *Maza!* bai ta'ba sanya mata a cikin al'amuranshi ba, saboda sanin hallayarsu! yana da tausayi mussaman akansu amma baya yarda da raini daga garesu, mace daya ce yake jinta a cikin zuciyarsa, domin duk ta tara abinda yake da bukata, hankali nutsuwa ilimi tarbiya da sauransu, ita kad'ai! yake ji a zuciyarsa zai rayuwa mai tsayi da ita, ya kai ma'kura a gurin iskancin da yarinyar nan take masa, yana tausaya mata amma ya lura ita bata gani ta daukeshi a matsayin macuci! to yana ganin zai fita daga harkata domin ya samu zaman lafiya. tare da gudanar da aikin dake gabanshi.




*#500 via 0542382124...Binta umar gtbank, idan kati zaki tura ki min magana ta WhatsApp da wannan number... 07084653262........Mutanan Nijar ku tuntunbi wannan number....*
*22796074090* dala dari katin Mov ko airtal




*GOJE!*🏹
🐕‍🦺🐕‍🦺🐕‍🦺
_(SADAUKI OMAR RETURN👑💫_)


*BINTA UMAR ABBALE🍒*


*_MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION🖊️📚_*
_____________________







*RASHIN ADALCI A TSAKANIN MATA*
___________
_*Mata da yawa su kanyi kukan rashin adalci da mazajensu keyi a tsakaninsu. maza kuji tsoron Allah kuyi adalci a tsakanin matanku. lallai wajibi ne kuyi adalci tsakanin matayenku ga wanda yake auran mace sama da d'aya dole yayi adalci, ya sani cewa dukkan abinda yake gudana Allah yana sane kuma yana ganinsa, kuma wallahi sai Allah ya tambayeshi akan zaman da yayi dasu a goben kiyama.*_


*Manzon Allah SAW yana cewa." (Dukkan wanda yake da mata biyu sai ya karkata ga daya baya yiwa dayar adalci, to zai zo ranar alkiyama bangaran jikinsa guda a shanye)*


*Malamai sunce karin aure ba wajibi bane, ba mustahabi bane ga wanda yake da ikon ya 'kara amma wajibi ne kayi adalci, idan har kasan ba za kayi adalci ba to kada ka fara neman k'ara auran ma domin k'arin zai iya kai ka zuwa ga halaka.*
*Manzon Allah SAW yana cewa." (Dukkaninku masu kiwo ne kuma dukkan ku abin tambaye ne akan abinda aka baku kiwo a gobe kiyama)*
*Allah a cikin alkur'ani yayi hani akan kada maigida ya karkata gabadaya zuwa ga wata daga cikin matansa ya kyale sauran matan saboda rashin adalci*
*Allah ya baku ikon adalci a tsakanin matayenku🙏🏻*








FREE PEGE
*25&26*
"Kada ku yarda ku bari ya kubce daga hannunku, mugu! ne macuci! ya jima yana ta'addanci a k'asa! kuyi masa hukunci mai tsauri! domun da bakinsa yake fadin cewa yafi karfin hukuma! yau tsayin kwana shida kenan daya raba ni da iyayena yayi kidnapping dina domin samun makudan kudi daga gurin mahaifina, " Sunana ZINATU ni 'yar asalin jahar kano ce mahaifina kuma shine sarki dake kan kujerar mulki a jahar." Bilhaki da gaskiya take maganar.


Gabad'aya hankalinsu ya koma kanta a lokacin da take wannan maganar, da yawa daga cikinsu ba su lura da ita ba, maganarta ce ta janyo hankalinsu kanta. ganinta a firgice babu sutturar arziki yasa suka gazgata maganarta, babban cikinsu ya kwantar mata da hankali da cewa komai yazo karshe kuma sunyi alkawarin kaita gaban iyayenta idan sun gama gudanar da binkice.


Beyi mamaki da jin furucinta akansa ba, ita kad'ai ce zata bada cikakkiyar sheda a kansa, amma ba tayi hakan ba, to ba zai tsananta ba, ba kuma zaiyi jayayya da hukuma ba, zai bi doka da odar amma ya san ita gaskiya d'aya ce kuma a kanta yake babu gudu babu ja da baya babu shakka! Allah za bayyana mai gaskiya.


Da kansa ya haura ya shiga motar ya zauna, sojoji uku suka zauna hagu da damanshi, ya kalli na hannun damansa cikin nutsuwa yace." Akwai sauran yarana da suke n........ ya katseshi ta hanyar buga masa tsawa da fadin.


"Rufe mana baki ko kai zaka nuna mana aikinmu."? Kansa ya girgiza, yace." To kabi umarnin mu domin shine samun zaman lafiyarka."


Be sake cewa komai ba ya kauda kansa gefe yana hangensu suna ta binkice a gurin...........Can ya hango sun taso sauran yaransa a gaba! suna dukansu! bai dauke idonsa ba har sai da suka karaso gurin, gabadaya sun galabaita domin wasu harda rauni a jikinsu bayan wa'inda suka kone sakamakon bomb din daya tashi, ya tausaya musu sosai, domin ya san shine mujaza! domin da yawa daga cikinsu ba'a son ransu hakan ta faru ba.


Suka dinga turasu cikin motar suna dukansu da wata murtukekiyar bulala irin ta karfe!


To duk iya binkincensu a gurin Allah bai nuna musu dungulmin hannun *Uban daba!* da 'kasa ta turbudeshi a gurin ba, Yana kallonsu suka 'karaci dube-dubensu suka shishshiga mota da niyyar fita daga dajin.


'Bude baki yayi da niyyar magana kawai ya hangota tare da wani soja yana kokarin bude mata gaban mota domun shiga........Yaji wani irin ciwo a cikin ranshi! bakinsa ne yayi nauyi ya gaza furta maganar dake cikin cikinsa har suka fita daga cikin dajin bai dago kanshi ba! wani irin kuttun bakin ciki ya tsaya masa a wuya, tunda yake bai ta'ba ganin butulu irinta ba.


Da yayi motsi zasu saita shi da bindiga! da fadin." Ya kiyaye idan kuma yayi wani yunk'uri na gudu to zasu harbe shi! murmushi kawai yake musu, wanda hakan ke 'kara tunzura musu zuciya.


Labari kaf ya cika garin Katsina da kewayenta cewa A yau 11/3/2007 jami'an tsaro sunyi nasarar kama babban dan ta'addah nan wato *Mashekin daji!* wanda ya addabi k'asa da jama'ar dake cikinta.


Headquarter 'yan sandan kuwa cike take da 'yan jarida da jama'ar gari masu ganin kwal uwar daka.




Koda motocin jami'an tsaron suka shiga headquarter 'yan sandan sai gurin ya hargitse da hayaniya kowa burinsa yayi ido hudu dashi, Mussaman 'yan jarida masu daukar rahoto.


Sai da suka rufe masa fuska sannan suka fito dashi a dadd'aure! Suka rirrikeshi da kyar yake cire k'afa sakamakon sark'ar da tayi masa dabaibayi!


Duk da hakan sai da yan jaridan suka dinga daukar hotonsa tun daga sama har kasan Kafafunsa, da yawa daga cikin 'yan jaridar da jama'ar dake gurin sunyi mamakin ganinsa ingarmar namiji a labari dai sun san cewa ba haka kammaninsa yake ba gajere ne mara fasali ya akayi kuma a zahiri basu ga haka ba.


Har sai da aka shiga dashi ofis din Asp sannan kowa ya watse, jama'ar gari suka tafi da zancan a bakunansu, su kuma 'yan jarida suka fara gudanar da ayyukansu.




****
Cikin tsananin tashin hankali Saude matar Alba ta shiga gidan tana kuka hannunta rike da jarida.


Uwale ta tare ta tana tambayarta abinda ke faruwa.


Jaridar ta nuna mata da fadin." Uwale kin san abinda yake faruwa kuwa."? ta kar'bi jaridar tana dubawa tace." Saude kin san ban iya karatu ba me yake faruwa."


Tace."Ki duba hoton jiki mana Mijina Alba ake tuhumarsu da ta'addanci."


Gabanta ya fadi! tace." Ta'addanci kuma Saude! su da suka tafi farauta mai ya hadasu da ta'addanci inace gobe zasu dawo."


Saude na kuka tace." Uwale kisa kunne da kyau ki saurari jawabin da zanyi miki."


Jiki a sanyaye tace." Ina sauraranki."


"Jami'an tsaro ne suka kama UMARU wato jikanki dashi da yaransa saboda zargin da ake musu na ta'addanci, a yanda na karanta rahoton cewa wai ana tunanin shi UMARU shine wannan d'an ta'addan da ya addabi kasa! yanzu haka dai gabad'ayansu suna hannun hukuma! jama'a da yawa sunyi imani da cewa hukuncin kisa za'ayi musu."


Hankalinta ya tashi sosai sai ta fashe! da kuka ta tsirawa hotonsa ido duk da fuskarsa a rufe take hakan be hana ta ganeshi ba, ta tsirawa kafafunsa ido tana wani irin kuka tace." UMARU wannan ranar nake gudu a gareka, itace rana mafi muni da ba zan ta'ba mantawa da ita ba, ashe tsautsayi ne ya sanya ka tsunduma kanka wannan harkar, ni na san halinka UMARU kuma zan bada sheda a kanka, ka taka sawun 'barawo insha Allah sai Allah ya wanke ka daga zargin da ake maka." Kuka sosai takeyi hawayenta duk ya jika takardar dake hannunta.


Hamra'u ta shigo gidan cikin kuka na fitar hayyaci! tana zuwa ta rugumeta da fadin."Uwale ya za muyi da wannan kaddara hukuma ta kama Yayana da laifin ta'addanci! bayan bashi da laifi Yayana bashi da mugunta baya cin hakkin wani burinsa kullum ya za'ayi k'asa ta samu cigaba, amma ya taka sawun barawo jami'an tsaro sun kamashi dumu-dumu a cikin sansanin da *Uban daba!* yake zaune da jama'arsa, Uwale ya za muyi bamu da kudi bamu da ikon da zamu tunkari hukuma! domin kalubantar zargin da sukeyi akan wanda bai ji bai gani ba."


Tace."Hamrau bamu da komai wanda zamu tunkari hukuma dashi, amma muna da Allah shi kadai zai ne zai mana jagoranci Allah ba azzalimin sarki bane yana tare da masu gaskiya insha Allah cikin hikimarsa zai bayyana mai gaskiya."




Asp Musa Baharu shine shugaban 'yan sandan jahar, kuma duk wani jami'in tsaro a karkashinsa yake, mutumin yana da hankali da nutsuwa gami da sanin makamar aiki, koda aka shigar masa dashi ofis din kallo daya yayi masa ya tabbatar da cewa bashi suke da bukata ba, amma be nuna hakan a zahiri ba, sai kawai ya bawa wa'inda suka shigo dashi umarnin fita, ya rage su biyu kacal a ofis din.


Shi baya ganin komai saboda har yanzu fuskarsa a daure take, amma shi Asp din yana kallon duk wani motsinsa.


K'ira ne ya shigo wayarsa, daga gidan gwamnati , cikin cikin girmawa ya daga da fadin." Ranka ya dade barka da wannan lokaci."


Mai girma governor yace." Barka dai Asp barkanmu da samun nasara! wannan ranar ba zamu ta'ba mancewa da ita ba, yana kuma da kyau ayi rubutu na mussaman domin ajiyewa a kudin tarihi."


Asp ya d'anyi murmushi da fadin." Hakane ranka ya dade, labarin samun nasara ya cika gari da sauran garuruwa jama'a da yawa sun kirayi waya suna yi mana murna! amma ban san me yasa ni nake shakku! akan hakan ba."


Mai girma governor yace." Asp wannan wace irin magana ce? da farko kafin isowar rudunar da muka tura kaine ka kirayi wayata kake sheda min cewa an samu nasara ya za'ayi kuma yanzu kace na shakku akan hakan."


Gilashin dake idonsa ya cire ya ajiye saman tevur din dake gabansa, ido! ya tsira masa yana sake nazartarsa, yace." Ranka ya dad'e ni da kai da sauran jama'ar gari bamu ta'ba ganin *Uban daba!* a zahiri ba, sai dai muna hasashe akansa cewa shi din wani irin mutum ne mara fasali sanin hakan ma ya samo asali ne daga bakin d'aya daga cikin yaransa da Allah ya bamu ikon kamawa a shekarun baya, shine yake sheda mana kammaninsa, a lokacin da al'amarin ya faru, banyi 'kasa a gwiwa ba na samu yaron daya haddace zane ya zana min kammaninsa domin samun sauki gurin binkice a kansa, amma abin mamaki! a yanzu wanda yake gabana a yanzu kuma muke hasashen cewa shine wanda muke nema ruwa a jallo kammaninsa yasha bambam! da wannan hoton zanen da nasa aka zana min a shekarun baya."


Mai girma governor yace." Asp ya akayi hakan ta faru? kana so ka sheda min cewa bashi bane."?


Ya mi'ke tsaye da wayar a kunnasa, kujerar ya janye ya fito daga tsakankanin kai tsaye inda yake zaune ya nufa!.......Yana wayar yana kokarin kwance masa fuska dake d'aure.


Tsaf ya warware d"aurin fuskar, idanuwansu suka hadu guri guda, kujera yaja ya zauna suna fecing din juna.


Ya cigaba da cewa." Gani gashi a halin yanzu kuma yanzu zan dauki hotonsa na turo maka dashi domin ka sheda maganata, amma duk wani binkice zanyi a kansa domin samun tartibiyar magana."


Mai girma governor ya sauke ajiyar zuciya da fadin." Okey to babu damuwa ina tsumayinka." sallama sukayi kafin ya kashe wayar, ya tsira masa ido! shima nasa idon ya tsira masa suka dinga kallon kallo suna nazarta juna, shi Asp din shine ya fara janye idonsa daga kanshi, ya jima kanshi a kasa kafin ya dago ya sake mai da idonsa gareshi yace." Inaso naji cikakken sunanka gami da jin asalin tarihin rayuwarka."?








*#500 via 0542382124...Binta umar gtbank, idan kati zaki tura ki min magana ta WhatsApp da wannan number... 07084653262........Mutanan Nijar ku tuntunbi wannan number....*
*22796074090* katin mov ko airtal.






*GOJE!*🏹
🐕‍🦺🐕‍🦺🐕‍🦺
_(SADAUKI OMAR RETURN👑💫_)


*BINTA UMAR ABBALE🍒*


*_MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION🖊️📚_*
_____________________





*JAMILA MUHAMMAD-ALI*
_(( (MMN BOBO💞) )_
Ina gaisuwa gami da fatan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login