Showing 18001 words to 21000 words out of 49794 words
Chapter 7 - GOJE SADAUKI UMAR RETURN NA BINTA UMAR ABBALE .txt
karewa a daure a biya kudin karatu🙏🏻 don Allah idan kin san ba siyan littafin nan zaki ba kada ki dauki number ta kiyi min magana*
*#500 via 0542382124...Binta umar gtbank, idan kati zaki tura ki min magana ta WhatsApp da wannan number... 07084653262........Mutanan Nijar ku tuntunbi wannan number....*
*22796074090* dala dari. katin airtal ko mov.
*GOJE!*🏹
🐕🦺🐕🦺🐕🦺
_(SADAUKI OMAR RETURN👑💫_)
*BINTA UMAR ABBALE🍒*
*_MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION🖊️📚_*
_____________________
*_KADAN DAGA CIKIN IRIN SAKKONIN DA NAKE CIN KARO AKO DA YAUSHE_*
_*1-* Mijina baya bani kulawa bayan kafin muyi aure yana masifar sona_
_*2-* Mijina baya iya biya min bukatata._
_*3-* Mijina baya hira dani kullum idan ya dawo daga aiki ko kasuwa wayarsa ce abokiyar hirarsa_
_*4-* Mijina kazami ne sai yayi sati ko kwana goma beyi wanka ya wanke bakinsa ba._
_*5-* Dangijin mijina sun matsa min basa kaunata saboda bana haihuwa._
_*7-* Bana jin dadi a duk sanda mijina zai kusanceni da kyar nake amincewa saboda zafi._
_*8-* Mijina yana cutar dani baya sauke hakkina dake kansa bayan Allah ya hore masa._
_*9-* Mijina mazinaci ne yana neman mata bayan ina iyakacin bakin kokarina gurin ganin na dauke masa bukata._
_*10* Mu biyu ko uku ko hudu ne a gurin mijinmu amma baya adalci a tsakaninmu._
_*11-* Mijina yana da taurin kai da wani irin hali baya sarrafuwa._
_*12-* Mijina Miskili ne kullum babu mu'amular arziki a tsakaninmu sai muyi kwana da kwanaki babu magana._
_*13-* Ina fama da rashin nutsuwa da kwanciyar hankali a gidan aurena bayan ta kowane bangare bani da matsala._
_*14-* Mijina shaye-shaye yake nayi - nayi ya daina yaki baya sallah a kan lokaci sannan idan mukayi mu'amula ta aure baya wankan tsarki._
_*15-* Mijina baya dogon zango yake release kuma bai damu dani ba, haka zai tashi ya barni cikin halin damuwa._
FREE PEGE
*13&14*
Sosai yayi namijin kokarin tunkarar inda take kafin ya karasa ya cire duk wani kawazucin dake cikin zuciyarsa yana isa ya bude mata wuta sosai yana mata fada tare da nuna mata illar abinda ta aikata.
Tsaye ta mike tana masa wani irin kallo kafin tace."Wai shin ubana ne kai da zaka zo kana min tsawa ina ruwanka da rayuwata, idan har baka san ganina a haka to kayi gaggawar mayar dani inda ka daukoni."
Ya nuna ta da yatsa kamar zai tsole mata ido Yace." Banyi ra'ayin haka ba kuma ke baki isa kisa na tafi ba tare dana shirya tafiya ba, idan kina san kanki da arziki ki dauki rigarki kasa a jikinki."
Ta nuna masa jikakkiyar rigar dake yashe a gefe, ya kalleta da fadin." Meye manufarki na jika rigarki da ruwa ko kinyi hakane don kija ra'ayina akanki.?
Wulakantaccen kallo tayi masa kafin tace."Allah ya kiyaye meye abin sha'awa a tattare da kai da har kake wannan maganar."
Ya zuba mata jajayen idanuwansa yana kallo, ta gyada kanta idonta a soye a kansa tana kara tabbatar masa da maganarta.
Yace."Idan babu abin sha'awa a tattare dani to ni naga abinda ya burgeni a jikinki kuma ke zaki janyo na aikata abinda ba shikkenan ba."
Gabanta ya fadi da jin furucinsa, amma bata saduda ba, ta ya mutsa fuska da fadin.'' Da kuwa nayi maka illah! domin ka kuskura ka keta min haddi wallahi sai ka dawwama a daure. a kurkuku."
Leb'ansa yasa a bakinsa ya dan ciza kafin ya furzar da wani irin huci! yace."Baki san ni bana d'auruwa ba? ko ba kiji sunana ba *GOJE!* nake ko kuma ki kira ni da *MAI DAWA!* Babu wani mahalukin da ya isa ya tunkari inda nake ban ci Uwarsa ba!"
Sai ta tsargu! ta nuna kirjinta da hannu da fadin." Ni kake zagi ko? shin ka san su waye iyayena a fadin kasar nan kuwa"?
Ya gyda kansa da fadin" Babu ruwana da ko su waye iyayenki ni na fada miki wanene ni! babu wanda ya isa ya daureni ba tare dana rikirkita masa al'amuraba."
Ta dinga kallonsa tana mamakin furuncinsa, babu wanda ya isa ya daureshi ba tare da ya rikirkita masa al'amuraba ba."
"Kana nufin kafi karfin hukuma kenan."? tafada idonta a tsaye a kansa.
Tsaki! yaja mai karfi kafin ya nuna kirjinsa da fadin." Ni nan! ni ne hukuma! duk wani mai bukatar kwanciyar hankali a kasar nan to kada ya ta'boni."!
Cike da Izzah! da jin kai ya fadi maganar, kai daga jin yanda yake magana kasan akwai abinda da ya taka.
Ta sunkuyar da kanta tana mamakin furucinsa wato shi bai yarda ma akwai hukuma ba! to bari ta ta'bashi taga abinda zai yi.
Yanke shawarar zaginsa tayi, ta dago kai suka hada ido, yana tsaye kikam! a kanta, tsoro ta cire
Cikin turanci ta fara zazzzaginsa tana kiransa da sunayen dabbobi........ Iyakacinsa secondary skull turancin nata yayi tsayi sosai da kyar ya fahimci wasu kalmomin mussaman sunayen dabbobin da take kiransa dashi.
Bahagon mari! ya kifa mata a fuska a take taurari masu haske suka gilma, ta rintse idonta hawayen azaba na zuba!
Tana cire hannunta daga gurin shatin yatsunsa suka fito radau!
Ta tsira masa ido gabanta sai faduwa yake, tunda take a duniya babu wanda ya taba fitar da hannu ya tsinka mata mari sai shi.
Ta dinga bin sassan jikinsa da kallo, shi kuma yana dogare a kanta yana tsuma! da alama tsumin ne ya tashi.
Kafin kiftawa da bismillah tayi wani tsalle sai kace aljanna ta fizge kaifaffar wukar dake soke a gaban rigarsa.
Ta rike da kyau! tana kallonsa da fadin" Sai na zubar maka da jini yau! *GOJE!* kake ko? har kana Ikirarin cewa wuka bata huda ka, bayan haka yaranka suna kumbura maka kai kana d'aukar kanka wata tsiya! to yau ni zanyi ajalinka."!!
Da gaske take domin hannu bibbiyu ta ri'ke wukar da kyau sai huci take! tana mazari! kanshi tayi da wukar zata yankeshi, ya kauce! tabi iska! a sukwane ta sake kai masa sarah! ya kauce ta sake bin iska! dariya ta kusa kufce masa ganin yanda ta dage! wai dole sai ta yankeshi da wukar wanda duk kokarin da take a banza bata samu damar saka wukar a jikinsa bama ballanatana ta fitar mai da jini.
Haka suka dinga bugawa ya dinga watangaririya da ita yana bata wahala! ta galabaita mutuka gumi duk ya jika mata jiki shi kanshi tsumman data daure cinyoyinta dashi ya kwance,ribbon din data d'aure gashinta dashi ya cire ya fadi kasan gurin, kafafunta sunyi bududu! amma saboda tsabar karfin hali taki saduda!.
Yana sane ya dinga bata wahala sai da ya tabbatar data galabaita sannan ya murde hannunta ya kwace wukar! faduwa tayi a gurin tana wani irin kukan bakin ciki!
Tausayi ta bashi! wannan artabun da sukayi koda namiji ne zai ji jiki ballantana mace irinta da bata saba da wahala ba, yayi mamakin karfin halinta mutuka.
Kusa da ita ya tsuguna yana duba kafafunta duk ta taka k'ananun k'ayoyi, hannu yasa domin cire mata k'ayoyin ta harbeshi da kafa daya, kallonta yayi cikin zafin nama! ta ciko hannu da kasa zata watsa masa ya kautar da fuskarsa, ta watsawa iska. tana daga kwance tana nishi ta cigaba da cin mutuncinsa da turanci, hakan be dameshi ba tunda ya kaita kasa bukatarsa ta biya.
Duk buge-bugen da take bai hanashi ciccire mata kayoyin da suka huda kafafunta ba, ya cire rigar jikinsa ya rufa mata a jiki.
Da sauri ta cire ta jefar da ita.
Yace." Ni zan iya kawar da kwadayina akanki amma kika yarda wata dabbar ta gilma ta hangi tsaraicinki ba zaki kai labari ba, bayan dabbobi akwai aljanu a gurin nan kiyi hattara."
Jin maganar aljanu yasa jikinta mutuwa idan akwai abinda take tsoro a duniya aljan ne! hakura tayi kan dole ta karbi rigar sa tasa.
Tana share hawaye ta mike tsaye, ya kalleta yana jimanta karfin halinta, wai dashi za tayi fada, dariya yayi wacce ta dauki hankalinta ta kalleshi tsantsar kyawunshi ne ya bayyana a lokacin, ganin tana kallonsa yasa ya gimtse fuska yaje ya dauki rigarta da tsumman ya bar gurin dasu a hannunsa,
*********
Yau ma da wuri ta isa gidan, ta sameta ta shirya tsaf domin fita! A gabanta sabbin atampopi ne irinsu nicham hartget da makamantasu, cike da ladabi suka gaisa, tace."Kinga sabbin atampopi ne Rakiya ta kawo min na saya wai itama a cikin gari ne aka bata su shine nakeso nayi musu kudi a ganinki duk daya za tayi nawa."?
Hamra'u ta kalli atampopin kafin tace."Uwale ke kin kasa yi musu kudi ballanatani ni da ba sana'ata ba."
'Yar dariya tayi kafin tace."Don kar nace da ita dubu uku taga kamar wulakanci ne abun amma iyakacin abinda zan iya siya kenan.''
Cike da mamaki tace."Uwale dubu uku a tamfa turmi hudu haba Uwale kiyi adalci mana shiyasa jama'a suke zaginki har suna kiranki da mummunan suna."
Ta 'bata rai da fadin." Sun jima basu zageni ba! ai Hamra'u a wannan duniyar idan zaka dauki maganar mutane to wallahi babu abunda zaka tsinana, amma meye laifina don na saya dubu uku, itama ai kyautarsu a ka bata.
Tace."Duk da haka dai sunyi arha da yawa duka cotton ne babu leda a ciki maimakon ki saya dubu biyar gabadaya."
Tace."Aa ba zan iya saya dubu biyar duka ba, dubu uku zan saya kuma ke da kike surutu ai idan na saya to tanadi nake miki kayan lefanki ne."
Murmushi tayi kafin tace."Uwale nifa jikina yayi sanyi sai nake ganin kamar burina ba zai cika ba."
Murya na rawa ta karashe maganar.
Tace."Aa ki daina sanya damuwa a ranki insha Allahu ba zakiyi zaman banza ba UMARU zai aureki koda baya sonki to ni zan umarceshi ya aureki.
Tace."Aa Uwale ni nafi so ya aureni dan yana sona bana so muyi irin wannan auran da iyaye suke hadawa daga baya a samu matsala."
Tace."Insha Allahu ba za'a samu matsala ba, domin ni kaina na gaji da ganinsa a haka babu aure sa'anninsa sun jima da aure da 'ya'yansu amma shi yana zaune a haka, idan za'a biye masa to zai kare rayuwarsa a haka wannan dalilin yasa zan tilasta masa auranki."
Hawaye ta share tana girgiza kai, itafa kwata-kwata bata son irin wannan auran tafi so da bakinsa ya furta mata kalmar so, amma dole haka zata hakura tunda yaki gane irin son da take masa. watakila idan Allah ya kaddara auran nasu Allah ya sanya masa kaunarta a cikin zuciyarsa.
Tace."Ki goge hawayenki ki daina kuka mutukar ina raye to kamar kin auri UMARU kin gama, shiyasa duk tsumi da tanadina ya kare akanki gashi cikin ikon Allah na kusa kammala hada miki lefe, kinga sai komai yazo da sauki."
Tace."Nagode Uwale Allah ya tabbatar mana da alkairi" Ta amsa da "ameen" tana kokarin tashi, Rakiya tayi sallama, gabadaya suka amsa, Uwale tayi saurin fadin." Yanzu nake maganarki a cikin raina nace har gida zanje na kai miki kudinki."
Tace."To ai baki fada min nawa kika sayi atampopin ba."
Ta ya mutse fuska da fadin." Gabadaya dubu uku na saya domin dai kema kin san atampopin naki an daina yayin irinsu bayan hakan haka kuma sun jima a ajiye sai warin ajiya suke."
Rakiya ta mika hannu da fadin." Ban siyar a hakaba bani na kai inda za'a saya da mutunci."
Baki ta bude da fadin." Rakiya ina zaki kai a siya da mutunci bayan nan, kin san dai idan kika kaiwa Delu siyan banza za tayi miki gwara ki tsaya mu sassanta."
Taja tsaki da fadin." Ai har gwara Delu a kanki Uwale sai kace kayan sata zaki saya dubu uku duk daya a kasuwa dubu biyu da dari biyar ce, idan sayan mutunci zakiyi ina laifi ki saya dubu biyar gabadaya."
Tace." Oh!oh zan dai saya dubu hudu idan kin sallama min a haka."
Jim tayi kafin tace."Na siyar miki amma kada ki tsinka min kudi ki bani kudiba cif."
Tace."Maganar kike so Rakiya ai a inda ba kasa anan ake gardamar kokawa da ban shirya ba ai ba zan karbi kayanki ba."
Rigar jikinta ta daga ta zuge zif din lalitar dake daure a jikinta kudi ta fito dasu, a dukunkune yawanci duk 'yan dari biyu ne, duk sun ya mutse, Hamra'u tasa hannu suka lissafa dubu hudu kudin me kayan ta mika mata da fadin." Gashi maganin karya hallara ki lissafa a gabana na san halinki kada ki dawo kice min basu cika ba." Rakiya ta dangwali yawun bakinta ta fara lissafa kudin ta kalleta da fadin "Sun cika." Tace."To masha Allah idan an samu wasu kayan ina bukata." Tana kokarin fita tace." To shikkenan idan an samu zaki jini."
Bayan fitar Rakiya daga gidan itama Uwale kayan dillancinta ta dauka ta fita, ya rage saura ita kadai a gidan, ta jima tana sakawa da kwancewa kafin ta tashi cikin sanyi jiki ta gyara gidan tsaf ta kulle da kwado, gidan Tasallah ta shiga ta bayar da mukkulin kafin ta kama hanyar gidansu, salo-salo take tafiya kamar wacce kwai ya fashewa a ciki........."Hamra'u." da sauri ta juya jin muryar kawarta Zabbah, taja ta tsaya tana wasa da karan dake hannunta har ta karaso gurin da faratin goro da lemon tsami a kanta.
Zabbah ta karaso inda take da fadin." Daga ina kike haka naga duk jikin a sanyaye."?
Ajiyar zuciya ta sauke kafin tace." Daga gidan yayar mahaifina nake kullum ina zuwa nayi mata aiki kafin ta fita.
Zabbah ta fashe da dariya irin ta shakiyanci kafin tace."Hamrau kenan wai kenan kina kamun kafa ko? wallahi kina wahalar da rayuwarki domin kaf cikar karkarar nan banga wata mace da zata ja ra'ayin *GOJE! ba*
Tace." To ke Zabbah waye ya fada miki ina kamun kafa da Uwale a matsayin uwa take a gurina laifi ne don naje gidanta."
Zabbah ta tabe baki da fadin." Hamra'u bari na fada miki abunda baki sani ba, kaf 'yan matan garinan babu wacce bata san halin da kike ciki akan *GOJE!* ba kowa ya san kece kike sonsa baya sonki kullum sai kinji kinyiwa kakarsa aikace-aikace sai kace baiwa bayan haka ance idan yana gari kece kike masa wankin kayansa ki goge ki wanke masa takalma saboda rashin hankali irin naki kin mayar da kanki yar aiki bayan baki da tabbacin zai aureki.
Tace."Zabbah! duk abinda kika fada hakane babu karya ina san UMARU kuma ina rokon Allah yasa ya zama uban 'ya'ya na, bayan haka kuma duk wata bauta da nake masa ra'ayi na duk surutun da jama'a za suyi akan hakan bai dameni ba."
Ta girgiza kai da fadin." Shikkenan ai tunda kinyi nisa duk abinda zan fada miki a yanzu ba zaki fahimta ba, saboda haka muna zuba ido muga yanda za'ayi wannan auran.
Shuru kawai tayi bata sake magana ba, ita Zabbah ce keta surutu tana bata labarin saurayinta wanda zata aura uffan bata ce ba har suka rabu da juna.
Cikin kunci da damuwa ta shiga gidansu, nan ma ta iske wani bacin ran don mahaifiyarta fada ta rufeta dashi sosai tace."Ina ji ina gani kinfi karfina Hamra'u! saboda kulafucin namiji kullum da gari ya waye hankalinki na wani guri kisa kafa ki fita ki barni da aikin gida, kina can kina bauta a wani gurin, to wallahi nagaji ba zan hanaki ba tunda ke ki kasa kanki amma ba zaki kara fita ba sai kin gama min aikin gida."
Daki kawai ta shige tana kokarin danne kukan dake kokarin kufce mata, wai shin da wane bala'in za taji? ko'ina babu sassauci, bata samun nutsuwa da kwanciyar hankali sai a gurin Uwale ita kadai ce ke kwantar mata da hankali, amma ita kanta wacce ta haifeta kullum habaici take mata akan wanda ta kwallafawa rai! kowa yana ganin laifinta bayan itama ba ita tayi kanta ba, Allah ne ya halliceta ya sanya mata soyayyar wanda bai san ta nayi ba, dole idan ya dawo ta cire kunya ta sameshi da maganar ko ta san matsayinta..
*Don Allah idan ba sayan littafi zaki ba kada ki dauki number ta Nagode🙏🏻*
*Ga mai bukatar Sadauki Omar 1k zai tura domin samun damar karanta littafi biyu Goje sadauki Omar return*
*#500 via 0542382124......Binta umar gtbank, idan kati zaki tura ki min magana ta WhatsApp da wannan number... 07084653262........Mutanan Nijar ku tuntunbi wannan number....*
*22796074090* dala dari Katin airtal ko Mov
Aa
*GOJE!*🏹
🐕🦺🐕🦺🐕🦺
_(SADAUKI OMAR RETURN👑💫_)
*BINTA UMAR ABBALE🍒*
*_MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION🖊️📚_*
_____________________
FREE PEGE
*29&30*
Kusan a tare suka d'auke idonsu daga barin kallonta, Asp din yayi magana amma shi uffan bece ba har ta gama harare-harare! ta fita daga ofis din. Ya d'an ja k'aramin tsaki da fadin." Yarinya nan babu tarbiya a tattare da ita duk kuwa da cewa ta fito daga tsatso mai kyau, ba ta gaji dattako da karamci irin na mahaifinta ba, duk da ba a garin kano muke zaune ba muna da labarin dattakon mahaifinta mutum ne mai karamci da mutunci yana aiki da hankali da ilimi yana kuma gudanar da mulki a bisa tsari na isalama."
Beso ya tanka a cikin al'amarin yarinyar ba amma ganin yanda Asp din yake jaddada maganar yasa yace." Akwai irinsu da yawa wa'inda suka dauki mulki wata tsiya idan akace mahaifinsu nada sarauta ko wani muk'ami sai su dauki girman kai su dora a kansu suna ganin babu wanda ya isa dasu, hakane maganarka mutumin kwarai yana iya haifar baragurbi acikin al'umma jarabtace kawai daga Allah.'' Yace." Kwarai kuwa wannan haka yake sai dai kawai mu roki Allah ya shirya mana zuria baki d'aya." Ya amsa da ameeen ya Allah.
Shuru na minti biyu ya ratsa gurin, cikin 'yar tsokana Asp din yace." Akwai abinda na manta ban tambayi *MAI DAWA!* ba."?
Murmushi yayi da fadin." Akwai sauran tambayoyi kenan."? Girgiza kai yayi da fadin." Tambaya daya ce shin kana da iyali kuwa.''?
Girgiza kai yayi gami da dan ta'be bakinsa.........Asp ya dan zare ido da fadin." Kana nufin babu iyali kenan."
Kai ya daga masa still da murmushi a fuskarsa.
Sai kawai ya shiga girgiza kansa da fadin." Gaskiyar magana yanda kake jarumin namiji