Showing 6001 words to 9000 words out of 49794 words
Chapter 3 - GOJE SADAUKI UMAR RETURN NA BINTA UMAR ABBALE .txt
ganawa da maimartaba akanta, suka tattauna sosai maimairtaba ya fahimceshi ya san me kaunarsa shine zai zo har gabanshi ya fahimtar dashi abunda ya shige masa duhu, a lokacin ya tashi tsaye a kanta, kuma ya gargadeta kan cewa mutukar bata sanja hali ba to zaiyi mata aure duk wanda yayi ra'ayi, hakan ya tsorarta da ita, tayi sanyi na kwana biyu amma kwanaki suna turawa ta cigaba da abinda take, Gabadaya sai ya dauki al'amarin ya jinginashi a matsayin jarabta, abin na damunsa mutuka amma ya rasa me yasa baya son bacin ran yarinyar, Dan uwanshi, Abbas wanda yake Waziri a gareshi ya bashi shawara kan cewa aurene kadai abinda zai daidaita nutsuwar yarinyar saboda haka shi zai umarci babban yaron sa domin yazo su fahimci juna, maimartaba yaji dadin shawarar dan uwansa.
Koda Taufiq ya sameta domin bin umarnin mahaifinsa rufe ido tayi taci masa mutunci harda zagi kamar ba jininta ba, aikuwa ya fusata! ya gaggaura mata mari hade da farfada mata mumunan magana, "Bani da ra'ayi auran mace mara tarbiya irinki umarnin mahaifina nabi har nazo neman auranki saboda haka wallahi ko ba dazi rasa mijin aure ba zan aureki ba shashaha mara hankali kawai "
Bata saduda ba tana kuka tana zaginsa, Magajin sarki ya samu labarin abinda tayi wa abokinsa ya shiga har dakinta ya zaneta da belt ya fito yana huci! Gimbiya Aysha na zaune a falo yazo ya wuce ba tace masa komai ba.
Washe gari ta hada kayanta kaf ta koma sashen Safa, itama anan din bude mata wuta tayi ta nuna mata kuskuranta, kafin ta bar sashen sai da tayi mata rashin kunya tasa wata baiwa ta daukar mata akwatin kayanta ta nufi sashen Maijidda, a maimakon ta nuna mata kuskuranta, sai ta hau rarrashinta ta nuna mata cewa itake da gaskiya kuma ba zata bari ayi mata auran dole ba, a takaice dai da sanya hannun Maijidda komai ya lalace! itace kuma ke daure mata gindi tana iskanci iya son ranta.
To wannan dalilin yasa ita Ayshan take ganin harda sa hannunsa dana matarsa gurin lalacewar yarinyar, amma tun sanda al'amarin ya faru ya dauki laifi ya dora mata, kullum idan zai budi baki magana daya yake fada *(Tarihi ne zai maimata kansa)* tana jin bala'in haushin wannan magana, ta san a lokotan baya tayi sharafi amma abinda tayi be kai wanda ita yarinyar keyi ba, dalili iyayenta da tayi rashinsu a halin yanzu a tsaye suke a kanta, abunda tayi be kai wanda 'yar cikinta keyi a yanzu ba, ita dashi suka san hakan, amma idan ya tashi magana saboda rashin gaskiya a gaban kowa fadi yake abinda yarinyar take gado ne don haka itace sila akan faruwar al'amarin.
Ta kalli Safa bayan fitar yaron nasu, tace."Duk ranar da Maijidda ta sake magana al'amarin nan sai tayi data sani domin duk irin abinda take aikatawa ina fahinta na gane itace ke zugashi yana daukar laifin yana dorawa a kaina."
Safa ta girgiza kai da fadin." Eh ba zan hana ki ba ni kaina zan tayaki cin mutuncinta domin ta kai ni bango abin mamaki kuma har yanzu laifinmu yake gani, akan hakan ta shigo ta sameni cikin halin damuwa tana min maganar banza ya goya mata baya, ta kaini karshe duk sanda ta sake min katsalandan a gabanshi zan taka mata burki sai dai duk abinda zai faru ya faru."
Tace."Safa ba zaki iya dasu ba, ki kyaleni ita dashi duk zanyi maganinsu, nagaji da wannan abun zanyi magani."
Zuciyarta tayi sanyi da jin furucinta, ba tun yau ba, ta san halin Aysha ba kanwar lasa bace da sannu za tayi maganinsu gabad'aya.
*********
Lokacin data farka garin yayi duhu, kuma bai kunna fitila ba tun bayan daya gabatar da sallahr isha'i sai ya kishingida a gefenta, saboda ita ya sanya bai jagoranci yaran sa farauta ba, sai kawai ya turasu daga shi sai ita ya rage a gurin, sai kuma kukan 'kananun dabbobin dake tashi.
Cike da tsananin tsoro! da firgici! ta mike zaune tana lalube a gurun, masifaffan tsoro ne da ita, rarrafe ta fara ko'ina zata oho! yana kokarin tashi zaune ta afko kansa, fuskokinsu suka hadu, bakinta ya hadu da nasa, lokaci guda numfashinsu ya had'u! da sauri ta kautar da fuskarta, ta danne kirjinsa da hannu tana kokarin barin jikinsa, ba tare da wata manufa ba ya zuba dukka hannuwansa kan kwankwansonta, gefe guda ya ajiyeta, ta sake yunk'urin barin gurin domin kan ciyayi a ajiyeta tana kuma jin tsoron wani mugun k'waron ya cijeta, kafarta daya ya rike, can kasan makoshi yace." Ki samu nutsuwa."! kafarta ta fizge, da rarrafen ta lalubi daddumar ta zauna tana ya mutse fuskarta, gabadaya cinyoyinta sun dauki kaikaiyi da azabar zafi.
Fitila ya kunna yana kallonta, sai yamutse ya mutse take, mikewa yayi ta kalleshi, yana kokarin barin gurin, da sauri tace." Ina zakaje."?
Bai juyo ba domun ji yayi tambayar tayi kama data rainin hankali sai kace uwarsa tana masa magana gatse-gatse! Ya cigaba da tafiyarsa ba tare da ya amsa maganarta ba, kallonsa ta dinga yi tana mamakin girman jikinsa dogo mai garin jiki yana yanayi da jarumin kasar hindu *( Parbahs bahubali)* idonta a hanyar da yabi gabanta sai faduwa yake, can taji wani irin kukan dabbah! a bayanta, a zabure! ta juya tana zare ido! jin kukan na kara kusanto inda take yasa ta kurma ihu! sai ta fara jan gwiwa tana waiwayenta bayanta.
Jin ihunta ya tashi hankalinsa da saurin gaske yasa bakin kokon dake hannunsa ya kamfaci ruwan dake gudana ya juyo da saurin gaske, me zai gani ita ya hango a gigice! tana rarrafe tare da d'aga masa hannu, haushi ta bashi, bega abun gudu a gurin ba, tuntuni sun saba yada zango a gurin, babu wata dabbah mai cutarwa da ke zuwa gurin. saboda su kansu dabbobin sun gane gurin, basa tunkarar zuwa sun san idan sun shiga basa fitowa cikin dadin rai.
Koda ya k'arasa inda take sai kawai ta rike masa kafafu tana karkwarar jiki, "Allah yasa tsakanina daku azzalimai macuta." Kalmomin da suka futo daga bakinta kenan ta nayi tana dukan gwiwarsa harda cizo.
Gabadaya ta kanainayeshi, tana dukansa, kuka take sosai! bece mata komai ba har sai da ta gaji da kukan ta cikashi, ta daga kai tana kallonsa, ya cije baki kamar yanda ya saba idan zaiyi magana "Na fahimci duk gidan da ki kaka fito babu tarbiya, bana shiri da mara kunya ba kuma na san raini! meye laifina anan? ina iya kokarina akanki kina zagina saboda kina takama da mulki da sarauta ko."?
Hannu ta daga masa da fadin." Kaga malam ya isa haka kawai ni ka daukeni ka bar gurin nan dani."
Ya girgiza kansa kamar koda yaushe idan zaiyi magana yace."Ba zaki samu hakan ba, yanda kika rarrafo da gwiwarki hakanan zaki biyo bayana." yana gama maganarsa ya fizge kafafunsa ya barta a gurin.
Da kyar tayi yunkurin tashi tsaye, ta daga masa hannu da fadin." Don Allah kada ka tafi kayi hakuri ka dawo kafafuna sunyi tsami ba zan iya tafiya mai tsayi dasu ba."
Yana jin maganarta be juyo ba ya cigaba da tafiyarsa, yana so ya fara koya mata hankali tunda ya fuskanci bata da mutunci.
Takawa take tana ciccije baki, hawaye kuwa sai karakaina yake a fuskata, abubuwa da yawa sunyi mata dabaibayi, ciwo! tsananin fargaba da tashin hankali bakar azaba da yunwa ta rasa da wane bala'i za taji.
Tun tana hangensa har ta daina, ta dinga tafiya cikin ciyayi tana jin saukar kwarika a kafafunta, ta riga ta saduda ta barwa Allah da wannan masifar da take ciki gwara wata dabbar ta cinyeta.
Ya kai minti ashirin da isa amma shuru babu labarinta, a jikinsa yaji akwai wani abu tunda babu wata tazara mai tsayi tsakaninsu da bakin kogin.
Bayanta yabi yana haske fitilar hannunsa, yaci tuntube da ita, kwance kafafunta sun rufta cikin wani rami da alama na wasu dabbobin ne, sai kici-kici take tana kuka, hannunsa ya mika mata, ta rike da kyau! yasa karfi ya fizgota!
Ajiyar zuciya suka sauke a tare, be jira komai ba, ya sunkuya tare da juya mata baya, kafira!😂 bakin rashin kunya ya mutu, tana zazzare ido ta haye bayansa ya mike tsaye da ita, hannunta tasa sosai ta matseshi, sai ajiyar zuciya take, shi kam cakumar da take masa ta sanyashi shiga tashin hankali wanda sai yayi shekaru be shiga irinsa ba, huci kawai yake yana cizan lips dinsa,
cikin mawuyacin hali suka isa gurin,
Yayi gaggawar sauketa, tayi kwance a gurin tana fitar da numfashin wahala, shi kam can gefe ya matsa tare da juya mata baya, matsalarshi guda a yanzu halin da ya shiga, shigarsa a wahala amma fitarsa nada wuya yakan yi kwana da kwanaki kafin yanayin ya bar jikinshi.
*Ga wa'inda basu samu damar karanta Sadauki Omar ba, zasu biya 1k domin samun damar karanta littafi biyu*
*#500 via 0543282124...Binta umar gtbank, idan kati zaki tura ki min magana ta WhatsApp da wannan number... 07084653262........Mutanan Nijar ku tuntunbi wannan number....*
*22796074090* katin Mov ko airtal
*GOJE!*🏹
🐕🦺🐕🦺🐕🦺
_(SADAUKI OMAR RETURN👑💫_)
*BINTA UMAR ABBALE🍒*
*_MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION🖊️📚_*
_____________________
_*INA MAFITA?*_
_*Matsalar dai guda daya ce data addabi tsakanin ma'aurata rashin hakuri da juna, wanda shike haddasa fitintinu masu yawa, ma'aurata shifa aure gabad'ayansa ibadah ne, jin dadinsa kadan ne, to mai yasa ba za'ayi hakuri da juna a mayar da hankali gurin ribatar ladan dake cikin auran ba*_
*WA YAFI LAIFI*?
_*Shin wa yafi laifi a tsakanin ma'aurata biyu wato mace da namiji? ni dai ba zance ga wanda yafi laifi a tsakanin ma'aurata ba, saboda i dan akayi duba na tsanaki za'a fahimci cewa kowanne bangare da nasa laifin. a matsayina na mace bana goyon bayan 'yan uwana mata akan matsalar data shafi zamantakewar aure wanda kullum ta Allah sai na samu sakon da ya danganci wannan maganar da nake a yanzu, hankalina ya kan tashi idan naji yarinya karama auran fari haihuwa daya biyu kai wata ma auran beyi shekara ba zata kira waya ko ta turo sako tana kuka a taimaka mata da shawarwari yanda zata zauna lafiya a gidan auranta, haka zalika daga b'angaran mazan ma ina samun irin wannan sakkonin cewa baiwar Allah matata tana karanta littatafai na hausa amma bata daukar darasin komai karshe ma tarbiyar tace take lalacewa sakamakon karance-karance littafan da kuke rubutawa. ire-iren wannan sakkonin ba zasu lissafu ba, shin wai ta yaya marubuci zai lalata tarbiya? a ganina marubuci har in dai ya san abinda yake bai cancanta da a kirashi da mai aikata 'barna ba."*_
FREE PEGE
*11&12*
Tun bayan tafiyarsa farauta, Uwale ta samu 'kafar yawo, wanda idan yana gari ko nan da can baya bari taje a cewarsa ta tsufa abinda yafi cancanta a gareta ta zauna a gida ta huta, tunda shi yana iyakacin bakin kokarinsa gurin daukar dawaniyarta da duk wani abu da take bukata na yau da gobe.
Ita kuma a nata bangaran haushin abinda yake mata take, ta dingi mita da surutai tana fadin ba zata zauna zuciyarta ta mutu ba sai ta fita ta nemi kudi kodan bada gudumawa idan sabga dangi ta tashi,
Hakan ya sanyashi
yanke hukunci a duk sanda zai fita sai ya sakar mata kare a gidan ya rufe kofar daga waje yayi tafiyarsa.
A ranar yini take d'aki bata fitowa saboda yanda Allah ya zuba mata tsoron kare a rayuwarta, idan ya dawo gidan sai ta fashe da kuka tana fadin." *UMARU* saboda bani na haifeka shine kake azabtar dani, ka san sarai bana san kare amma saboda mugunta zaka sa min kare sannan ka rufe kofa ka tafi yawo to babu shakka wata rana zaka dawo ka samu gawata."
Sai yace."Uwale idan kina so mu shirya dake ki daina dillanci domin kuwa kina zubar min da mutunci a gari, ni mutum ne mai zuciya da gudun magana bana son jama'a na ganin gazawata a kanki."
*"UMARU* Ba zan daina dillaci ba saboda itace sana'ar data ci da kai ta shayar da kai har ka kai munzali, sannan kuma kana maganar zagin jama'a kai yanzu *UMARU* wane irin zagi ne jama'ar gari ba suyi maka irinshi ba, babu fa wanda yake maka kallon mutumin kwarai mai daraja, kowa yana maka kallon banza tare da kiranka da sunaye masu muni! *B'arawo* *'Dan ta'addah!* duk saboda wannan harkar daka jefa kanka a cikinta, Mahaifinka da bakin cikin hakan ya mutu dalili irin zagi da habaice-habaicen da mutanan gari ke masa, bana rana dayan biyu bakin cikinka ne ya kasheshi."
Duk sanda zata fad'i wannan maganar hankalinsa yana tashi mutu'ka, shi fa har yanzu bai ga illar abinda yake aikatawa ba, na farko bai ta'ba tare wani a hanya ya k'waci abunsa ba, na biyu tunda yake ba'a ta'ba kamashi ya haura wani gida yayi sata ba, na uku bai ta'ba yiwa yarinyar wani fyade ba, abu na karshe shine baya muggan! shaye-shayen da zai janyo masa zubewar kima da mutunci, abunda ya sani shine yana busa Sigari sa'i da lokaci sai shan Shisha da ya zame masa masifa, wannan abu biyun sune abunda ya san yanayi bayan haka azimi sallah akan lokaci basa wuceshi, a ganinsa zagin da jama'ar gari ke masa k'in gaskiya ne, babban abin mamaki kuma duk sanda yayi nisan kiwo dashi da jama'arsa ma'ana suka fita farauta, to duk sanda ya dawo gari da yawa masu zagin nasa sune suke zuwa su gurfana a gabansa domin kar'bar maganin sanyin da yake guzurin zuwa dashi.
Ita kanta Uwalen matan da suke zuwa gurinta kar'bar magani suna da yawa, wani sa'in yana kallo zata zabga kudi masu yawan gaske sai sun nemi alfarma a gurinsa sannan take sassauta musu, amma shi anasa b'angaran 'karamar sadaka yake kar'ba wani sa'in ma kyauta yake bayarwa yace sadaka ayi wa Annabi Salati dubu, Uwale tayi ta jin haushin hakan, idan ya fita sai ta samu buhu mai zurfi ta shiga dakinsa ta kwashe rabin maganin ta boye a karkashin gadonta, idan ta samu sarari ta fita cikin gari ta siyar akan kudi masu yawan gaske.
Wannan dabi'ar ta kakar tashi tana b'ata masa rai, mutuka idan yana so ya tsoratar da ita akan ta daina abinda take sai yace." Uwale shifa aljani ba'a wasa dashi kuma wannan magungunan da nake zuwa dasu ba a banza nake samu ba, musulman aljanu ne suka lamunce min da hakan domin kin san kowane bawa da hanyar abincinsa to nima bani sukayi domin na taimaki jama'a idan kika wuce gona da iri zan barki dasu."
Sai ta tsorata ta dinga rokansa kan cewa ya basu hakuri ta daina abinda take, yace shi babu ruwansa taje ta nemi inda suke ta basu hakuri ba maganarsa bace, kuka irin na tsofaffi take sawa ta rikeshi ta hanashi fita tace lallai sai ya basu hakuri sannan zai futa. sai ya fahimci tayi laushi sannan sai yace tayi shuru ya basu hakuri sun hakura amma kada ta sake aikatawa,
Zata amsa da cewa ba zata sake ba, amma cikin ikon Allah idan aka kwana biyu zata manta ta cigaba da sayar da magani da tsada tana boye kudin a cikin adaka a cewarta da kudin zata hada masa lefen auransa.
***********
Kishingide suka sameshi a gurin hutawarsa, ya mike zaune tare dan gyara zama ido ya tsira musu har suka samu guri suka zauna kafin su gaisheshi, ya amsa still idonshi na tsaye a kansu mussaman mutuniyar tashi da yake hango rashin walwala a tare da ita, koda yake tunda al'amarin ya faru gabadaya walwala da farin cikinsu ya gushe duk abinda suke karfin hali ne.
Gyaran murya yayi kafin yace." Idan kaga wata to za kaga zarah Aysha Safara'u wannan tafiyar taku tana burgeni."
Babu wacce ta saki fuska a cikinsu, domin kuwa suna ciki dashi sakamakon hade kai da yayi da matarsa suna daukarsu a matsayin marasa tawakkali.
D'aya daga cikin hadimanta ne yaje ya sheda mata cewa yanzu - yanzu ya gansu sun nufi gurin hutawar Maimartaba
Da saurin gaske ta shiga daki ta shiryo ta fito kai tsaye can ta nufa, tana sauri taje ta riski abinda ya kai su bayan itace da girki.
Tunda ta doshi gurin take hangoshi gabadaya hankalinsa yana kan wacce ta tsana a cikin matan nasa fuskarsa akwai alamun sassauci da rarrashi, gabadaya ma kamar ita kadai ce a gurin babu Safah.
Ta isa gurin da sallama wacce bata fito sosai ba.
Ya amsa yana kallonta kafin ya kallesu da fadin." Kuna ji 'yar uwarku na muku sallama kunyi shuru."
Safah ta amsa a ciki Aysha kam ko kallonsa ba tayi ba ballanatana 'yar koran nasa.
Ta samu guri ta zauna tana ya mutse fuska da fadin." Ranka shi dade barka da dare."
Ya amsa "Barka dai Maijidda ya hidima." Ta amsa "Alhamdullhi."
Gurin yayi shuru na 'yan mintina kafin gimbiyar ta kalleshi babu fara'a tace."Ranka ya dade wannan magana iyakacin nida kai da 'yar uwata muka tattauna bana son wani yaji abinda ya shafeni da zuriata."
Ya 'bata rai da fadin." Aysha wannan wace irin magana ce? shin ita Maijiddan bare ce a cikinmu."?
Ta d'aga masa hannu da fadin." Allah shi gafarta maka tunda na fara maganata kaji sunan Maijidda a bakina."?
Ransa ya baci mutuka, yace." Ki sauke hannunki idan ba hakana ranki ya b'aci zaki nuna min abinda zanyi ne? ko kuma zaki hanani iko da abinda na haifa? dake da ita Zinat din da ita Safa da Maijiddan duk ikona ne to ke baki isa ki tsara min yanda zanyi ba."
Maijidda ta fashe da kuka da fadin." Ranka ya dade na rasa me yasa