Showing 15001 words to 18000 words out of 49794 words
Chapter 6 - GOJE SADAUKI UMAR RETURN NA BINTA UMAR ABBALE .txt
da maigidansa ba, da sai ya fasa mata baki domin yaji ciwon kallon banza da tayi masa.
Har gari yayi haske sosai tana takure cikin rigar har yanzu ta kasa tantance a wane iri yanayi take,
Can ta hangoshi yana zuwa inda take, ido kawai ta tsira masa babu kiftawa sosai take mamakin tsananin kamar da yake da jarumi(Barbahs) tana bala'in son jarumin saboda jarumtarsa da iya soyayyarsa idan yana abu a film kamar gaske, zazzafar ajiyar zuciya ta sauke tana kokarin karyata abinda zuciyarta ke raya mata a kansa.
Tsaf yake cikin shirin fita, ya sauya rigar jikinsa doguwar jallabiya ce browan mai gajeran hannu sai ya sanya dogon wadon jens kanshi nannad'e da bakin yadi yayi gammo sosai! idanuwan nan rad'au! da bakin kwalli! kafad'unshi rakwacam! da tarin kayan farauta, har da irin doguwar bindigar nan, hakanan wuyanshi da damtsan hannuwansa wasu irin abubuwa ne a d'aure.! kafafunsa sanye suke da wani irin takalmi mai tarin igiyoyi a jikinsa.
Tunda ya tsaya a kanta take kallon kafarshi, mamakin kyawun kafar take, bata ta'ba kallon kafarsa ba sai yau, faratanshi tas babu kazanta sai kananun gashi dake kwance saman yatsun kafar.
A tsorace ta dinga sauke ajiyar zuciya tana kokarin kawar da idonta daga kan kafar. taji muryarsa cike da wani irin amo!! "Tashi zaune."
Yanda ya fadi maganar babu wasa yasa ta tashi tana kallon fuskarsa, babu fara'a yace." Zanja ragamar yara na wani aiki a cikin dajin nan, ina so ki kula da kyau! kada kiyi kuskuran barin gurin nan! ki kiyaye! mutukar kina so ki cigaba da rayuwa a duniya.
Kuka tasa tana kallonsa da fadin." Me yasa ba zaka tafi dani ba, saboda tsabar mugunta shine zaka had'a kan yaranka ku tafi ku barni ni kad'ai! bayan ka san dajin bashi da kyau komai yana iya faruwa da rayuwata."
Yace." Nan gurin yana da tsaro bayan haka kuma gurin da zamu shiga yana da had'ari shiyasa na yanke shawarar barin ki anan sai yafi miki kwanciyar hankali."
Ta girgiza kai tana shakar hanci tace."Aa nifa ba zan zauna ba wallahi ko kun tafi sai na biyo bayanku."
Yanda tayi maganar babu alamun wasa a tare da iya yasa yaji shakkar tafiya ya barta.
Ya kalleta a lokacin da take kokarin mi'kewa. "Na fad'a miki abinda yake da akwai kina kuka ko."?
Hannu ta d'aga masa da fadin." Nifa ba zan zauna ni kadai a wannan gurin ba." Tana gama maganarta ta kama tana tafiya babu takalmi a kafarta, ga kanta babu dankwali."
"Ki tsaya nan nace."! Cikin tsawa yayi maganar. taja ta tsaya ba tare da ta juyo ba.
Yaja tsaki tare da komawa baya, takalmi ya lalobo mata tare da wani farin yadi.
Ya karasa inda take da fadin." Kar'bi wannan ki rufe jikinki dashi." ba tayi musu ba ta kar'ba, ta lullube jikinta har kasa. Ya bata takalmi ta tsuguna tana kokarin sawa, ganin tana 'bata masa lokaci yasa ya tsuguna da kansa ya d'aura mata takalmin sosai yanda duk wuya ba zai fita a kafar ba.
Hannunta ya rike a cikin nasa suka nufi inda ayarin jama'arsa suke tsayuwar jiransa, ganinsa tare da ita ya basu mamaki! amma babu wanda yayi magana a cikinsu, yayi gaba suka rufa masa baya.
karnuka wasu a gaba wasu a baya, sai kuma bushe-bushe da gangi! da ya cika dajin!
*Free pege ya kusa 'karewa a hanzarta biyan kudin karatu.*
*0542382124...Binta umar gtbank* a tura sheda ta wannan number...... 07084653262
*Ayi kokari a duba wannan👇🏻*
_Mijina baya bani_ kulawa bayan kafin muyi aure yana bani kulawa da duk wata soyayya
___________
*Watakila kece kika janyo faruwar hakan, na farko dai namiji yana da bukatar kulawa, ta kowane fanni, watakila kafin kuyi aure ke din 'yar gayu ce mai tsafta, bakya rabo da kwalliya kamshin turare ako da yaushe, sai bayan auranki kuma ki mayar da kanki jakar mata, da kuruciyar da komai ki shiririce wanka ma sai kiyi kwana biyu ko uku ba kiyi ba mussaman a cikin wannan lokacin, sai kiyi kwaskwarima ki shafa mai akan dauda kina tsamin hammata! to me zai hana namiji bai kyamace ki ba, babu mummunar mace, kuma komai shekarunki mutukar kina da miji to kada ki zauna a lalace domin hakan zai janyo miki bacin rai mai tsanani mussaman idan kina da abokiyar zama to zaki zama koma baya ta kowane fanni, tsafta jigo ne a cikin zamantakewar aure don haka ki kula da wannan abubuwan.*
*1- Wanka sau biyu a rana*
*-2 yawan aske sassan dake fitar da gashi a jikinki*
*4-Zama cikin kamshin turare mai sanyi da sanyaya zuciya*
*3-Kitso duk bayan sati ko kwana goma kuma kafin ayi kitson a wanke kan*
*5-Wanke baki sau biyu ko uku mussaman idan zaki kwanta*
*6- Taraiyaya da iya kalami mai dadi a lokacin da kike tare da mijinki*
*7-Sauya kalolin abinci masu inganci*
*8- Sanya kaya na mussaman domin zuwa turaka*
*9- Shagwaba wata abace mai muhimmanci*
*10- Banda yawan dariya mara ma'ana a gaban miji murmushi zaki yawaita yi masa kina sarrafa kwayar idonki a kansa kina bashi labarai masu dadi.*
_Mutukar kin kula da wannan to zaki kama mijinki a hannu kuma zai baki kulawa ta mussaman_
*#500 via 0542382124...Binta umar gtbank, idan kati zaki tura ki min magana ta WhatsApp da wannan number... 07084653262........Mutanan Nijar ku tuntunbi wannan number....*
*22796074090* Dala dari Katin Airtal ko Mov
*GOJE!*🏹
🐕🦺🐕🦺🐕🦺
_(SADAUKI OMAR RETURN👑💫_)
*BINTA UMAR ABBALE🍒*
*_MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION🖊️📚_*
_____________________
*MIJINA BAYA IYA GAMSAR DANI*
________________
*_Wannan ba sabon abu bane, da yawa mata suna kuka da hakan cewa duk sanda za suyi rayuwar aure da mijinsu basa samun gamsuwa, matsalar daga shi mijin ne daga zarar ya biya bukatarsa zai tashi, bai damu da damuwar matasa ba, wannan kuskure ne babba! idan kasan baka da cikakkiyar lafiya to kayi hanzarin neman magani domin kana aikata kuskure! mata suna da kawaici da hakuri mussaman a wannan bangaran, duk macan data bud'e baki tafadi wannan maganar to ka tabbata tura ta kai bango! shi aure na mutum biyu ne to kai d'an uwa bai kamata ka ajiye mace a gida don kana ta'kama kana ci da ita ka tauye mata hakkin aure ba, wannan abun shine ginshikin aure domin daga ranar da akace babu shi to matsala ta dinga afkuwa kenan, saboda haka d'an uwa kayi hattara daga ranar daka fahimci cewa ka gaza gurin sauke hakkin matarka, to ka tashi tsaye ka nemi magani, idan kuma kasa taurin kai kace kai lafiyarka lau ba zaka sha magani ba to babu shakka! komai yana iya faruwa..... ke kuma 'yar uwata, kada ki yarda shaid'an ya rimbaceki ki aikata wani mummunan aiki ta sanadiyar wannan matsalar, domin da yawa daga ciki akwai matan da suka famtsama kansu harkar banza, saboda rashin samun kulawa daga mazajensu, akan ki aikata hakan gwara ki rabu da auran ki roki Allah ya baki daidai da rayuwarki_*
FREE PEGE
*21&22*
Hakika baka sanin amfanin mutum a rayuwarka sai ranar da wata musiba ta sameka, ya taimakawa rayuwarta, ita kuma ta daukeshi a matsayin abokin gabarta! tayi masa mummunar fahinta duk da irin taimakon da yake akanta, ni a ganina idan shi din macuci kamar yanda kullum take kiransa ba zata kai labari ba, domin da tuni ya keta mata haddi ya yasar da gawarta a dajin. koda yake kowane dan adam da irin tunaninsa, har yanzu ita tana shakku akansa cewa bashi ne ya sato ta daga gaban iyayenta ba.
Kwanciyarta da kamar minti goma mugun k'aikaiyi ya tasheta, ashe tsutsar data sauka kan kafad'arta tana da dafi! kuma ta cijeta a gurin har ya kumbura sai tsuko! yake mata, yatsunta biyar tasa a gurin tana aikin sosawa amma kamar 'kara angiza kaikaiyin take, fatar gurin tayi jajawur! saboda susa duk ta kwaile.
Hawaye kawai take tana jan hanci! daga wannan sai wannan! ciwuka a jikinta iri-iri! sosai take kuka tana kiran innalillahi-wa'ina ilaihi raji'un!
Ya rage shi kadai a waje yana kai kawo a gurin, har yanzu zuciyarsa taki aminta da gurin, yana ganin kamar idan yaje ya kwanta wata matsalar zata faru! zagaya gurin yake karnukansa na binsa duk inda ya nufa sai koke-koke suke.........Alba ya cimma inda yake tsaye cikin girmamawa yace."Maigida yarinyar nan fa tun dazu ta ishi mutane da kuka."
Yace."Me kukayi mata."?
Da sauri yace."Wallahi maigida babu abunda mukayi mata kawai dai munji tana kuka shine nace bari na sheda maka."
Ya girgiza kansa da fadin." Jeka gani nan zuwa." da sauri ya juya ya tafi.
D'azu ta 'bata masa rai! ya hakura ya shanye amma baya tsammanin yanzu zata kawo masa shiririta ya saurara mata.
Ya sameta sai gursheken kuka take gabad'aya ta cire rigar dake jikinta sai breziya sai soshe-soshe take.
Ganinta a haka ya 'bata masa rai! rashin kamun kanta yana bashi haushi, idan ba hakaba ta san da cewa ita kadai ce mace a cikinsu mai yasa ba zata suturta kanta ba, kullum shike k'okarin ganin ya suturta ta a matsayinsa na namiji amma ita a cikin maza! saboda rashin sanin darajar kai take bude tsaraicinta.
Tsaki mai karfi yaja ya juya yana kallon gurin da ya yaransa ke zazzaune! akwai tazara a tsakanin inda take, baya kuma tsammanin zasu hangeta saboda kafin ya fita sai da ya katangeta.
Murya a sama! yace."Mayar da rigarki." ido gaja-gaja da hawaye! ta kalleshi, ya murtuke fuska! ko alama bata bashi tausayi ba, ya bude mata dukkanin idanuwansa! umarni ya sake bata, a dashe tace." Ka daina yi min tsawa! ko ka san abinda yake damuna."?
Yace"Babu abunda ke damunki sai hauka! da gidadanci! idan ba haka mai zai sanya ki cire riga cikin maza."
Wani abu mai nauyi ya tsaya mata a wuya! wai ace wannan gantalallan ne yake kiranta da mahaukaciya.
Nauyin abunda ya tsaya mata a wuya ya hana ta magana sai uban hawayen dake tsere a saman fuskarta, abu biyu ne suka dameta a halin yanzu.
"Mtswwww! tsaki mai tsayi yaja kafin ya fita da gurin, ya dawo da fitila a hannunsa sai da ya rage karfinta sannan ya tunkari inda take.
Ta sake takure jikinta tana kallonsa yana dube-dube a gurin, rigar ya mika mata da fadin." Kar'bi kisa ko kuma yanzu nayi abinda ba kiyi tsammaninsa ba."
Ta tsira masa ido! da jin shakkar maganarsa, ganin babu alamun wasa a fuskarsa yasa tasa hannu ta kar'bi rigar amma bata sanya ba, ta rike kawai a hannunta tana cigaba da sosa gurin dake mata ciwo.
Ya haskata da fadin." Cire hannuki a gurin! da sauri ta cire! tsigar jikinsa ta tashi! ganin yanda gurin yayi jawur! har da kumburi! zuciyar musulunci, duk sai jikinsa yayi sanyi haka kawai baya so wani abu ya cutar da ita, burinsa bai wuce ya kaita gaban iyayenta lafiya lou ba.
Sassauta murya yayi yace."Sannu yaushe hakan ya faru."? a maimakon ta bashi amsar tambayarsa sai kawai ta sake rurucewa da kuka!!
Yatsansa yasa saman bakinsa da fadin." Shiiiiii." kukan bashi da amfani kiyi shuru zan taimaka miki."
Ba tayi shuru ba kuma bata daina kallonsa ba, yace."Kina bukatar hakan ko."?
Kamar wata sakarai ta daga mai kai!
Yace."To ki zama jaruma! ki daina yawan kuka bashi da fa'idah."!
Taji kamar ta kai masa duka! ta'ina zata iya daure wannan azabar!
Fita yayi da kamar minti biyar ya dawo da magani a hannunsa. yayi zaman ra'kuma a gabanta cikin muryar da ya saba rarrashinta ya mi'ka mata maganin da fadin." Jarumata! kar'bi maganin ki shafa a gurun zai daina miki ciwo."
Maganin ta kar'ba ta lakato a yatsanta, can bayan kafad'arta gurin ciwon yake ta daga hannu sosai tana kokarin shafawa hannunta ya gaza kaiwa!
Ganin haka yasa ya kar'bi maganin daga hannunta ya lakato kan yatsansa, ya kalleta da fadin." Kin bani izini."?
Shuru tai masa.
Ya sassauta murya yayi da sake maimaita maganarsa.
Kai kawai ta iya daga wa gabadaya jikinta ya mutu! ya lalubi gurin yana shafa maganin a hankali yana sake kwantar mata da hankali da cewa gurin zai daina ciwo insha Allah!
Ido kawai ta lumshe tana jin maganganunsa sama-sama a cikin kunnanta, har ya gama shafa maganin fuskarta ya dan kalla sai yayi sauri ya janye idonsa jin yanayinsa na neman sauyawa, gefe ya matsa tare da sassauta murya ya kirayi sunanta............ *GIMBIYA!* a kasalance ta bude idonta! tana kallonshi , tana masifar son taji ya kira ta da wannan sunan. yace."Sannu ki kwanta ki huta na shafa miki maganin." Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta zame ta kwanta tana tattakure guri daya, Shima ajiyar zuciya ya sauke kafin ya lalubi wani zani mai kauri ta fara k'okarin rufa mata a jiki akayi rashin sa'a gwiwarsa ta zame ya fad'i kanta! fuskarsu ta hadu! da sauri yayi gaggawar rabuwa da jikinta yana bata hakuri! uffan ba tace ba asalima lokacin da hakan ya faru idonta a rufe yake.
Ganin tayi shuru ba tace masa komai ba yasa a gaggauce ya fita yana auziyya a zuciyarsa, be san me yasa ba kullum zuciyarsa take kwadaita masa wasu gurare na jikinta, a duk sanda zasu kasance a guri daya yakan rasa nutsuwarsa.
Itama anata bangaran hakane, har yanxu idonta a rufe yake ta rasa abinda yake mata dadi! yanda yake sassauta murya yana rarrashinta yakan karya mata garkuwar jiki, tana jin dadin hakan sosai, a rayuwarta tana masifar son namiji wanda ya iya soyayya, bayan haka kuma bata san lusarin namiji tafi son tsayayye shiyasa wasu lokatan yake birgeta domin dik ya tara abubuwan da take bukata.
Ajiyar zuciya ta sauke tare da jan zanin daya rufa mata ta rufe gabadaya jikinta harda fuskarta, addua take a zuciyarta Allah ya sa bacci ya dauketa. Cikin ikon Allah kuwa bacci mai nauyi ya dauketa................
Kamar a mafarki! ta dinga jin ihu!!! da hayaniya tare da kukan karnika! da karar wu'ka'ke! a firgice ta tashi tsaye! tana bin gurin da kallo, babu kowa duk sun fice! yanda 'kura! da guguwa! take shigowa har gurin da take shi tabbatar mata da cewa babu lafiya!
Fitowarta daga gurin yayi daidai da tashin bomb! gabadaya gurin ya kacame! ya hargitse! da hayaki! da rarrafe ta koma katangaggen gurin ta takure guri daya tana kiran sunan Allah.
Ta jima a haka kafin ta dago kanta, still tana jiyo hayaniya da kuwwa! tare da kukan karnika! ga wani irin b'akin hayak'i! da ya turnuke! a gurin!
Hannu tasa ta toshe hancinta tare da sake takurewa a guri daya jikinta in banda rawa babu abunda yake, bakinta sai motsi yake adduar yaye masifa takeso tayi amma bata iya ba, sai kawai ta dingi nanata innalillahi da karfin gaske!
Hakan ya janyo hankali d'aya d'aga cikin yaran *uban daba* wanda yake shawagi a gurin...........Gurin ya shiga yana zazzare ido! ita kuma ganin b'akuwar fuska yasa ta sake rikicewa! shi kuwa murmushin farin ciki yayi ya nufeta da saurin gaske!
Hannunta ya fizgo! ta turje! tana rirrike itaccen dake katange da gurin, kuka take tana rokonsa yayi hakuri, ya d'auke fuskarta da mari! da tafkeken hannunsa!! a take hancin ya fashe! ya dinga tsiyayar da jini!
Janta yake tana turjewa da bashi hakuri cewa bata da laifi itama sato ta sukayi, ya sanya kan k'otar lafceciyar wu'kar dake hannunsa ya dinga bubbuga mata a gwiwa, lokaci guda ta galabaita! ta zube a gurin! d'aukarta yayi ya sa'ba a kafad'a ya fito da ita. kai tsaye mafarkarsu ya nufa da ita a kafad'arsa.............
Tashin hankali kenan! lokacin daya hangeta sa'be a kafardar gardi! sai da wukar hannunsa ta subce! ta kusa fad'uwa amma yayi muzzakaracin riketa da kyau a hannunsa!! Wani uban ihu! ya kurma! wanda ya razana! abokan fad'an nasa suka ranta ana kare, amma ina! basu samu nasara ba, sai da ya kama su, ya sanya wata narkekiyar igiya ya daure musu hannuwa da kafafu!
Gabad'aya gurin ya hargitse! sakamakon bomb din da ya tashi, yayi sanadiyar kona biyu daga cikin yaran shi, suna kwance magashiyan! rai a hannun Allah...... Duk da cewa sune suka samu nasara amma beso wata matsala ta afku da yaran sa ba..
Ya kallesu gabad'aya kammaninsu ya sauya hatta da fuskokinsu sun rine! da baki! sakamakon tashin bomb din, wannan ce hanya mafi sauki da abokin hamayyar ya samu nasara a kansa!
Ya kallesu da fadin." Yayi imani! da cewa idan ya tunkari inda muke da wu'ka ko wani abu makamancin haka ba zai samu nasara akanmu ba, wannan shine dalilin daya sanya shi jefo mana bomb! ba tare da munyi tsammanin hakan ba, to Alhamdullhi duk da hakan be samu nasarar da yake bukata akanmu ba, yanzu kalubalan dake gabanmu tunkarar sansaninsa domin gwabzawa a tsakanimu, babu yanda za'ayi mu tafi mu bar masa wannan yarinyar da yayi nasarar dauke mana ita, duk da cewa tsintar ta mukayi akan hanya bamu san daga ina take ba, hakan ba zai sanya mu bar masa ita ba, duk yanda za'ayi sai mun samu nasara a kansa."
Da yawa daga cikinsu sun tausaya mata, amma wasu sun kalubalanci maganarsa! bai ta'ba sanya kara sun tsallake ba, amma da alama akwai wa'inda za suyi masa tawaye a cikinsu.
Ya dinga kallonsu yana nazarin yanayinsu, yace." Babu wanda zan tursasa! cewa ya take min baya! a cikunku. zan iya tunkarar sansanin ni kadai! ba tare da kowa ba! saboda haka wanda yake ganin zai bi bayana bisimillah." Yana gama maganarsa sai yayi gaba, wasu suka bi bayan shi da sauran karnukan! dake raye, wasu kuma suka tsaya suna surutai da mai da magana a tsakaninsu!
*Free pege ya kusa