Showing 21001 words to 22530 words out of 22530 words
Chapter 8 - Mutun Ko Aljana Part 1 Complete by Sakeena Isma'il Cameroon--(Mom Muwadda)----.txt
ɗaya sannan ya zare nashi hannun ya bar iya namu,
Wani yarrr! Ɗuk muka ji,
Hanun namu da yake a haɗe Asaf ya matse sannan ya ɗago ya kalleta ni,
Yana kallonna muna haɗa ido na yi saurin k'auda nawa gefe kana na shiga zare hannunna daga cikin nasa amma na kasa dan ba karamin riƙo ya yi wa hannunna ba.
Wani zare ne Malam ya d'auko ya d'aura ma na a hannu,sannan ya ce "Kowa ya rufe ido kuma ko mai muka ji karmu kuskusa mu buɗe idanunmu"
Da "Toh muka amsa sannan ɗukan mu _mu biƴun muka rufe ido,amma banda Malam Iliyasu da Mus'ab, tunɗa su abun bai shafe su ba.
Addu'a Malam Shuaibu ya fara yi ya na yi ya na tofi a cikin kwalbar da ke gabansa,yana kiran sunan Aljanar Mazwara,
Bai fi mintuna biƴar da fara addu'ar ba ɗak'in ya fara ba da wani irin sauti mara dad'i, jikin Mus'ab ne ya d'auki ƙerma,
Haka ma bangaren mu ni da Asaf .
Malam Iliyasu kam ko a jikinsa,dan a bunda yafi wannan ma ya gani .
Tunda ya saba kawo mutane a wajan sa,
Sai da Aljanar Mazwara ta gama yin dariya kafin daga visani ta bayyana a gaban Malam Shuaibu.
Wani irin murmushi Malam Shuaibu da Malam Iliyasu suka yi mai sauti amma banda Mus'ab da ya tsorata sosai,dan zuwa wannan lokacin har ma da fisari ya yi,dan tu ni wandonsa ya gama jikewa da fisari.
Mikewa ya yi da zumbar barin wajan sai Malam Iliyasu ya gansa nuni ya yi masa da ido da ya koma ya zauna,ba bu shiri ya koma ya zauna.
ba tare da ransa ya so ba.
Ya yi ne ka wai saboda zaman lafiya,
Ni da Asaf kam jin shiru ba mu kara jin dariyar ba ne yasa hankalinmu ya kwanta
Addu'ar da Malam yake d'azu ya ci gaba yana yi yana tofi a cikin kwalbar ne ya dawo tofa shi a jikin Mazwara
Ihu Aljanar Mazwara ta so ma yi tana dan kwanta wa a kasa kaɗan_ kaɗan har ta gama kwatar da duka jikinta akan tabarmar.
Sai da Malam Shuaib ya tabbatar ta kwanta rigingine sannan Malam ya yi anfani da wannan damar da ya samu ya kwantar da kwalban d'azu kan kwalbar na fuskantar kan Mazwara.
Sai ya ci gaba da addu'an da yake yi.
A hankali jikin Mazwara ta soma shigewa cikin kwalbar har ya zo ya shiga duka,
Sauri Malam Shuaibu ya yi ya dauƙo wannan jan Klellen ya sa ya d'aure bakin kwalbar da shi sosai ta yen da ba bu ta in da za ta samu damar fitowa.
Ɗaga kwalbar ya yi yana hamdala.
Shi ma Malam Iliyasu Hamdalan ya yi,
Kallon su Asaf ya yi ya ce "Komai ya kammala yanzu za ku iya buɗe idanun ku".
Buɗewa muka yi muna kallon Malam Shuaibu,
Asaf ne ya buɗe bakinsa ya ce "Malam tana ina ?"
Kwalbar da ke gefen sa ya nuna ma sa ya ce "Gata nan a cikin wannan kwalbar "
Kallon kwalbar Asaf ya yi sannan ya kalli Malam Shuaibu ya ce "Malam yanzu ba bu a bunda zai faru zan iya auren ?".
"Kwarai kuwa Ɗana za ka iya auran ka ba tare da wata masa'ala ba"
Murmushi Asaf ya saƙi kana ya matse hannun Siyama da ke cikin nasa,
Ɗagowa ya yi ya kalle ni ya sakar min murmushi da tunda yake bai taɓa sakarwa wata Ƴa mace ba.bayan mahaifiyarsa da yen uwansa,
"Dan Allah yellow mutumin ka sakar min hannu "
Dariya Mus'ab da ke bayan su ya yi,
Juyowa Asaf ya yi ya kalli Mus'ab ya buɗe baki zai yi magana sai idonsa ya sauka akan fisarin da ya sula akan tabarma.
Ido Asaf ya zaro waje yana sakin murmushi,
Kallon in da Asaf yake kalla Mus'ab ya yi ya ga fisarin,ai ba shiri ya miƙe ya bar wajan.
Su Malam Iliyasu da Malam Shuaibu suka bisa da kallo su na sakin murmushi
Kuɗaɗe masu yawa Asaf ya fito da shi daga cikin aljihun wandonsa ya ajiye a gaban Malam ya ce "Gashi Malam ayi sadaka da shi"
Kallon ƙuɗin Malam ya yi yana zare ido waje dan tunda yake bai taɓa ganin maƙodan ƙuɗi kamar wannan ba.
"A'a yaro wannan ya yi yawa ka rage"
"Eh gaskiya wannan ƙuɗin ya yi yawa Muhammad ka rage"Shima Malam Iliyasu ya yi maganar.
"A'a bai yi yawa ba,ba fa karamin taimako kuka yi min ba fa.da za ku ce wannan ƙuɗin ya yi yawa"
"Ni dai ayi sadaka da shi please "
Shi ke nan ɗana za'a yi kamar yanda ka ce."
Wata tsohuwar agogon da ya d'aura a hannunsa ya duba ya ga ɗaya harda y'en mintuna
Dan haka ya kalle su ya ce"Ku tashi muje masallaci lokacin sallah ya yi "
Kai Asaf geɗa haɗe da miƙe suka yiwa Malam Shuaibu godiya suka bar gidan.
Umarni babana ya ba ni da na koma gida su bari su je sallah,na amsa da"Toh" Sannan na wuce gida
*Bayan awa biyar*
D'azu da aka idar da sallar la'asar ne aka d'aura auren Muhammad Zubairu tare da Siyama Iliyasu.
Zaune suke a cikin bukkan da aka s'auke su ya yi shiru,tun da aka d'aura auran jikinsa yake a sanyaye,ya resa murna yake ko kuma akasin haka.
Shi dai in an tambaye shi ba zai ce yana bakin cikin da auren ba.
Dafa sa ya ji anyi yana,ya ɗago ya ga Mus'ab ne
"Are you okay my friend?"
" I'm Okay "
"Me ka ga ni?"
"Ga ni nayi tun da muka dawo daga wajan d'aurin auren nan jikinka yake a sanyaye "
"Tunanin a bunda zan cewa Hajiya nake dan sauran in sun tambayeni na san amsar da zan ba su ".
" Karka damu na san in kayi wa Hajiya bayani za ta fahimce ka,tun da Na san Hajiya na da sauk'in kai sosai."
Da haka dai Mus'ab ya samu ya rarrashi Asaf suka ci gaba da hira kamar yanda suka sama in suna tare,
Banyan magriba mai gyaran mota ya dawo ya je ya duba mota ya ce shi bai ga in da motar ta samu masa'ala ba. asalima shi da ya kunna motar ya ga yana yi dan haka motar su ba ta lalace ba.
Mus'ab da Asaf ne suka fara mai masifa wai bai iya gyara ba shi ya sa ya ce motar su bai lalace ba.
Ganin ba fahimta za su yi bane ya sa Malam Iliyasu ya sallami mai gyaran mota ya tafi.
Kallon su ya yi ya ce su nitsu sosai zai mu su bayanin komai,
Shiru suka yi su na jiran su ji mai Malam Iliyasu zai gaya mu su
Bayani Malam Iliyasu ya fara mu su kamar haka "Ni ban yi mamakin da mai gyara ya ce motar ku bai lalace ba.saboda wannan Aljanar zai iya yi muku komai "
"Yanzu Baba kana nufin ita ce ta lalata mata mota ?".
Asaf ya tambaya
"Kwarai kuwa ita ce ta lala ta muku"
"Amma ba komai mu ta taimaka dan da a ce motar ku ba lala cewa tayi ba.da yanzu ba mu haɗu ba"
"Wannan gaskiya ne,da yanzu tana can a waje tana yiwa mutane abunda bai kamata ba"
Mus'ab ya yi maganar
Da haka dai suka wuce sallar i'sha, suna dawowa daga masallaci suka dan ci abinci,suka kwanta.
*Washe gari*
Tunda suka tashi da asubaha ba su koma ba.dan so suk'e kawai su gansu a gida.
Dan ɗuk a takure suke anan,
*Bangaren Siyama*
Na haɗa komai na wa sannan mahaifina ya kira ƙanwarsa, watoh goggon na,akan cewa ta zo ta raka ni in ya so shi ya zo daga baya,ta amsa da toh.
Dan kuɗin da Malam yake da shi ne ya tattara duka ya bawa goggo Asabe ya ce in sun je can ta siyo min kafida da kwanuka da tukwane da zan dinga anfani da shi kafin ya karo min wasu ,ta karba ta amsa da "Toh ",
Ai Asaf na jin haka ya amshi ƙuɗin ya mayar wa Malam Iliyasu ya kara da cewa "Komai mu na da shi Baba ba sai ka siyo mata komai ba"
Baba ya buɗe baki zai yi magana Mus'ab ya karbi zancen da cewa "Da gaske kwai komai Baba karka samu damuwa".
"Shi ke nan Allah ya yi muku albarka ya kuma baku zaman lafiya" Suka amsa da "Ameen"
Har baƙin mota Malam Iliyasu ya raka su,
Muta nan Ƙauye ma ba'a barsu a baya ba,dan kuwa suma sun zo su ba wa idanun su abinci.
Rungume mahaifina na yi ina kuka.
Shafa kaina Baba ya yi cikin sanyin murya ya ce"Haba Siyama ba fa rabuwa muka yi ba.zan dinga zuwa ina kawo miki ziyara kema in an kwana ɓiyu za ki kawo min ziyara ".
Da haka dai Baba ya samu ya rarrashe ni na haƙura,
Bayan motar da Mus'ab ya buɗe mun ne na shiga ya rufe kuma dama ita goggo ta riga da ta shiga tun tuni,saboda goggo akwai ta da son mota Kamar me.
Tada motar Mus'ab ya yi suka ɗagowa Malam hannu ya ja suka bar Ƙauyen.
Karfe goma na safe suka isa kofar gidan su Asaf,
Home Mus'ab ya yi mai gadi ya wangele mu su gate ya cilla hancin motar cikin gidan.
Kallon kallo muka shiga yi, ni da goggo,har aka yi parking,
Shanye mamakin na nayi na fito daga cikin motar
Ita ma goggo fitowa ta yi tana zazzare ido.
Muje suka ji Asaf ya faɗa
Soma tafiya suka fara yi har suka karasa bakin kofar,
Danna kararawar ya yi ba bu jimawa aka zo aka buɗe kofar suka yi ido huɗu da.......
*Fulanin of Jajirtattu ce ✍️*
Comment's and share fisabilillah 👏