Showing 18001 words to 21000 words out of 22530 words

Chapter 7 - Mutun Ko Aljana Part 1 Complete by Sakeena Isma'il Cameroon--(Mom Muwadda)----.txt

yi ta waje sannan ta kalli Asaf ta ce " Mu je".






Kai kawai Asaf ya geɗa mata da shi sannan ya kama hannunta suka wuce part dinsa.








*Part din Asaf*




Suna zuwa ba su saya ko ina ba sai cikin ɗakin,sai yanzu Hajiya Rukayya ta fahimci akan wa Asaf yake magana,cikin tashin hankali ta juya ta kalli Asaf ta ce "Asaf tana ina ?kuma mai ka yi mata ?".






"Mom Mazwara ce take son sani na yi kisan kai".








"Wace ce Mazwara kuma ?".




Mom ta tambayi Asaf.


"Mom wannan fa aljanar ce, da ta hanani aure ".




"Toh ba ita ce aka rufe cikin kwalba_ ba ?".
"Eh Mom ita ce,ni ma abun ya bani mamaki sosai,dan Siyama ta ganta ido da ido dan har barazana ma ta yi mata ".




"Zo kiga wani abu Mom".




Asaf ya fadi yana kara kamo hannun Hajiya Rukayya suka nufi baƙin gado .




Jinin ɗazu da ya gani ne ya nuna wa Mom dinsa,






Mom na gani ta shi ga furta "Innalillahi wa inna ilahi rajiun !."






Shi ne kalmar da take ta maimaita wa ke nan.






"Yanzu kana nufin Asaf kai ne ka yi wannan ɗanyen aikin ? Yanzu tana ina ?".




Toilet Asaf ta nuna mata da hannu ta juya a fusa ce ta yi hanyar toilet ɗin.






Tana zuwa bakin kofar toilet din ta murɗa da niyar shi ga ta yi kicimis da Siyama za ta fito,




Sai cize labe take ,tana daɗdafa bango tana ganin Mom ta juya za ta koma toilet dan kunya fito da tawol a gabanta take yi.






Saurin rike hannunta Mom ta yi, Siyama kamar jira take sai kawai ta faɗa jikinta ta saƙi wani kuka mai suma zuciya,






Mom bata hana ta kukan ba, ta barta sai da ta yi mai isar ta sannan ta yi shiru tana maida numfashi,






Karaso wa bakin kofar toilet din ya yi ya na fadin " Haba Mom barinta fa kika yi tana kuka?".




"An barta ɗin,kai ba kaga abunda ka yi mata ba?mara kunya kawai ".




Asaf bai ce komai ba sai ma karaso wa da ya yi ya sungumi abarsa sai cikin ɗaki.




Akan kujera dake cikin ɗakin ya ajiye ta,kana ya je gaban wardrobe ya buɗe ya tiro wani Bedsheet din ya zo ya ya ye wan can ya shimfida wanda ya ɗauko.






Lokacin Mom ma har ta karaso wajan Siyama,




Bayan Asaf ya kammala gyaran gadon ne ya sake zuwa ya ɗauko ta ya kai ta kan gadon.




Kallon Asaf Mom ta yi ta ce " Ka fita ka bamu waje ka koma palo in mun gama komai za mu yi magana?".




Baki Asaf ya buɗe da niyar yin magana sai Mom ta haɗa rai ,ba shiri Asaf ya bar ɗakin ya koma palo.






Ƴata Siyama kwanta,ba musu na kwanta, ɗuk da ina son yin magana amma ba fuska,






Dan har ga Allah ba na son kwanciya da wannan tawol din a jikina,tun da a gida ma,zani nake d'aura wa idan na ta shi yin wanka.






Yanzu ma dalilin da ya sa na d'aura tawol din ban samu abun d'aura wa ba ne,kuma ba na son fitowa a haka.shi ya sa Kawai na d'aura.








Bayan na kwanta Mom ta saka hannunta ta kwance tawol din dake jikina ta shiga ware min kafafuna,




Saurin haɗe kafafun nawa na yi na shiga faɗin "Dan Allah! Hajiya ki yi haƙuri ".






"Siyama da ma ɗa yana boyewa uwa wani abu ne ?".




"A'a ".Na fada,


"Toh in dai har ɗa baya boyewa uwa wani abu ina so ki bani haɗin kai a matsayina _na mahaifiyarki kuma tsohuwar likina na duba ki ".




Ido na zaro waje kana na ce"laa! Hajiya ke ma likita ce ?".




Kai Mom ta geɗa min tana dan yin murmushi,saboda daga yana yin yanda take magana zai tabbatar maka ita din yarinya ce,






Duba Siyama Hajiya Rukayya ta yi, taga iri barnar da ɗanta ya yi mata.






Tunda taga wajan ta san ba karamin ɗauriya Siyama take yi ba.






Wani irin t'ausayinta ne ya kamata ,




Dole ta yi mata dinki,ta kuma samo mata paracetamol ta sha kar zazzabi ya rufe ta,amma kafin nan dole sai ta fara sanin meye faru ?mai kuma wannan aljanar ta faɗa mata ?




Gyara zama Mom ta yi kana ta kamo hannun Siyama ta hada da na ta ta shiga tambayarta .






"Siyama ina so ki fada min duk abunda ya faru tun daga farko har karshen saboda mu san ta inda zamu bullowa alamarin ".




"Toh ". Na ce sannun na shiga bata labarin abunda ya faru saka ni na da Sir yellow,har da abunda Mazwara ta fada min ɗuka ban boye mata ba.






Cikin mamaki da kuma tashin hankali Mom ta saki hannuna ta mike ta fita ta bar ɗakin,




Tana fita ta samu Asaf a palo, Asaf na ganin Mom dinsa ya mike yana tambayarta "Ya Mom kin duba ta ne ?".




"Na duba ta naga aika_ aikan da ka yi ".






"Mom wallahi ba da sani na ba ne na aikata mata wannan abun,asali ma ni ban san lokacin da wani abu ya shiga saka nin mu ba.sai bayan angama komai.....". "Gaga daka ta asaf !ta fada min duk abunda ya faru zo ka raka ni ɗakin ajiye kayan sirri na duba in ina da kayan aiki acan na zo na na yi mata ɗinki,dan dole sai an yi mata ɗinkinki sannan zata dawo daidai ".


"Toh mu je Mom ".




Asaf ya faɗa sannan suka gyera suka tafi.






Suna zuwa ya sa key ya bude kofar ɗakin,ma kunnin ya taba ya kunna fitilar ɗakin sai haske ya gauraye ko ina.




Ido suka zaro waje gaba ɗayan su a lokacin da idanun su ya yi tozari akan......










In na kara one page nagama free page 😉🥰








Duk wacca ta shirya biya ga number din da zai yi min magana.


07049322735 .wannan ita ce number,sai a yi min magana a WhatsApp.
Sai na jiku masoyan Asaf da Siyama 🥰 har ma da Mazwara duka 😆 dan na tabbata ita ma tana da masoya 😂😂💃








*Fulanin of Jajirtattu ce ✍️*










Comment's and share fisabilillah 👏
[30/09, 23:04] Sakeena Isma'il Cameroon🥰: 💫MUTUN 👩‍🦰KO ALJANA 👹💫




Story and Written ✍️




By: Sakeena Isma'il Cameroon
(Mom Muwadda)




________________________________________________






Utilise ce lien pour intégrer mon groupe WhatsApp : https://chat.whatsapp.com/KN5jaKvQOu02sqXTMBtbRJ




________________________________________________






https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️




________________________________________________




*Diamond 💎Star 🌟 Ladies* 🧝‍♀️
*(We stand together)*
🤝🤝🤝




Paid Book ₦500






Karshen free page 1️⃣5️⃣






Kamar yanda na sanar da ku cewa daga wannan page ɗin na kammala free page,dan haka ɗuk wacca ta shiya yin palmpay kofar a buɗe take,ga account number ɗina nan 8068569407.


Sai a tura shaidar biya ta wannan number 07049322735.sai na ji ku masoyana masoyan littafin Mutun ko Aljana 😍bari muga irin son da kuke yi wa Asaf da Siyama shin mai karfi ne. ko kuwa?😂






Bismillahi rahmani rahim






Ido suka zaro waje gaba ɗayan su a lokacin da idanun su ya yi tozari akan kwalbar dake tarwatse a kasar tayel ɗin ɗakin.






Cikin sauri suka karasa inda kwalbar ta fashe,har suna rige _rige






Sugunnawa Mom ta yi ta kalli kwalbar da kyallen dake gefe,ta juya ta kalli Asaf da shi ma yake a durkushe,kana ta ce "Asaf wannan ba kwalbar da ka dawo da shi ɗazu da safe ba ne ?".




Kyallen ya ɗauka ya kare mata kallo sosai kana ya juya cikin mamaki ya ce "Wallahi shi ne Mom ". Asaf ya faɗa yana kallon mahaifiyarsa.






"Toh waye fasa shi?ko ba ka ajiye shi inda ya ce ba ne ?".






"Wallahi Mom na ajiye ta inda ya dace, ban san ya aka yi ta faɗi ta fashe ba.sai dai in wani ne ya shigo ɗakin ya ɗauka ya fasa ".






Asaf ya kare magana cikin sanyin murya.






" Haba karka gaya min maganar ban za Asaf. wa zai shigo ɗakin nan ?
Kafi kowa sanin cewa iya mu ƴan gidan kawai muke bude wannan ɗakin,bayan mu babu kowa,kuma ka san s'arai ma su aiki ba su da key ɗin ɗakin nan da sai mu ce su suka shigo ɗakin suka fasa " .






"Haka ne Mom amma ni abun ba karamin mamaki ya ba ni ba gaskiya ".






"Ni ba wannan ba.ta shi ka nuna min wajan daka ajiye ".






Kai Asaf ya geɗa yana miƙe wa ya nufi wajan da ya ajiye kwalbar kafin ta fashe .






Wajan ya nuna wa Mom d'insa ya ce "Mom nan na ajiye fa ".






"Haba_ haba wannan wajan da ka ajiye ba dole ta faɗi ta fashe ba Asaf ?gaskiya koma wa kauye ya kamaka gobe ya zama dole ka koma gobe_ goben nan dan ba zai yu ba, ka zauna da ƴar muta ne a haka ba.dole sai ka koma ,dan kana ganin fitowar ta yau daga cikin kwalbar nan abunda ya jawo maka ka kusa kashe ƴar muta ne,
Ni bari ma na duba abunda ya kawo ni na koma wajanta na yi sauri da gama na koma wajan Dadinku kar ya farka bai ganni ba ".






Ta faɗi tana karasa inda take ajiye kayanta ma su mahimmanci ,





Buɗe wajan ta yi ta d'auko akwatin ta juya ta kalli Asaf ta ce "Mu je".








Kai kawai ya geɗa masa suka fita ya kulle kofar suka bar wajan.








Kafin su karasa part dinsa ne Mom ta kalli Asaf ta ce "Sai ka faɗa wa Goggo ta shirya ku tafi tare daga nan ka maida ita ".




"Ta tafi ".




Ya bata amsa






"Ta tafi ina ?".




Mom ita ma ta tambaye shi,






"Na sa dreve ya maida ita dan ba zai yu na barta anan ba ".




"Wai yanzu Asaf sai daka sa aka maida matan nan ?".




"Toh ai Mom ita ta jawo da bata yi abunda za'a maida ita ba ai da yanzu tana nan ".






"Gaskiya ba ka kyauta ba. ta ya ya ko kwana ɗaya mutun bata yi ba ka sa a maida ita ?ai ko mai ta yi bai kamata a maida ita yau_ yau ɗin nan ba ".






"Dan Allah Mom ki yi hakuri ki zo mu karasa dare na yi ".






Da haka suka karasa ba tare da kowa ya kara cewa komai ba.






Ana zuwa Mom ta cewa Asaf ta jira su a palo ko kuma ya wuce ɗayan ɗakin in yana jin bacci ya kwanta,ya ce a'a zai jira ta a haka dai ya samu waje akan ɗaya daga cikin kujerun palon ya zauna,ita kuma ta karasa cikin ɗaki,domin yiwa Siyama ɗinki.






Mom na shiga ya miƙe ya nufi ɗayan dakin domin yin wankan tsarkin da bai samu ya yi ba tun ɗazu,dan ya ma manta shaf da maganar wanka tun lokacin da ya ga Siyama a wannan yana yin Sai yanzu abun ya faɗo masa.








Mom tana shiga ta tarar da Siyama kwance akan gado ,bacci har ta fara daukarta,ta ji shigowar mutun zumbur ta _tashi daga kwancen da take.






" Sannu ƴata ". Mom ta faɗi tana karasa baƙin gadon ta zauna ,






"Yauwa sannu Hajiya ".




Ni ma na faɗi cikin jin kunya,








*Bayan awa ɗaya*






Bayan Mom ta gama yi min dinki ne ta miƙe ta nufi inda Asaf yake ajiye magungunan sa ta buɗe ta duba min paracetamol da ibuprofen ta kawo min da ruwa na sha,




Bayan na kammala sha ta karbi glass cup din ta ajiye sannan ta kalle ni ta ce "Yauwa ƴata Allah ya kara sauƙi ni zan tafi sai na dawo da safe mai kike so a faɗa miki ?".




Cikin jin kunya na ce "A'a Hajiya ni bana son komai,bai kamata a matsayinki na babba na saki girgi ba,ni ce ma ya kama a ce na yi miki girki ba ke ba ".




Ƴata ke nan ba ni ce zan yi ba wannan yarinyar da ta kai ku ɗakin bakin nan ne take yi,dan haka ki faɗi abunda kike so a dafa miki?".






Shiru na yi kamar ba zan ce komai ba.tuna wa da na yi da wannan girkin da na gani wata ƴar burni ta dafa a cikin film din da na gani rannan ne ya sa na ɗago da sauri ina cewa "Yauwa Hajiya akwai wani abinci da na ga wata ƴar burni ta yi a TV rannan shi nake so a dafa min ".






Dan murmusha wa Hajiya Rukayya ta yi kana ta matso kusa da ni ta ce"Toh ya sunan abincin ƴata?".








Jin Mom ta tambaye ni sunan abincin ne ya sa jikina yin sanyi,dan kuwa ko za'a kashe ni ba zan iya cewa ga sunan
abincin ba.








Fahimtar hakan da Mom ta yi ne ya sa ta cewa "ɗan kwatanta min yan da aka faɗa abincin sai ayi miki ".




Jin abunda Mom ta kara faɗi ne , ya sa ni sakin murmushin jin dad'i har dimple dina ta lotsa,






Kallon ta Mom ta saya yi,dan ba karamin burgeta ta yi ba.komai nata abun burge wa ne,gashi cikin sanyi take yin komai.




Ɗuk da a kauye ta fito amma in ba ta yi magana ba_ ba za ka taba cewa a kauye ta fito ba.








Saboda kwata_ kwata bata yi kama da su ba.






Kwantan ce na yiwa Mom tun kafin na karasa kwantacen ma ta gane jolof din shinkafa ce da kwaisilo da pepe ciki nake nufi .






Dan haka ta ce in sha Allah za'a dafa min,






Godiya na yi mata da kuma sai da safe ta juya ta bar ɗakin.






Tana fita ta samu Asaf a palo yana gengeɗi sai da ta ɗan buga gafen kujeran sannan ya buɗe ido haɗe da miƙa wa ya ce "Mom kin gama ?".




"Eh na gama ".




"Saura ka kara yaga ƴar muta ne kaga abunda zan maka ". Tana kaiwa nan bata saya jiran mai zai ce ba ta bar ɗakin .








Da kallo ya bita har ta bar palon,key ya je ya saka wa kofar sannan ya juya ya nufi bedroom,






Yana shiga ya tarar da ita tana addu'ar bacci karasowa ya yi ya z'auna ya kura mata ido yana kallon wannan ɗan karamin bakin nan nata dake ɗan motsa wa kaɗan_ kaɗan saboda karatun da take yi.






Har ta gama ta shafa.






Ta zame zata kwanta ya riƙo hannunta ya hana ta kwanciyar,






Baki sake nake kallon sa ina jiran in ji mai zai ce,dan in dai wannan abun yake so ya kara min yanzu zan fada mai ihu.






"Ni baki shafa min addu'an ba my heartbeat "?.






"Toh bacci zaka yi ne kai ma ?".






"Eh bacci zan yi bari ma ki ga ni ".Ya yi maganar haɗe da zame wa ya kwant gadon ya ja pillow ya ɗora kansa akai.








Ban ce mai komai ba,na fara addu'a bayan na gama na shafa masa na,na zira kafafuna da niyar sauka daga kan gado sai ya juya da sauri ya kalle ni, ya shiga tambayata ina zan je ?




"Zan je na kwanta kan kujera ne".






Na ba shi amsa ina koƙarin sauka,






Hannuna ya ja na faɗa kansa na kwanta,ina
faɗin washhhhh!




"Ya dai meye faru".






"Dinki na mana ka ja ni da karfi fa ".






Na faɗa a shogobe




Abun ba karamin burge Asaf ya yi ba,




Kara rungumeta ya yi ya ce"Sorry ki yi hakuri toh kin ji?".




Kai na_ nageda na yi kamar zan mike ya maida ni na kwanta,
A haka dai na hakura na kwanta har bacci ya dauke mu daga ni har shi ba tare da mun sani ba.






*Washe gari*




Kamar yanda ɗabiyarsa yake in zai yi tafiya ba ya iya cin abinci haka yau ma ta ka san ce,dan ba abunda ya ci,ya yi mun sallama akan cewa zai koma wajan Malam Shuaibu ya faɗa masa abunda yake faruwa,






Da na ji kauyen mu zai je sai na ji kamar na bi shi saboda a iya kwana ɗaya da na yi sai na ji gaba ɗaya ina kewar Babana,






Bayan mugana sallama ya je wajan iyayensa ma ya yi mu su sallama ya hau mota ya wuce kauye,dan wannan karon shi ƙad'ai ya tafi bai tafi da kowa ba.








*Kauyen masanawa*






Ba karamin mamaki Malam Iliyasu ya yi ba da yaga Asaf a gidan sa yau,






Amma ya shanye mamakin sa ya yi mai sannu da zuwa,






Bayan sun gaisa Baban Siyama ya kawo masa fura ya dan sha ne, yake faɗa mai dalilin zuwan sa yau,da kuma abunda ya faru da kwalba,






Shiru Malam Iliyasu ya yi ba tare da ya ce komai ba.






Cikin sanyin murya Asaf ya shiga tambarsa Lafiya ya yi shiru ko akwai matsala ne ?




Gyara zama Malam Iliyasu ya yi kana ya ce "Ɗana ka yi hakuri da abunda zan gaya maka.......
















Toh masu karatu mai Malam Iliyasu (mahaufin Siyama)zai gayawa Asaf 🤔kar fa ace akwai matsala 😱










Mu haɗu a sabon group,dan jin ya zata kasan ce Kuma me ya faru?










*Fulanin Jajirtattu ce ✍️*
















Comments and share fisabilillah 👏 mutanan amana 🥰
[04/10, 17:28] Sakeena Isma'il Cameroon🥰: 💫MUTUN 👩‍🦰KO ALJANA 👹💫




Story and Written ✍️




By: Sakeena Isma'il Cameroon
(Mom Muwadda)




________________________________________________






Utilise ce lien pour intégrer mon groupe WhatsApp : https://chat.whatsapp.com/KN5jaKvQOu02sqXTMBtbRJ




________________________________________________






https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️




________________________________________________




*Diamond 💎Star 🌟 Ladies* 🧝‍♀️
*(We stand together)*
🤝🤝🤝




Paid Book ₦500




Free page9️⃣






Bismillahi rahmani rahim






Ɗuk fito wa suka yi har da ni, ni kam ba karamin tashin hankali na shiga ba da jin wannan maganar Aljanar.






*Bayan mintuna 9*




Zaune suke a gaban wani Babban Malamin garin da ɗuk garin ba bu kamar sa dan shi yake tire mu su irin su Aljanu da ɗuk abunda ya shafi jinnu.






Tunda su Malam Iliyasu suka zo yake kallon Asaf ko giftawa ba ya yi.




Ɓangaren Asaf kuwa ba karamin haushi kallon da Malam yake masa ya ba shi ba.dan shi mutun ne da ya tsani kallo a rayuwarsa






Sai da ya kalle shi sosai sannan ya ɗauke idonsa ya juya ya dubi Malam Iliyasu "Ya ce gaskiya kun kyauta da kuka zo akan lokaci,da ba ku zo yau ba.da shi ke nan ba zai taɓa yin aure ba har karshen rayuwarsa amma tun da kun zo in sha Allah yanzu zamu fara aiki "


Malam Shuaibu ya faɗa yana ɗauko wata katuwar kwalba da wani jan kelle ya ajiye a gabansa.ya sake kallon Malam Iliyasu ya ce"Yauwa kowa ya nitsu zamu fara aiki ".




Ɗuk nitsuwa suka yi, ya d'auko wata alkur'ani ya buɗe ya ajiye shi a gabansa ya buɗe wannan kwalbar da ya ɗauko ɗazu "ya kara kallon Malam ya ce"Tare da ita za'a daura mu su auren ko?.Kai Malam Iliyasu ya geɗa mishi alamar "Eh".






"Okay ku matso nan kusa da ni"




Matsowa Asaf da ni muka yi gaban Malam,hannun Asaf Malam ya kamo ya haɗa da na nawa ya haɗa hannayen waje

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login