Showing 12001 words to 15000 words out of 22530 words

Chapter 5 - Mutun Ko Aljana Part 1 Complete by Sakeena Isma'il Cameroon--(Mom Muwadda)----.txt

masa da daddare ya ce in ya koma gida ya samu wajen da ba wanda yake shiga a cikin sai family dinsu kawai ya samu waje mai kyau a ciki ya boye kwalbar .






Ya ce wa Malam Shuaibu mai zai hana shi ya ajiye kwanbar a wajan shi.ya ce a'a shi ba shi da wani mahalli mai kyau da zai ajiye mai a cikin dan in har ya ajiye zai samu yaran da za su buɗe kwalbar ku ma in an buɗe aiki zai dawo baya,




Juyowa ya yi ya kalle su ɗaya bayan ɗaya ya ce " " Kunganta gata nan ɗuk suka miƙe suka taho in da yake ido huɗu suka yi da Aljanar Mazwara cikin kwalba sai mutsu _mutsu take tana zazzare ido,cikin tsoro Mom ta kalli Asaf ta ce "Kaga Asaf ta shi ka je ka ɓoye ta a ɗak'in ma ajin kaya na musamman "." Da toh "Asaf ya amsa sannan ya maida kwalbar cikin akwatin ya rufe ya yi musu sallama ya wuce cikin.






Ya na barin wajan bai saya ko ina ba sai cikin ɗak'in ajiye kaya na musamman.






Waje na musamman ya nemo ya tire kwalbar daga cikin akwatin ya ɓoye.






Sannan ya juya ya fita daga cikin ɗak'in ya sa key ya kulle ɗak'in sannan ya ja akwatinsa ya bar wajan ya nufi part dinsa.....










*Fulanin of Jajirtattu ce✍️*














Comments and share fisabilillah 👏
[20/09, 23:15] Sakeena Isma'il Cameroon🥰: 💫MUTUN 👩‍🦰KO ALJANA 👹💫




Story and Written ✍️




By: Sakeena Isma'il Cameroon
(Mom Muwadda)




________________________________________________






Utilise ce lien pour intégrer mon groupe WhatsApp : https://chat.whatsapp.com/KN5jaKvQOu02sqXTMBtbRJ




________________________________________________






https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️




________________________________________________




*Diamond 💎Star 🌟 Ladies* 🧝‍♀️
*(We stand together)*
🤝🤝🤝




Paid Book ₦500




Free page1️⃣1️⃣






Bismillahi rahmani rahim






Sannan ya juya ya fita da ga cikin ɗakin , ya sa key ya kulle ɗakin, sannan ya ja akwatinsa ya bar wajan ya nufi part dinsa,






Yana zuwa part dinsa bai saya palo ba ya wuce ɗaki darek,




Yana shiga ya ajiye akwatin gefen wardrobe d'insa ya shiga rage ƙananan kayan da ke jikinsa.




Bayan ya kammala rage kayan ne ya d'auki tawol ya d'aura ya wuce toilet,




Sai a lokacin na karewa ɗakin kallo.




Komai na ɗak'in fari da gwalɗin ne,kama daga bed, wardrobe, dressing mirror, carpet ɗin da ke sakiyar dakin har ma da kujerar mai zaman mutun biƴun da ya saka a can gefe,ɗuk fari da gwalɗin ne,sai lamulayen ne ƙad'ai mai kala gwalɗin.






Ɗakin ya haɗu iya haɗuwa,dan ita wardrobe din sakiyar sa ma glass ne.




Bayan na karewa ɗakin kallo na fita na ja masa ƙofa na wuce wajan su Siyama dan ganin me suke yi a cikin ɗakin baƙin da aka ba su😂




*Bangaren su Siyama da Goggo*




Bayan Sa'ade ta kai su wani haɗɗan wani ɗakin baki mai masifar kyau ne ta nuna mu su komai har da toilet ta fita ta bar su.




Ɗakin d'auke yake da ƙananun gaɗo guda ɓiyu sai dan karamin wardrobe a sakiya




Ɗakin ya yi kyau ba bu laifi,




Goggo ce tun da ta shigo ɗakin take nuna k'auyenci,




Ta taɓa wannan ta taɓa wancan




Ni kam sai kawai nake girgiza wa.




Ɗuk da kuwa ni ma ina so na yi kallon amma in na yi za su raina ni tun yanzu shi ya sa na dage na haƙura






Baki na buɗe na ce "Haba Goggo mai haka dan Allah ki dena nuna wannan k'auyenci karki zubar min da mutunci tun yanzu,yanzu ma kina ganin ko kallo bamu ishi wa su ba.ba dan yellow na da kirki ba ma da tuni mun daɗe da barin gidan nan"






Na ƙare magana ina mai miƙawa daga kan gadon da nake zaune,na wuce toilet domin yin alwala dan Allah ma ya sani ba zan yi wanka yanzu ba.tun da ban daɗe da yi ba.






Har na buɗe kofar toilet zan shiga sai na ji Goggo na cewa" Mara kunya in ba ki yi haka ba ma baza'a gane Zainabu ce uwar....".Goggo ba ta karasa magana ba ta ji ina cewa"Goggo yi sauri ki zo ki ga wani abu ".Yana yin yan da na yi maganar ne ya sa Goggo saurin karasa in da nake kafin Goggo ta buɗe baki ta yi magana idonta ya sauka in da nake kallo.




Toilet ne mai kyau hadda su mirror da bahon wanka da dai sauran su.




Toilet din ya yi kyau ba laifi,






Goggo ce ta kalli Siyama ta ce "Wai Siyama anya wannan bayan gida ne kuwa ?"."Eh Goggo bayan gida ne,saboda na taɓa gani a wani film ni da Indo lokacin da mu ka je wannan gidan kallon ta unguwar mu ".




"Ki na nufin gidan kallon na Ado ?".




"Eh can nake nufi Goggo".




" Rannar zagayowa ranar haihuwata ce Baba ya ba ni ɗari biyar shine na d'auki Indo muka tafi gidan kallo aka saka mana film mai dad'i , a cikin film din ne aka nuno wata yarinya ta shiga toilet ɗin ta hau wancan abun ".Ta faɗa tana nuna wa Goggo mats'ai




Kallon wajan Goggo ta yi ta ce " Ikon Allah !yanzu Siyama ki na nufin a nan zan hau in ina jin kashi?"."Kwarai kuwa Goggo tsaya ma ki ga na nuna miki".




Na faɗi ina shiga cikin toilet ɗin,




Zama na yi akan mas'ai ɗin.




Ina washe baƙi ,na ce " Goggo ha ka zaki dinga yi kin ga in kin gama sai ki ta shi ki ɗanna anan ".




Na faɗi ina saƙin ihu kamar mara hankali,




Saboda yana yin yan da na ji wannan abun da yake kore kashin dana taɓa yana ɗan yin kara.




Dariya Goggo ta saƙi tana tafa hannu,




"Yauwa Siyama fita toh da ma kashin nake ji "




"Kai Goggo wai ke ko kunya ma bakya ji ne ? Zaki din ga wani cewa kashi_ kashi dan Allah in wani ya shigo fah "






Goggo ba ta ce komai ba ta karasa cikin toilet din,ci kanta ban ce ba. na juya zan fita ban san ya aka yi hannuna ya taɓa wajan kunna famfon saman nan ba. kawai saukara na yi a kaina.




Goggo na ganin haka ta fashe da dariyan mugunta.






Ƙ'ok'arin kashe famfon nake amma na ƙasa,






Da yake ina da cutar limoniya ne ya sa bana son ruwa san yi ya taɓa mun jiki ko ka ɗan ballanta na a kai,




Shi ya sa ko a gida in na je wajan ɗibar ruwa da zarar na ga haɗari a gari nake yin saurin komawa gida.




Numfashi na ne ya din ga yin sama da kasa.






Ya fito daga wanka kenan sai ya tuna da su,




"Kai shaf na manta wallahi ban gaya wa Sa'ade ta nuna musu yan da za su yi anfani da kayan toilet din ba.bari na yi sauri na saka jallabiya na je na nuna musu kafin na zo na ɗan kwanta na wuta ".






Ya faɗa sannan ya yi saurin zuwa gaban wardrobe dinsa ya buɗe ya tiro milk din jallabiya mara n'auyi sosai ya riza ko wando bai saya sakawa ba ya yi bakin kofa ya bar dakin nasa ya wuce ɗak'in su baƙi,




Da yake dakin baƙin ba bu nesa yana kallon part d'insa shi ya sa bai wani jima ba ya karasa ɗak'in.




Tarar da kofar ɗak'in ya yi a wankale dan haka bai jira nemon iso ba ya shiga cikin ɗakin




Kallon dakin ya yi ya ga ba bu kowa har ya juya zai bar ɗakin sai ya ji numfashin da Siyama take fitar da shi daga cikin toilet ɗin,ga kuma dariyar Goggo da ke tashi daga cikin toilet ɗin,




Tun da ya ji yanayin yan da take fitar da numfashin ya san ba lafiya ba.






Dan haka bai yi wata_ wata ba ya faɗa cikin.






Yana shiga ya ganta tsaye ta d'afa bango ta kasa ƙwaƙwaran kotsi sai numfashi kawai take fitarwa sama_ sama




Cikin tashin hankali ya karasa wajan ta ya furta "Subhanallah !".




Sai a lokacin Goggo ta ankara da abunda yake faruwa dan ɗazu kwata _kwata bata lura da halin da Siyama take cikin ba.




Saurin karaso wa ya yi ya riƙo ta,sannan ya kashe famfon.




Sai a lokacin ya juya ya kalli Goggo ya saki tsaki Mtsiii ,sannan ya d'auke ta cak ya fito da ida daga cikin toilet ɗin.






Bai sa ya ko ina da ita ba sai part d'insa,




Da Goggo ta zo zata bi su ya juya ya kalleta suna haɗa ido ta koma ciki ta zauna,




Ana haka ne aka turo kofar ɗak'in aka shigo Sa'ade ce ta zo ta kira su su ci abinci ta tarar ba Siyama anan ne Goggo take gaya mata abunda ya faru,ai tana jin haka da gudu ta koma ta je ta fadawa su Hajiya,




Su Hajiya Rukayya suna zaune Sa'ade ta zo ta faɗa musu binsa yake faruwa suna jin haka ɗuk suka miƙe suka wuce part ɗin Asaf,






Tana sama ta ji abunda Sa'ade take faɗi ai ba shiri ta miƙe ita ma ta sauko tabi bayan su Hajiya Rukayya tana sakin murmushin mugunta.






Yana shiga ɗak'in ta ita bai saya a ko ina da ita ba.sai kan makeken gadonsa,




Kwantar da ita ya yi akan gadon sannan ya miƙe ya je ya kashe AC dake a kunne.




Ya dawo gaban gadon har zai zauna sai ya tuna bai rufe kofar ɗakin ba ya koma ya kulle sannan ya dawo ɗak'in,




Gaban wardrobe d'insa ya je ya tiro ɗaya daga cikin jallabiyan ya d'auko tawol ya dawo ya zauna kusa da ita,sai a lokacin ya kalli yanda rigar jikin ta ya jiƙe har ana iya hango komai nata,gashi bata saka ko bra ba,duk irjinta a waje.




Saurin kauda kansa ya yi gefe yana runtse ido,




Kansa na dege ya shiga tire masa rigar.....
















*Fulanin of Jajirtattu ce ✍️*










Comment and share fisabilillah 👏
[22/09, 23:38] Sakeena Isma'il Cameroon🥰: 💫MUTUN 👩‍🦰KO ALJANA 👹💫




Story and Written ✍️




By: Sakeena Isma'il Cameroon
(Mom Muwadda)




________________________________________________






Utilise ce lien pour intégrer mon groupe WhatsApp : https://chat.whatsapp.com/KN5jaKvQOu02sqXTMBtbRJ




________________________________________________






https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️




________________________________________________




*Diamond 💎Star 🌟 Ladies* 🧝‍♀️
*(We stand together)*
🤝🤝🤝




Paid Book ₦500




Free page 1️⃣2️⃣




Kansa na gefe ya shiga tire mata rigar,


Yana cikin tire mata rigar hannunsa ya sauka a wani abu mai laushi da shi kansa bai san mene ne shi ba.




Dan shi tun da yake bai taɓa jin abu mai laushi kamar wannan abun da ya taba ba.




Har zai ci gaba da tire mata rigar da yaƙe yi sai yaga ba zai iya cin gaba _ba in har bai ga wannan abun da ya taɓa ba.




Dan haka ya ɗago rinennun idanunsa ya ɗora su akan manya _manyan irjinta da hannunsa yaƙe kai,




Ai yana ganin abunda yake riƙe da shi ya yi tsaurin tire hannunsa yana runtse ido.




Dan shi tun da yake bai taɓa _ta ba ko da hannun mace ba.ballantana har ta kai ga kama irji,




Ni kam tun da ya taɓa min irji nake girgiza masa kai alamar ba na so saboda a irin yana yin da nake ciki ba zan iya hana shi ba.



Ci gaba da tire min rigar ya yi ana haka ne ya ji ana nocking ɗin kofar ɗakin,dan haka ya dakatar da tire min rigar ya miƙe ya nufi baƙin kofar,
Yana karasa baƙin kofa kafin ya buɗe ya ce "Waye ?".


" Mu ne Asaf ka buɗe mana kofa ".


Ya ji Mom ta faɗa,
" Mom ke da waye?".




" Shi ma ya je fa wa Mom tambaya ?".


" Wannan wacca irin tambaya ne Asaf?
Toh ni da ƴan gidan gaba ɗaya ".


Ita ma Mom ta ba sa amsa cikin jin haushin tambayar .




"Ki yi haƙuri Mom kayan jikinta ne nake tire mata ya jiƙe gaba ɗaya da ruwan famfon da ta kunna, ɗazu na je da niyar nuna musu yan da za su yi anfani da kayan toilet din na tarar ta kunna famfon kuma ba ta kunna hita ba,shi ne ruwan sanyi ya jikata,kuma da alama tana da cutar asma ".




"Subhanallah! Toh ba su na tare da Goggon nan nata ba.ya aka yi ta bar ta har ruwan ya jika mata jiki?".






"Mom! wallahi dariya na tarar tana yi, ba dan na je ba ma,da Allah ne Kaɗai ya san irin halin ta za ta shiga ba,kai Mom zam ma iya cewa ma. ta riga da ta saka ta wani hali tun da yanzu ma numfashinta sam yake yi,
Dan Allah Mom ku kiramin doctor Jamil ya zo ya duba ta".




" Toh shi ke nan Asaf bari yanzu Mu'azzam zai kira sa kafin ya wuce wajan aiki, Allah ya kara sauƙi,in ka gama canza mata kayan na dawo anjima daga nan ma sai na haɗa mata tea mai k'auri ka samu ka bata ta sha ko kaɗan ne ".




"Toh shi ke nan Mom na gode Allah ya kara girma,bari na koma ciki".



Da"Toh ".Mom ta amsa sannan ta juya ta kalli su Zahra da Jamilah da ma sauran ta ce su tafi ɗuk suka juya suka bar baƙin kofar.




Aunty Jamilah kam sai da ta saya ta yi wa kofar wani irin kallo kafin ta bi bayan su.




Kai sai ka ɗ'auka kofar ce ta hana ta shiga.




Cikin ɗakin ya koma ya kara sa tire mata kayan jikinta.






Miƙewa ya yi ya je toilet ya kunnu hita ya taro ruwan zafi a wata ɗan karamin botiki ya haɗa hadda baby tawol ya dawo ɗakin.







Zama ya yi a gefen gadon ya ɗauko tawol din da ya saka cikin ruwa ya matse shi ya shiga goga mata ita a jiki, a haka ya dinga yi mata har sai da ya ga jikinta ya dan yi ɗu mi sannan ya tashi ya maida botikin cikin toilet ya sake dawowa,
Jalllabiyan shi da ya ɗauko ɗazu ne ya ɗauka ya sa mata,
Sannan ya zare sket ɗin shi ma,
Ya rage daga ita sai kajeran wando da ta saka a ciki.








Da yake ita ma ta jiƙe ne ya sa bai barta a jikinta ba ya shiga tire mata ita,


Yana cikin tire mata hannunsa ya sauka akan santa_ santa cinyoyinta masu laushi,
Wani irin bugawa irjinsa ya yi a lokacin da ya ji gabansa na sake ci gaba da miƙawa.
Dan tun ɗazu da ya yi harba da irjinta ido da ido gabansa ya miƙe,ga shi yanzu ma ya k'ara taɓa cinyoyi.


"Ya Allah! Me yake faruwa da ni ne wai?".
Ya tambayi kansa,


Dan har ga Allah yanzu kam jikinsa ya fara yin sanyi ga kuma wani irin ciwo da ya ji mararsa na yi.


Daure wa ya yi ya karasa tire mata wandon,yana ji tana riƙe mai hannu amma bai kulata ba.har sai da ya kammala tire mata ya ja mata rigar,ya rufe mata cinyoyinta.




Hannu ya sa zai ja bargo ya rufe ta da shi sai ya ji an kara yin nocking,




" Waye?".




" Ni ne ranka shi daɗe ".




Ya ji doctor Jamil ya yi magana,


Da ya ke ya ga ne muryar doctor Jamil ne ya sa shi miƙewa,ya karasa baƙin kofar ya buɗewa doctor Jamil ya shiga har zai rufe sai yaga Mom dinsa dan haka ya bata hanya ita ma ta shiga ciki,sai ya maida kofar ya rufe.






Bismillah ! Ya yi musu har cikin ɗakin inda Siyama take kwance.




" Gata ka duba ta doctor ina ga asma ne da ita ".




" Okay " doctor ya ce sannan ya karasa kusa da Siyama,




Ni kam tun da naga mahaifiyar yellow ta shiga ɗakin na shiga ƙ'okarin miƙewa




Doctor ne ya kalle ni ya ce "Haba ƴammata ina kike son zuwa na ga kina ƙ'okarin ta shi ?".


"Cikin sanyin murya irin ta marasa lafiya na ce "Zan sauka ne na gaida Hajiya ?".




Murmushin jin dad'i Mom ta yi sannan ta ce "Koma ki kwanta ƴata,ke da baki da lafiya ina ke ina gaida mutun ".


" Toh amma Baba yace in naga Babba na dinga gaida shi ko ba ni da lafiya ".




Ta faɗa da iya gaskiyarta,


" Toh shi ke nan ni daga yau in baki da lafiya na yafe gaisuwar taki,in kuma ki na so mu gaisa zan zo har inda kike sai mu gaisa amma ba sai kin tashi ba ".




" Toh amma Hajiya bai kamata a gaida manya a kwance ba ai ".




Baki Mom ta buɗe da niyar bata amsa sai Asaf ta riga ta cewa" Pls Siyama ki bari a bu ba ki sauran maganar ayi ta daga baya ".




Kai kawai ta geɗa ba ta ce komai ba,ta gyara kwanciyarta.


Duba ta doctor ya yi,ya rubuta mata magungunan da za ta sha,sannan ya ce ta kula sosai,


Bayan ya gama ya yi musu sallama ya fita,


Asaf ma ya ce bari ya je ya siyo magungunan da aka rubuta yanzu zai dawo, Mom ta amsa da toh,sannan Mom ta kara da cewa bari ta kira Goggonta ta zauna da ita kafin ya dawo,ai yana jin haka ya ce shi bai san da wannan zancen ba.




Shi wallahi Goggo ba za ta zauna da Siyama ba,shi gwara a kira ko Aunty Zahra .




"Shi ke nan ni bari na zauna da ita tunda ba jimawa zaka yi ba ".




Mom ta faɗi,
" A'a Mom bari na kira Aunty Zahra ta zauna da ita saboda na san Daddy na can na neman ki ".




"Bacci yake kuma ka san in ya yi bacci ba ya tashi ta wuri,dan haka kai dai ka je ka dawo ".




" Toh shi ke nan bari na yi sauri toh ".




Ya fadi bai jira jin mai Mom za ta ce ba ya fita ya bar ɗakin.








*Bayan mintuna sha biyar*






Ya dawo Mom ta yi musu sallama sannan ta koma part dinta,






Dama bayan tafiyan Asaf Mom ta sa an kawowa Siyama tea mai k'auri ta sha,dan haka magani ya bata ta sha ta kwanta.








*Da daddare*




Ganin dare ya yi sosai ne ya sa ni miƙewa zan koma ɗakin da aka ba mu,




Bango na shiga dafawa dan jiri nake ji ga wani zazzabi ta nake ji sosai a jikina,amma ba zan iya zama a wannan ɗakin ba.


Har na kai baƙin kofa sai na ji wani irin jiri ya ɗibeni zan faɗi.




Fitowarsa ɗaga wanka kenan daga shi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login