Showing 9001 words to 12000 words out of 22530 words
Chapter 4 - Mutun Ko Aljana Part 1 Complete by Sakeena Isma'il Cameroon--(Mom Muwadda)----.txt
ta bar wajan ta na kuka,
Sai a lokacin mutanan wajan suma su ka watse
Cikin san yin jiki Mus'ab ya kalli Asaf ya ce ma sa"Abokina mu haƙura da jira bakanikin nan mu koma in da motar mu ta ke sai mu kira dreva ya kawo mana wata motar da ga nan ma sai ya taho mana da bakanikin da zai gyara mana motar"
"Eh gaskiya ka kawo shawara mai kyau ni tun d'azu ma ban yi wannan tunanin ba wallahi ka ga da ace tun d'azu muka yi wannan tunanin ma da yanzu mun daɗe da barin wajan nan tun da ba wani nesa muka yi sosai ba".
"Haka ne"
Cewar Mus'ab,
"Toh amma me ya sa na gan ka wani iri ?"
"Wai kana nufin baka ji a abunda mutanan nan suka faɗa ba?"
Kai Asaf ya girgiza alamon bai gane ba.
Kwashe komai Mus'ab ya yi ya gaya ma sa ya kara da cewa "Toh ka ga gwara mu bar wajan nan,dan in mun zauna ba mu san wana irin huƙunci za su ɗ'auka akan ka ba,ni wallahi bam ma san me ya sa ka taɓa ta ba kai da ko hannun mace ba ka ta ba taɓa wa ba,sai ga shi yau har da riƙe Kwankwason mace ka na kallon ta.
Kai ka san me? abun fa ya burge ni gaskiya "Mus'ab ya kare magana ya na fashewa da dariya harda riƙe ciki.
Asaf kam ba karamin kulewa ya yi ba da irin dariyan da Mus'ab ya ke yi uwa uba shi bai ga abun dariya nan ba, da har zai tsaya ya na dariya,
Juyowa ya yi ya soma tafiya,
Mus'ab na ganin haka ya sai da dariyarsa da yake yi ya ce "Asaf ba mu je mun yi wa Baba sallama ba za mu tafi ".
Sai da tafiya Asaf ya yi ya juyo ya ce"Kai tun da Babanka ne sai ka je ka yi masa sallaman ai "
Ya na gama faɗar haka ya juya ya ci ga ba da tafiya
"Tsaya ɗana akwai wata magana mai mahimmanci da na ke so mu yi kafin ka tafi"
Ya ji an faɗa cak ya tsaya shi bai juya
ba.shi bai ci gaba da tafiya ba.
"Ku zo mu shiga ɗaga ciki" Ya tsake ji an faɗa.
Wannan karon juyowa ya yi ya kalli Malam Iliyasu ya ce "Ai Baba na kira dreva gidan mu zai kawo mana wata mota har ma da mai gyaran motar ɗuka "
Murmushi irin na su na manya Malam Iliyasu ya yi kana ya ce"Shi ke nan ba bu damuwa amma dai ku zo mu je ciki kafin drevan na ku ya kara so da ga nan ma sai ku samu ku sha furan da Siyama ta dama muku "
Har Asaf ya buɗe baki zai yi magana jin an ambaci sunan fura ne ya sa shi yin shiru .
Saboda shi mutun ne da yake kaunar fura sosai a rayuwar sa,
Uwa uba ba karamin ƴinwa yake ji ba,tun da bai karya ba ya fito,
Juyowa Malam Iliyasu ya yi ya fara tafiya,
Bayan shi su ka bi har su ka karasa z'auren gidan da aka yi shi kamar bukka
Wata bukka da sai an sunkuya sosai ake iya shiga ya nuna musu da su shiga,kallon Mus'ab Asaf ya yi shi ma Mus'ab kallon Asaf din ya ke yi dan sun rena bukkan sosai
Kamar Malam Iliyasu ya shiga zuciyoyinsu ya ce "Ku shiga zai ishe ku"Kai su ka geɗa sannan su ka shiga,
Ka san cewa ba wani jiki ne da su nazo ka gani ba, shi ya sa ba su wani sha wahala wajan shiga bukkan ba.
Sai da malam Iliyasu ya tabbar sun shiga kafin ya juya ya koma cikin gidan ya kalli Siyama da tun d'azu take ta aikin rusa kuka ya ce.
Ke in kingama kukan naki ki ɗauki wannan furan da ki ka dama mun d'azu ki kai musu ki zo mu yi magana "
Kai kawai Siyama ta geɗa ba tare da ta yi magana ba,ta miƙe ta shiga ɗak'in mahaifinta ta d'auki kwariyar furan da ta dama ta fita,
Da ta zo bakin kofar shiga ɗak'in sai da ta tsaya ta gyara mayafinta kafin ta chusa kanta ciki haɗe da yin sallama.
Su na z'aune cikin bukkan sai karewa bukkan kallo su ke yi dan Asaf ma Mus'ab kallon bukkan,
Duk da bukka ne amma ko mai dake cikin bukkan saf _saf ba bu ko datti ko kaɗan a ciki,ga wani kamshin turaren tsinke dake ta shi a ciki,
Katifa ne a cikin ɗak'in sai bargo da aka ajiye akan katifan sain wani dan karamin carpet ma daidaici da aka shimfiɗa a kasa,ka san cewa garin akwai sanyi sosai shi ya sa rabuwa da wuta a ɗakin,kullun cikin kunna gawayi su ke a ɗak'in.
Ɗak'in ba karamin burge Asaf ya yi ba,har ya ji zai iya rayuwa a cikin ɗak'in ba tare da ya ji komai ba.
Duk da shi mutun ne da ya tsani Ƙauye amma ya ji wannan Ƙauyen ya bambanta da sauran k'auyukan da yake zuwa,kuma bai san me ya sa ba.
Haka ma bangaren Mus'ab shi ma ba karamin burgesa ɗak'in ya yi ba,ɗuk da kuwa shi da ma can ba shi da masa'ala zai iya rayuwa a ko ina,
Jin siriryar murya na yin sallama a bakin kofa ne ya sa shi ɗagowa haɗe da amsa sallamar da aka yi,
zu ba wa ba kin kofar shiga ɗak'in idanu ya yi yana jiran ya ga mamallakin muryan
Fararen hannunta ta sa ta yaye labulan ɗak'in.
Kanta a kasa ta nufo in da su ke zaune,durkusawa ta yi ta ajiye kwariyar furan a gefen kafarsa,
Idanunta ne ya sauka a kan kafararen kafafunsa sai da ta tsaya ta yi wa kafar kallo na y'en second kafin ta ce "Ina wuninku?"
Ba ta jira sun amsa ba ta miƙe ta fita ta bar ɗak'in.
Da kallo ya bita da shi har ta bace wa ganinsa,
"Ta tafi sai ka haƙura da wannan kallon haka"
Ya ji Mus'ab ya yi magana
Juyowa ya yi ya kalli Mus'ab ya ce"Mus'ab mai ma ka ce ɗa zu muna waje ?"
"Wanne kenan?"Mus'ab shi ma ya tambaye shi,
"San da na riƙe wannan yarinyar da ta fito yanzu,mai mutanan Ƙauyen su ka ce?".
"Ohhh! Sai yanzu na gane tambar naka,Cewa su ka yi ba'a taɓa mata a nan Ƙauyen sai muharramin ta,
Wani irin miskilin murmushi ya yi da shi ƙa ɗai ya san manarsa,
"Amma me ya sa ka yi mun wannan tambayar ?".
"Karka damu kai dai ka matso ka sha fura"
Asaf ya yi maganar yana buɗe furan dake gabansa ya d'auki ludayi ya fara sha,
Ya na sha ya na lumshe ido,dan furan ba karamin dad'i ya yi ma sa ba.
Mus'ab ma matsowa ya yi,ya dauƙi ɗayan ludayin ya fara sha.
*Bayan mintuna 20*
Da sallama ya shigo ɗak'in Siyama na biye da shi a baya kara sowa ya yi ya samu wuri ya zauna ita ma zama ta yi
Gyaran murya ya yi ya fara magana kamar haka "Na san ba ku san dalilin da ya sa na tara ku a nan ba ? Ba dan komai ya sa na tara ku ba sai dan abun da ka yi ɗazu Malam ya karasa maganar ya na kallon Asaf,
Shiru Asaf ya yi ba tare da ya yi magana ba.
Ci gaba da magana Malam Iliyasu ya yi "Amatsayin ka na muslimi ka san tsarai ba bu kyau taɓa macen da ma mu harraminka ba.
"Eh na sa ni asalima ni tun da nake ban ta ba taɓa ko y'en yatsun mace ba ballantana akai ga runguma,ita ma wannan d'in har zan barta sai naga bai kamata ina kallo na barta ta faɗi ta jiwa kanta ciwo ba shi ya sa kawai na taimaka mata"
Asaf ya kare maganar
Murmushi Malam Iliyasu ya saƙi sannan ya buɗe baki ya ce"Ammma na san ba ka san dalilin da ya sa ka ji tausayin ta ba ko?"
"A'a Baba na sani mana naji t'ausayin ta ne a matsayinta na mace "
"Toh Amma me ya sa baka taɓa jin t'ausayin mace ba sai ita?ko su baka taɓa ganin wani abu ya same su ba?"
"A'a Baba akwai wata da ta taɓa faɗuwan a gabanta kuma ya yi kamar bai gani ba".
Mus'ab ya yi magana.
" Ɗana! Malam ya kira Asaf?". "Na'am Baba Asaf shima ya amsa.
"Mai ma sunan ka ?"
"Sunana Muhammad amma ana kirana Asaf!"
"Toh Muhammad ! Maganar gaskiya kana son Ƴata Siyama dan haka na baka ita saboda ko baka son ta ma yanda wannan abun ya faru a gaban jama'a dole na baka ita ballantana kana son ta,dan haka yau da la'asar za'a d'aura muku aure ka tafi da ita"
"Toh amma Baba...."
Malam Iliyasu ya katse sa da cewa"Karka ce komai ɗana .nasan kana tsoron a bunda iyayenka za su ce.toh karka tamu in an d'aura ni da kaina zan bi ku mu tafi tare na je na yi musu bayanin komai"
"Toh Baba amma mai zai hana a nari sai an je can ɗin sai a d'aura auren "
A'a ba na so Ƴata ta tafi tabar abun magana ne shi ya sa,amma in an d'aura auren anan ka ga kowa ya sh'aida matarka ce"
"Yanzu dai ba wannan ba akwai abunda yafi wannan?"
"Toh Baba muna jinka mene ne shi ?".
Akwai Aljanar da ta ke sonka kuma nan ba jimawa ba za ta aure ka dan a yanzu haka ma shirye _shiryen auren su ke yi da ita da ƴ'an uwanta Aljana ɗan haka ka gagg'auta yin wannan auren"
Yanzu sai mun ce wajan wani Malam an yi maka addu'a sosai a kuma kuma rufe Aljanar cikin kwalba dan in ba'a rufe ta ba ,ba za ta taɓa bari ayi wannan auren ba.dan haka ku tashi muje wajan malamin"
Kai su ka geɗa,
Cikin sanyin jiki su ka miƙe.
Ɗuk fita su ka yi har da Siyama,ita kam ba karamin tashin hankali ta shiga ba da jin wannan maganar Aljanar...
Kuyi haƙuri kwana ɓiyu kunjini shiru MIJINA ne bashi da Lafiya ya na gida sai yau ya samu ya fita shi ya sa kwana biyu ban samu dabar yin typing ba.
*Fulanin of Jajirtattu ce ✍️*
Comment's and share fisabilillah 👏
[16/09, 13:10] Sakeena Isma'il Cameroon🥰: 💫MUTUN 👩🦰KO ALJANA 👹💫
Story and Written ✍️
By: Sakeena Isma'il Cameroon
(Mom Muwadda)
________________________________________________
Utilise ce lien pour intégrer mon groupe WhatsApp : https://chat.whatsapp.com/KN5jaKvQOu02sqXTMBtbRJ
________________________________________________
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
________________________________________________
*Diamond 💎Star 🌟 Ladies* 🧝♀️
*(We stand together)*
🤝🤝🤝
Paid Book ₦500
Free page 1️⃣0️⃣
Bismillahi rahmani rahim
Ɗanna ƙararawar ya yi ba bu jimawa aka zo aka buɗe kofar suka yi ido huɗu da Aunty Jamilah matar ɗaya daga cikin yayyan Asaf .
Jamilah ta ka san ce irin matanan ne da ba sa son talaka ko kaɗan.
Gata kuma da son abun duniya,
Lolacin da ta buɗe kofar idonta ya s'auka akan Asaf fuskarta a sake,amma tana ganin su Siyama ta kalli kayan da ke cikinsu ta ɗaure fuska ta juya ta kalli Asaf ta shiga tambayarsa "Asaf su waye way'ennan kuma ?". Ɗan haɗa rai shima Asaf ya yi sannan ya buɗe baki ya ce "Haba Aunty Jamilah daga dawowa.ko shigowa ba mu yi ba shine zaki saya kina min tambaya ".Baki Aunty Jamilah ta buɗe da niyar kara yin magana sai ta ji Hajiya Rukayya ta yi magana"Bar su _su shigo Jamilah ?".
Ba shiri Jamilah ta matsa,
Kallon su Siyama da jikinsu ɗuk ya yi san yi ya yi ya ce "Ku zo mu shiga daga ciki ".
Kai suka geɗa masa sannan suka bi bayan sa,
Da suka shiga palon gidan suka haɗu da ƴayyan Asaf a palo da suka gansu suka buɗe baki za su yi tambaya su na haɗa ido da Mom ta girgiza mu su kai alamar su bari ba yanzu ba.
Sai kawai suka haƙura suka yi shiru,
Kallon su na yi na ce "Ina kwan ku ?"
"Da lafiya lau suka amsa gaba ɗayan su amma ban da Aunty Jamilah da ta suƙe fuska kamar bata taba yin dariya ba.
G'aisawa suka yi da goggo ma kafin Hajiya Rukayya ta fara kiran mai aikin su.
Mai aiki Hajiya Rukayya ta shiga kwallawa kira "Sa'ade! Sa'ade!!. Can ciki aka amsa da"Na'am Hajiya gani nan zuwa ".
Ba bu jimawa wacca aka kira da Sa'ade ta karaso palon Har k'asa ta durƙusa ta ce"Hajiya Babba gani ?".Ki je da way'ennan baƙin ki kai su ɗak'in baƙi su samu su yi wanka".
" Toh Hajiya ",
Sa'ade ta amsa sannan ta kalli su Goggo ta ce "Ku zo,na kai ku ma s'auƙin ku".
Kai Goggo ta geɗa sannan ta juya ta fara bin bayan Sa'ade,jin bata ji Siyama a bayanta ba ne ya sa ta juyowa ta ganta saye in da ta barta,
"Ki zo mu tafi mana "
Ban tankawa goggo ba na juya na kalli yellow mutumin muna hada ido ya geɗa min kai alamar na bisu,kai na geɗa sannan na bi bayan su Goggo,
Da kallon mamaki mutanan palon suka bini da shi,
Ga mamakin da ya kasa ɓoyuwa akan fuskokin ko wannen su,
Ba mamakin komai suke yi ba illa irin kallon da suka ga Asaf na yiwa Siyama,ga shi kuma sai da ya ce mata tabi su Sa'ade sannan ta bi su.
Abun ya ba su mamaki matuƙa,
Juyowa shi ma Asaf ya yi ya so ma jan akwatinsa da zummar barin palon sai mahaifiyarsa ta yi Magana "Dawo Asaf magana za mu yi"Ya ji mahaifirsa ta yi magana,
Ba shiri ya dakatar da tafiyan da yake yi ya dawo ya zauna akan ɗaya daga cikin kujerun da ke cikin palon.
Yana jira Mahaifiyarsa ya yi mai tambaya,dan ya san tambayar da za ta mai bai wuce na su Siyama ba.
"Su waye way'ennan ?Kuma mai alakar ka da wannan yarinyar da take neman izininka kafin ta bi wannan matar da suka zo tare?".
Irjinsa ne ya buga da karfi ya dage ya buɗe baki ya ce "Matata ce"
" Meee?"
Mutanan palon ɗuk suka haɗa baki wajan faɗi.
In ka tire Alhaji da ke zaune akan kekensa yana saƙin murmushi da alama maganar da Asaf ya yi ba karamin dad'i ya yi masa ba.
"Mom kalli Dada yana murmushi Mu'azzam ya faɗi ".
Ɗuk kallon Alhaji suka yi suka ga gaskiya ne murmushin yake yi
Ita ma Hajiya Rukayya bata san_ san da ita ma ta saki murmushi ba.dan rabon da daga Alhaji ya yi murmushi an ɗaɗe dan tun kafin ya kwanta ciwo.
Ba karamin farin ciki Hajiya Rukayya ta yi ba.
Asaf ma ɗagowa ya yi yana sakin murmushi da bai san yana yi ba,
A zuciyarsa kuwa son Siyama ne ya ji yana kara rasa mai jiki da jijiya dan ya tabbata shigowar ta rayuwarsu alheri ne,tun da ko kwana ɗaya ba ta yi a cikin gidinsu ba amma ya fara ganin canji.
Ha ka ma bangaren Hajiya Rukayya dan ita ma kallo ɗaya ta yi wa yarinyar ta ji ta kwanta mata a rai,
Matsowa Hajiya Rukayya ta yi kusa da Mijinta ta durkusa a gabansa ta fara magana "Alhaji ya na ga da Asaf ya ce wancan yarinyar matarsa ce ka yi murmushi ?".
Abun mamaki sai ya kara sakin wani murmushin wanda yafi na ɗazu yana geda kai sannan ya shiga ƙ'okarin daga hanunsa amma ya ka sa ganin abunda yake son yi ne ya sa Hajiya Rukayya taimaka masa daga hannun good 👍ya yi da babban yatsun hannunsa kana ya ci gaba da sakin murmushi.
"Alhamdulillah tun da ka amince da maganar auren mu ma mun amince ",
"Amma gaskiya Asaf sai ka gaya min yaushe ku ka haɗu har ku ka fara soyayya kaje ka aure ta ba tare da kowa ya sa ni ba ?".
Ɗan busar da iska Asaf ya yi daga cikin bakinsa kafin ya buɗe baki ya fara magana kamar haka "Wallahi Mom jiya ne da muka yi tafiya ko isowa in da zamu je ma ba mu yi ba motar mu ta lalace a wani Ƙauye...."
Kwashe komai ya yi ya gaya mu su daga haɗuwar su da Malam Iliyasu har da taimak'on Siyama da ya yi a lokacin da take son faɗuwan har da irin maganganun da 'ƴan Ƙauyen suka dinga yi,da kuma wanda Baba Siyama ya gaya mai,har da zuwan su wajan Malam Shuaibu da kuma irin wahalan da ya sha kafin ya rufe Aljanar Mazwara cikin kwalba.
Duk sai da ya gaya musu ba bu abunda ya boye mu su.
Bayan ya gama yi mu su ba ya nin komai ne ya ɗago ya dubi mahaifiyarsa ya ce "Mom kin ji dalilin da ya sa aka d'aura auren ba tare da an faɗa muku ba ke nan ",
"Ba dan komai ya sa na bari aka d'aura wannan auren jiya ba.sai dan irin son ganin na yi auren da kuke yi ",
Da a ce jiyan nan ba'a d'aura wannan auren ba. da tuni aljanar nan ta aure ni,kuma in ta aure ni _ni da aure har abadan ha ka Malam Shuaibu ya ce min ".
Ajiyar zuciya ɗuk mutan palon suka s'auke
Hajiya ce ta yi magana kamar haka"Gaskiya abunda ka yi shi ne daidai,da a ce ba ka yi ha kan ba. da ba zan taɓa yafe maka ba Asaf ".
Lumsh ido Asaf ya yi ya buɗe ya dora su akan ƴaƴansa kuda ɓiyu
Su ma kai suka geɗa alamar sun gamsu sosai da maganarsa.
Kallon yayan mahaifinsa ma ya yi wa toh goggonsa ke nan,ita ma geɗa masa kai ta yi tana murmushi sannan ta ce "yarona abunda ka yi.ya yi daidai ".
Miƙewa ya yi ya je kusa da Auntynsa Zahra matar yayansa Mu'azzam ya zauna kusa da ita kana ya ce " Mom karama ke fa ?".
Murmushi ta sakar masa sannan ta ɗora hannunta samar kansa cewa "Haba Boy ai ni ko kowa bai amince ba ni zan amince saboda nafi kowa son ganin matarka kuma Alhamdulillah! na gani kuma na ji dad'i ɗuk da ba haka na so auren ya kasan ce ba amma ba bu komai tun da lafiya aka d'aura an kuma raba ka da wannan muguwar Aljanar lafiya "
Tsaki duk suka ji an yi su na juyowa suka ga Aunty Jamilah ce ta yi,kafin su yi magana ta miƙe ta bar palon ta wuce bangarenta,suka bita da kallon mamaki.
Miƙewa ya yi ya je gaban akwatinsa ya kwantar da akwatin a hankali ya buɗe ya d'auƙo kwalbar da aka rufe Aljanar Mazwara a cikin wanda Malam Shuaibu ya kawo