Showing 24001 words to 27000 words out of 28291 words
cikin ruwan, abin al ajabi tana fitowa kafin tayi ƙoƙarin guduwa kamar an fizgota haka ta faɗa cikin ruwan, tun tana ihu iyakar ƙarfinta har tayi tsit.
Su Jafar da suka samu suka baro cikin ruwan jin shirun Mandiya tayi yawa yasa suka fara tunanin ya zasuyi su samu su fiddota.
Jafar kallonsu Biba yayi fuskarshi da alamun damuwa ya fara magana.
"Yanzu ba lokacin yin dogon tunani bane, kamata yayi musan yadda zamuyi mu ceci rayuwar Mandiya kada ruwan nan yayi mata wata illar, garin naiman magani kuma asamu wata matsalar, niba muharramata bace da sai in fiddota, amma cikinku yakamata ku yi ƙoƙarin fiddata a ruwan nan."
Tsuru_tsuru sukayi tamkar basuji abinda ya faɗaba, Biba ita tayi ƙarfin halin fara magana.
"Jamcy da Kulu ku yakamata mu haɗa karfi mu fiddota tunda mune mata."
"Wa! Allah ya tsare gatari da sarar suka, haka kawai kinta6a ganin wanda yakai kanshi ga halaka yanaji yana gani?, to nidai har yanzu ina son rayuwata inku bakuda buƙatar taku."
Jamcy ta ƙarashe maganar tana jan kitson attach ɗinta dayaji wuya yayi burcin_burcin.
"Mtssw! Allah wadaran naka ya lalace, yanzu ke ki taimaka aceci rayuwar baiwar Allah amma kitsaya kina 6ata mana lokaci, Biba zo muje ni koda wannan aikin da zaniyi zai zamto ƙarshen rayuwata ba shakka zani aikata, ina roƙon Allah sanadinshi yasa mahaifana su yafe mani laifinda nayi masu na barin gida batare da izininsu ba."
Tana ƙarashe maganar taja hannun Biba suka nufi ruwan.
Suna shiga sukayi nasarar samun Mandiya amma babu alamun tana motsi.
Da ƙyar suka samu sukayi nasarar fitowa da ita, kowa yayi tsit ganin kamar Mandiya ta mutu.
Fuskarta da suka kalla ganin ta koma suffarta ta ainahi yasan yasuka ji wani irin farin ciki ya ziyarci zuciyoyinsu.
Motsi da suka ga hannunta nayi wadunsu suka dare daga wurin, Rabson bayan Jafar ya koma yana leƙe yaga yadda zata kaya.
A hankali take ƙoƙarin buɗe idanuwanta da sukayi mata matuƙar nauyi,ɗaya bayan ɗaya tariƙa ƙarema su Jafar kallo.
Yunƙurawa tayi ta miƙe zaune tana murmushi ɗauke a fuskarta.
Rabson gani yayi kamar shi ɗaya take kallo tana dariya tana lashe baki, ihu ya ƙwalka tare da cikuikuye Jafar yana ƙoƙarin kayar dashi.
"Innahumin sulaimanu..., La'ilaha illallahu, shikenan kallona take tana lashe baki zata cinyeni, wayyo nashiga ukku lokacina yayi, Busurulle da Salma zaku zama marayu, shikenan Kakata yau zani mutu in barki."
Ganin Rabson na ƙoƙarin kayarda Jafar ya sanya Jafar mangarema Rabson geya.
"Kai ko anya zaka yi hankali?, mufa take yima murmushi ba kaiba, yanzu ta dawo ainahin Mandiyarta ba horror bace, kadawo cikin hankalinka."
Jin wannan maganar tasa Rabson ƙara kallon Mandiya da kyau, gani yayi ita ɗince ta dawo ainahin mutum ɗinta.
Ajiyar zuciya ya sauke tare da fadar;
"Wai Allah nagode maka, ashe inada sauran shan ruwa nan gaba, inada rabon auren Salma masoyiya."
Kaɗan ta hana su dara ganin wannan wauta ta Rabson.
Wurin Mandiya suka matsa suna mata sannu.
Amsawa taruƙayi hawaye na wanke mata fuska tana ƙara nadamar rayuwar da tayi abaya, tayi alƙawali har cikin ranta insha Allah bazata ƙara karuwanci ba har ƙarshen rayuwarta.
Jafar ya ji daɗi sosai, domin ya tuno da wani hadisi dayace, _KASHIRYAR DA MUTUM ƊAYA YAFIYE MAKA JAJAYEN RAƘUMA_
Allah sukayi ma godiya suna masu ƙara tawakkali da addu'a, domin sai yanzu suke ƙara tabbatarwa a baya sunyi sakaci da addu'a.
Yunwar dake cikinsu ce ta fara addabarsu, tunanin inda zasu samu abinda zasuci suka farayi, sallolinda ake binsu suka farayi, inda Biba ita tafarayi sannan ta anshi ɗankwalin kulu ta yafa ta basu hijabinta da ta Sha gwagwarmaya amma har yanzu tana nan saidai cukuikuyewa da tayi.
Bayan gama sallar wasunsu kwanciya sukayi suna hutawa, su duka sun lula duniyar tunani.
Ƙarar da sukaji ce ta sanya su miƙewa tsaye tare da dunƙulewa wuri ɗaya duna masu dafe kunnuwansu dake bara zanar tarwatsewa.
Tsagaitawa sukayi tare da rufe wangama_wangaman bakunansu.
Ɗago kawunansu sukayi jin ƙarar da sukeji ta tsaya, abinda majigin idanuwansu suka hasko masu ya sanyasu ƙara matsewa wuri ɗaya tare da fara sallallami wasu kuma suka fara hawaye tareda sabbatu.
Wasu irin maridan Aljanune mace da namiji tsaye fuskokinsu a matuƙar murtuke ba alamun imani a tattare dasu.
Namijin ya wangame baki ya fara 6a66aka dariyar da ta haddasa dajin girgiza, tsaida dariyar yayi tareda tur6une fuska ya nunasu da yatsa ya fara magana.
"Yau kwananku yazo ƙarshe, a baya kunyi nasara a kanmu mun iskeku kuna bacci kun ƙona mana hannuwa nida matata, na tsananta bincike aka wane irin sihiri kuke amfani dashi inda na gano kai wannan matsitsiyar halitta kai ka yi sanadin faɗawarmu wannan hali."
Ya nuna Jafar dake taye.
"Alokacin nayi ƙoƙarin ɗaukar fansa a kanku amma wannan sihiri da kuke amfani dashi nakasa koda taba akaifarku, nafara ɗaukar fansa akan abokan tafiyarku dana haɗu dasu su Ukku maza a hanya ta ta zuwa inda kuke tuni na hallakar dasu, yanzu kuma zani kashe ku in ba matata Matsayi kyautar masoya saboda tsananin ƙaunar da nike mata."
Jin an kashe Garba, Nura da Audu Jafar yaji zuciyarshi ta fara tafasa, wani irin ƙarfi yaji yazo mashi yayo kan waɗan nan halittu ba tsoro ko fargaba a tare dashi, ya nunasu da yatsa tare da fara magana.
"Ƙarya kuke yaku waɗan nan la'anannu kuma ta6a66u, ubangijinmu bai koya mana sihiri ba Sai dai addu'a wadda insha Allah ko a yanzu da ita zamuga bayanku, kun kashe mana ƴan uwa amma nasan lokacinsune yayi, domin bawa baya mutuwa sai Kwananshi sun ƙare, ku baku isa kuyi mamu komiba sai in Allah ya rubuta hakan zai faru damu."
"Hhhh! Yauni hatsabibi marz mijin marhaz naga halitta mai ƙarfin hali da taurin rai, tunda nike a dajin nan na kaikazo bantaba arba da halittu barasa tsoroba kamarku, yanzu zaniyi fata_fata da naman jikinku in shayar da matata jinanenku."
Ya ida maganar tare dayo kan Jafar da mummunan nufi a zuciyarshi.
" _LA'ILAHA ILLAH ANTA SUBUHANAKA INNIKUNTUMINAZZALIMIN._ "
Jafar ya furta a bayyane.
6acewa Jafar yayi a idanun aljani Marz, dube_dube yahauyi amma bai ganshi ba.
Gefe dasu Jafar ya hango wani irin icce mai tsinin gaske, ɗaukarshi yayi ya daka ma Aljanin a zuciya tare da kwala kabbara bakinshi ɗauke da sunan Allah.
Kuwwa aljanin ya ƙwala dayayi sanadin jawo hankali matarshi itama tayo kanshi da azababben gudu, kafin ta iso har yafaɗi ƙasa jini na malala ta hancinshi da baki.
Kafin ta iso wurin mijinta sul6i ya kwasheta ta faɗa cikin wannan ruwa da Mandiya ta faɗa.
Ihu take tana naiman taimakon mijinta, amma ina tana samu tafito daga cikin ruwan ta kama da wuta ta ƙone ƙurmus shima mijin ƙonewa yayi iska ta kwashe tokarsu tayi sama.
Ganin wannan al amari daya faru su Nas da Tk mamaki suka riƙayi na yadda Jafar yake da ƙarfin hali.
Jimamin rashin abokan tafiyarsu suka yi tare dayimasu fatan rahamar Ubangiji.
Sunyi kwana biyu a wurin saida jikin Mandiya da Su Salma suka gama warkewa.
Sun yanke shawarar zasuyi tafiya batareda tsayawaba ko da cin abinci Sallah ce kaɗai zata tsaidasu.
Sunyi kwana yakai biyu suna tafiya ba ƙaƙƙautawa batare da sun samu abinda zasuciba koda ƴa'ƴan itatuwane.
Kallo ɗaya zakayi masu kagane sun fita hayyacinsu, ga bakunansu sun bushe jikinsu duk yayi yaushi.
A kwana na ukku ne suna tsaka da tafiya ƙarfinsu ya kusa ƙarewa kamar daga sama bazato ba tsammani suka gansu bakin hanya, wasu mutane suka hango sunyo kansu amma ina kafin su ida ƙarasowa wurinsu tuni su duka sun yanke jiki sun sume.
Ogan sojojin ne ya ƙarema Salma kallo dan gano ko i ta ce wadda suke naima, ganin tafita hayyacinta tamkar ba itaba.
"Yess."
Ogan ya furta ganin i ta ce wadda suke naima , umarni yayi akira motar asibiti domin abasu taimakon gaggawa....
*COMMENT*✅
*SHARE*✅
*MEEN@RT...✍🏻*
08133562798
[10/11, 10:29 PM] Meen@t A Yandoma: 💀 *BAƘAR TAFIYA* 💀
( *HORROR STORY* )
*BY MEEN@T A YANDOMA*
*MARUBUCIYAR FATALWA*
🌍 *MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION*🌍🖊️
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
*SALONSHI NA DABAN NE 💃🏼*
*ALLAH KAJIƘAN MAHAIFINA DA DUKKN MUSULMI BAKI ƊAYA KASA YA HUTA, KA KAI RAHAMA A KABARINSHI, ALLAH KA GAFARTA MASHI ZUNUBBANSHI, ALLAH YAJI ƘANKA ABBANA*
*MASOYA INA MATUƘAR GODIYA DA SOYAYYAR DA KUKE NUNAMA LITTAFIN NAN, ALLAH YA BARMU TARE, INA MATUƘAR GODE MAKU MASOYA A DUK INDA KUKE*
🤸🏻♀️🤸🏻♀️🤸🏻♀️
*ƳAN BAƘAR TAFIYA FANS COMMENT ƊINKU YANA MATUƘAR TAFIYA DANI KUNA SANI NISHAƊI DA COMMENT ƊINKU ALLAH YA BARMU TARE,MASOYA INA GODIYA*
*ALLAH YA BIYAKU MY PEOPLE, ALKHAIRIN ALLAH YA KAI MAKU HAR GADON BACCINKU, ƳAN BAƘAR TAFIYA FANS, KUNA SANI FARIN CIKI DA ADDU'O'INKU, ALLAH YA ƘARA DANƘON ZUMINCHI, KUMA BAZANI MANTA DAKUBA SAURAN MASOYA INA MATUƘAR GODIYA DA SOYAYYAR DA KUKE NUNAMA WANNAN NOVEL ƊIN ALLAH YA BARMANIKU MASOYA INA ALFAHARI DAKU.* 🤗🤗
__________________________
*PAGE 36,37,38,39 and 40*
الحمدلله!
الحمدلله!!
الحمدلله!!!
_End_
..............."Assalamu alaikum, kiranka nayi in sanar da kai ansamu yarinyar nan yanzu haka gamunan motar asibiti ta kwaso mu domin suna cikin mawuyacin hali."
Cikin hanzari gami da zaƙuwa daga ɗayan 6angaren aka fara managa.
"Kuyi sauri kukaisu asibiti, nima gani nan zuwa."
Asibiti mafi kusa Pravet hospital suka kai su, suna isa Emergency aka nufa dasu likitoci suka duƙufa ceton rayuwarsu.
Alhamdulillah ansamu nasarar ceton rayuwarsu, anyi masu allurar bacci da sun tashi zasu dawo cikin hankalinsu.
Dukkansu a ɗaki ɗaya aka ajesu, gadajensu ajere suke.
Ƙofar ɗakin likitocin suka jawo, suna niyyar barin wurin.
Har tuntu6e yake ya kama hannun likita ya riƙe gam yafara magana muryarshi na Kyarma.
"Likita!, ina Mamana?, ina ɗiyata?, wane hali take ciki."?
Ya ƙarashe maganar cikin zaƙuwar jin amsar da zai bashi.
"Ka kwantar da hankalinka, yarinyarka tana nan lafiya Ubangiji ya taimakemu munyi nasarar ceto rayuwarsu, yanzu allurar bacci mukayi masu da sun tashi insha Allah zasu dawo cikin hankalinsu, saidai zamu riƙesu harsu dawo ciki hayyacinsu, domin yanzu suna buƙatar kulawa jikinsu ba ƙwari."
"Zani iya shiga inganta."?
Ya faɗa a hanzarce.
"A'a, yanzu suna buƙatar hutu sakamakon allurar bacci da mukayi masu."
"Zaniyi haƙuri harsu tashi, ina nan."
Ranar nan Alhaji Abdallah ya yini bayan ya sallami yaran abokinshi da suka samo su Salma, tare da yima amininshi godiya.
Ɗakin yayi tsit bakajin komi sai ƙarar A.C da ta gauraye ɗakin, A hankali ma'aikatan jinya mata suka turo ƙofar ɗakin domin bin umarnin Ogansu daya umarce su suzo suka insun farka, su duddubasu sunje kan Rabson, yatsun hannunshi yafara motsawa tare da ƙoƙarin buɗe idanunshi.
Ida buɗesu yayi ya saukesu akan ma'aikaciyar jinyar dake kanshi, a firgice ya ida buɗe idanunshi tare da ƙwala wata mahaukaciyar kuwwa.
"Innalillahi, nashiga ukku, lawakiri ki taimaka kada kiyi mani komi, wayyo ashe mutuwa nayi, yau ni Rabi'u na lalace kodai lahirama akwai Horo, wayyo bunsurulle shikenan na mutu na barka."
Yana ƙarashe maganar yayi tsalle ya diro daga saman gadon yayi hanyar ƙofa tare da cigaba da darza ƙara yana naiman taimako.
Sistocin kallonshi suke suna mamaki kodai baida hankali, ko kuma haɗarin daya samune ya maidashi haka.
Rabson jin ƙofa akulle babu hanyar fita ya juyo wutsiya zage yafara bin sistocin da kallo.
Wani tunani yazo kanshi, wata kujera dake nesa dashi ya raruma ya nufi sistocin da niyyar zai Make kawunansu sumutu kowa ya huta.
Ganin haka suka ƙara tabbatarwa bashakka Rabson mahaukacine, ihu suke suna naiman taimako, da ƙyar suka buɗe ƙofar suka fice a guje Rabson ya mara masu baya.
Alhaji Abdallah dake zaune yana dakon farfaɗowar Salma ganin mutane sun nufi inda yake a guje ya sanyashi miƙewa ya riƙe Rabson.
"Bawan Allah mizakayi masu daka biyosu da wannan makamin a hannu."?
"Kada ka yarda da waɗannan Horunan a nan lahirar ma biyoni sukayi su ƙara kashewa, dan haka barni dasu yanzu inga bayansu duk in kwaɗe masu kawuna da wannan kujerar."
Jin wannan wautar ta Rabso ba sistocin dake 6oye bayan Alhaji abdallah ba har shi kanshi saida ya tuntsure da dariya.
"Bawan Allah waya ce maka ka mutu?, kata6a ganin wanda ya mutu yana magana har ya riƙa fallawa da gudu da ƙafafunshi, alamu sun nuna kai majinyacine ba mutuwa kayiba nan asibitice aka kawoka."
Wata iriyar kunyace ta lullu6e Rabson jin ashe yana raye bai mutu ba.
Likitane ya ƙaraso wurin jin hayaniya ta yawaita.
Ganin Rabson tsaye yasa likita fara tambayarshi miya fiddoshi?.
Nan Alhaji Abdallah ke sanarda likita abinda ya faru.
Saida likitan yayi dariyarshi mai isarshi sannan ya lalla6a Rabson akan ya koma ɗakin da aka kwantar dashi.
Suna tura ƙofar ɗakin suka hango su Jafar duk sun farka suna jingine da gadajensu.
Salma ganin mahaifinta da tayi tamkar a mafarki yasa tayi wani tsalle ta rungumeshi batare da tunanin shiɗinne ko bashi bane.
Wani kukane ya kubce mata , ashe tanada rabon sake ganin mahaifinta, tana roƙonshi ya yafe mata ta tuba da sa6ama umarninshi, bazata sake tsallake maganarshi ba.
Rarrashinta yake yana jin wani sabon tausayinta na ratsashi.
Kowa wurin sai yanzu ya fahimci wannan shine mahaifin Salma.
Rabson da dai ya lura tabbas mutumin ɗazu shine sirikinshi,wata irin kunyace ta rufeshi, sulalewa yayi ya haye gado tare da rufe ido kamar yana bacci.
Bayan komi ya lafa, mahaifin Salma Odar abinci yayi masu sukaci suka hantse, domin rabonsu da irin wannan abincin tun kafin su fara Baƙar tafiya.
Salma ita ta gabatar da sauran abokan tafiyarta ga mahaifinta bayanta ƙwashe labarin dukkan abinda ya faru a tafiyar ta faɗa mashi, yaji irin gudumawar da Jafar da Biba suka bata a wannan tafiyar.
Juyowa yayi da nufin yimasu Jafar godiya, saidai suna haɗa ido da Jafar yaji gabanshi yayi wata irin mummunar faɗuwa
Saboda kama da Jafar yayi da wani ƙanenshi daya 6ata.
Godiya yayi tare dayi masu alƙawarin zai sanar da iyayensu Halinda suke ciki zai samesu har gidajensu, suyi masu kwatancen unguwannin da suke bama yara zai aikaba shi da karan kanshi zaije.
Kamar yadda yayi alƙawari tunda safe ya fara da gidansu Jafar, ya aika ayimashi da matar gidan, ƙanwar Jafar ce ta leƙo, ya sanar da ita halinda ake ciki tare da faɗa mata halinda ake ciki, rugawa tayi ta faɗama Ummansu abinda ke faruwa.
Suna isowa har Alhaji Abdallah ya 6ace a wurin ƙurar da motarshi ta tayar kaɗai ta rage, a hanzarce suka shirya suka nufi asibitin.
Lokacinda Alhaji Abdallah ya faɗama Kaka jikanta na asibiti, kuka ta fara tana shikenan Rabi'unta zai mutu shima ya barta.
Saida Alhaji yayita kwantar mata da hankali.
Shiryawa tayi itama ta nufi asibitin.
Da habib yaji abinda ya samu Basma bai wani kaɗuba dominshi yanzu matarshi Hanan ta gama mashi komi.
Badan yasoba sai dan Hanan da ta sanya baki ta lalla6ashi akan yaje ya dubo Basma, asibitin yanufa kai tsaye yana jin wani irin haushin Basma a zuciyarshi.
Haka yabi gidajensu Kulu, Jamcy, tk, da Nas ya sanar da iyayensu.
Hanyar asibiti ya ɗauka domin sanar dasu Jafar ya cika alƙawarin daya ɗauka.
Yana isa Kaka na isowa da gudu ta shige ɗakin tana mararin ganin tilon jikanta.
"Labson ɗina, wayyo jikana sannu , haka ka koma duk kafita hayyacinka."?
Ta ƙarashe maganar batare da tasanin ko sunan Rabson ɗin bata faɗa dai_dai ba.
Hannuwanta ya kama ya riƙe gam Tamkar za'a ƙwace mashi ita.
"Da farko dai kaka yanzu Rabi'u nike ba Rabson ba, kaka ki yafeni dan girman Allah, bazani ƙarayimaki gardama ba, nabi Allah nabiki Kakata."
"Tuni nayafe maka Rabi'u na, kullum banida gurin daya wuce Allah ya maidomani kai marayan Allah."
Shigowar iyayensu Kulu yasa kaka yin shiru.
Su Kulu kam sunsha bala'i da masifa wurin iyayensu, dan Nas Mamanshi cewa tayi saita kwara kanshi da bango zata huce, Momyn Jamcy kuwa yi tayi kamar zata jawota daga gadon ta karya mata ƙafar da ta yi alƙawari.
Alhaji Abdallah mamakin halin iyayensu Jamcy ya bashi mashi mamaki, haƙuri ya rinƙa basu akan suyima Allah godiya da bayyanar ƴa'ƴansu basu hau bala'i da masifa ba.
Jikinsu sanyi yayi sukayi tsit.
Umman Biba ce da ƙanwarta suka iso.
Har kukan murna saida Mahaifiyar Biba tayi tare dayima Allah godiya.
Biba kuwa tsabar farin ciki jitake kamar ta koma cikin mahaifiyarta ta kama ta ta riƙe gam.
Sallamar maman Jafar ce ta sanya kowa kallon ƙofar.
Zabura Alhaji Abdallah yayi ya miƙe tare da nuna Maman Jafar ya furta Hindatu!.
Maman Jafar itama kallonshi take da mamaki ta furta Abdallah.........
Juwar dayaji tana ɗibarshi ce tasashi yayi saurin zamewa ƙasa tare dayin zaman ƴan bori.
Hindu kuwa wasu hawaye ne taji sun wanke mata fuska, wai yau i ta ce take ganin Abdallah, anya kuwa ba mafarki takeba.
Jafar ganin mahaifiyarshi yasa yayi yunƙurin tashi.
Ganin haka ummansu tayi saurin ƙarasowa wurinshi cike da farin ciki marar misaltuwa.
Alhaji Abdallah hawaayen fuskarshi ya sharce, ga wani gumi daya tsatstsafo mashi ta ko ina ajikinshi.
Kallon Jafar yayi yaƙara tabbatarwa tabbas yanzu yaƙara ganin kamarsu da husaininshi.
Abdallah tashi yayi ya isa gabansu Hindatu tare da zaunawa amma bakinshi ya kasa furta koda kalma ɗayace.
"Umma! Dama kinsan Mahaifin Salma?, koɗan uwankune."?
Ya ƙarashe maganar ya mai ƙara fuskantar Mahaifiyarshi.
"Ɗana ne kai, Jafar tunda na haɗa ido dakai jikina yabani kai ɗin jinina ne, Jafar Ashe kaine ɗan, ɗan uwana Husaini daya bata, babu inda ban bancika ba domin ganin nasamuko amma abin yaci tura ban gankuba."
Alhaji Abdallah ya ƙarasa magana muryarshi a matuƙar karye.
Hawayen dake fuskarta ta share ta ɗora da faɗar.
"Tun bayan rasuwar iyayenku, Husaini yashiga wani mawuyacin hali, saiya zaunar dani yayita yimani wasu maganganu masu kama da wasiyya, ana cikin haka Allah ya nufeshi da 6acewa inda haryau bamu ganshiba."
Kukan da taji yana naiman ƙwace matane yasata yin shiru.
"Mahaifanmu mu biyu suka haifa taƙwaye, muntashi muna matuƙar ƙaunar junanmu, har mahaifanmu suka rasu lokacinne kuma Husaini ya bata, na nemeku lungu da saƙo amma ko labarinku bansamuba, kullum cikin yima iyayenmu addu'a nike da Husaini har izuwa yau da Allah Ya bayyana mani ku."
Jafar ji yayi anya ba mafarki yake ba, ace wai yau shine gashi ga yayan mahaifinshi, Allah mai yadda yaso, yana ƙara roƙon Allah ya bayyana mahaifinshi aduk halinda yake ciki.
Salma wata gagarumar kunyace ta ƙara rufeta, wai yau ace wanda ta gama wulaƙantawa ashe yayantane, yanzu ta ƙara tabbatarwa ɗan adam ba abin wulaƙantawa bane, wata sabuwar nadama taji tana ƙara shigarta.
Mahaifiyar Habib da Alhaji Abdallah gaisuwar yaushe gamo suka hauyi ciki da farin ciki da ƙaunar juna.
Sallamar Habib dasukaji ta maido hankalinsu ga ƙofar.
Basma tunda taga Habib wani farin cikin marar misaltuwa ya ziyarci zuciyarta, ashe tanada rabon ganin mijinta farincikinta, tana ƙara miƙa godiyarta ga Allah.
Bayabo ba fallasa bayan gaisawarsu da ƴan ɗakin ya dubi Basma yana mata ya jiki.
Ba ƙaramin mamakin Habib Basma tayiba, ya matuƙar chanza mata sai wani shareta yake ga wani haske da yayi da wata ƙiba da yayi abinshi.
Haƙuri ta hau bashi tana kuka ya yafe mata tayi nadama, ko kallonta baiyi ba ya furta naji kanshi na sunkiye yana kallon screen ɗin wayarshi.
Tamkar Alhaji Abdallah zai