Showing 18001 words to 21000 words out of 28291 words

Chapter 7 - BAƘAR TAFIYA BY MEENART A YANDOMA.txt

13 Dec 2024

1428

ta ƙwala ce ta dawo dasu cikin hankalinsu, Mandiya suka gani ta kasama Basma haƙora awuya jini yafara malala, wata wahalallar ƙara Basma ta Ƙwala......................


______________________________
Gudun ceton rai su Rabson suke tamkar zasu tashi sama ga waɗannan halittu Dasun Juya sai suka sun kusa cimmasu.




Abinda basu saniba halittun nan kamar fara haka suke Tashi sama.


Basu ankaraba sai gani sukayi halittun nan sun dira gabansu, ja sukayi suka tsaya kafin su ankara halittunnan sun lullu6esu tamkar yadda fara ke lullu6e ganye.


Biba gani tayi halittun nan da ƙarfi taɗaga murya tana ƙwararo addu'a tana kai masu naushi da hannuwanta, duk wadda ta kaima bugu saida kaga tafaɗi ƙasa ƙasusuwanta sun karairaye.


Rabson dayaga biyu sunyo kanshi gudu yafara kafin ya ankara sun wawuro ƙafafunshi, ganin sun buɗe baki sunyo kanshi ya fara ihu yana karanto duk addu'ar da tazo bakinshi
"Innalillahi, la'ilaha illallahu, inna ansarnahu, amanarrasulu, wayyo kaka ɗan bunsurulle, wayyo Salma masoyiya ku kawo mani ɗauki."
Haka yaita ihu, ganin babu mai cetonshi yafara gano mutuwa ido buɗe yasa ya dage iyakar ƙarfinshi yana kaima halittun harbi da ƙafafunshi.


Kulu da Nas wuri ɗaya suka haɗe Nas ganin halittun sun nufoshi Ya koma bayan Kulu yana.
"Kulu ki taimaka mani wayyoh Allah innalillahi nashiga ukku, Kulu kin cuceni da kikasa mukayi wannan Baƙar tafiyar."
Yaƙarashe maganar yana ƙara shigewa jikon Kulu.


Ganin addu'ar da Biba tayi Allah ya kawo mata mafita, ta ɗaga murya tana mai umarta su Rabso dasuyi koyi da ita.


Sunjigatu sun matuƙar jin jiki kafin suyi nasarar gamawa da halittun.


Fuskar kowa tasha karta duk sawune jiki in banda Biba.


Bayan sun sun dawo cikin hankalinsu Rabson yayi ƙarfin halin miƙewa.
"Kun lura kuwa har yanzu muna cikin kogon nan? Kamata yayi mubar kogon nan nidai bazan tsaya in mutu a banza ba."
Ya ida maganar yana dudduba inda Salma ta shige.




Chan ya hangota ta tayi ɗai ɗaya a ƙasa tana maida numfashi.
"Hhh, Salma masoyiya kece kika zama haka?, kinga yadda kikayi buɗu_buɗu, wayyo masoyiya miya karceki a fuska taimaka kitashi muƙarasa fita."
Ya ƙarashe maganar yana yimata dariyar mugunta.


"Allah ya isa inka ƙara kirana Masoyiyarka, mugu mai suffar mutanen 6oye."
Taƙarashe maganar tana ƙoƙarin miƙewa.


Baikulata ba dariyarshi yacigaba dayi.


Kulu kallon Nas tayi tare da jan dogon tsoki.
"An daiji kunya, kabani mamaki lusarin banza kawai wanda mace ma tafishi jarunta."
Ta kuma jan wani tsokin.


"Am..uhm..kingane Kululu wallahi kawai kinsan ni ina tsoron ƙwarangwal, amma kin gane kibari a karo nagaba zani baki mamaki, haba my sweet Kululunah."
Ya ƙarashe maganar da daɗin baki.






"Allah dai yasa da gaske kake."
Tafaɗa tana yamutsa fuska domin yau Nas ya matuƙar bata haushi.


Sun yi yawo cikin kogon harsun gaji basu samu hanya ba.






Har sun haƙura da fita daga kogon sai suka hango wata ƴar hanya ƙarama wadda mutum ɗaya zai iyabi ya wuce, haka suka riƙa fita da ɗai ɗaya.






Ganin sun fita kogon wani irin farin ciki ya baibaye zuciyoyinsu.




Abinda idanuwansu suka hango masu ne yasasu ja da baya cikin matsanancin tashin hankali da kuma tsoro...........






















*COMMENT*✅
*SHARE*✅




























*MEEN@RT...✍🏻*
08133562798
[10/11, 10:29 PM] Meen@t A Yandoma: 💀 *BAƘAR TAFIYA* 💀


( *HORROR STORY* )


*BY MEEN@T A YANDOMA*
*MARUBUCIYAR FATALWA*


🌍 *MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION*🌍🖊️




*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


*SALONSHI NA DABAN NE 💃🏼*




*ALLAH KAJIƘAN MAHAIFINA DA DUKKN MUSULMI BAKI ƊAYA KASA YA HUTA, KA KAI RAHAMA A KABARINSHI, ALLAH KA GAFARTA MASHI ZUNUBBANSHI, ALLAH YAJI ƘANKA ABBANA*




*MASOYA INA MATUƘAR GODIYA DA SOYAYYAR DA KUKE NUNAMA LITTAFIN NAN, ALLAH YA BARMU TARE, INA MATUƘAR GODE MAKU MASOYA A DUK INDA KUKE*


🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️
*ƳAN BAƘAR TAFIYA FANS COMMENT ƊINKU YANA MATUƘAR TAFIYA DANI KUNA SANI NISHAƊI DA COMMENT ƊINKU ALLAH YA BARMU TARE,MASOYA INA GODIYA*




*ALLAH YA BIYAKU MY PEOPLE, ALKHAIRIN ALLAH YA KAI MAKU HAR GADON BACCINKU, ƳAN BAƘAR TAFIYA FANS, KUNA SANI FARIN CIKI DA ADDU'O'INKU, ALLAH YA ƘARA DANƘON ZUMINCHI, KUMA BAZANI MANTA DAKUBA SAURAN MASOYA INA MATUƘAR GODIYA DA SOYAYYAR DA KUKE NUNAMA WANNAN NOVEL ƊIN ALLAH YA BARMANIKU MASOYA INA ALFAHARI DAKU.* 🤗🤗🥰


______________________________
*PAGE 26_27*


..............Ahankali iskar da ta kwasosu ta fara lafawa.


Tare da 6acewa 6at! Tamkar bata ta6a wanzuwa ba.




Hannu Jafarne ya fara motsi, idanunshi suna ƙoƙarin budewa, samun kanshi yayi da furta, "
_ALHAMDULILLAHILLAZI AHYANA BA'ADA MA AMATANA, WA ILAIHINNUSHUR_"


Kanshi daya ji yana barazanar tarwatsewa ya dafe yana Ambaton " _INNALILLAHI WA'INNAH ILAIHI RAJIUN, ALLAHUMMA AJIRNI FIYMUSIBATI WA'AKLIFINI KHAIRAN MINHA_ Ya ubangiji ka kawo mana ɗauki akafitar damu daga wannan musiba."


Dubanshi yakai inda su Basma ke kwance basu san mike faruwaba.


Abinda idanuwanshi suka hasko mashi ya sanyashi idan miƙewa daga kwanciyar da yake yayi saurin zaunawa, hannuwanshi yakai kusa da idanunshi ya murza idanun yaga kodai gizone suke mashi.


Ƙara tabbatar wa yayi ta hanyar tsinkulin kanshi yaji kodai mafarki yake, da gaskene su Rabson ne ba gizo idanuwanshi keyi mashi ba.




Wani farin ciki marar misaltuwa ya wanzu azuciyarshi baisan lokacinda ya kalli alƙibla yayi sujadar godiya ga Allah daya bayyanar masu da abokan tafiyarsu.


Motsin dayaji ne ya sanyashi saurin juyawa.




Su Basma, Jamcy da Tk ne yaga sun farka lokaci ɗaya suna dafe kansu dake masu tsananin ciwo.




Rabson ne yafara harba ƙafarshi saman wuyan Salma, ita ma motsi ta fara alamun zata farka Kulu da Nas suma farkawa sukayi.




Rabson waige_waige yafara kamar yana naiman wani abu, su Jafar daya hango yasashi fara ja da baya yana salallami.
" _INNAHUMIN SULAIMANU, LA'ILAHA ILLALLAHU_, ku kuke ganinmu bamu muke ganinkuba,wayyo namutu na lalace, shikenan gasunan sunzo mana da suffar abokan tafiyarmu, wayyoh Salma masoyiya kina ina."?
Ya ƙarashe maganar yana janƙugu yana baya_baya.


"Hhh! Kai Rabi'u Rabson ɗin Kaka, munefa da gaske ba horror bane."
Jafar ya ida maganar yana dariya.




"Mtssw! Sauna kawai, kabi ka cika ma mutane kunne ko ina kaga horrorn."?
Salma ta faɗa tana hararar Rabson.


Wiƙi_wiƙi Jafar yayi yana rarraba ido.


Gaisawa sukayi ta yaushe rabo, bayan sun gama shan hira da taya juna jimamin rashin fitarsu wannan baƙin daji.


Shawara suka yanke ta yanzu bazasu ƙara tafiyaba gudu zasuci gaba dayi sallah da abinci kaɗai zai tsaidasu.




Matsawa sukayi wurin wani iccen gwaba suka tsinka, Jafar ne yafara rarrabama masu.


Salma gani tayi Jafar bai kawo kantaba, miƙewa tayi a fusace ta bangaje Jafar gwabar ta 6are ƙasa, taga_taga Jafar yayi zai faɗi ya tsaya, wani icce ya kama ya riƙe yana mamakin halin irin na Salma.




Salma gwaibar ta hau tsinta tana tattarawa, tatss! Kake ji Biba ta ɗauke Salma da wani irin gigitaccen mari.




"Tabbas rashin tarbiyya da rashin sanin darajar ɗan adam babban ciwo ne, ke yanzu in banda bakida wayo wanda yakasance shine jigon tafiyarmu shikike bangajewa?, ke kowa baki ɗaukarshi da mutumci kin raina kowa, sakara wadda batasan indake mata ciwo ba."


Zafin marin da Biba taima Salma ya sanya ta zunduma mata duk wani irin zagin dayazo bakinta tana faɗar in suka koma gida saitasa anɗaure Jafar da Biba.




Haukan da Rabson yaga Salma nayi yasanyashi fashewa da dariya tareda tashi ya kamo hannunta.
"Haba Sweet Salma ta Rabson na Kaka da Busurulle!, miye nasa ke bakida hankali da kuma wayo, ya kamata fa kisan yanzu tare kike da mijinki, kisan abinda zaki faɗama mutane kowa da kika gani yanada rana fa."
Ya ida maganar yana dariya.




"Ba'a sani, inka ƙara kirana da matarka saina samu dutse na rotsa maka kai dashi, mtssw aikin banza kawai."
Ta ƙarashe maganar tanajan dogon tsoki.


Kowa banza yayi da ita suka haushan gwaibar su.


Biba dasun haɗa ido da Jafar saisu sakarma juna zazzafan murmushi ta sadda kai ƙasa.




"Abokai kamar yadda na faɗa maku yanzu bazamu sake tafiyaba, gudu kawai zamu riƙayi daga sallah sai cin abinci zamu riƙa tsayawa."




Oga Rabson wandonshi inna tayani cirewa ya nannaɗe suka fara gudu ba kama hannun yaro.




Gudu suke irin gudun da ake kira gudun yada ƙanin wani, yunwar cikinsu ita ta tsaida gudun da suke, tsayawa sukai suna maida numfashi.


"Wayyoh Momy, Daddy ina bataliyar sojojin da nike mafarkin ka turo afiddani adajin nan."?


"Hhh! Shegiya ƙarya, ko gidan wane baban ne zakiga wata bataliyar sojoji, nabi bataliya da gudu, bataliyo."
Ya tuntsure da dariya.




Jikin Basma a hankali yake komawa green da baƙi tana canza kala.


Nan suka tsaya suna hutawa.


Motsi sukaji alamun tafiyar mutane Nufo inda suke.


Zumbur suka miƙe tare da cibrewa wuri ɗaya suna jiran bayyanar abinda ke tunkarosu.




Abinda majigin idanuwansu suka hasko masu yasa su ƙara dunƙulewa wuri ɗaya.




Garba kisa, Nura shila, Audu gwarama da Mandiyane suka nufosu da wasu irin wuƙaƙe a hannunsu.




Cikin Salma wani irin sauti yabada ƙuu.




Ganin wannan bala'i yasanya su Jafar da Biba fara ƙwararo addu'a.




Wani wawan tsalle sukayi tare da rabuwa suka yimasu Rabson ƙawanya.


Harshe suka riƙa fiddowa tare dayin wata kuwwa marar daɗin saurare.




Tuni Rabson ya maƙalƙale jikin Jafar ya fara kuka yana sabbatu.
Tsawar da Jafar ya Ƙwatsama Rabson ya ɗora da faɗar;
"Yanzu lokacin yaƙine domin a ceci rayuwa, tabbas yanzu lokacine da kowa zaiyi takanshi kuma zaiyi ƙoƙarin ceton rayuwarshi domin in Allah ya ƙaddara musamu ko mutum ɗayane ya kai labari."


Bashakka jin wannan maganar jikinsu yayi sanyi sun sadaƙar zasuyi faɗa su mutu ko suyi rai.




Garba Jafar ya warto da nufin ya luma mashi wuƙar hannunshi, kokawa suka hauyi da Jafar bakinshi ɗauke da addu'a.




Nura Rabson ya jawo, Rabson naganin haka ya jawo ƙafar Salma suka tai tare.


Rabson baisan yanada ƙarfi ba sai yau dayaga mutuwa tsirara, yaga ya dage yana kaima Nura naushi ta kowane 6angare.


Kulu da Nas tare Audu ya fizgosu, Kulu itace mai ƙoƙarin ceton rayuwarta tasa ƙafa tana kaima Audu duka ta ko ina.




Su Jamcy da Tk su biyun sun bada himma suna zabga kabbara suna ƙoƙarin ceton rayuwarsu.




Bashakka wannan yaƙin na ceton rayuwa yazo da abun mamaki, domin duk da su Garba sunjima kowa ciwo da makaman hannunsu amma haka suka dage.




Wata ƙaƙƙarfar guguwa dasu Rabson sukaji ita ta sanyasu zubewa ƙasa, mahaukaciyar ƙara Rabson ya ƙwala ya dafe hannunshi da Garba yayi sanadiyyar gutulema Rabson ƙaramin yatsan hannunshi.
"Nashiga ukku sun maidani gundul sun guntule mani yatsa, wayyoh Kaka wayyo Salma masoyiya, Wayyoh ni Rabi'u nakoma Rabson gundul na busurulle."




Wannan guguwar ta kwashe su Garba kisa tayi sama dasu.......












*COMMENT*✅
*SHARE* ✅














































*_MEEN@RT...✍🏻_*
08133562798
[10/11, 10:29 PM] Meen@t A Yandoma: 💀 *BAƘAR TAFIYA* 💀


( *HORROR STORY* )


*BY MEEN@T A YANDOMA*
*MARUBUCIYAR FATALWA*


🌍 *MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION*🌍🖊️




*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


*SALONSHI NA DABAN NE 💃🏼*




*ALLAH KAJIƘAN MAHAIFINA DA DUKKN MUSULMI BAKI ƊAYA KASA YA HUTA, KA KAI RAHAMA A KABARINSHI, ALLAH KA GAFARTA MASHI ZUNUBBANSHI, ALLAH YAJI ƘANKA ABBANA*




*MASOYA INA MATUƘAR GODIYA DA SOYAYYAR DA KUKE NUNAMA LITTAFIN NAN, ALLAH YA BARMU TARE, INA MATUƘAR GODE MAKU MASOYA A DUK INDA KUKE*


🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️
*ƳAN BAƘAR TAFIYA FANS COMMENT ƊINKU YANA MATUƘAR TAFIYA DANI KUNA SANI NISHAƊI DA COMMENT ƊINKU ALLAH YA BARMU TARE,MASOYA INA GODIYA*




*ALLAH YA BIYAKU MY PEOPLE, ALKHAIRIN ALLAH YA KAI MAKU HAR GADON BACCINKU, ƳAN BAƘAR TAFIYA FANS, KUNA SANI FARIN CIKI DA ADDU'O'INKU, ALLAH YA ƘARA DANƘON ZUMINCHI, KUMA BAZANI MANTA DAKUBA SAURAN MASOYA INA MATUƘAR GODIYA DA SOYAYYAR DA KUKE NUNAMA WANNAN NOVEL ƊIN ALLAH YA BARMANIKU MASOYA INA ALFAHARI DAKU.* 🤗🤗
_____________________
*PAGE 28_29*


................Kuka take tamkar ranta zai fita, ga wani gumi daya wanke mata fuska duk sanyin da ke gauraye ɗakin.


"Wallahi ko ki fiddoman ɗiyata ko kuma kiyi ta bakin aurenki, kinji na faɗa maki, ace yau tsawon wata hudu kenan kinturata biki ashe bama bikin danginku bane can biƙin ƙawar dana hanata zuwane, tsabar kin ɗaukeni banda mutumci a wurinki shine kikayi mani ƙarya,to kinji na rantse maki indai ɗiyara ta ƙara kwana goma bata dawoba kema saidai kitafi gidanku."Alhaji Abdallah
Ya ƙarashe maganar yayi waje ranshi a matuƙar 6ace.


Cikin muryar daga jinta kasan tasha kuka harta gaji, ga idanunta da suka kumbura saboda kukan da ta sha ta fara magana;
"Yau ni Zaliha nashiga ukku, watan tonen asirina ya kama, nibama sakin da Alhaji zai mani ke damuna ba face muggan mafarkan danike da Salma, ya Allah nagane kuskurena Allah ka maido mani ɗiyata gida lafiya."
Kukan dayaci ƙarfinta ne yayi sanadin haɗiye sauran maganar.


_________________________
"Habib wai bazaka cire damuwar yarinyar nan aranka bako?, yau wata huɗu da tafiyar ba ba bamo ba labari ga Ɗanka kanata fama dashi,sai wani ciwo ya sameka ita batama san kanayiba tana can wurin biki, to munyanke shawara da kawunka ga Hanan nan da aurenta ya mutu ƴar ƙanwata, yarinya mai hankali da natsuwa, gata yarinyace ko haihuwar fari batayiba,tunda ta gama idda ranar Juma'ar nan za'a ɗaura maku aure ranar zata tare tunda komi nata yana nan, Allah yasa wannan za6in danayi maka yazame maka Alkhairi arayuwarka."


Tunda ta fara maganar kanshike sunkuye aƙasa cikin girmamawa da yin na'am da za6in da Hajiyarsu tayi mashi yace;


"Amin Hajiya, insha Allah nimai biyayyane a gareki, bazakiyi kuka daniba."


"Nagode Habib, Allah yayi maka albarka, Allah ya shirya maka zuri'a."


"Amin Hajiya."


Yaune jama'a da dama suka shaida ɗaurin auren HABIB BELLO da amaryarshi HANAN HANIF, ɗaurin aurene daya samu halattar manyan ƴan kasuwa da ma'aikatan gamnati harma da ƴan siyasa ta 6angaren abokan Alhaji Bello mahaifin habib da kuma shi kanshi Habib ɗin.


Ƙarfe huɗu dai_dai aka ɗauki amarya zuwa gidan mijinta.


Zama suke irin wanda inka gani saiya birgeka, Hanan wayayyar yarinyace mai ilimin addini dana boko, shiyasa bata sha wahalaba ta sace zuciyar Habib tasamu babban gurbi azuciyarshi ta zauna daram, ga Walid da take kula dashi ta maidashi tamkar ɗan da tahaifa acikinta, shiyasa Habib ke ƙara ƙaunarta.


Allah sarki Habib duk auren dayayi bai manta da Basma ba, kullum cikin yimata addu'a yake, saboda muggan mafarkar da ye da ita, yana mata fatan tadawo dumin har yanzu akwai ƴar sauran soyayyarta kaɗan azuciyarshi.


(🤣😂 Basma ana can cikin daji ana gantalewa, Habib yayi sabon aure yana nan ysna soyewa, kina can kina shirin zama horror.)


___________________________________
Uban tagumin da ta yi hannu bibbiyu ta lula duniyar tunanin Rabi'un ta jikanta ɗaya ƙwali daya rage mata, da yau har tsawon wata Huɗu bai dawoba shiru kamar Malam yaci shirwa, abinda yafi ɗaga mata hankali shine munanan mafarkan datake tana ganinshi cikin mawuyacin hali.


Kukan da Busurulle ya fasa da ƙarfine ya dawo da ita daga duniyar tunanin data lula.


"Kai nikam nagaji dakai wannan bunsuru, ga abincinka yau ya ida ƙarewa, yanzu nike tashi in kai ka wurin tsalha sarkin fawa in saida in raba ƙuɗin biyu in sawo kyan abinci sauran kuma in ajema ɗan kaka inyadawo."
Ta miƙe ta zari mayafi ta kwance bunsuru tajashi tayi waje.


Tsalha sayen wulaƙanci yayima bunsurun, wai yunwa ta kamashi ya saya dubu ukku.


"Kai tsalha kaji tsoron Allah, wannan Bunsurun alalace ai zaiyi dubu goma."
Ta ƙarashe maganar tana kamo iggiyar ƙafar Bunsurun.


"Iyakar yadda na saya kenan hajiya, nifa bama zani sayi Bunsurun nan ba, saboda jikanki ko kin saidashi inya dawo nasan nizaima wulaƙanci in biyashi."


"Kai arr! Shiyasa kai mashi tayin wulaƙanci?, to nima nafasa saidawa."
Taja Busurulle ta mai da gida ta ɗaure tana mai addu'ar Allah ya mai do mata Rabi'unta gida lafiya.
__________________________
"Umma wai yaushe Aunty Biba zata dawo."?
Ƙanwar Biba ta jefoma Ummansu tambayar.


Tagumin da ta zuba da hannu biyu ta cire tana mai kallon Siyama.
"Siyama ku taya Habiba da addu'a, insha Allah jikina yana bani tabbas Habiba nacikin mawuyacin hali, duba ga muggan Mafarkan da nike da ita, insha Allah darajar addu'ar danike mata zata dawo gidannan."


"Umma ki kwantar da hankalinki insha Allah aunty zata dawo ta samemu cikin ƙoshin lafiya."


"Amin siyama, Allah ya maidota lafiya."


Alwallah sukayi tareda kabbara sallah suna masu kai ma Allah kukansu, domin Allah gafurun rahimunne.


________________________________________
Giɗan yayi tsit, Umma da Hanifa kowa da abinda yake saƙawa cikin zuciyarshi.


"Ni ko Umma ƙwanan nan sai inta ganin Yaya Jafar cikin mawuyacin hali cikin wani baƙin jeji."


Jin wannan maganar ya sanya jikinta ya ƙarayin sanyi, cikin ƙarfin hali da nuna mafarki ba duka ne gaskiyaba ta fara kwantarma Hanifa da hankali.


"Marfarki ba duka ne gaskiya ba kinji Hanifa, Yayanki yana nan dawowa kiriƙa yimashi addu'a inkinyi sallah , yana nan dawowa insha Allah."




"To Umma Allah ya maidoshi lafiya, amma Umma mike danmunki kwanan nan sai inta ganinki cikin damuwa."?




Duk yadda take ƙoƙarin 6oye damuwarta amma tasan fuskarta ke fallasa sirrin zuciyarta har agano halinda take ciki game da mafarkan da take da Jafar.
"Lafiyata lau Hanifa, wani lokaci ina fama da zazza6i shiyasa kike gani na haka, amma nasha magani, yanzu tashi kiyi shirin islamiyya lokaci yayi kadaki makara."


"To Ummu."
Ta miƙe tahau shirin tafiya makaranta.




Wasu guntayen hawaye Ummu ta sharce tare da addu'ar Allah ya maido mata ɗanta gida lafiya.
____________________________________
Zaune suke Saman kujerun Alfarmar da suka zagaye tsakiyar falon.


Kallo ɗaya zakayi masu kasan hutu ya zauna ajikinsu.


Hajiya kubra momyn jamcy dogon tsoki taja tare da kaɗa kanta ta fara magana cikin takaici;
"Wato idan Jamcy ta dawo gidannan ta iskeni saina karya mata ƙafar gaba data baya, shegun ƙafafu kamar na Zal6e, yau wata Huɗe kenan sun faki idanunmu sun tafi ganin ƙwam."


Hajiya Hafsa mahaifiyar Kulu ita ta amshe zance;
"Ke kike faɗi anaji, wato ni idan Kulu ta dawo innayi mata Wata zauna sai ƙasusuwanta sunkarairaye, kaga yarinya ta sani cikin masifa mahaifinta gani yake kamar nice na sanyata ta tafi Baƙin dajin nan ganin ƙwam."


"Ai ni narasa yadda zaniyi da Daddyn Nas, kullum cikin tada mani hankali yake yana tunanin dasa hannunna nasani Nas yabar gida, ai yadda Nas ya tada mani hankali in Allah ya maidoshi saina gwara kanshi da bango ko naji sauƙin abinda nikeji azuciyata."
Hajiya asabe Mahafiyar Nas ta ƙarashe maganar tana huci.




"Ai ni dangin Mahaifin Tk gani suke kamar dan Mahaifinshi ya rasu shiyasa nabarshi sakaka harya tafi dajin nan, wallahi sun sakoni gaba niduk nafiku shiga matsala."


Ranar haka suka wuni suna jimamin halinda ƴa'ƴansu suka jefasu ciki, yamma nayi kowacce ta nufi gidanta cike da jimamin halinda suke ciki.


_____________________________________
Ihu Rabson keyi iyakar ƙarfinshi ga hannunshi nata zubar da jini.


Ganin halinda yake ciki yasa Jafar rugowa yana duba yatsan, ashe duk ihun da yake yatsan yankarshi kawai akayi ba gundulewa yayi ba.


Tsoki Jafar yayi ganin asheba datse yatsan akayiba tsabar rikicewa sai cewa yake yatsanshi ya gundule.


"Kanatsu Rabson, yatsanka ba gundulewa yayi ba yankarshi akayi."




Ihun da yake ya tsaida;
"Da gaske kake Jafar yatsana nan."?
Ya jefoma Jafar tambayar yana mai kallonshi.




"Eh yana nan."
Ya faɗa a taƙaice.


"Alhamdulillah, Allah nagode maka ashe banida rabon zama Rabson gundul, Allah na godemaka."




Biba kallabinta ta kwace ta yaga aka ɗaurema Rabson Hannu.


Zaune sukayi sunyi jigum_jigum ga yunwa ga ƙishirwa da suka addabesu.


6angare ɗaya kuma ga jikin Basma nata ƙara rikiɗewa.


"ALHAMDULILLAH."
Jafar ya furta fuskarshi ɗauke da murmushi.


Kallinshi sukayi cikeda son jin abinda ke faruwa suka furta, "Jafar miya faru."?








*COMMENT*✅
*SHARE*✅
















*MEEN@RT...✍🏻*
08133562798
[10/11, 10:29 PM] Meen@t A Yandoma: 💀 *BAƘAR TAFIYA* 💀


( *HORROR STORY* )


*BY MEEN@T A YANDOMA*
*MARUBUCIYAR FATALWA*


🌍 *MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION*🌍🖊️




*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


*SALONSHI NA DABAN NE 💃🏼*




*ALLAH KAJIƘAN MAHAIFINA DA DUKKN MUSULMI BAKI ƊAYA KASA YA HUTA, KA KAI RAHAMA A KABARINSHI, ALLAH

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login