Showing 21001 words to 24000 words out of 28291 words
KA GAFARTA MASHI ZUNUBBANSHI, ALLAH YAJI ƘANKA ABBANA*
*MASOYA INA MATUƘAR GODIYA DA SOYAYYAR DA KUKE NUNAMA LITTAFIN NAN, ALLAH YA BARMU TARE, INA MATUƘAR GODE MAKU MASOYA A DUK INDA KUKE*
🤸🏻♀️🤸🏻♀️🤸🏻♀️
*ƳAN BAƘAR TAFIYA FANS COMMENT ƊINKU YANA MATUƘAR TAFIYA DANI KUNA SANI NISHAƊI DA COMMENT ƊINKU ALLAH YA BARMU TARE,MASOYA INA GODIYA*
*ALLAH YA BIYAKU MY PEOPLE, ALKHAIRIN ALLAH YA KAI MAKU HAR GADON BACCINKU, ƳAN BAƘAR TAFIYA FANS, KUNA SANI FARIN CIKI DA ADDU'O'INKU, ALLAH YA ƘARA DANƘON ZUMINCHI, KUMA BAZANI MANTA DAKUBA SAURAN MASOYA INA MATUƘAR GODIYA DA SOYAYYAR DA KUKE NUNAMA WANNAN NOVEL ƊIN ALLAH YA BARMANIKU MASOYA INA ALFAHARI DAKU.* 🤗🤗
____________________________
*PAGE 30_31*
........... "insha Allahu matsalarmu tazo ƙarshe da izinin Allah." Jafar ya faɗa yana fuskantarsu Rabson.
Cikin zaƙuwa suka fara tambayarshi ta yaya matsalarsu tazo ƙarshe?.
"Haƙiƙa Alƙur'ani cikinshi akwai waraka, ubangiji ya sanya na tuno da wani malami na daya koyar damu yadda ake karya sihiri da wasu daga cikin ayoyin Alƙur'ani mai girma, domin wannan annobar ta zama Horror da wasun mu suka yi sihirine, kuma da izinin Allah zamu karyashi, dan haka yanzu wasu daga cikinmu zasu tafi naiman ganyen magarya wasu kuma su tafi naiman ruwan da zamuyi amfani dashi, dan haka yanzu Rabson da Salma ku zaku naimo mana ganyan magarya guda bakwai."
Rabson wata irin miƙewa yayi jin ance su biyu zasu tafi.
"Kwarankwatsi dubu babu inda zani, yoce maku akayi Kakata bata sona zaku turamu mu biyu aradu babu inda zani, haka kawai so kuke inje acinyeni shikenan Bunsurulle ya zama maraya."
Ya ƙarashe maganar yana zare idanu kamar ankama 6era a buta.
"Kai dai kam anyi ragon maza lusari marar amfani, to nida Tk zamu tafi tare daku munzama muhuɗu ko."
Jamcy ta ƙarashe maganar tana hararar Rabson.
"To masha Allahu, yanzu cikinku wayasan yadda ganyar magaryar yake."?
Jafar ya jefo masu tambayar yana mai ƙare masu kallo.
"Ni nasani saboda nata6ayin projet akanshi."
Tk ya faɗa yana hura hanci.
"Ku tabbata kunyi addu'a kafin kubar wurin nan."
Jafar ya faɗa cikin taushin murya.
Su duka kowa yayi addu'a musamman Rabson a bayyane ya ƙwararo abunshi, Salma ko bata ce uffan ba tana hura hanci tana taka ƙasa da ƙyar haka suka nausa cikin jejin naimo ganyan magarya.
Sunyi tafiya harsun gaji amma basu samu koda itaciyar da zusu tsuguna susha inuwa ba bare kuma ta ganyen magarya.
"Wash!."
Rabson yafada yana riƙe ƙugu kamar zaiyi kuka.
"Ka taka ƙafa muyi gaba yanzu ba lokacin lalaci bane, in kuma kasake muyi gaba mubarka."
Salma ta ƙarashe maganar tana aikama Rabson kallon banza.
Murmushi Rabson yayi, "to masoyiya Matar Rabson mu tafi."
Daddagewa tayi ta danna mashi wata gagarumar ashar taɗora da faɗar
"In ka sake kirana matar ka tsaf zani biyemaka mu dambata a wurin nan, maye sai naci saikace talauci Mtssw."
Fashewa da dariya yayi "in kina tunkuɗo bakin nan sai yayi yanayi da in tsohuwa zata kira tukurr."
Ya ƙarashe maganar yana kwaikwayar ta.
"Kutt! Amma gayen nan nikake zagi ka kira sunana kana iya shege, yanzu ko zani tumurmusaka ka gane shayi ruwa ne."
Tk yayo kan Rabson gadan_gadan.
Ruƙoshi Jamcy tayi cikin matuƙar 6acin rai ta fara magana;
"Yanzu naiman abinda muka fito kenan?, kun rinca6e da faɗa, so kuke ayita yimana dauki ɗai_ɗai saboda mugun hali irin namu muntsaya faɗa amaimakon naimo abinda aka aikemu naimowa."
Kowa tsit yayi suka ƙara gaba naiman abunda suka fito.
Sun ƙara tafiya mai nisan gaske sannan suka iso inda ya kasance ga ganyayen magarya birjik aƙasa.
Hamdala sukayi wani irin farinciki ya ziyarci zuciyoyinsu.
Tsugunawa Tk yayi ya tsinci guda bakwai.
Yajuyo yace masu suyi gaba su koma wurinsu Jafar kawai.
Ihun da Salma ta ƙalla ne yayi sanadiyyar janyo hankalinsu, abinda suka gani ne yayi sanadiyyar daskarewarsu suka kasa koda ƙwaƙwƙwaran motsi.
Mandiyace tsaye cikin mummunar kama, jikinta yayi kacha_kacha da jini, tazarar dake tsakaninsu da Salma batafi taku biyu ba tsakaninsu.
Kafin Salma ta ankara tuni Mandiya tayi wawan tsalle ta dira gabanta, wuyanta ta raruma sukayi ƙasa atare.
Zafi gami da azabar cizon da Mandiya tayima Salma a wuya yasanyata fasa wata mahaukaciyar kuwwa.
Wannan mummunan gani da Rabson yayi yasanya shi sakin wani zazzafan fitsari yana kuka yana kiran "Salma masoyiya shikenan bakida rabon ganin bunsurulle, naci gurin yanka maki shi in munyi aure muci amarci dashi."
Ganin surutan bazasu fishsheshi ba yasanya shi runtse ido ya ɗauki wani reshen iccen magarya daya karye ya faɗo.
Mandiya da ta riƙe da wuyan Salma jini nata tsiyaya.
Shammatar Mandiya yayi ya buga mata iccen a tsakiyar baya, sakin wuyan Salmatayi tare da fasa wata firgitacciyar kuwwa.
Ganin haka yasa Rabson fizgo hannun Salma data galabaita ga jini na ɗibarta, ganin haka yasa su Jamcy maramasu Rabson baya sukaci gaba da gudu.
Gudu suke na ceton rayuwa ga Rabson guy riƙe da hannun Salma.
Da ƙyar da ji6in goshi suka isa inda su Jafar suke, suna isa Salma ta zube ƙasa tana maida wahalallen numfashi kamar ranta zaifita.
Ganin irin jinin da Salma ke zubdawa yasa Biba cire kingin gutsuren ɗan ƙwalinta ta ɗaurema Salma wuyan.
Ganin taimakon da Biba tayima Salma ya sanya Salma jin wasu hawaye sun wanke mata fuska, yanzu gashi mutanen data gama wulaƙantawa hartana iƙirarin inta koma gida saitasa an ɗauresu, yau sune ke taimakonta, lallai duniya kabita sannu ba matabbata bace.
Jitayi wuyanta kamar ana hura mata wuta ansa wuƙa ana daddaka mata a wuya.
Jin wannan sabuwar azaba ya sanya ta fasa wata ƙata tareda faɗuwa ƙasa tana harbe_ harbe.
Sunyi matuƙar mamakin baƙon yanayin dake shirin samunsu, sudai iya saninsu sunsa ko harror yacijeka baka abinda Salma keyi.
Babban abinda ya ƙara tayar da hankalinsu bai wuce ganin cikin lokaci ƙanƙani jikin Salma yafara komawa green wasu jijiyoyi naƙara bayyana.
Ganin haka yasa Jafar umartar matan dasu danne mashi Salma, haka akayi suka danneta da ƙyar tana fizge_fizge ya fara yin auziyyah yayi basmala ya fasa karanto suratul baƙara cikin daddaɗar muryarshi.
Jitayi karatun da yake mata tamkar yana watsama wuta feturne tana ƙara ƙonata, ƙoƙarin fizgewa take ganin haka yasa Rabson riƙe hannuwanta gam.
Jafar bai tsaya da karatun ba face ƙara himma da yayi wurin rero karatun.
Lura sukayi Salma ta daina motsi, hankalinsu yayi mummunan tashi sun ɗauka mutuwa tayi, saida Jafar yace masu bacci ne ya ɗauƙeta sauƙi ne taji.
Fuskar kowa ka kalla wurin jimamin wannan al'amari yake.
Jafar ne yayi ƙarfin halin fara masu bayani kamar haka;
"Tabbas wannan al'amari sai mun tashi tsaye mundage da addu'a, lokacinda zaku tafi gudun faruwar haka saida nayi maku tuni da kuyi addu'a, inagani kowa yayi amma Salma taƙiyi, to kunga abinda ake gudu gashinan yadda ta kasance da ita, jikina nabani in bamu gaggauta naiman ruwaba mukayi mata addu'a da ganyen magaryar nan ba to bashakka bazata ɗauki lokaciba zata zama horror."
Sunyi na'am da wannan shawara sun jinkirta Salma ta tashi daga bacci su ƙara gaba su naimi ruwa.
Anɗauki lokaci sosai sannan Salma ta fara buɗe idanunta da take jin sunyi mata nauyi.
Tana ida buɗesu ta sauje su kan Rabson da tun lokacin da yaga ta fara motsi ya kafeta da ido.
Abinda Rabson yagani cikin idanun Salmane ya sanyashi miƙewa jikinshi na mazari.
Idanunta wannan baƙin na idonta ya rikiɗe ya koma green.
Ganin wannan al'amari Jafar ya umarcesu suyi azamar tashi su samo ruwa.
Salma kallon jikinta tayi da tufafin harsun fara yagewa, ga ƙasar da ta kwanta ƙasa duk ta ida bata jikinta ta koma kamar wata mahaukaciya, hawayen dake jerangiya afuskarta ta sharce, wai yau i ta ce ahaka, Salma da take ƴar gayu mai ƙwalisa bashakkayanzu ta koyi darasin yadda rayuwa take.
Nas da Kulu ganin yadda Salma ta koma yasa suka matsa daga inda take cike da tsoronta azuciyoyinsu.
Ganin su Nas sun matsa daga inda take ta sakejin wani sabon kuka ya kufce mata, wai yau i ta ce ake gudu, lallai rayuwa ba tabbas.
Biba ce take kwantar mata da hankali ta ɗauki Ƙaddara musulmi da ɗaukar ƙaddara mai kyau ko akasin haka aka sanshi.
Wata soyayyar Biba ce Salma taji ta ƙara shigarta da kuna nadamar abubuwanda ta aikata masu a baya.
Biba ita ta kama kannun Sallam ta ranƙwafo ta aza wuyanta bisa kafaɗar Biba sukaci gaba da tafiya.
Sunyi tafiya mai nisa sosai suka isa wani wuri da ruwa ke gudana ta cikin wani dutse.
Su duka nan suka zube suna masu kamfatar ruwan da hannayensu tare da bismala suna kaiwa bakunansu.
Basma jitayi wani jiri na ɗibarta, bashiri taji ta kaima Jafar karo tayi ƙasa tareda dafe kanta dake bara zanar tarwatsewa, ga jikinta da saura kaɗan ya ida komawa green..........
_ina matuƙar godiya da addu'o'inku ga Auntyna, Allah ya sauketa lafiya ta samu baby girl, godiya ta musamman masoya nagode da addu'o'inku_👏🏼❤️
*COMMENT*✅
*SHARE*✅
*MEEN@RT...✍🏻*
08133562798
[10/11, 10:29 PM] Meen@t A Yandoma: 💀 *BAƘAR TAFIYA* 💀
( *HORROR STORY* )
*BY MEEN@T A YANDOMA*
*MARUBUCIYAR FATALWA*
🌍 *MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION*🌍🖊️
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
*SALONSHI NA DABAN NE 💃🏼*
*ALLAH KAJIƘAN MAHAIFINA DA DUKKN MUSULMI BAKI ƊAYA KASA YA HUTA, KA KAI RAHAMA A KABARINSHI, ALLAH KA GAFARTA MASHI ZUNUBBANSHI, ALLAH YAJI ƘANKA ABBANA*
*MASOYA INA MATUƘAR GODIYA DA SOYAYYAR DA KUKE NUNAMA LITTAFIN NAN, ALLAH YA BARMU TARE, INA MATUƘAR GODE MAKU MASOYA A DUK INDA KUKE*
🤸🏻♀️🤸🏻♀️🤸🏻♀️
*ƳAN BAƘAR TAFIYA FANS COMMENT ƊINKU YANA MATUƘAR TAFIYA DANI KUNA SANI NISHAƊI DA COMMENT ƊINKU ALLAH YA BARMU TARE,MASOYA INA GODIYA*
*ALLAH YA BIYAKU MY PEOPLE, ALKHAIRIN ALLAH YA KAI MAKU HAR GADON BACCINKU, ƳAN BAƘAR TAFIYA FANS, KUNA SANI FARIN CIKI DA ADDU'O'INKU, ALLAH YA ƘARA DANƘON ZUMINCHI, KUMA BAZANI MANTA DAKUBA SAURAN MASOYA INA MATUƘAR GODIYA DA SOYAYYAR DA KUKE NUNAMA WANNAN NOVEL ƊIN ALLAH YA BARMANIKU MASOYA INA ALFAHARI DAKU.* 🤗🤗
____________________________
*PAGE 32_33*
...........Biba da Kulu da sauri suka riƙo Basma da ta fara chanza kamanni.
Ganin haka yasa Jafar juyawa domin samun wani abu wanda zai iya zuba ruwa ciki, ya duba ko ina baisamu inda zai zuba ruwanba, chan gefenshi ya hango wani fasasshen ƙoƙo, ɗaukoshi yayi tare dayin basmala ya wankeshi tas, ya ɗauki ganyan Magarya guda bakwai ya zuba cikin ruwan tareda kanga bakinshi kamar zaisha ruwan ya fara karanto fatiha iskan bakinshi na bugun ruwan, saida ya karanta fatiha ƙafa bakwai, ya nufo inda Basma ke kwance batare da tasan wandake kantaba.
Biba ya miƙama ruwanya umarceta da ta bata ruwan ta kur6a sauran kuma ta shafa mata ajiki.
Kulu da Jamcy suka taimaka mata ta samu da ƙyar Basma tayi kurba biyu, sauran ruwan ajikinta ta ida shafe mata ajiki, Jafar umartarsu yayi su Kwantar da ita.
Matsawa sukayi daga inda take.
Kama an tsikareta da allura haka tayi wuf tamiƙe zaune tafara kwarara wani irin amai baƙiƙirin, tamkar zata amayo ƴan cikin ta.
Fuskarta kaɗai zaka kalla ka tabbatar ta wahala iya wahala.
Tana gama aman tayi baya luuu! Ta sume.
Biba hada gudunta zata kamo Basma Jafar yayi saurin tsaidata.
"Alhamdulillah da alamu maganin ya fara aiki, kada wanda ya matsa inda take har sai ta farka."
Cikin jimami da matuƙar tausayin Basma su duka suke kallonta kwance kamar matatta.
Abinda majigin idanuwansu suka hasko masu ne ya sanyasu matuƙar kaɗuwa zuciyoyinsu suka fara bugawa da sauri da sauri.
Aman da Basma tayine ya zama wasu irin baƙaƙen tsutsotsi sunata bille_bille, lokaci ɗaya suka kama da wuta suka ƙone ƙurmus.
Jikin su yayi matuƙar sanyi, wasunsu wani sabon imani ya riƙa shigarsu.
Dubansu suka kai ga Basma dake kwance, ilahirin jikinta yadawo lafiya lau takoma ainahin Basmarta, sai dai abinda ba'a rasaba na baƙar azamar da suke sha a wannan Baƙar tafiya.
Hamdala Jafar yayi tare da kallon Salma data ke raku6e wuri ɗaya tamkar wata mairainiya.
Itama ruwan ya ɗebo yayi mata ƙwatan ƙwacin yadda yayima Basma.
Tana gama shan ruwan ta maka sauran a kanta, yana ida isowa inda Mandiya ta cijeta ta ƙwala wata gagarumar ƙara tareda faɗuwa ƙasa ta fara bille_bille tana tada ƙura tamkar ana yaƙi.
Mamaki ya kashesu Jafar ko motsi suka kasayi, su dai sunyi tsaye suna kallon ikon Allah.
Ihun da Salma ke ƙwalawa ta tsaida tare da dafe wuyanta, alamar kamar wani abu zai fito tacikin wuyanta tayi, ba shiri ta janye hannunta tare da ƙwala ƙarar da tafi ta ɗazu jin fitowar wani abu daga wurin.
Wani abu ne mai kama da maciji ya fito daga cikin wuyanta yajo kansu Rabson dake gefe tamkar yayima Salma kuka.
Ganin wannan abu yayo kansu a take suka tarwatse kowa yayi ta kanshi, Nas da Tk sune kan gaba wurin gudun.
Rabson tinti6e yayi da wani dutse atake yafaɗi ga wannan halitta tayo kanshi baki buɗe.
Ihu yake yana kuka ga hawaye ga wata majina sun wanke mashi fuska.
Ganin ya kasa tashi dagewa yayi ya miƙe tanufi inda rafin nan yake, cikin rashin sa'a yasake faɗuwa yacigaba da mulmulawa ya faɗa cikin ruwan.
Wannan halitta ita azabar da takeji ajikinta ta sanyata biyo duk wanda tagani gabanta, kamawa tayi da wuta ta fara ƙonewa tana wani irin kuka marar daɗin sauti.
Ganin wannan halitta tagama ƙonewa yasa su nufar inda Salma ke kwance, kamata Biba tayi suka miƙar da ita.
Wani baƙin ruwane ke fita awuyan Salma, saidai Biba ta yanki gefen hijabinta suka tare ruwan.
Yadda kasan fanfo inya fara zuwa kafin yayi ƙarfi yana kawo ruwa haka wuyan Salma ke tsiyayar da wannan ruwan.
Ƙallen hijabin Biba sai da ya gama jiƙewa da ruwan sannan ruwan ya tsaya, jefar da ƙyallen sukayi atake ya kama da wuta ya kone shima.
Hamdala sukayi ganin jikin Salma ya dawo dai_dai, cizon dake wuyanta kaɗai ya rage ya warke.
Lura sukayi babu Rabson, motsin da sukaga ruwa nayi ya tabbatar masu da Rabson na cikin ruwan, Jafar yayi ƙarfin halin fiddo Rabson da yayi tsamo_tsamo, da ruwa.
Jafar faɗa ya fara yimashi akanmi zai faɗa ruwa bayan yaga halinda suke ciki.
Baki yabuɗe da ƙyar ya tofar da ruwanda ya cika mashi baki yafara magana;
"Kawai sai in tsaya wannan halittar ta cijeni nima inzama Horror abanza, amma kaga inna faɗa ruwa in na mutu ciki nayi shahada."
Ba Jafar kaɗai ba harsu Nas halinda suke ciki bai hanasu fashewa da dariyaba saboda jin abinda Rabson y faɗa.
Bayan sun lafa da dariyar
Jafar ya fara masu bayani kamar haka;
"ALHAMDULILLAH godiyata tabbata ga Allah mai fidda matacce acikin rayayye, kuma ya fitar da rayyaye acikin matacce, cikin ikonshine ya sanya abokan tafiyarmu suka samu lafiya, Muna ƙara miƙa godiyarmu ga Allah, yanzu abinda yayi saura kuma yafi komi haɗari shine mu naimo su Mandiya dasuka zama Horror suma muyi masu magani, Abinda zamuyi shine yanzu fantsama zamuyi cikin jejin mu jawosu saimu rugu izuwa wannan rafin mai ruwa mu faɗa ciki, mu kuma dama munriga da mun yima wannan rafi addu'ar da mukayimasu Salma, idan Allah ya ƙaddara suma su komo mutane."
Ya ƙarasa maganar yana dubansu Rabson.
Kowa yayi na'am da wannan shawarar sunan sun fara shirin tinkarar su Mandiya.
Basma tunda ta farka daga nannauyan baccin daya ɗauketa take godiya ga Allah, ga wata gagarumar nadama da kewar mijinta da kuna Ɗanta, batasan lokacin da wasu zafafan hawaye suka wanke mata fuska ba, tayi kukanta mai isarta tana mai addu'ar Allah ya maidata gida kodan ta gyara kuskuren da tayi a baya.
Kwanansu biyu a wurin jikin Basma da Salma ya warware sunji sauƙi sosai sun warke, tun bayan warkewarsu Salma ta dawo cikin hankalinta take daraja ɗan adam, wani irin girma takema Jafar da yayi silar warkewarta.
A yaune zasu fita naiman su Mandiyi, kowa ya kimtsa.
Alama sukayima rafin domin in suka jawo su Mandiya su gane wurin.
Nausawa suka ƙarayi cikin jejin suna masu addu'ar samun nasara.
_________________________________
Cikin tsawa da hargagi yake magana tamkar zai kai mata naushi.
"Yau tsawon kwana goman dana ɗibar maki ya cika, dan haka kije gidanku na sakeki saki ɗaya, duk radda ɗiyata ta bayyana zani naimeki, yanzu zanije in samu shugaban sojoji abokina da kika sani in naimi taimakonshi atura wasu iyakar dajin koda Allah zaisa su Salma suna fitowa ayi sa'a su maido manasu gida, maganar ƙarshe da zaniyi maki i ta ce kitattara duk abinda kikasan naki ne ki bar gidan nan kafin in dawo."
Alhaji Abdallah mahaifin Salma ya ƙarashe maganar zuciyarshi na matuƙar yimashi ƙuna.
"Dan Allah ka gafarceni wallahi nayi nadama, kada ka tona mani asiri, yanzu innaje gida muzanice?, dan Alkah ka rufa mani asiri."
Ta ƙarashe maganar muryarta na sarƙewa saboda kukan da take cizga.
Bai ko kalli inda take ba yayi ficewarshi ya barta nan tsugunne.
____________________________
Basu yi nisa sosai da inda suka baroma suna cikin tafiya Jamcy taji kamar wani abu ya gilma da gudu ta bayanta.
"Wayyo Allah! Yauni Jamila nashiga ukku."
Ta ƙanƙame jikin Tk tana ƙyarma.
"Miya faru Jamcy?, yau ke ce ke faɗar ainahin sunanki wanda kin hana mutane kiranki da Jamila sai dai Jamcy, to wai mima ya firgitaki har haka."?
Tk ya Ƙura mata ido tare da jefo mata tambayar.
"Uhm! Ai wani abu nagani ta baya ya gilma."
"Haba Jamcy babu komi fa, kawai tsorata kikayi."
Jinin Jamcy kan akaifa sukaci gaba da tafiyar.
Kamar daga sama Jamcy taji an warci hannuta an jawota da ƙarfin tsiya ta faɗi ƙasa.
Ƙarar faɗuwarta ita tayi sanadiyyar jawo hankalinsu Jafar.
Ganin Jamcy ƙasa warwas ga Mandiya kuma sunata kokawa yasa Jafar fara dube_dube ko zai ga wani mabigi, sai dai duk iya dube_dubenshi bai samu komi ba.
Ganin bai samu komiba ya dunƙule hannuwanshi ya kaima Mandiya wani wawan bugunda yayi sanadiyyar rabata da jikin Jamcy ta faɗi chan gefe, ganin aka ya sa su duka suka fara gudu Mandiya ta mara masu baya.
Gudu suke suna waigen mandiya har suka iso inda rafin nan yake, basu bata lokaciba suka faɗa ciki, Mandiya da idanunta suka rufe itama bin bayansu tayi ta tsunduma cikin ruwan.
Ida isarta cikin ruwan yayi dai_dai da ƙwala wata gagarumar kuwwa da tayi ta haddasa ma wurin amsa kuwwa...........
*COMMENT* ✅
*SHARE*✅
*MEEN@RT...✍🏻*
08133562798
[10/11, 10:29 PM] Meen@t A Yandoma: 💀 *BAƘAR TAFIYA* 💀
( *HORROR STORY* )
*BY MEEN@T A YANDOMA*
*MARUBUCIYAR FATALWA*
🌍 *MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION*🌍🖊️
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
*SALONSHI NA DABAN NE 💃🏼*
*ALLAH KAJIƘAN MAHAIFINA DA DUKKN MUSULMI BAKI ƊAYA KASA YA HUTA, KA KAI RAHAMA A KABARINSHI, ALLAH KA GAFARTA MASHI ZUNUBBANSHI, ALLAH YAJI ƘANKA ABBANA*
*MASOYA INA MATUƘAR GODIYA DA SOYAYYAR DA KUKE NUNAMA LITTAFIN NAN, ALLAH YA BARMU TARE, INA MATUƘAR GODE MAKU MASOYA A DUK INDA KUKE*
🤸🏻♀️🤸🏻♀️🤸🏻♀️
*ƳAN BAƘAR TAFIYA FANS COMMENT ƊINKU YANA MATUƘAR TAFIYA DANI KUNA SANI NISHAƊI DA COMMENT ƊINKU ALLAH YA BARMU TARE,MASOYA INA GODIYA*
*ALLAH YA BIYAKU MY PEOPLE, ALKHAIRIN ALLAH YA KAI MAKU HAR GADON BACCINKU, ƳAN BAƘAR TAFIYA FANS, KUNA SANI FARIN CIKI DA ADDU'O'INKU, ALLAH YA ƘARA DANƘON ZUMINCHI, KUMA BAZANI MANTA DAKUBA SAURAN MASOYA INA MATUƘAR GODIYA DA SOYAYYAR DA KUKE NUNAMA WANNAN NOVEL ƊIN ALLAH YA BARMANIKU MASOYA INA ALFAHARI DAKU.* 🤗🤗
_______________________
*PAGE 34_35*
.......Kamar yadda kibiya ke fita daga cikin ƙwari haka Mandiya tayi tsalle ta fito daga