Showing 15001 words to 18000 words out of 28291 words

Chapter 6 - BAƘAR TAFIYA BY MEENART A YANDOMA.txt

13 Dec 2024

1430

Nas.


Ihu suke suna naiman agajin abokan tafiyar su, amma ina suma ta kansu suke.


Tsalle tayi tadira jikin Kulu, ƙara Kulu ta fasa tana"Nawan kataimaka mani kacire mani ita, kayi sauri wayyo nashiga ukku Nas kodai bakajin minike faɗa ne?."


Nas cikin muryar da ta gama karaya yafara magana tsoro ya gama baibayeshi.
"Aa Kulu na barki har abada kiyafe mani Allah yatsayar da mutuwarki ke kaɗai kinga tafiyata kiyafe mani, in ana doyayyah alahira muyi a chan."
Ya ruga aguje yayi bayansu Rabson da suke ƙoƙarin guduwa bankesu yayi ya ƙwara kan Salma dana Rabson yayi gaba.


Basuji zafin abinda Nas yayi masuba suka bi bayanshi.


Biba kowace addu'a tazo bakinta furta ta take tana naiman kariyar ubangijinta.


Kulu tariga ta yanke rai da tsira ta sadaƙar yau mutuwa zatayi.


Ganin halinda Kulu take cikigasu Nas sun gudu, wani ƙarfin hali taji yazo mata lokaci ɗaya ta furta, "LA'ILAHA ILLAH ANTASUBUHANAKA INNI KUNTU MINAZZALIM, ya Allah ka kawo mana ɗauki, kafitar damu daga wannan bala'in ya Allah mundogara gareka ya Allah kakawo mana mafita."
Tashi tayi tanufi inda Kulu take ga wannan tsutsa ta kanannaɗe ilahirin jikinta, wani ƙarfe tagani mai suffar wuƙa, ɗaukarshi tayi ta nufi inda Kulu take, shammatar tsutsar tayi ta luma mata wannan ƙarfen ajiki bakinta ɗauke da addu'a take ta saki Kulu ta ƙwala wata irin ƙara, take wurin ya6ule wani ruwa green mai kauri ya riƙa fita tamkar anbuɗe famfo, nan tagama bullayi ta mutu.


Kamo hannun Kulu Biba tayi tana mata sannu, tashi tayi jikinta duk ya baci saboda faɗuwar da tayi, lura Kulu tayi daga ita sai Biba da ƙyar tabuɗe baki tana tambayar ina sauran abokan tafiyarsu.


"Yanzu dai ki miƙe musamu mafita daga nan."
Biba ta kamo hannunta.


Wata kunya ce takama Kulu da ta tuna da rashin kunyar da ta yima Biba ɗazu amma yanzu gata itake taimakonta.


Lallai duniya kakiyayi wulaƙanta mutum bakasan ranar da zai maka wata rana ba, ɗan adam ba abin wulaƙantawa bane duk yadda ka ganshi.


Abinda idanuwanta suka hasko mata ya kusa datse numfashinta na wucin gaɗi, jikinta kyarma ya ɗauka tamkar mazari, hannunta yana kyarma ta ɗagoshi tana nunama Biba abinda idanuwanta suka hasko mata.


Ruwan jikin wannan tsotsane ya dunƙule ya rarraba kashi_kashi yana wata irin kumbura tamkar zai tashi sama, a hankali yake miƙewa tamkar yadda hayaƙi keyin sama yana miƙewa,wasu irin halittu masu suffar ƙwarangwal saidai su basukai tsayin ƙwarangwalba gasu da ƙaton kai yatsun hannuwansu kwara ukku rak!,idanuwansu jajur tamkar garwashin wuta jikinsu irin na ƙwarangwal sak.


Misalta halindasu Biba suka shiga bai misaltuwa, ga halittun sun fara miƙewa,Biba hannun Kulu ta kamo suka bi bayansu Rabson aguje.


Sunyi rasarar riskarsu Rabson, "ya kunkashe tsutsar?."
Salma ta tambaya tana maida kallonta ga Biba.
"Ta mutu amma kuduba bayanmu wani sabon bala'in ke tunkaro mu."ta ƙarashe maganar tana maida numfashi da ƙyar.


Hayaniyar da sukajiyo tasasu juyawa ganin abinda ke faruwa, halittun ne sun nufo inda suke bakunansu buɗe.


Ganin haka yasasu bin wata wangamemiyar ƙofa dasuka gani tabi tacikin kogon.


Bawan Allah Rabson yana gudu wani dutse ya taɗe shi ya faɗi kasa warwas, da rarrafe yasamu yana bin bayansu Alkah yabashi sa'a yayun ƙura yamiƙe tare dayi bayansu, ga waɗannan halittu biye dasu bakunansu buɗe.














*COMMENT*✅
*SHARE*✅














*MEEN@RT...✍🏻*
08133562798
[10/11, 10:29 PM] Meen@t A Yandoma: 💀 *BAƘAR TAFIYA* 💀


( *HORROR STORY* )


*BY MEEN@T A YANDOMA*
*MARUBUCIYAR FATALWA*


🌍 *MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION*🌍🖊️




*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


*SALONSHI NA DABAN NE 💃🏼*




*ALLAH KAJIƘAN MAHAIFINA DA DUKKN MUSULMI BAKI ƊAYA KASA YA HUTA, KA KAI RAHAMA A KABARINSHI, ALLAH KA GAFARTA MASHI ZUNUBBANSHI, ALLAH YAJI ƘANKA ABBANA*




*MASOYA INA MATUƘAR GODIYA DA SOYAYYAR DA KUKE NUNAMA LITTAFIN NAN, ALLAH YA BARMU TARE, INA MATUƘAR GODE MAKU MASOYA A DUK INDA KUKE*


🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️
*ƳAN BAƘAR TAFIYA FANS COMMENT ƊINKU YANA MATUƘAR TAFIYA DANI KUNA SANI NISHAƊI DA COMMENT ƊINKU ALLAH YA BARMU TARE,MASOYA INA GODIYA*




*ALLAH YA BIYAKU MY PEOPLE, ALKHAIRIN ALLAH YA KAI MAKU HAR GADON BACCINKU, ƳAN BAƘAR TAFIYA FANS, KUNA SANI FARIN CIKI DA ADDU'O'INKU, ALLAH YA ƘARA DANƘON ZUMINCHI, KUMA BAZANI MANTA DAKUBA SAURAN MASOYA INA MATUƘAR GODIYA DA SOYAYYAR DA KUKE NUNAMA WANNAN NOVEL ƊIN ALLAH YA BARMANIKU MASOYA INA ALFAHARI DAKU.* 🤗🤗🥰




🤧🤧
_kwana biyu kunjini shiru, hakan ya farune sanadiyyar rashin lafiya danayi, masoya na haƙiƙa naga saƙonninku ina matuƙar godiya,Allah yabar zuminci_


___________________________
_dan Allah ku sanya auntynah cikin addu'a, yau kwana Ukku tana labour Allah ya sauketa lafiya_




*PAGE 24_25*


..........A guje sukayo wurin Basma domin ceton rayuwarta.


Sunyi iya ƙoƙarinsu wurin fiddo Basma a cikin ruwan amma abun yaci tura, saboda ruƙon da Mandiya tayi mata bana wasa ne.




Ƙarfi suka haɗa suka fizgota daga cikin ruwan.


Tare da Mandiya da ta yi mata mugun ruƙo suka fiddota.


Ganin yadda Mandiya ta koma yasa sauran abokan tafiyar ja da baya in banda Jafar da yake naiman hanyar da zai taimaki Basma.




Tamkar yunwataccen zaki haka Mandiya tayi wurgi da Basma tayo kan Jafar gadan_gadan.


Da nufin cizonshi ta iso takamashi da kokawa sukayi ƙasa.


"A'uzubillah! Subhanallah!!."
Jafar ya furta ganin mace wadda ba muharramarshi ba ta ta6i jikinshi suna kokawa a ƙasa.


Tunyana kare kanshi daga muggan hare_hare da take kawo mashi harya fara mai da mata martani.


Su Jamcy ba kata6us tsaye suke sun haɗe wuri ɗaya ita da Tk suna surutan da ko su basu san mi suke faɗaba.


Ƙoƙarin yakiceta Jafar yayi ya wurgar da ita can gefe.


Abinda ya lura da waɗannan Horror ɗin basu taba mutuwa sai dai suyi doguwar suma inkayi nasarar luma masu wani makami ta bayansu.


Dube_dube ya fara naiman inda suka yada itatuwanda suke kamun kifi da su.




Can nesa da inda suke ya hango su.


Da gudu ya nufi inda suke, yana gaf da ida isa yaji an warto ƙafarshi ba shiri yayi ƙasa.




Ganin Mandiya na ƙoƙarin kawo mashi hari ta kowace hanya ya sanyashi kai mata harbi da ƙafafunshi cikin zuciyarshi yana karanto duk wata addu'a data zo mashi, yana ƙara ƙaimi wurin isa ga iccen da yake ƙoƙarin kaiwa.


Yayi nasarar ɗauko icce inda yayi nasarar luma matashi a tsakiyar baya, wata firgitacciyar ƙara ta kwala ta faɗa cikin ruwan ta 6ace 6at.


Wurin Basma dake kwance magashiyan dafe da wuyanta suka yo aguje.


Jamcy ta yagi rigarta ta ɗaure mata raunin Jafar ya tofa mata addu'o'in suna mata sannu.




Basu ɗauki lokaci ba Jamcy ta kamo Basma suka bar wurin saboda ganin abinda ya faru.
(Ni nace Su Jamcy ina aka baro faɗan ko harkun sauko 😂🤣 Hanya mai haɗin zumuntar dole)


Tafiya suke batare da sanin inda suke nufa ba.


Ga wata ƙishirwa da ta addabesu kamar su zube.


Wata inuwa suka samu domin su huta saboda zafin ranar da ake zubawa.




Tunaninsu ɗaya shine imna zasu sami abinda zasu ci dazai Gusar masu ƙishin da suke ji.


Ƙarar faɗuwar wani Abu sukaji a bayansu, Suna juyawa sukaga bishiyar kwakwa ce gasunan sun nuna manya sun Zubo ƙasa birjik.


Kallon_kallo suke an rasa wazai je ya kwaso masu suci.




Jafar ne yayi ƙarfin hali yayi addu'a ya duƙa ya fara tsinta yana tarawa.




Sai da ya tsinto masu mai yawa ya fara fasawa sukayi Basmala suna shanye ruwan ciki.


Sai da suka gama shanye ruwan sannan suka fara cin kwakwar.


Sunci sun ƙoshi lokaci ɗaya sukaji wani irin bacci na ɗibarsu, kwanciya sukayi domin su huta Jafar yayi Basmala tare da kwanciya.


Tunkafin baccin ya ida ɗaukarsu sukaji iska mai ƙarfi tana iso inda suke, kafin su ankara wata irin guguwa mai matuƙar ƙarfi ta kwashesu tayi sama dasu......


_____________________________
...............Abinda suka gani shi yakusa sanadiyyar datsewar numfashinsu.




Tsintar kansu sukayi a saman wani ƙaton tsauni wanda ƙasanshi ya kasance wasu irin itatuwane masu tsawo naban mamaki, itatuwan sune zaka kama ganyayensu masu tsananin faɗi da ƙauri da suka rufe saman tsaunin In kana da sa'a ka isa ƙasan tsanin da rayuwarka.








Gashi duk iyakar hangensu sun duba amma basuga Wata hanyaba saidai wannan.


Tafiya sukaji tamkar irinta ƙwaro in ya doso inda kake.


Amatuƙar firgice suka juyo danganema idanunsu mike faru.




Wasu irin ƙwarine masu kama da gizogizo.




Idanunsu jajur tamkar garwashin wuta, ga jikinsu duk wani irin gashi abun kwanin ban bantsoro.






Wani yawu suka haɗe atare ƙuutt!, Salma da Rabson tuni suka rungume juna suna salallami kamar basu bane suka gama gwabza faɗa ɗazu.




Ƙwari gudu suke suna ƙoƙarin isowa wurinsu Biba, ganin haka ya sanya su Biba ja da baya har suka iso ƙarshen ramin, ganin basuda wata mafita lokaci ɗaya tamkar sun haɗa baku suduka suka daka tsalle sukayi ƙasan ramin.




Ganin haka ƙwarin suka mara masu baya.




Saman ganye ɗaya suka faɗa su dukan su suna rarraba ido da tsananin mamakin wannan wane irin ganyen bishiyane?.




Basu ankara ba sukaji dirowar ƙwarin saman ganyen.




Suna son miƙewa amma tsoron in suka tashi tsaye tabbas sil6in ganyen zai kayar dasu.




Rabson da dai yaga bashakka in suka tsaya mutuwa zasuyi, wuf! Yayi ya miƙe "Ku miƙe muyi ta kanmu, bashakka in muka tsaya ƙwarin can zasu zuƙe jinin jikinmu abanza."




"Kai kam bakada tunani arayuwar, yanzu in bayaga kanada tunani irin na bunsurunka ta ina zamu gudu bakaga ƙasa rami bane?."
Salma ta ida maganar tana aikoma Rabson da kallon raini.




"Hhh, sai shegen surutu kamar aku, ja'ira mai zubin muciya baki kamar na agwagwa, nan gabafa nine mijinki kuma Oga awurinki kisan irin maganar da zaki riƙa furta mani."
Ya ƙarashe maganar yana dariyar mugunta dan yasan ya gama tunzura Salma.


Ashar ta mulmula ta dura mashi tana Allah ya tsareta da auren faƙiri talaka irinshi.




Biba da taga faɗan nasu bamai ƙarewa bane tsalle ta daka tayi ƙasan ramin.


Bayanta suka bi suma, saman ganyayyaki suka riƙa faɗawa kafinsu ida isa saman wani ganyen sul6i ya kwashesu sunyi ƙasa, haka aka riƙa tilli_tilli dasu.




Masu ihu nayi masu addu'a nayi.


Rabson daya bugu kanshi ya fara juyawa idanunshi suka fara hango mashi mutane suna komawa bibbiyu.
"Ƙalu innalillahi, la'ilaha'illallahu, shikenan namakance nalalace wayyoh busurulle wayyoh kaka uwata,Salma masoyiyi bibbiyu nike ganinku, lokacina yayi wayyon nazama makaho, yau Rabi'u nike ba Rabson ba namakance nadaina gani shikenan nayi Expired Salma ko auren mukayi saidai ki riƙa yimani jagora, inkuma namutu inkin koma gida kice ɗan busurulle Nabarma kakata ta yanka ta cinama ta ƙoshi, wayyoh nazama makaho."




(🤣🤣🤣 Wuya ba daɗi, yaji wuya ya ɗauka makancewa yayi)


Duk da har yanzu gwarasu ake sunayin ƙasa masifar dake cin Salma saida ta tanka.
"Allah ya ida makantar da kai, bakinka yasari ɗanyen kashi, mai muguwar fata,kaga ɗan bunsunru can inka mutu."
Bugata da akayi ta bugu da reshen wani icce ya sanyata yin shiru ta sume a take.


Sai da aka kawosu ƙarshen ramin suka faɗo tim! Batare da sanin inda kansu yake ba.


Wata guguwa mai masifar ƙarfi ta kwashesu tayi sararin samaniya dasu......




🤧🤧
A haɗa da haƙuri Har yanzu kwance nike, ƙarfin hali yasa nai maku wannan.












**COMMENT* ✅
*SHARE*✅


























*_MEEN@RT...✍🏻_*
08133562798
[10/11, 10:29 PM] Meen@t A Yandoma: 💀 *BAƘAR TAFIYA* 💀


( *HORROR STORY* )


*BY MEEN@T A YANDOMA*
*MARUBUCIYAR FATALWA*


🌍 *MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION*🌍🖊️




*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


*SALONSHI NA DABAN NE 💃🏼*




*ALLAH KAJIƘAN MAHAIFINA DA DUKKN MUSULMI BAKI ƊAYA KASA YA HUTA, KA KAI RAHAMA A KABARINSHI, ALLAH KA GAFARTA MASHI ZUNUBBANSHI, ALLAH YAJI ƘANKA ABBANA*




*MASOYA INA MATUƘAR GODIYA DA SOYAYYAR DA KUKE NUNAMA LITTAFIN NAN, ALLAH YA BARMU TARE, INA MATUƘAR GODE MAKU MASOYA A DUK INDA KUKE*


🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️
*ƳAN BAƘAR TAFIYA FANS COMMENT ƊINKU YANA MATUƘAR TAFIYA DANI KUNA SANI NISHAƊI DA COMMENT ƊINKU ALLAH YA BARMU TARE,MASOYA INA GODIYA*




*ALLAH YA BIYAKU MY PEOPLE, ALKHAIRIN ALLAH YA KAI MAKU HAR GADON BACCINKU, ƳAN BAƘAR TAFIYA FANS, KUNA SANI FARIN CIKI DA ADDU'O'INKU, ALLAH YA ƘARA DANƘON ZUMINCHI, KUMA BAZANI MANTA DAKUBA SAURAN MASOYA INA MATUƘAR GODIYA DA SOYAYYAR DA KUKE NUNAMA WANNAN NOVEL ƊIN ALLAH YA BARMANIKU MASOYA INA ALFAHARI DAKU.* 🤗🤗🥰


_____________________________
*PAGE 22_23*




..................Iskar lokaci ɗaya ta tsaya tamkar anyi ruwa an ɗauke.


Ganin waɗannan halittu ba ƙaramin dugunzuma hankalinsu Basma yayiba.


Jamcy da Basma tuni suka runƙunƙume juna jikinsu na mazari.


Wata mahaukaciyar dariya suka fashe da ida, wadda ta haddasama dajin. Girgiza.
"Kun ɗauka zaku iya guje mana ne,kunyi kuskure yanzu zaku girbi abinda kuka shuka ."


Asuƙwane suka yo kan su Jafar tamkar yunwatattun zakunan da suka shekara basuci abunci ba.


Muggan makaman dake hannuwansu Suka fara kaima su Jafar hari da su.


Kowa kagani wurin takanshi yake yana ƙoƙarin ceton rayuwarshi.


In suka kawoma mutum harida makaman hannunsu ya kauce ya samu wani icce take iccen yake darewa gida biyu, in ƙasa ce makamin yasama sai dai kaga wurin yayi rami.


Basma da Jamcy wani Aljani yayo kansu da mugun nufi , sun riga sun sadakar yau kwanansu ya ƙare jira kaiwai suke ya iso garesu.




Shurun da sukaji ta sanyasu buɗe idanunsu cikin kaɗuwa.




Ganin Jafar sukayi tsaye riƙe da wani abu mai kama sa sanda gefenshi gawawwakin Aljanun nan yayi nasarar kashe wasu.


Cikin kakkausar murya ya fara magana.
"Yanzu ba lokacin tsoro bane, lokacine na tashi muyi fafutukar tseratar da rayukan mu ko mu mutu ko muyi rai, dan haka ku kasance masu ruƙo da addu'a domin ta tasa nayi nasarar kashe wasu daga cikin Aljanun nan dako taruwa mukayi bazamu iya yaƙarsu ba,amma saboda tasirin addu'a gashinan Ubangiji yasa nayi masarar kashesu, dan haka kumiƙe kuceci rayuwarku ko kuma kuyi asararta nan bada jimawaba."
Yana ƙarashe maganar yayi wurin sauran Maridan bakinshi ɗauke da kabbara.




Kafin Maridan su ankara Jafar yayi masu gagarumar 6annan domin dayayi kabbara yadaka tsalle ya kaima tsakiyar bayan Aljani bugu saidai kaga yayi kururuwa ya zube ƙasa matacce.




Ganin irin illar da Jafar ke masu yasa mukayo kanshi da mugun nufin su raba kanshi da gangar jikinshi.




Addu'a yaci gaba da kwararowa abakinshi yana mai dogaro ga ubangijin shi tare da naiman ɗaukinshi.




Ƙarfin kabbarar da yake ta sanya Aljanun wasunsu yada makamai suna toshe kunnuwansu domin ji suke tamkar ana zuba masu ruwan tafasashshiyayar darma a kunnuwansu, ganin haka su Tk dake boye a mabanbantan wurare yin koyi dashi suna masu ɗaga murya tareda ƙwala kabbara.




Damar da Jafar ya samu ga Aljanun ta sanyashi ƙara ƙaimi wurin ragargazar aljanun, cikin ikon Allah yayi nasarar ƙararda Aljanun wasu kuma suka 6ace.


Iya jigatuwa Jafar ya jigata ga wata yanka da wani Aljani ya shammaceshi yayi mashi a hannu, yana gama faɗan ya yanke jiki ya faɗi.




Tk ganin Jafar ya ƙarar da Aljanun ya sanyashi fitowa suka yo kan Jafar.


Duk iya ƙoƙarin su akan jafar da wani taimako da zasu bashi sunyi, ga hannunshi dake zubda jini, Tk rigarshi ya yaga ya ɗaurema Jafar hannu yayi nasarar tsaida jinin, sunyi duk abubuwan da suka san anayi ma wanda ya suma domin ya tashi amma abin yaci tura domin ba alamun zai tashi.




Sunyi jigum_jigum suna tunanin halinda zasu shiga indai da gaske Jafar mutuwa yayi to bashakka kashinsu ya bushe a tafiyar nan.


Sunan nan zaune jikinsu ya gama mutuwa, zuciyoyinsu sun sadaƙar lallai Jafar bazai tashiba, ga duhun magriba daya farayi wurin ya ɗauki wani irin sanyi mai shiga ƙashi.




Hannunshi dake ɗaure yafara motsawa a hankali yana ƙoƙarin buɗe idanunshi bakinshi ɗauke da addu'a.




Ganin haka yasa su Tk sukayo kanshi zuciyoyinsu cike da wani irin farin ciki marar misaltuwa.




Kamashi Tk yayi ya ida miƙewa zaune.


Sannu suke ta keta kwararo mashi yana binsu da yawwa.




Sai da Jafar ya ida dawowa cikin hankalinshi sannan ya umarcesu dasu tashi suci gaba da tafiya, domin zama bai gansu ba.




Tafiya suke ga duhu daya yayi tsayawa sukayi sukai taimama suka gabatar da sallolin da aka biyo su.


Ƙara nausawa sukayi cikin jejin duk da yunwar da ta addabesu ga matsanancin sanyin da ake zubawa hakan bai hanasu cigaba da tafiyaba.




Yada zango sukayi saboda baccin daya rinjayi idanuwansu.


Wurine mai yalwar ciyayi ko ina ka wurga idonka lullube yake da ciyawa tamkar cikin yanayin damuna.


Kwantawa sujayi Jafar ya umarci kowanensu da yayi addu'ar kwanciya bacci kafin ya kwanta.




Bayan kwanciyarsu Jafar ya warware hannunshi domin ganin yadda raunin ya koma.




Abunda ya tada mashi hankali kuma ya bashi mamaki bai wuce ganin yayi wani irin rami tamkar an yanke fatar wurin, addu'o'i yacigaba da kwararowa yana tofama raunin domin yasan babu abinda ya gagari Allah.


Kowa yayi bacci wurin in banda Jafar da sai da yatofe jikinshi da addu'a ya kuma tofe inda suke kwance ya kakka6e inda zai kwanta ya kwanta bakinshi ɗauke da Basmala.


Wurin yayi tsi! Bakajin motsin komi sai munsharin da Tk ke yi kamar wani bujimin sa.




A hankali wata irin iska mai kaɗawa cikin natsuwa ta gauraye wurin, ciyawar dake ƙasan wurin a hankali ta fara kaɗawa rana motsawa, Bayyana sukayi cikin muguwar suffar mai tsananin ban tsoro.




Rashin sani yafi dare duhu, domin dasu Jafar sun san inda suk kawo kawunansu da tuni tun bar wurin.




Tsaye suke jikinsu baida maraba da jikin Fatalwa, gasu wasu irin dogaye fuskarnan tasu ba kyangani idanunsu guda ukku jere reras basuda hanci sai wani irin bakuna tanan suke shaƙar iska, fuskar su cike take da gashinda yayi nasarar lullu6e ilahirin fuskar,ga jikinsu sanye da wasu fararen kaya da jini yayi nasarar mai dasu jajaye.


Cikin tsananin 6acin rai macen takawo hannu da nufin ta ɗauko Jafar ta tsotse jininshi, sai dai mi, hannun na ida isa inda Jafar ke kwance taji wani irin zafi Kamar ta sanya hannunta cikin Wuta, bashiri tayo baya tana mai yarfa hannunta da fatar wurin ta dare jini Ya fara zuba.




Ganin abinda ya samu matar ya Sanya mijin zura hannuwanshi biyu da nufin ya tattaro su Jafar su duka ya hallakasu.




Abinda yaji yasanyashi ja da baya ga hannuwanshi dasuka fara ƙonewa.


Yaja matarshi suna mamakin abinda ya yi masu shamaki da kashe waɗan nan halittu, bacewa sukayi zuciyoyinsu cike da ƙudirin ɗaukar fansa.


Kamar cikim bacci Jafar yaji hayaniya amma yana buɗe idonshi yaga babu kowa.




Addu'a ya ƙarayi tare da komawa ya kwanta.




Sanyin asubar daya ratsasu shine yayi nasarar farkawarsu daga bacci,buɗe raunin hannunshi Jafar yayi, abun msmaki raunin nan ya warke tamkar bai ta6ajin ciwoba wurin, taimama sukayi suka kabbara sallah bayan sun gama suka zauna suna tunanin inda zasu samu abinda zasu sama bakinsu.


Gari na ida yin haske suka tafi naiman abinda zasuci.


Ƙoramace mai matuƙar kyau da ɗaukar hankali, kana hango yadda kifaye ke wasansu saboda ruwan ba zurfi.


Shawara suka yanke sukama kifayen su gasa su ci.


Jafar da Tk su suka shi suka samu wasu dogayen tsinkunan icce suka riƙa chako kifayen dashi.


Basma da Jamcy suna daga wajen ruwan suna kallonsu, Basma jitayi kamar ankira sunanta waigawa tayi tareda hango wasu kyawawan kifaye sunata iyo nesa kaɗan da inda su Jafar suke kama kifayen.


Zuciyarta kwadaituwa tayi data matsa taganema idanunta waɗannan kifaye, duƙawar da zatayi domin ta kamo kifin Taji an fizgi wuyanta anyi Cikin ruwan da ita, ƙarar faɗuwar ta tajawo hankakinsu Jafar suka nufo inda take aguje, abinda suka gani ne yasanya numfashinsu yakusa ɗaukewa na wucin gadi, Mandiya suka gani kamanninta sun koma na horror, ƙarar dasukaji Basma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login