Showing 1 words to 3000 words out of 28291 words

Chapter 1 - BAƘAR TAFIYA BY MEENART A YANDOMA.txt

13 Dec 2024

1425

[10/11, 10:29 PM] Meen@t A Yandoma: 💀 *BAƘAR TAFIYA* 💀


( *HORROR STORY* )


*BY MEEN@T A YANDOMA*
*MARUBUCIYAR FATALWA*


*BISMILLAHIR RAHAMINIR RAHIM*




🌍 *MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION*🌍🖊️




*WANNAN LABARIN ƘIRƘIRARREN LABARINE, SUNAYEN GARURUWA DA WASU WURAREN DUK ƘIRƘIRARRUNE*




*BAN YARDA AJUYA MANI LABARI TA KOWACE SIGABA SAI DA IZININA, DAN ALLAH A KIYAYE*


____________________
*PAGE* 1️⃣


....Wallahi ƙarya kake Habib, baka isaba ka hanani zuwa bikin ƙawata dole ne inje duk wani tsoratar dani da kake akan kar inje."


Miƙewa yayi a fusace.
"Ke harni zaki kallah kice ina maki ƙarya, to in har kika bar gidan nan bada yawuna ba kuma duk abinda yabiyo baya kada ki kuka dani ki kuka dakanki."


"Oho dai! Tafiyace ko kana so ko baka so sai nayi, yardarka da rashinta kai suka dama banga wanda ya isa ya hanani tafiyar nan ba."


"Haka kika ce?, to Basma jeki zaki gani, sai kinyi nadama kuma kada ki sake ki jemani da Ɗa ko ƙofar gidan nan ne."


"Ina zani da Ɗanka haka kawai ya takura mani, shakuruminka Ɗanka gida zani barshi."


Ficewa yayi daga gidan zuciyar shi na matuƙar yimashi ƙuna.
__________
💀💀💀💀
....Kuka take kamar ranta zai fita ga mahaifinta tsaye kanta da wayar wuta, jibgarta kawai yake babu ƙaƙƙautawa,
"Ni zaki zubda ma mutunci Salma! Ince maki kiyi hakuri amma ki kafe sai kinje bikin wata ƙawar banza, kinko san illar dake tattare da hanyar da zakubi?, to ƙara in karya ƙafafunki inga da wadanne ƙafafun zaki tafi,"


"Haba Alhaji!, kasheta kakeson yi?, dan Allah karabu da ita hakanan kada kayi mata zata illar kanakasa ta."




"Ki barni in nakasata inga da wadanne ƙafafun zata bar gidan nan, wurgar da bulalar yayi ya fice daga falon."


"Yanzu Mama ace duk yadda muke da hajara amma ace Daddy ya hana ni zuwa bikinta, kawai dan ance hanyar nada haɗari."


"Ke fah sakara ce, yanzu so kike a gabanshi in goyi bayanki, ai dole ne kije bikin hajara kada ki damu in lokacin yayi ce mashi zaniyi kinje biki a dangin mu."




(Kuji abun takaici uwa daya kamata tabada tarbiyya itake watware wadda mahaifin yabada, 🤣🤣 Basma kinyi kuskure kina kai kanki ga halaka dakinsan mizaku iske ga tafiyar da kinyi zamanki gida 🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️ muje zuwa.)


Rungume momyn ta tayi tana murna.
"Yawa momy na shiyasa nike ƙara sonki, yanzu Momy zani nunawa daddy na haƙura da tafiyar dan kada yayi zargin wani abu."


"Yauwa kinuna mashi, shima nasan dan yaga ke ɗaya ya mallaka shiyasa bai so kiyi tafiyar, ga kuma abokinshi munafuki daya ce mashi Wai hanyar bata da kyau."


Tashi Salma tayi ta nufi ɗaki.
"Momy na tafi in shirya kayana kinsan wallahi na ƙagara inga lokacin nan yayi."
_______________
"Jafar abinda zani faɗamaka kaji tsoron Allah aduk inda kake, tafiyar nan da zakayi nemo Mahaifinka daya daɗe da bacewa aka ce an ganshi achan garin, Jafar ka riƙe addu'a ka kiyaye yin sallah a duk halin daka tsinci kanka, wallahi jinike badan Mahaifinka daya bata zakaje nema ba da na hanaka tafiyar nan saboda an ce hanyar wata shu'umar hanya ce sai dai addu'a."


Tunda ta fara maganar kanshi yake ƙasa sai yanzu ya ɗago.
"Umma addu'arki nike nema i ta ce kaɗai nike buƙata a duk inda nike Umma."


"Jafar Allah ya tsare hanya, Allah ya kareka a duk inda kake, yanzu tashi ka fara haɗa kayanka."


"To Umma nagode da addu'arki, insha Allah kamar yadda kika buƙata zani kasance mai ruƙo da addini da kuma addu'a."




______________
"Yanzu Rabi'u tafiya zakayi ka barni, katai maka kada kayi rafiyar nan ance hanyar shu'umar hanya ce, kada kaje a kashe mani kai."
Ta ida maganar hawaye na wanke mata fuska.


"Haba! Haba!! Haba!!! Kaka nifa kidaina ce mani Rabi'u, Rabson guy nike haba in cikin abokaina ne ai saiki kunyatani."


"Nidai ina roƙonka ka janye maganar tafiyarnan Rabi'u."


"Kutt! In zanye fa kika ce?, Kaka ai dole in yi tafiyar nan ga inda ɗan ladi yace zani samu kuɗi amma kina maganar in zauna ai sam bazai yiwu ba, kinga bari inje in fara shin tafiya."
Ya fice yana tafiya yana yin doro kamar waninzabo irin tafitar gayun zamanin nan.


Binshi tayi da kallo zuciyarta na mata ƙuna saboda kinjin maganarta da jikanta yayi, ahalin yanzu shi kadai ya rage mata tun bayan rasuwar iyayenshi sanadiyyar gobara shi kadai ya tsira.


Shima gashi yanzu yana shirin kai kanshi ga halaka, dan tun tana budurwa takejin labarin dajin kai kazo, mugun daji ne wanda indai ka fita cikinshi ka auna babban arziƙi


____________
"Biba ba wai banison tafiyarki bane, Aa ina jin tsoron hanyar da zaku bi, Biba Mahaifinku ya rasu tunda Allah ya amshi abunshi ke kike sana'a kina hidima damu yanzu ace kema karatu zaki tafi, ni babbar damuwata wannan shu"umar hanya da zaku bi ta wurinta, in na tuna hankalina na matuƙar tashi Biba."


"Mama addu'ar ki a duk inda nike ita nike buƙata, Mama inna zauna banyi karatun nan ba dami zani taimake ku nan gaba nidai kiyi mani addu'a Mama."


"Shikenan Biba Allah ya tsareki a duk inda kike, abiba ki riƙe maraicinki kada ki bsnzatar da rayuwarki Allah yayi maki jagora Allah ya kareman ke aduk inda kike."


"Amin Mama."


"Bari inje in samo rancen sayayyar da zaki ida."


"To Mama sai kin dawo."




*MUJE ZUWA LABARIN BAI FARABA, SOMIN TABI NE NAN,KUDAI KU BIYONI.*




*COMMENT* ✅
*SHARE* ✅










*MEEN@T...* ✍🏼
08133562798
[10/11, 10:29 PM] Meen@t A Yandoma: 💀 *BAƘAR TAFIYA* 💀


( *HORROR STORY* )


*BY MEEN@T A YANDOMA*
*MARUBUCIYAR FATALWA*


🌍 *MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION*🌍🖊️




*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


*ALLAH KAJIƘAN MAHAIFINA DA DUKKN MUSULMU BAKI ƊAYA KASA YA HUTA, KA KAI RAHAMA A KABARINSHI, ALLAH KA GAFARTA MASHI ZUNUBBABSHI, ALLAH YAJI ƘANKA ABBA*




*WANNAN LABARIN ƘIRƘIRARREN LABARINE, SUNAYEN GARURUWA DA WASU WURAREN DUK ƘIRƘIRARRUNE*




*BAN YARDA AJUYA MANI LABARI TA KOWACE SIGABA SAI DA IZININA, A KIYAYE*




*BANI DA BAKIN DA ZANIYI MAKU GODITA MASOYA, TUN DAGA PAGE ONE NA WANNAN LITTAFI KUN NUNA MASHI ƘAUNA, INA MATUƘAR GODIYA ALLAH YA BIYAKU*


____________________


*PAGE 2_3*
....Fizge akwatin hannunta yayi, yana nuna ta da yatsa cikin tsananin bacin rai.


"Yanzu tsabar baki da mutumci in hanaki tafiyar nan amma sai kinyi?."


Kallon shi tayi awulaƙance.


"Tafiya sai nayi banga ɗan yarinyar daya isa ya hananiba, kabani akwatina kafin in zabga maka rashin mutumci, dan da in fasa tafiyar nan ƙara aurena ya mutum in je bikin."


Tsabar bacin rai idanunshi har sunyi jajur jikinshi har kyarma yake, wurga mata kayan yayi yana mai nunata da yatsa.


"Basma yau ni kike kira Ɗan yarinya?, har wata ƙawa tafini awurinki?, to bazance maki komiba kije zaki gani, sai kinyi nadamar tafiyar nan sai kinyi kuka da idanunki, sai kin yi nadama a lokacin da bata da amfani a wurinki."


Ɗansu dake ta darza kuka amma Basma ko ajikinta bata damu dashiba ya ɗauka yayi daki dashi.


"Oho dai ni kaga tafitata."


Tayi gaba tana wata rangwaɗa kamar budurwa, ga ɗamammun kaya ansha jikinta duk ana ganin shi ga ɗan figigin gyale ansha.


(Ya ubangiji ka shiryi matan auren wannan zamanin, wallahi wata shigar banzar da zatayi ko budurwa bazatayi ta ba, ko ni nan nasha ganin matar auren da tayi wannan shigar samari sun ɗauka budurwa ce sukayi ta tsai da ta, Allah ka shiryemu.)


________________
"Kai Momy! Ni dai kiyi sauri lokacin tafiyar fa yayi, kada inje in iske mota ta tashi."


"Kin ci gidanku Salma! Yaushe garin ya waye da har mota zata barki tasha."


"Mamana har an shirya kenan?, to i ta tafiya tana buƙatar guzuri ungo nan ki ƙara riƙe wa zasuyi maki amfani, ki gaida mani su kaka da ƴan uwa sosai."


Amsar kuɗin tayi tana godiya.
"To daddy na zasuji, zanyi missing ɗinka daddy na."


"Nima haka Mamana, ki kula da kanki sai kin dawo byee."


Ya faɗa yana ida shigewa ɗakinshi.


"Momy ki rakani bakin Get ko nasan yanzu idi Driver ya fita."


Suna fitowa ya nufosu yana gaidasu, amsar kayan dake hannun Salma yayi yasa a boot ɗin motar, shigeqa motar tayi na ɗagama Momyn ta hannu.


Sulalawa motar ta cimin haɗaɗɗen Get ɗin gidan ta fice.


Suna fita Momy taji jikinta yayi sanyi, zuciyarta na bugawa da sauri da sauri, jitayi dama ta hana Salma tafiyar alokaci ɗaya, sai dai ina bakin alƙalami ya bushe.


___________________
Tsaye gaban Mahaifiyar ta, cikin shiga ta kamala tasha hijabinta tana sauraren nasihar da take mata.


"Biba kiji tsoron Allah aduk inda kike, ki zauna da mutane lafiya, ki riƙe addu'a, ita addu'a takobin muminice, Ki kasance mai riƙon amana da faɗar gaskiya aduk halin da kika tsinci kanki, Allah ya tsareki ya dawo dake lafiya Habibata."


"Amin Umman."


Juyowa tayi ta kalli ƴan ƙannenta da suka yi jigum_jigum.


"Bakuyi mani addu'a ƙannena?, ko baku so in zani dawo inyi maku tsaraba."


Hada baki sukayi cikin farin ciki dajin maganarta, "Allah ya kiyaye aunty Biba, sai kin dawo."


Sallama tayi da Umma tafito jiki ba kwari tayi addu'ar fita daga gida ta hau a daidaita ta nufi tasha.


_______________
"Rabi'u yanzu tafiyar nan zakayi?."


"Chan Allah ya haɗaki da Rabi'u, ni Rabson guy nike, kada ki bata mani lokaci ni tafiya zaniyi."


"Kakus ki kula mani da Ɗan bunsuruna, dan ranar dana dawo lokacin na samo kuɗi ranar zai sha wuƙa."


"Rabi'u kai kaɗai ka rage mani tunda mahaifanka suka yi haɗari suka mutu, yanzu kai ma tafita zakayi ka barni."


"Haba kakus! Kuɗi fa zani samo, kuma inna tai ba daɗewa zanyi ba zani dawo."


"Ni dai bada yawuna zakayi tafiyar nan ba, in katai komi ya faru ba ruwana tunda bakajin maganata."


"Heeey! Chau_chau kakus, kina bata mani lokaci kinga tafiyata."


Yafice yana waka abakinshi ba tare da addu'ar fita daga guda ba.


Binshi tayi da kallo wasu zafafan hawaye na wanke mata fuska, ji take aranta kamar Rabi'un ta ba zai dawo ba.


________________
Har ka fito Jafar?.


"Eh Umma lokaci nata ja."


Nan tayi mashi nasiha mai shiga jiki mussam kan ruƙo da addu'a aduk halin da mutum yashiga.


Bankwana sukayi jikinsu yayi sanyi.


Jafar ya fito na nufi tasha.


________________
Hayaniya ce ke tashi acikin tashar kowa nata hada hadarshi.


Basma, Salma, Biba, Rabson guy, da Jafar duk lokaci ɗaya suka iso tashar.


Gudu_gudu suka iso gaban motar da kwandastan keta faɗi.
"Kai kazo! Kai kazo!! Saura mutum biyar mota ta cika."


Basma, Rabson, Jafar, da Biba sunyi nasarar shigewa motar amma banda Salma data bige wata tsohuwa.


"Kai amma dai ke wace irin jakar tsohuwace?, idanunki basu gani hanya koko?."


"Ɗiyata kiyi haƙuri." amma abinda zani faɗa maki kada ki kuskura kiyi tafiyar nan Ta fada tare da kamo hannun Salma.


Tatss! Ta ɗauke tsohuwar nan da mari.


"Kina ƙazamarki har zaki kamo hannu na, talaka marar amfani kawai."


Tayi gaba tabar tsohuwar tsaye.


Abun mamaki tsohuwar dafe take da kumci amma dariya take mai ban tsoro.


Salma na isa motar ta cika, dan dama Motace mai cin mutum goma.


Sun ɗauki hanya an fara tafiya.


Salma da Rabson guy kujera daya suke zaune.


Sai Biba da jafar suna gaban kujerarsu Salma.


Sai Basma ita da wani mutu aka haɗata.


Gudu motar ke shararawa akan titin, in da motanen motar kowa da abunda yakeyi.


Biba da Jafar Hisnul muslum ne hannunsu suna karanta azkar.


Basma earpiece ne kunnenta tana shan ƙiɗa.


Rabson da Salma charting kawai suke sha, Rabson satar kallon Salma kawai yake.

Sauran mutanen motar hirarsu kawai suke sha.


Wani mahaukacin birki da direban yayi shiya sanya kowa kallon abunda ya haddasa faruwar haka, tuni kowa ya ruɗe wasu suka hau iface_iface wasu suka hau salati.




Komi nene suka gani 😜😜


Yanzu labarin ya fara, muje zuwa.💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼






*INA MATUƘAR ƘAUNARKU MASOYANA* 💃🏼💃🏼💃🏼






*EDITING* ❌
*COMMENT* ✅
*SHARE* ✅






*MEEN@RT...✍🏻*
08133562798
[10/11, 10:29 PM] Meen@t A Yandoma: 💀 *BAƘAR TAFIYA* 💀


( *HORROR STORY* )


*BY MEEN@T A YANDOMA*
*MARUBUCIYAR FATALWA*


🌍 *MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION*🌍🖊️




*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


*ALLAH KAJIƘAN MAHAIFINA DA DUKKN MUSULMU BAKI ƊAYA KASA YA HUTA, KA KAI RAHAMA A KABARINSHI, ALLAH KA GAFARTA MASHI ZUNUBBABSHI, ALLAH YAJI ƘANKA ABBANA*




*WANNAN LABARIN ƘIRƘIRARREN LABARINE, SUNAYEN GARURUWA DA WASU WURAREN DUK ƘIRƘIRARRUNE*




*BAN YARDA AJUYA MANI LABARI TA KOWACE SIGABA SAI DA IZININA, A KIYAYE*




*BANI DA BAKIN DA ZANIYI MAKU GODIYA MASOYA, TUN DAGA PAGE ONE NA WANNAN LITTAFI KUN NUNA MASHI ƘAUNA, INA MATUƘAR GODIYA ALLAH YA BIYAKU*


____________________
*PAGE 4_5*


........iface_iface kai ketashi acikin motar, Jafar da Biba addu'a ce abakin su, sunata mai_maitawa.


*LA'ILAHA'ILLAH ANTA SUBUHANAKA INNI KUNTU MINAZZALIMINA*


suke ta nanatawa, wannan addu'ar in dai ka dogara da Allah kariƙa yinta alokacin da kake cikin bala'i Allah zai fiddaka da izininsa,,,Tunatarwa ce.


"Munshiga ukku direba meya faru?."


Direba ko motsi baiyi rai yayi halinshi.


Suna ganin haka suka ƙara ruɗewa.
Duka mutanen motar fitowa sukayi ganin hanya ta tsage gida biyu ya ƙara tada hankulansu sukayi cikin dajin da mugun gudu.


Gudu suke ko wai waye basuyi iyakar ƙarfinsun suna ƙara kutsawa cikin dajin.


Dajine wanda ko daga yanayin bishiyoyinshi kaɗai sun isa su sa mutum sumewa, wani irin shu'umin daji ne wanda bishiyoyin cikinshi kansu suffar dodanni garesu, ga wata irin duhuwa dake gareshi, duwatsune manya_manya cikin dajin ga wani irin iska wanda shi kaɗai ya isa ya tabbatar maka da kuna cikin tashin hankali,masifa da bala’i.


Iskane ke kaɗawa kamar kana cikin maƙabarta wani shuuuuw! Ga iska ya game da kukan wasu irin tsuntsaye, yana bada sauti mai firgitarwa.


Gudu suke kamar ransu zai fita, abinda basu sani ba duk gudun da suke haryanzu suna farkon dajin.


"Wayyoh zani Mutu! Kutsaya mu huta, wayyoni ƙishirwa ku taimaka mani."


Basma ke maganar numfashin ta na fita da ƙyar.


Abokin zaman kujerarta a mota afusace ya fara magana.


"Kee amma bakida hankali kina nufin mutsaya musanya rayuwarmu ga halaka?, to in bazaki zo mu ida fita adajin nan ba wallahi nan zamu barki muyi gaba.




Kafin ya ida rufe baki dajin ya gauraye da wata mahaukaciyar dariya.




"Kunyi kuskuren shigowa DAJIN KAI KAZO!! Ku masu taurin kai Dukkan ku babu wanda zai fita da rayuwarshi,zamu riƙa yimaku ɗauki ɗai_ɗai har sai mun ƙarar daku hahaha."




Wata mahaukaciyar guguwace tayo kansu.




Gudu sukaci gaba dayi suna waiwayen iskar dake biyosu, tim! Daya daga cikinsu ya fadi tsayawa sukayi domin taimakonshi, Jafar ya tsaya suna kokarin isowa gareshi, suna daf da isowa gareshi iskar nan ta sureshi tayi sama dashi.


Firgicewa suka ƙara yi masu koke_koke da iface_iface nayi.


Sauƙinsu ɗaya duk gudun da suke basu rabu da juna ba.




Gudu suke har duhun magriba ya fara.




Wani wuri suka tsinci kansu mai yalwar bishiyoyi manya_manya gasu kuma dogaye abun tsoro.




"Assalamu alaikum!, jama'a ya kama tafa musan abunyi, kamata yayi musan inda muke kutsa kanmu, karfa wurin gudun ceton rayuwa mukai kanmu ga halaka."


"Maganarka haka take, kamata yayi mubar gudun nan musamarwa kanmu mafita ga duhu ya fara."




Biba ta fad’a tana mai ƙara dubar mutanen.




Wani saurayi mai zubin ƴan daba daga cikin fasinjojin motar ya fara magana.




"Yanzu kamata yayi mu samu inda zamu ƙwana shine kawai mafita in safiya tayi saimu nemi hanyar fita daga dajin nan."




"Wallahi baka isa ba mu babu inda zamu kwana cikin wannan ƙazamin dajin, in kai ƙazamine toni dubarni da kyau banyi kalar da zani haɗa wurin kwanciya daku ba." Salma ta faɗa tana aikamai da kallon wulaƙanci.(Nikam dake danazo nan seda na shek’e da dariya😂)




"Kuturun chan kayyasa! Yau Garba kisane mace ke faɗawa magana, yarinya kinci arziƙin a wani hali muke da hukuncin kisa shi zai hau kanki, amma yanzu sai dai in maki bugun da ko kallon banza bazaki ƙara yi mani ba."




Wani wawan tsalle ya daka ya isa gabanta ya fara ɗauketa da ta gwayen maruka.




Mutanen wurin sukayo kanshi suna rirriƙeshi ana bashi haƙuri.




"Ni ka mara?, wallahi sai kayi nadama sai ka ƙwammace bakazo duniya ba, ko daddy na bai taba marina ba sai kai matsiyaci talaka da kai."




Jafar ya daka mata wata irin tsawa.
"Keee! Ya isa, yanzu a wannan halin damuke ciki haɗin kai muke buƙata bawai mu tsaya muna faɗa da juna ba, daga yanzu bazamu laminci wannan faɗace_faɗacen naku ba, ku zo muyi gaba muga in da ya dace mu yada zango."




Sunyi ƴar tafiya mai nisa suka ga wani gida a gabansu.




Gidane wanda aka gina da katako, da alamu gidan ya daɗe a kulle saboda yanar data lullube ƙofar gidan.




Hayaniya aka farayi ta wanda zai shiga ya duba.




Rabson guy da akace ya shiga su duba karkace kai yayi yace shi in dare yayi bai gani sosai.




Cikin abokan tafiyarsu na mota mutum huɗu da suka rage Garba kisa, da wani audu gwarama, sai wani nura shila su duk abokai ne wani aiki na shiyasa suka samu zasuje su tada rikici abiyasu.
Sai mace ɗaya mandiya Ita kuma karuwa ce labari ta samu anfi samun kuɗi a abirnin Kai kazo shiyasa ta fito yawon duniya zataje Birnin kai kazo.




Jafar, Garba kisa, audu gwarama sai nura shila, su zasu shiga gidan su duba masu.




Ƙofar gidan kulle take gam, da ƙyar suka samu suka buɗeta, wata irin k’urace ta ke fitowa daga gidan dole suka ja da baya sai da ƙurar ta gama ficewa sannan Jafar yai bisimillah suka kutsa kai cikin gidan.


Duhu ne sosai gidan ko tafin hannunka baka gani, sai lokacin Jafar ya tuna da wayarshi, fiddota yayi amma abun mamaki kwata_kwata babu network gurin ko alamun shi babu.




Touchligh ya kunna, tuni haske ya gauraye wurin, wani irin gidane mai wani irin fasali, inda suke tsaye wani tangamemen falo ne mai ɗauke da gadaje uku gefe daya kuma kujerune aduk da katakai akayi su, sai wasu ɗakuna biyu dake kulle, in ka matsa bayan kujerun wurin dafa abincine shima da katakai aka ƙera wurin, amma duk yana ta lullube kayan gidan da kuma ƙura,idanunsu ne suka hasko masu wani hoto amma ƙura ta lullubeshi, matsawa mukayi a hankali Jafar yayi bisimillah tare da goge ƙurar,Hoton Turawane ya bayyana mata da miji da kuma ɗiyarsu, sunyi dariya aka ɗauki hoton su, sunyi matuƙar kyau.




Kansu kullewa yayi, suna ma kawunansu tambayar miya kawo turawa acikin dajin nan har sukayi gida?, lallai al amarin nan akwai ban tsoro.




Ƙofofin ɗakin suka buɗe da tagogin take haske ya bayyana duk da lokacin duhun magriba ya fara.




Sun duba ko ina amma basuga wani abu na cutarwa ba.




Ɗakunan nan biyune kaɗai basu buɗeba.




Fitowa sukayi suka umarci abokan tafiyarsu dasu shigo daga ciki.




Bayan shigarsu ne kowa ya naimi wuri ya zauna yana jimamin halin da suke ciki.




Jafar ne yayi gyaran murya ya fara magana.




"Ƴan uwana ya kamata mutashi mu gabatar da sallolin dake kanmu, nasan da wuya musamu ruwa a hanlin da muke ciki yanzu amma abinda yafi shine muyi taimama kawai zai fi mana."




Basma da Biba, Mandiya tare sukayi sallah, ƙiri_ƙiri Salma taƙiyin sallar cewa tayi ita gobe in an samu ruwa ta haɗa tayi.




Garba kisa da yaranshi kuwa sai dai shiriyar, domin tabarsu kusa fiddo daga cikin aljihun wando da ahana suka hau hura hayaƙinsu.




Dare yayi nan ido ya raina fata, kowa ka kalla zakaga tsantsar tashin hankali atare dashi.




Bayan sun kakkabe ƙurar da yana kowa ya fara neman inda zai kwanta, Mandiya,Basma,Biba da Salma gado ɗaya suka kwanta, inda Salma tayita tsoki wai ita bazata haɗa jiki da su

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login