Showing 6001 words to 9000 words out of 28291 words
ta lura babu gyalenta ya faɗi sana diyyar gudun da suka sha, ga suturar jikinta ba ta kirki ba duk ta matseta, dubanta ta kai ga Salma wadda ita ma hakan ta kasance gareta dan figaggen gyalenta ita ma tun suna cikin wannan gidan ya faɗi.
Duk cikin su Biba Ita kaɗai ce shigarta har yanzu hijabinta bata cireba sai dai cukuikuyewa da ta fara saboda wahalar da suke sha.
Abinda su Jafar basu sani ba tunda suka fara gudun nan wata ƴar ƙaramar barewa ke biye dasu.
Ba zato ba tsammani suka ga barewa ta nufo inda suke gadan_gadan.
Miƙewa sukayi a matuƙar razane suka dun ƙule wuri ɗaya.
Rike ɗewa barewar tariƙayi har ta koma wani farin tsoho mai cikar kamala da kwarjini.
"Ku kwantar da hankalinku ni taimakon ku nazo yi ba cutar daku ba, nima da kuke gani musulmi ne ɗan uwanki, abunda nike buƙata ku dogara da Allah ku zauna in sanar daku abinda baku saniba game da tafiyar da kuke.
Jikinsu kyar ma kawai yake sun kasa zama sai da Jafar da Biba suka ƙara masu tuni akan su dogara da Allah su zauna.
Mai da hankalinsun sukayi ga wannan tsoho.
"Kamar yadda na faɗa maku a baya ni ba mutum bane, kamarku ni Aljani ne, suna nana Ammar bin asad, basai na sanar daku yanayin dajin nan ba nasan yanzu kun fara sanin yadda yake, wannan daji da kuke gani tun asali ya kasance wani irin shu'umin jeji wanda ko dabba ce ta shigo cikin shi da wuya ta fita araye, asalin fara zaman wannan daji wasu turawa ne ma'aurata bayan aurensu suna binciken inda keda abu buwan mamaki domin su Allah yayi su da son abubuwan al ajabi, nan suka binciko wannan daji, sunyi ƙokarin zuwa dan ganema idanunsu abinda ke faruwa ana hana su zuwa amma suka nace, daga ƙarshe suka sulale suyo Nageria, bayan zuwansu Nageriya basu yadda sun shiga wannan daji kai tsaye ba gida suka kama suka zauna suna hulɗa da hausawan mu har suka iya hausa abakunan su, Alƙawari mijin yayi in matarshi ta haihu ɗiyar tayi shekaru biyu lokacin ne zasu nausa cikin dajin dan gane ma idanusu abunda ke faruwa."
"Ba'a ɗauki wani dogon lokaci ba Matar wannan Bature ta haihu, ranar da ɗiyarshi ta cika shekaru biyu ranar suka ɗauki hanyar wannan daji da duk guzirin da suke buƙata, Sanin halin wannan daji yasan ya dereban dazai kai su dajin yace sai dai ya ajesu nesa da dajin su ida isa da ƙafafunsu, idansu ya rufe ga son shiga wannan daji dan haka basuji komi ba suka amin ce , gorinsu ya cika sun samu damar shiga cikin wannan daji daya kasan ce shine zai zama ajalinsu, tun shigar su dajin suke murna ganin dajin ko ƙasashen su basu taba ganin daji mai duhuwa da manya_manyan duwatsu, dajin kallonshi kaɗai abun tsorone amma su a wurinsu wannan shine kaɗan daga cikin abubuwan mamakin da suke naima,itatuwa mijin da matar suka hau sarewa suna haɗa katakan yin gidan da zasu zauna, sunyi aiki natsawon watanni biyu iya wahala sun wahala kafin suyi nasarar i hada gidan, har yau babu abinda ya firgita su koya tsorata su tun shigarsu dajin, rayuwa suke tajin daɗi acikin dajin nan suna ɗiyarsu, ranar da bazasu taba mantawa ba ita ce ranar suna daga wajen gidan ɗiyarsu na nesa dasu tana wasa su kuma suna zaune suna hirarsu, wata irin ƙara kunnuwan su suka Jiyo masu, a firgice suka kwalama ɗiyarsu kira dake wasa nesa dasu baban ya ruga ya ɗauko ta suka nufi gidan, sai dai mi! Suna buɗe gidan suka ga ɗiyarsu nata wasanta ita ɗaya cikin gidan, dagowa tayi ta kallesu tana sakar masu murmushi, sakin wadda ke hannunsu sukayi suna nunata da yatsa suna ja da baya, su duka taran biyu da ta cikin gida da ta hannunsu nufo su sukayi suna momy ni ce Lara ɗiyar ku waccen ƙarya take, ruɗewa sukayi sun rasa gane ainahin ciki wacece ɗiyarsu, Lara ta ƙarya ta shago wuyan ta gaskiyar ta ɗagata sama ta wujijjigata ta wullata gefe, juyowa tayi kan iyayen tana dariya idanunta na zubda jini, nuna su tayi da hannu take wata iska ta yi sama dasu tana bugasu da bishiyoyin wurin tun suna ihu suna kiran abun bautar su har suka daina numfashi, bacewa. Basu farfaɗo ba sai da marece yayi sanyi bugesu sannan suka farfaɗo kan ɗiyarsu sukayi da gudu suna kiran sunan ta, kayansu suka haɗa suka nufi haryar da suka shigo dajin, abun mamaki haka suka ƙaraci yawonsu har duhun dare ya fara amma hanyar ta bace masu, dole suka haƙura suka dawo gidan suna tunanin abunda zai same su nadamar shigowa dajin na shigarsu , dare ya raba babu abuda kunnuwanka ke jiyo maka illa kukan tsuntsaye da ya haɗe da Iska yake bada wani firgitaccen sauti, ƙofar da suka kulle sukaji tana budewa da kanta ɗiyarsu suka jawo suka ƙara rungumewa, wani baƙin wayaƙi ya Cika ɗakin, a hankali ya fara haɗewa wuri ɗaya yana komawa doguwsr halittah mai suffar mutum, ko ina jikinta hannuwa ne, idon ta guda a tsakiyar goshi, dariya ta kece da ita "ku masu taurin kai yau kwananku ya ƙare,yau zaku bar duniyar nan sakamakon ganin ƙwaf daya kawoku dajin nan," tana rufe baki ta chafko miji ta wullashi sama ya fado ƙasa kanshi ya fashe ko shurawa bai yi ba ya mace, matar ta nuna da hannu take wani hayaƙi ya fito ta hannunta ya shigajikin matar da ɗiyarta take jini ya riƙa ambaliya ta hancinsu da baki suka sulale ƙasa matattu, atare gawawwakin su suka bace tare da wannan hali halittar, wannan shine abunda yafaru da waɗan da suke shigowa ɗakin nan, taimako ɗaya zaniyi maku shine kada kusake wannan addu"ar ta fita daga bakunan ku, *LA'ILAHA ILLAH ANTA SUBUHANAKA INNI KUNTUMINAZZALIMIN*, san koda wasa kada kusake ku sake ku rabu da abokan tafiyarku, ƙarfina bazai iya fiddaku daga dajin nan ba addu'ar ku ita zata taimake ku, nabarku lafiya Allah ya fitar sadaku, ya bace."
Jikinsu sanyi yayi dajin wannan bayanin, basu ankara ba wurin da suke ya fara duhu bishiyoshin na komawa baƙaƙe flower ɗin wurin suna bacewa, Basma tsalle tayi ta faɗa jikin Biba jikinta na kyarma, Rabson Basma dake kusa dashi ya maƙalƙale.
"Bakada hankali?, ina matar aure zaka riƙa shigemani?."
"Ke da auren na haɗaku a turmi na Ƙulƙule, kina matar aure tsabar gantali miya fito dake wannan tafiyar?."
Kafin ya rufe baki duhu ya ida rufe idanunsu, ji sukayi an shure su anyi sama dasu shuuuuu!✈️✈️
😜😜😜
*MASOYANA KU KOYAMA WANNAN LITTAFIN YAWO, YAJE KOWANE GROUP NA NOVE💃🏼💃🏼💃🏼*
*COMMENT*✅
*SHARE*✅
*MEEN@RT...✍🏻*
08133562798
[10/11, 10:29 PM] Meen@t A Yandoma: 💀 *BAƘAR TAFIYA* 💀
( *HORROR STORY* )
*BY MEEN@T A YANDOMA*
*MARUBUCIYAR FATALWA*
🌍 *MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION*🌍🖊️
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
*SALONSHI NA DABAN NE 💃🏼*
*ALLAH KAJIƘAN MAHAIFINA DA DUKKN MUSULMU BAKI ƊAYA KASA YA HUTA, KA KAI RAHAMA A KABARINSHI, ALLAH KA GAFARTA MASHI ZUNUBBABSHI, ALLAH YAJI ƘANKA ABBANA*
*MASOYA INA MATUƘAR GODIYA DA SOYAYYAR DA KUKE NUNAMA LITTAFIN NAN, ALLAH YA BARMU TARE, INA MATUƘAR GODE MAKU MASOYA A DUK INDA KUKE*
🤸🏻♀️🤸🏻♀️🤸🏻♀️
*ƳAN BAƘAR TAFIYA FANS COMMENT ƊIN YANA MATUƘAR TAFIYA DANI KUNA SANI NISHAƊI DA COMMENT ƊINKU, ALLAH YA BIYAKU INA MATUƘAR GODIYA*
🥰🥰🥰🥰
*WANNAN FEJIN SADAUKARWA NE GA DUK MASOYANA ADUK INDA KUKE, ALKHAIRIN ALLAH YA KAI MAKU, INA GODIYA*
__________________
*PAGE 10_11*
.....Lulawa akayi dasu a sararin samaniya, addu'ar da suke ta sanya aka yo ƙasa dasu ba shiri.
Wuri ne mai tsananin huduwa da manya_manya duwatsu, ga bishiyoyi masu wata firgitacciyar suffa ko ganye ɗaya babu jikin su, sai wasu irin dogayen saiwa ajikinsu.
Aka watsosu, sanyin daya fara ratsa jikinsu ya sanya su buɗe idanu suka miƙe a firgi ce.
"Innalillahi wa'inna ilaihi rajiun, Mi mukeyi nan?, ina sauran abokan tafiyar mu."
Jafar ya faɗa yana mai kallon mandiya da Basma da suke rarraba idanu ido.
Hannu Basma ta ɗora akai ta fashe da kuka.
"Wayyo Ɗana wayyo Mijina ashe kallon ƙarshe nayi maka bazamu sake haduwa ba ajali ke kira na."
Ya isa, Jafar ya daka mata tsawa, "da kukan ki zamujin ko da halinda muke ciki, harkin manta da nasihar Ammar?, babban tashin hankalinmu ayanzu shine an raba mu da abokan tafitayarmu."
Sai lokacin su Mandiya suka lura da basu tare da abokan tafiyarsu.
Nau sawa suka ƙarayi ciki jejin suna kwalama abokan tafiyarsu kira.
Tun suna kiran sunayen su da ƙarfi har muryoyinsu suka shaƙe amma ko alamunsu babu.
Tsayawa sukayi suna mai da numfasha saka makon tafiyar da suka sha.
"Ni fa ina ganin an rabamu da abokan tafiyarmu ne dan ayi galaba akanmu."
Mandiya ta fada tana fuskantar Jafar.
"Nima zuciyata ta kawo mani wannan tunanin tuni, amma duk da haka mu dage da Addu'a, Allah shine kaɗai mai iya fitar damu daga cikin wannan halin."
Tashi sukayi suka ci gaba da tafiya, sun ɗanyi nisa da wurin da suka baro sukaji takun tafiya a bayansu.
A hanzar ce suka juyo suna dunkulewa wuri ɗaya.
Sal...Sasa..Salma!.
Baku nan su, suka furta suna in ina.
Salma dake nesa dasu takowa ta farayi zuwa inda su Basma suke.
Mandiya murnan sun fara ganin abokan tafiyarsu ya sanyata rugawa ta maƙalƙale Salma.
"Muna ta naimanku ina kuka shige Salma?."
Shirun da taji anyi mata ne ya sanyata dago fuskarta tana kallon Salma.
Ganin fuskar Salma da ta chanza ta koma irin suffar Horror, rabin fuskarta ya kowa abun tsoro duk yayi dameji wani farin ruwa mai haɗe da jini na zuba,idanunta ɗaya babba ɗaya ƙarami ga bakinta daya rabe biyu jini na ɗiga, faratan hannuwan ta sunyi zaƙo_zaƙo irin na Horror.
Razanan niyar ƙara ta fasa tana ƙoƙarin kwace kanta a hannun Salma.
Sai da ta makaro domin Salma ta rigada ta mata kyakykyawan ruƙo.
Dariya Salma taci gaba da 6a66akawa da ta sanya dajin amsa kuwwa.
Kunyi kuskuren shigowa dajin nan yau sai dai wasu baku ba.
Ɗaga Mandiya tayi da ta wullata sama, tayi nuni da hannunta wata iska ta riƙa wulwula mandiya tamkar yadda fanka ke gudu, tun Mandiya na ihun naiman taimako harta daina motsi.
Nuna ta tayi da hannu take wannan iskar ta tsaya nan Mandiya ta faɗo ƙasa tim!.
Darita ta kuma kecewa da ita, sai da tayi mai isarta sannan ta turbune fuska, "ku masu kunnen ƙashi, yau zakuga yadda zamu ƙare daku musamman kai, tana mai nuna Jafar da yatsa."
"Na haɗa maku tarko amma nasara ya akayi kuka tsallake shi, kunci ƴa'ƴan itatuwanda nina san da kunci to mutuwa zakuyi, kai kasa suka furta wata kalma wadda lokacin da zakuci wadda ita ta sanya kuka tsira da rayuwarku abinda kukaci bai kasheku ba, dan haka yanzu anan take zani raba gangar jikinku da numfashinku."
"Baki isa kiyi mana abinda Allah bai rubuta zai faru damuba, kamar yadda Allah ya tseratar damu a wanchan lokacin nan ma muna sa ran zai tseratar damu."
Kafin tayi wani yunƙuri cikin jarumta da dakewar zuciya Jafar ya ɗaga murya ya fara karanto Ayatul kursiyu, ita ma Basma ta ɗauka sukaci gaba dayi tare.
Ƙara Aljanin yake jikinshi na tsagewa ba shiri ya zama guguwa ya bi iska ya bace.
Tsagaita karatun sukayi, suka nufi inda Mandiya ke kwance shame_shame ba alamun tana motsi.......
____________________
Tunda Aljanin ya wurgar dasu, buguwar dasu kayi ta sanya su sumewa.
Rabson ne ya fara farkawa, a hankali ya matsa kusa da Audu yana bubbuga jikinshi har yayi nasarar ta dashi.
Hayaniyar da su Rabson keyi suna naiman sauran abokan tafiyarsu ita tayi nasarar tada su Biba suka tashi.
Sun duba ko ina amma babu abokan tafiyarsu.
Tashin hankalin da suka shiga bai misal tuwa musamman su Rabson da Salma.
Gajikin Audu sai ƙara rikiɗewa yake yana komawa green da baƙi.
Duk cikin babu wanda ya lura da halinda Audu ke ciki tashin hankalin da suke ciki yasa sunmata da komi.
Ƙara nitsawa suke cikin dajin suna naiman su Jafar, amma ina sai da suka gaji liƙis basu ga koda sawayen ƙafarsu ba.
Zama sukayi suna mai da numfashin wahala.
"Mu yanzu haka zamu ƙare acikin wahala ga rashin tabbas na zamu fita daga jejin nan, Daddy dana bi maganarka da banzo wurin bikin nan ba, Hajara ban yafe makiba duk ke kika jawoni cikin wannan bala'in, gashi nan ke kinyi aurenki nikuma gani nan cikin masifa."
Salma ta ƙarashe maganar ta rashe hawayen fuskarta.
Jugum_jugum suka yi kowa da abinda yake tunanin.
Yana yin wurin da suke zaune bakajin motsin komi sai sautin numfashinsu dake fita.
Motsin tafiya sukaji alamun ana nufo in da suke.
Miƙewa sukayi jikina kyarma Salma ta kama hannun Biba ta riƙe gam kamar wani zai rabasu.
Motsin takun naƙara kusanto su, suna ƙara shigema junansu.
Abinda idansu ya hasko masu ne ya sanyasu suman tsaye la66ansu na makyarkyata suka furta Garrrba!....
___________________
Da ƙyar suka samu Mandiya ta farka daga sumewar da tayi.
Tana tashi ta riƙa ƙwala ihu tana gasu nan gasunan zasu kasheni.
Saida Jafar ya dage mata da addu'a sannan ta dawo dai_dai.
Shawara suka yanke bazasu ƙara zaunawa wuri ɗaya ba sai dai in dare yayi su yada zango su kwana su ci gaba da tafiya in gari ya waye.
Tafiya suke baji ba gani ga yunwar da ta addabesu da ƙishirwa.
Sunyi tafiya mai nisa suka iso wani wuri mai yalwar bishiyoyi masu suffar dodanni, wasu sun rankwafa kamar zasu faɗi ga jikinsu babu ganye ko ɗaya, wasu kuma Suffar mutumce tsaye ya buɗe baki yana dariya,wata bishiyar in kayi mata kallo ɗaya bazaka kuma kallonta ba.
Tunda suka shigo wurin suka sha jinin jikinsu, ba su Basma kaɗai ba hatta Jafar sai da zuciyarshi ta buga ganin yanayin wurin, sai dai shi bai fiddo tsoranshi ba a fili, sa6anin su Basma ita da Mandiya da suka maƙale juna suna bin bayan Jafar.
Busassun ganyayen dake baje wurin suka riƙabi ta saman su suna takawa domin su fita daga wannan sarƙakiya.
Takun da suke da sauri yasanya duk busashshen ganyen da suka taka yake bada wata ƙara rumutss!
A hankali wata iska ta fara kaɗawa ganyayen wurin suka fara tashi sama.
Lokaci ɗaya wata guguwa ta turniƙe wurin, dale su Jafar suka duƙa tare da rufe idanunsu.
A hankali iskar ta fara lafawa, buɗe idanunsu sukayi dan ganin mike faruwa.
Bishiyoyin wurin suka gani da wasu jajayen idanun tamkar garwashin wuta, sun buɗe bakunan su suna wata irin dariya mai kama da kukan jarirai.
Tsoron da ya kamasu bai hanasu miƙewa su falfala da azababben guduba.
Duk bishiyar da suka gitta ƙoƙari take ta kawo masu Chafka.
Gudu suke ba ƙaƙƙautawa, suna ƙoƙarin tsira da rayuwarsu.
Wata bishiya ce tayi nasarar sanya jijiyarta ta chafko ƙafar Basma dake gudu.
Ihu take janyo ta bishiyar keyi da ƙarfi jikinta na karcewa da ganyayyakin dake ƙasa.
Ganin halin da Basma ke ciki ya sanya su jafar juyowa domin kawo mata agaji.
Gudu suke suna binta bishiyar na ƙara janta.
Jafar ne yayi nasarar danƙo sauyar bishiyar.
Ƙoƙarin kufcewa sauyar keyi amma ta kasa saboda ruƙon da yayi mata.
Da ƙyar da addu'ar dake bakinshi yayi nasarar karya sauyar.
Bata damu da ciwokan dake jikinta ba tana samu ya kwanceta ta miƙe sukaci gaba da gudu........
__________________
Garba da kamanninshi suka gama rikiɗewa jikinshi yayi fari fat, idanunshi baƙin ciki ya bace sun koma farare tas, ga farautanshi sun ƙara tsawo, duk ya zama abun tsoro.
Wasu yawu Salma da Rabson suka haɗiye atare kutt!.
Biba tunda tayi mashi kallo ɗaya tashiga karanto duk wata addu'a da ta zo mata.
Kafin su ankara Garba yayo kukan kura ya turmushe Rabson yana kokawar kai mashi cizo.
Wato wani bala'in inka ganshi tsoro barinka yake ka hau ƙoƙarin ceton rayuwarka.
Rabson ƙoƙarin yakice Garba yakeyi bakinshi na karanto addu'o'in da ya koya tunlokacin da Kaka ta sanyashi islamiyyah.
Inya fara karanto kul a'uzu kafin ya ida ya kamo Walfajir, ita ma ya saki, ya kamo
Wata,ranar Rabson har addu'ar shiga kewaye (Toilet) sai da yayi. 😂😂😂
Allah ya dubi Rabson ya bashi sa'ar wurgar da Garba ya kwasa a guje su Salma suka take mashi baya.
Miƙewa Garba yayi yabi bayansu da azababben gudu suka ƙara nausawa cikin jejin.
*COMMENT* ✅
*SHARE*✅
*MEEN@RT...✍🏻*
08133562798
[10/11, 10:29 PM] Meen@t A Yandoma: 💀 *BAƘAR TAFIYA* 💀
( *HORROR STORY* )
*BY MEEN@T A YANDOMA*
*MARUBUCIYAR FATALWA*
🌍 *MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION*🌍🖊️
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
*SALONSHI NA DABAN NE 💃🏼*
*ALLAH KAJIƘAN MAHAIFINA DA DUKKN MUSULMU BAKI ƊAYA KASA YA HUTA, KA KAI RAHAMA A KABARINSHI, ALLAH KA GAFARTA MASHI ZUNUBBABSHI, ALLAH YAJI ƘANKA ABBANA*
*MASOYA INA MATUƘAR GODIYA DA SOYAYYAR DA KUKE NUNAMA LITTAFIN NAN, ALLAH YA BARMU TARE, INA MATUƘAR GODE MAKU MASOYA A DUK INDA KUKE*
🤸🏻♀️🤸🏻♀️🤸🏻♀️
*ƳAN BAƘAR TAFIYA FANS COMMENT ƊIN YANA MATUƘAR TAFIYA DANI KUNA SANI NISHAƊI DA COMMENT ƊINKU, ALLAH YA BIYAKU INA MATUƘAR GODIYA*
🥰🥰🥰🥰
*WANNAN FEJIN SADAUKARWA NE GA DUK MASOYANA ADUK INDA KUKE, ALKHAIRIN ALLAH YA KAI MAKU, INA GODIYA*
*MASOYA INA MAI BADA HAƘURI BISAGA JINA DA KUKA YI KWANA BIYU SHURU, HAKAN YA FARUNE BISA GA MATSALAR NEPA DA MUKA SAMU, AMMA YANZU KOMI YA DAI_DAITA, INA GODIYA MASU TURO MANI SAƘONNIN DA KIRANA DAMA WAƊANDA BASU SAMU DAMABA INA MATUƘAR GODIYA,ALLAH YABAR ZUMUNCHI* 🥰🥰🥰🥰
___________________
*PAGE 12_13*
.......Gudu suke iyakar ƙarfin su, domin ceton rayuwarsu.
Basu ankara ba suka gansu gaban wani kogo, basu tsaya 6ata lokaci ba suka kutsa kai cikin kogon.
Cirko_cirko sukayi suna mai da numfashi saboda gudun da suka sha.
Sai lokacin suka lura da inda suke,
"Mun shiga ukku minike gani nan?, ina muka kawo kanmu."
Salma ta faɗa tana nuna masu ƙwarangwal ɗin mutane birjik wurin.
Kogon ko ina ka kai dubanka ƙwarangwal ɗin mutane ne birjik ga yana duk ta mamaye wurin.
Ido suka fara rarrabawa suna ƙara bin wurin da kallo.
"Kada tsintar kammu a wannan ya tada mana hankali, mutsaya mu naimi mafita mu dage da addu'a,kada mu kuskura mu rabu da junan mu."
Biba ta faɗa tana binsu Rabson da kallo.
"Eh haka ya kamata mu riƙa tafiya tare da junanmu, kada muyi kuskuren rabuwa da ƴan uwanmu."
Salma ta faɗa muryar ta na kyarma tana ƙara shigewa jikin Biba.
"Muje mu naimi abinci nidai jina nike cikina kamar an hura wuta."
Rabson ya miƙe tare da yin gaba.
Bayanshi suka bi tare da nausawa ciki kogon.
Tunda suka fara tafiya Basu gamu da komi ba sai ƙasusuwan mutane da yanar da ta tare hanyar sai sun ɗebe ta da hannunsu suke samun hanyar wucewa.
Tirjiya suka ja ganin
Mutum tsaye.
Salma cikin in iyna ta furta da..da..daddyy.....
____________________
Sunyi gudu har sun galabaita.
Tsayawa sukayi ganin sun baro wurin duhuwar, sun bullo wani wuri mai yawan kwazazzabai ruwa na wucewa a hankali ta ƙasansu.
Yanayin wurin gwanin ban sha'awa.
Nan suka tsaya suka gabatar da sallolin da ake binsu.
Cikin ruwan da ke wucewa suka shiga suka ci gaba da tafiya, suna jan ƙafafu a hankali.
Jafar ne gaba sai su Basma a bayanshi.
Mandiya ji tayi kamar an tsunkule ta a ƙafa, a zabure