Showing 3001 words to 6000 words out of 28291 words
ba nan Mandiya ta taso mata kamar zasu bigi juna, sai da Garba yace duk wadda ta ƙara masu hayaniya zasu fiddata daga ɗakin sai dai ta kwana wajen.
Nan Salma tayi zuciya ta sauko ƙasa ta baza ɗan figaggen gyalenta ta kwanta sama.
Bayan kowa ya kwanta wasu sunyi addu'a wasu kuma ko uho.
Cikin bacci Salma taji kamar ana lasar mata ƙafa, afirgi ce ta buɗe idanunta ta sauke su kan wata irin ƙatuwar mage baƙaƙirin bakinta wasu zara_zaran haƙora jini na ɗiga daga bakinta ga wasu irin idanu manya_manya masu ban tsoro, wata mahaukaciyar ƙara ta ƙwala da tayi sanadiyyar farkawar kowa daga bacci daya ɗauke su.
Ganin irin halittar magen ba matan kaɗai ba har mazan sai da hantar cikinsu ta kaɗa.
Garba kisane yayi ƙarfin halin shaƙe wuyan magen.
"Kuyi sauri ku buɗe mani ɗakin nan."
Jafar ne yayi saurin buɗe ɗakin, Garba ya fita da guda magen na hannunshi a shage.
Sai dai kash! Daya san abinda zai iske a wajen bazaiyi gigin fitaba.
Kan Magen ya riƙa bugawa da ƙasa amma ko gezau batayi ba sai ma hannunshi dayaji kamar an daka mashi kaifaffar wuƙa, ihu ya ƙwala ya wurgar da magen yana duba hannun yaga ashe cizone ta sakar mashi a hannu, take jini ya hau zuba ba ƙaƙƙautawa, nufar hanyar gidan yayi zai shige, juyowar da zai yi yaga abinda ya kusa sanadiyyar tsayawar numfashin shi.
Magen nan ce ta rikiɗe ta koma wani basa muden Aljani jikinshi duk jini bakinshi wasu haƙora ne zaƙo_zaƙo irin na zombie, juyawa Garba kisa yayi da nufin komawa gidan horror ɗin yayo kanshi yana ƙoƙarin cizon Garba.
A tsorace Garba ya nufi ɗakin zai shige yana ihun su taimakeshi, ganin halin da suke ciki yasa su buɗe ɗakin, yana gabda shigewa ɗakin aljanin na kamo ƙafarshi mutanen daki hannuwan Garba suka kama domin ceton rayuwarshi, da kyar suka jawo Garba ɗakin suka maida ƙyaure suka rufe.
Nura ne ya lura Garba ba alamun numfashi a tare dashi, "kai Oga fa yabar numfashi ku duba ƙafarshi ga wani cizon nan ya ƙara samu."
Rigar jikin shi suka keta suka ɗaure mashi ciwon, suna yi mashi firfita.
"Yau ni Rabi'u nashiga uku na lalace, wayyo kakata ƙila shikenan mutuwa ke kirana ita ta raboni da gida."
Kowa ka kalla a ɗakin hankalinshi a tashe yake, yana tunanin makomarsu.
A hankali Garba ya buɗe adanunshi da suka yi mashi nauyi, ya sauke su ga ƙafarshi dayaga an ɗaure mashi.
Kwance wurin yayi sai dai abun mamaki ciwon ya warke sai dai wuri rauni yayi wani irin baƙi wasu jijiyoyi sun fito sun miƙe har wajen cinyarshi, kamar yadda jini ke gudana haka wannan baƙin abun ke gudana ajikin Garba kisa.
Sannu suka shiga yi mashi, baccin da basuyi ba kenan har gari ya waye.
Bayan sunyi sallah, nan suka shiga tunani abinda zasu samacikin su, kowa akayima maganar yafito su tafi naiman abinda zasu sama cikinsu sai ya noƙe yaki fitowa.
Daga ƙarshe dai Jafar da Biba suka ce su zasu fita su nemo.
Tunda suka fara tafiya basu samu komi ba ko bishiyoyin da zasu ciri ƴa'ƴan suci basu samu ba.
Ƙorama suka iske ruwa na gudana , tsayawa suka yi suka sha ruwan suka ɗibar ma sauran wanda zasu sha.
Sunyi tafiya kaɗan suka fara hango wata bishiyar kwaba a gabansu tsayawa sukayi.
"Kin ga dai tun ɗazu bamu samu komi ba duk yawo da mukasha, yanzu ni zani hau in tsinko ke kiriƙa ɗaukewa."
Haka kuwa akayi sun ɗibi mai yawa suka nufi hanyar komawa wurin abokan tafiyarsu.
Kowa yayi murna da samun abinda zasu sa ga bakinsu banda Salma da ta ce ita tafi ƙarfin cin gwaba, babu wanda ya matsa mata taci cikinta ne inma bataci ba.
Shawara suka yanke su ƙara kwana nan in Garba ya ji sauƙi sai su cigaba da tafiyar.
Dare yayi sosai kowa ka gani yasha jinin jikinshi yana tunanin abinda zai faru.
Garba tunda lamarin nan ya faru jikinshi ke rikiɗewa yana komawa baƙi, amma bai sanar da kowa ba.
Zaune yake ya sadda kanshi ƙasa kamar mai bacci, lura abokan tafiyar sukayi kamar Garba yabar motsi, audu ne yayo kanshi da sauri dan ganin halinda yake ciki, ya isowa jikin Garba na ida rikiɗewa ya koma green da baƙi.
Duƙawa audu yayi dan ganin mike faruwa da Garba.
Shak’arda Garba yayi ma audu gwarama yasanya ƴan ɗakin fara iface_iface ganin yadda kaman nin Garba suka chanza.
Rabson guy tsabar firgici sulalewa ƙasa yayi ya sume.
Garba ya tsunshi da suka zama zaƙo_zaƙo ya dakama audu su a wuya ya wurgar dashi ya bugu da bangon ɗakin ya faɗo ƙasa ba alamun numfashi atare dashi.
Garba juyawa yayi yai kan Salma da tayi mutuwar tsaye hada fitsarin dole yai wani irin kukan kura wanda seda ilahirin dajin yayi amsa kuwwar da ’ya’yan cikin kowa suka kad’a.......
Sake kallon Salma yayi akaro na biyu yayin da y..........✍🏻
💀💀💀💀💀
🤸🏻♀️🤸🏻♀️🤸🏻♀️🤸🏻♀️🤸🏻♀️🤪
*COMMENT* ✅
*SHARE* ✅
*MEEN@RT...✍🏻*
08133562798
[10/11, 10:29 PM] Meen@t A Yandoma: 💀 *BAƘAR TAFIYA* 💀
( *HORROR STORY* )
*BY MEEN@T A YANDOMA*
*MARUBUCIYAR FATALWA*
🌍 *MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION*🌍🖊️
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
*SALONSHI NA DABAN NE 💃🏼*
*ALLAH KAJIƘAN MAHAIFINA DA DUKKN MUSULMU BAKI ƊAYA KASA YA HUTA, KA KAI RAHAMA A KABARINSHI, ALLAH KA GAFARTA MASHI ZUNUBBABSHI, ALLAH YAJI ƘANKA ABBANA*
*MASOYA INA MATUƘAR GODIYA DA SOYAYYAR DA KUKE NUNAMA LITTAFIN NAN, ALLAH YA BARMU TARE, INA MATUƘAR GODE MAKU MASOYA A DUK INDA KUKE*
🤸🏻♀️🤸🏻♀️🤸🏻♀️
*ƳAN BAƘAR TAFIYA FANS COMMENT ƊIN YANA MATUƘAR TAFIYA DANI KUNA SANI NISHAƊI DA COMMENT ƊINKU, ALLAH YA BIYAKU INA MATUƘAR GODIYA*
🥰🥰🥰🥰
____________________
*PAGE 6_7*
......Tamkar yunwa taccen zaki haka Garba yayo kan Salma gadan_gadan, tsabar tsoro ko motsi takasayi ta rufe ido tana sauraren mutuwar data nufota.
Ganin halin da ake ciki yasa Jafar yin kabbara ya ya ɗauki wani katako yayo kan Garba kisa gadan_gadan, sai dai kafin ya iso Garba yayi nasarar shago Salma ya fara gama kanta da bango, tsabar azaba nan take ta sume.
Ya isa isowa daf da Garba yayi kabbara da ƙarfi ya ƙwaɗama Garba katakon nan a tsakiyar kan shi.
Take Garba yayi wata irin kururuwa ya faɗi ƙasa.
Salma gwara mata kai da bango ta sume batare da tasan mike faruwa ba.
Biba da ke labe bayan kujera tana addu'a tana hawaye gitowa tayi jin abun ya lafa, Ganin Garba da tayi kwace ƙasa Kanshi jini na malala nan hankalinta ya ƙara tashi, abun mamaki jikin Garba lokaci ɗaya yayi wani irin fari fat! Tamkar babu jini jikinshi ko ɗigo, kallon_kallo Biba da Jafar suka hau yima juna.
"Biba yanzu ba lokacin kuka bane musamu mafita, ni fa gani nike mu haƙura da dajin nan mu zauna cikin gidan nan kawai in Allah yayi zamu fita shi zai kawo mana ɗauki da kanshi, soboda faɗar Manzon Allah Sallallahu alaihi wasallam daya ce in annoba ta samu gari to naciki su zauna a garinsu na waje kuma kar su shigo garin."
"Nima ina da wannan tunanin Amma yanzu abinda ya kamata mu samu abokan tafiyarmu su farfaɗo sannan muyi gaggawar rabuwa da gawar nan, kaga fa yadda ta koma, ina tunanin barinta tare damu kamar wani haɗari ne babba."
"Maganarki haka take, yanzu bara mu fara shafa masu ruwa su farfado mujita bakunan su."
Wurin Audu gwarama suka fara zuwa sunyi sa'a suna shafa mashi ruwa a fuska ya ja a jiyar zuciya yana mai shafa wuyanshi dake mashi tsananin zafi, shi ma dai_dai in da Garba ya yakusheshi wurin ya fara green da baƙi.
Sannu sula riƙa jero mashi yana amsawa.
Wurin Salma suka matsa ita ma tana nan kwance tamkar gawa.
Jafar dubar Biba yayi yana mata magana a hankali yadda in ba kusa kake dashi ba bazakaji mitake fada ba.
"Biba Salma kinga mace ce bai kamata in tabata ba ke yaka mata ki fara duba inda Garba ya buga mata kai ki kiyi addu'a nasan a firgice zata tashi saboda halin firgicin da ta shiga,sannan ki shafa mata ruwa a fuska."
A hankali ta fara buɗe idanunta ta sauke su kan Biba dake tsugune kanta.
"Nashiga ukku ni Salma! Yanzu shikenan nima horror zani zama, wayyoh daddy na danabi shawararka da yanzu ina gida zamana, yanzu gashi na kawo kai na ga halaka."
"Aa Salma Garba bai cijeki ba, ya dai bugaki da bango yayi sanadiyyar sumanki."
Tamkar wata ƙaramar yarinya haka Salma ta maƙale jikin Biba tana kuka, 😂😂 niko nacr salma ina nuna isar da wulaƙanta muta ne da nuna masu ƙyama.
"Addu'a zakiyi ba kuka ba Salma, a wannan halin da muke ciki addu'a kaɗai ce magani, kuka bazai amfane mu da komi ba."
Biba ta faɗa tana ɗora hannayenta a kafaɗar Salma.
Audu lura yayi da halin da Ogansu ke ciki.
Da gudu ya rugo ya rungume Garba yana mai fashewa da wani irin kuka, "Oga shikenan katafi ka barmu cikin wannan halin, Oga ji nike dama nine na mutu na huta ba kai ba, haka muma zamuyi ta mutuwa ana kashemu ɗaya bayan ɗaya, ina nadamar yin Baƙar tafiyar nan yanzu nasan nayi bankwana da kakata."
Kukan dayaci ƙarfinshi yasa maganarshi sarƙewa.
Jafar ya iso wurin Garba ya rabashi da gawar yana bashi haƙuri, addu'a ce kaɗai zata kawo masu mafita.
Lura sukayi da abokan tafiyarsu babu Mandiya da Nura shila da Basma.
Sun bincike ko ina amma basu gansu ba.
Ɗakin farko sukayi shawarar buɗewa ko ciki suka buya.
Sai da suka haɗa ƙarfi wurin buɗe ɗakin, Ɗakine mai yalwar faɗi ba laifi, sai dai tsananin duhun ɗakin ya hana ka ga mike ciki, motsin da suka jiyo ne ya sasu juyowa a razane, Nura shila da Basma suka gani ƙarƙashin wani bencin katako sun boye ganin su yasa suke ƙoƙarin fitowa.
Bayan fitowarsu Biba ta fara magana, "Sanin haɗarin da muke ciki yasa daga yanzu ko wani bala'i ya samu ɗan uwanmu kada wanda ya ƙara ƙoƙarin guduwa ya rabu da sauran."
Kowa yayi na'am da wannan shawarar
Ɗayan ɗakin suka buɗe, buɗewarshi tayi dai_dai da bugawar zuciyoyinsu kallon_kallo suka fara yima juna, wannan ɗakin yasha banban da saura, saboda shi wani abun mamaki babu duhu acikinshi, kayan wasane na yara birjik aciki, su kansu kayan wasan in ka kallesu sau ɗaya bazaka ƙara ba saboda abin tsore, daga ɗiyar robar da aka cirema hannu ɗaya tana hawayen jini sai wadda ta cire kanta ta riƙe a hannu tana murmushi haƙoranta duk jini, wadda tafi masifar tada masu hankali wata ɗiyar babyce girmanta ya kai na jariri, zaune take jikinta jar riga ce hanta gashi ya baje ta ko ina baka ganin ko fuskarta, ga wasu irin wuƙaƙe a hannunta duk jini ya bata su, kallo ɗaya zakayi mata ka ɗauke kanka.
Wani yawu Rabson guy ya haɗiye ƙut! Da yayi sanadiyyar juyowar abokan tafiyarshi, sun naimi Mandiya lungu da saƙo sun rasa, motsi suka jiyo bayan ƙyaure, ƙin leƙawa sukayi kowa jininshi kan akai fa saboda tsoron dake ɗawainiya dasu.
Jafar ne yayi ƙarfin halin yawo ƙyauren, tsaye take tayi labo bayan ƙyauren jin an jawo ƙyaure yasa ta fara junduma ihu, "wayyoni Mandiyar uwar daba yau nakawo kai na ga halaka, Magaji kin cuce ni da kika bani shawarar zuwa garin Kaika zo! Ashe ajali ke kirana a wannan BAƘAR TAFIYAR, nashiga ukku na balbalce."
"Buɗe idonki ki gani mune fa abokan tafiyarki."
Jafar ya faɗa yana mai bata hanyar wucewa.
Idanu ta buɗe danjin muryar abokin tafiyarsu.
Shawara suka yanke suyima gawar Garba sallah su binneta.
Ruwan da ya rage masu suka yi alwallar dasu, sun gama sallar sun fara gina zasu binneshi wani baƙin hayaƙi ya bayyana ya ja gawar Garba suka bace.
Nan fa suka ɗiba aguje suka koma gidan suka rufe masu kuka nayi masu addu'a nayi.
Basma kuka take tana sambato ita kaɗai, "Allah sarki masoyina kuma mijina habibina, dana bi shawararka da yanzu ina gida amma haka na nace dole sai naje bikin ta gaban goshi, Allah ya isa tsakanina dake ta gaban goshi ke kikai ta turani ina ma habib rashin mutumci, yanzu gashi nan na baro ɗana mijina yana fUshi dani nasan mutuwa zaniyi."
Babu wanda ya rarrasheta koya bata hakuri domin kowa ta kanshi yake.
Nan suka faɗama sauran abokan tafiyarsu shawarar da suka yanke ta barin wannan gidan su ƙara gaba, amma ba haka ya kamata suyi ba, kamata yayi su zauna suga yadda zata kasance.
Wasu sunyi na'am wasu kuma sun bada shawarar abar gidan, sun yanke shawarar zasu bar gidan in gari ya waye.
Duhun dare ya fara kowa hankalinshi ya ƙara dugumzuma, kingin kwaibar da ta rage masu suka raba suka fara sha, Salmar tun kafin azo kanta ta warci biyu ta faraci.
Dare yayi sosai dajin babu abinda kakeji sai kuka tsuntsaye da wani irin iska mai bada wani firgitaccen sauti in ya haɗu da kukan tsuntsaye.
Mandiya, Basma, Biba da Salma yau gado ɗaya suka haye ba zancen nuna ƙyama yau Salma.
Mazan suma wuri ɗaya suka dunkule.
Bacci ma in kaga kana yin shi to baka shiga wani bala'in ba kokoma sai dai in bacci barawo ya sace ka.
Duka ɗakin kowa manne yake da ɗan uwanshi,idosu biyu sun kasa bacci gudun abinda zai biyo baya.
A hankali tagogin ɗakin (Window) suka fara buɗewa da kansu, jikake kit!_kit! Taga ta bude da kanta, karar da sukaji ce ta maido hankalinsu ga abinda ke faruwa.
Dirowa sukayi daga gadon suka cibre wuri ɗaya jikinsu na kyarma, duk wannan halin da suke ciki addu'a ce bakin Biba sabanin su Salma da suka fara kuka.
Ƙofofin na ida buɗewa wani farin hayaƙi ya fara shigowa yana dunƙulewa wuri ɗaya.
Yana gama haɗewa wuri ɗaya wata irin halitta Mai suffar kare ta bayyan, jikinta ko ina hannuwa ne idonta guda ɗaya ne a tsakiyar goshi, ga bakinta wagege da haƙora masu matuƙar tsini.
Dariya halittar ta kece da ita wadda ta haddasa ma ɗakin girgiza.
"Kunyi kuskure bil adama masu taurin kai da gadara, yau kwananku ya ƙare, a sannu zaku baƙunci lahira."
Jafar yayi ƙarfin halin fara magana.
"Ƙarya kike yake wannan la'anannar halitta, ke baki isa ki kashemu ba sai dai in kwanan mu ya ƙare ubangiji ya rabuta zamu mutu yau, amma badai ke ba."
"Hahaha! Gaskiya wannan bil adam jarumtarka ta burgeni, amma kayi kuskuren faɗa da ƴar tsito ƙaramar aljanu kuma shaiɗaniyar cikinsu, yanzu zani shanye jinin jikinka inyi gunduwa_gunduwa da naman jikinka."
Tana rufe baki tayo kan Jafar da mugun nufi a cikin zuciyarta.
Abun mamaki kafin ta ida isa wurinshi sanadiyyar addu'ar da yake ya bace ma ganinta nan ta hau dube_dube amma babu shi babu alamunshi.
Ganin haka ya sanya ta wawuro ƙafar Basma, ihu ta hauyi itama ta jawo ƙafar Rabson guy, shima ci gaba da ihu yayi "wayyoh kakata wayyoh ɗan bunsuruna yau nayi bankwana daku, mutuwata ta iso." cikin zafin nama shima ya damƙo ƙafar Salma, ita ma bata tsaya bata lokaci ba ta jawo ƙafar Audu, Nura shi ya riƙo hannun yana ƙokarin cetonsu.
Ganin halin da ake ciki ya sanya Jafar shammatar Aljanar yayi tsalle ya bankata ɗaki ya mai do ƙyaure ya rufe.
Gidan suka buɗe kowa yayi ta kanshi.
Gudu suke wanda su kansu in akace zasu iya yin shi bazasu yarda ba.
Gudune gudun yada ƙanin wani kowa ta kanshi yake.
duk gudun da suke a haɗe suke ɗayan su bai yarda ya rabu da ɗan uwanshi ba.
Gudu kawai suke amma basu san inda suke nufa ba, har sai da asuba tayi sannan suka zube suna mai da wani wahalallen numfashi.
Wata azababbiyar ƙishirwa ce ta taso masu, sanadiyyar gudun da suka sha, shawara suka yanke in safiya ta idayi sunemi ruwan sha.
Safiya nayi suka ƙara nausawa cikin dajin naiman ruwan.
A hankali jikin Audu gwarama yanata komawa green da baƙi, amma babu wanda yasanar halin dayake ciki.
Wani irin ruwa ne mai mugun fadi da yalwa gashi wucewa yake da mugun guda, suka iske a gabansu.
Nura har gudu yake ya isa ga ruwan ya sha saboda ƙishin daya addabeshi.
"Aa Nura kada ka sha ruwan nan ban yarda dashi ba." Jafar ya faɗa yana ƙoƙarin tsaida Nura.
"Ya zaka hanani in sha bayan kasan babu abinda muke buƙata yanzu kamar ruwa." ida gangarawa yayi cikin ruwan ya duƙa ya kam fato da hannuwanshi zai kai baki.
Wasu dogayen hannuwa ne suka bayyana suka, harya juyo zai fita daga ruwan hannuna nan suka fizgoshi suka nitsar dashi cikin ruwan yayi gaba dashi.
Tsabar tashin hankali su Jafar ƙara nausawa cikin jejin suka yi da azababben gudu.
*COMMENT* ✅
*SHARE* ✅
*MEEN@RT...✍🏻*
08133562798
[10/11, 10:29 PM] Meen@t A Yandoma: 💀 *BAƘAR TAFIYA* 💀
( *HORROR STORY* )
*BY MEEN@T A YANDOMA*
*MARUBUCIYAR FATALWA*
🌍 *MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION*🌍🖊️
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
*SALONSHI NA DABAN NE 💃🏼*
*ALLAH KAJIƘAN MAHAIFINA DA DUKKN MUSULMU BAKI ƊAYA KASA YA HUTA, KA KAI RAHAMA A KABARINSHI, ALLAH KA GAFARTA MASHI ZUNUBBABSHI, ALLAH YAJI ƘANKA ABBANA*
*MASOYA INA MATUƘAR GODIYA DA SOYAYYAR DA KUKE NUNAMA LITTAFIN NAN, ALLAH YA BARMU TARE, INA MATUƘAR GODE MAKU MASOYA A DUK INDA KUKE*
🤸🏻♀️🤸🏻♀️🤸🏻♀️
*ƳAN BAƘAR TAFIYA FANS COMMENT ƊIN YANA MATUƘAR TAFIYA DANI KUNA SANI NISHAƊI DA COMMENT ƊINKU, ALLAH YA BIYAKU INA MATUƘAR GODIYA*
🥰🥰🥰🥰
____________________
*PAGE 8_9*
..........Gusu ba tare da sanin in da suke nufa.
Iya gajiya sun gaji, tsayawa sukayi suna mai da numfashi, su Mandiya kuka kawai take tan ƙara tsinema magajiya da tun farko i ta ce sana diyyarta shiga karuwanci.
Su Rabson guy abun ba magana zama yayi ya miƙe ƙafafu shame_shame yana mai da numfashi, yana jin wata sabuwar nadama nashigar shi, da dana sanin bijirewa maganar Kaka.
Ranar nan suka wuni, ga ƙishirwa ka yunwa, sallah ma da suka auna lokaci aransu suka ga yayi nan suka yi taimama su kayita nan.
Ƙara nausawa cikin dajin suka yi naiman ko ƴa'ƴan itatuwa ne su sanyama cikinsu.
Sunyi tafiya mai nisa suka isa wani wuri mai matuƙar kyau, korayen flawer ne ko ina ga wata ƴar ƙorama ruwa na gudana cikin ta, bishiyoyin kayan marmari ne duk in da ka duba sunyi bul_bul gwanin sha'awa.
Kallon_kallo suka hauyi ma junan su, suna mamakin wannan Baƙin daji tunda suka shigoshi basu taba ganin wuri mai kyau irin wannan ba, gashi dai a halin da suke ciki babu abunda suke matuƙar buƙata kamar ruwa da abinci, sai gashi sun samu amma suna shakkar cin shi.
Jafar lura yayi basu yadda da wurin ba, dan haka ya fuskan ce su ya fara masu jawabi;
"A halin da muke ciki yanzu bamuda mafita face mu dogara da Allah muyi Basmala muci abubuwan da muka samu, Wamanyatawakkalu Alallah! Fahuwa hasbuhu."
Har cikin zuciyoyinsu sunyi na'am da maganar Jafar.
Ida isa sukayi wurin bishiyar Mangwaro Jafar na tsinkowa Audu na tsincewa.
A haka sun tara kayan marar mari mabanbanta masu yawan gaske.
Zama sukayi zasu fara sha koya bakinshi dauke da Basmala.
Alhamdulillah sun sha sun ƙoshi babu abinda ya faru dasu.
Nan suka yada zango suna hutawa, Basma sai yanzu