Showing 9001 words to 12000 words out of 28291 words
ta yi tsalle ta ruƙunƙume Basma tana.
"Nashi ga ukku na lalace miye ya cijeni a ƙafa?, wayyo uwar daba da magajiya Allah ya tsinemaku albarka, duk ku kuka jefani ciki halinda nike ciki."
"Ke ki sakini ya kike ƙoƙarin kayar dani, dake zaniji ko da yunwar dake ɗawainiya dani."
Basma ta yakice Mandiya ajikinta.
"Ya isa! Ku fahimci halinda muke ciki, ku daina yawan hayaniya kuna ɗaga muryoyinku hakan zai iya janyo mana wata matsalar."
Cigaba da tafiya sukayi.
Tim! Sukaji ƙarar faɗuwar Mandiya cikin ruwan.
Janta ake ba ƙaƙƙautawa ana gwarata da dowatsun wurin.
Ganin wanda ke janta ya sanya su haɗiye wani yawun tashin hankali.
Nura shila suka gani kamanninshi sun sauya jikinshi yayi fari sol ya koma suffar horror yana jan ƙafar Mandiya.
Ihu take tana kiran sunayensu, su taimaka mata.
Nura nasarar ida janyo Mandiya yayi, ya dasa mata haƙoranshi a ƙafa.
Wata irin kururuwa tayi jin azababben cizon da Nura yayi mata a ƙafa.
Ganin halinda Mandiya ke ciki ya sanya Jafar da Basma fidda tsoron da ke cikin ransu, Basma ta kamo hannuwanta tana janyota tana kuka.
wani dutsi Jafar ya ɗauka ya bugama Nura a tsakiyar baya.
Wata ƙara ya ƙwala da tayi sanadiyyar sanya wurin amsa kuwwa, tsuntsayen dake wurin suka yi sama.
Hannun Mandiya Basma ta kama suka yi cikin dajin da azababben gudu.
Nura ganin su Basma sun Tsere mashi ya ya sanyashi bin bayansu shima.........
____________________
"Daddy kai nike gani ko idanu nane ke yi mani gizo?."
"Nine Salma, Mahaifiyarki ta sanar dani abinda ya faru shiyasa na biyo bayanki nazo in fitar dake daga jejin nan, Zo muje kinji Mamana."
"Aa Salma kada ki yarda dashi, wsnnan ba Mahaifinki bane, yaudara ce kawai."
Biba ta faɗa tare da kamo hannun Salma tana ƙoƙarin hanata ida isa wurin Babanta.
"Dallah malama rabu dani, dan kinga ba mahaifinki bane yazo tafiya dake shiyasa kike ƙoƙarin hanani isa gareshi, ninasan dama zai zo da bataliyar sojoji ya fitar dani daga wannan jejin ."
Fizge hannunta tayi tare da rugawa ta rungume daddyn ta.
Wata Mahaukaciyar dariya taji an barke da ita, wadda ta haddasama Kogon girgiza.
Tuni su Rabson da Audu gwarama suka haɗe wuri ɗaya suna sallallami.
Biba baiwar Allah idanunta ta rufe taci gaba da kwararo duk addu'ar da tazo bakinta.
Salma jin Daddyn ta da ta rungume ne ke wannan dariyar ya sanya ta ɗagowa a matuƙar tsorace.
Ja tayi da baya ganin ya chanza suffa ya koma wannan tsohuwar da ta mara lokacin da zata shiga mota.
Cikin kakkausar murya tsohuwar ta fara magana.
"Ina kuma zakije ɗiyata?, ko har kin manta marin da kikayi mani?, bai kamata kiji tsoro tun yanzu ba."
Zubewa Salma tayi bisa guiyoyinta ta fara ba tsohuwar haƙuri.
Ƙara tun tsurewa da dariya tayi."Dole ki ɗauki hukuncin abinda kika aikata kigane wulaƙanci ba abu bane mai kyau."
Hannu ɗaya tasa ta suri Salma ta buga da ƙasa kanta ya bugu da wani icce take goshinta ya haye yayi suntum, jini yaci gaba da zuwa.
Hayaƙi Aljanar ta koma ta shiga jikin Kwarangwal ɗin dake wurin take suka fara motsi suna miƙewa.
Salma miƙewa tayi da ƙyar ga zafin da goshinta ke mata ga lebenta daya haye yayi suntum ga hannunta da ta faɗa samanshi yana mata azababben raɗaɗi.
Ganin kwarangwal ɗin sunyo kansu, yasa suka fara ja da baya tsabar firgici kasa gudu sukayi.
Rabson cikin daga murya yace.
"Kuna gani ana naiman hallaka mu amma kunyi tsaye sororo, toni nayi gaba saikun taho."
Zabgawa yayi da gudu ko waiwayowa bayayi.
Suna gani yayi gaba suka take mashi baya.
Kwarangwal ɗin suka bi bayansu a guje.
Gudu suke suna waiwayen kwarangwal ɗin.
Sunyi nasarar fita daga cikin kogon sukaci gaba da gudu.
Turjiya suka yi ganin wani wawakeken tsauni da suka tsinci kansu samanshi,ƙasan tsaunin ruwane ke gudu.
Basu da wata mafita face su dira cikin ruwan nan.
Juyawa sukayi gani sukayi kwarangwal suna ƙara kusanto inda suke baki buɗe suna wata irin kuwwa mai razanar da rihin bil adam.
Rabson cikin kyarmar murya yace dasu Audu.
"Nidai da in tsaya waɗan nan halinttun su kasheni a banza ƙara in faɗa ruwan nan."
Ƙafar wandonshi irin na gayun nan wanda ake kira Inna tayani cirewa ya duƙa ya nannaɗe ya nufi ramin yana nayi gaba sai kun iso.
Tsalle yayi ya dira ƙasan ramin, suma sauran take mashi baya sukayi suka tsunduma ƙasan ramin.
Lokacin da kwarangwal ɗin suka iso, har sun ɗira ƙasan.
Lokacin da suka dira cikin ruwan wani rin ruwane mai matuƙar yawa ga zurfi, iyo suka ci gaba dayi amma babu alamun zasu kawo ƙarshen ruwan, gilmawar wani baƙin abu suka gani ya wuce ta gabansu.
Tsananta yin iyon sukayi domin iskar da suka yi guzurinta ta kusa ƙaremasu.
Abun mamaki kowanensu cikin kwarewa yake iyo tamkar dama chan sun saba.
Rigar Audu akaja tareda yin ƙasan ruwan dashi, cikin kwarewa Rabson yayi saurin ruƙoshi yayo sama dashi.
Da kyar suka iso bakin gabar ruwan kowanensu yana jan dogon numfashi.
Basu bar wurin ba nan suka gabatar da sallolin da ake binsu, zama sukayi suna hutawa, domin a halin da suke ciki baza su iyacigaba da tafiya ba.
Jikin Audu ne ya ida zama green da baƙi, ga wasu iri jijiyoyi baƙaƙe da su ka bayyana a fuskarshi.
Kamar an ɗauje shi anyi jifa dashi haka aka wullar dashi gefe ko numfashi babu a tare dashi.
Cikin firgici su Biba sukayi kanshi suka tsaya chirki_chirko.
A hankali kamanninshi suka fara sauyawa yana komawa Horror.
Ganin haka ya sanya su Biba ja da baya cikin tsananin tsoro.
Tamkar an harba kibiya daga cikin kwari haka Audu yayi wata alkafira ya dira gabansu Rabson.......
*KU ƘARA DA HAƘURI, MATSALAR NEPA MUKA SAMU, AMMA YANZU ALHAMDULILLAH, MASOYA INA GODIYA NAGA SAƘONNINKU DA KIRANA DA KUKA RIƘAYI KUJI LAFIYA, INA MATUƘAR GODIYA ALLAH YA BARMU TARE* 🤗🥰🥰
*COMMENT ✅*
*SHARE ✅*
*MEEN@RT...✍🏻*
08133562798
[10/11, 10:29 PM] Meen@t A Yandoma: 💀 *BAƘAR TAFIYA* 💀
( *HORROR STORY* )
*BY MEEN@T A YANDOMA*
*MARUBUCIYAR FATALWA*
🌍 *MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION*🌍🖊️
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
*SALONSHI NA DABAN NE 💃🏼*
*ALLAH KAJIƘAN MAHAIFINA DA DUKKN MUSULMU BAKI ƊAYA KASA YA HUTA, KA KAI RAHAMA A KABARINSHI, ALLAH KA GAFARTA MASHI ZUNUBBABSHI, ALLAH YAJI ƘANKA ABBANA*
*MASOYA INA MATUƘAR GODIYA DA SOYAYYAR DA KUKE NUNAMA LITTAFIN NAN, ALLAH YA BARMU TARE, INA MATUƘAR GODE MAKU MASOYA A DUK INDA KUKE*
🤸🏻♀️🤸🏻♀️🤸🏻♀️
*ƳAN BAƘAR TAFIYA FANS COMMENT ƊIN YANA MATUƘAR TAFIYA DANI KUNA SANI NISHAƊI DA COMMENT ƊINKU, ALLAH YA BIYAKU INA MATUƘAR GODIYA*
🥰🥰🥰🥰
*WANNAN FEJIN SADAUKARWA NE GA DUK MASOYANA ADUK INDA KUKE, ALKHAIRIN ALLAH YA KAI MAKU, INA GODIYA*
*MASOYA INA MAI BADA HAƘURI BISAGA JINA DA KUKA YI KWANA BIYU SHURU, HAKAN YA FARUNE BISA GA MATSALAR NEPA DA MUKA SAMU, AMMA YANZU KOMI YA DAI_DAITA, INA GODIYA MASU TURO MANI SAƘONNIN DA KIRANA DAMA WAƊANDA BASU SAMU DAMABA INA MATUƘAR GODIYA,ALLAH YABAR ZUMUNCHI* 🥰🥰🥰🥰
___________________
*PAGE 14_15*
............Ganin sun tserema Nura yasan ya Mandiya faɗuwa ƙasa tana maida numfashi.
Dafe ƙafarta dake yi mata raɗaɗi tayi.
"Wayyoh ni Mandiya na bani na lalace, yanzu shikenan nima Horror zani zama."
Sauran maganar maƙalewa tayi saboda kukan da yaci ƙarfin ta.
Matsowa sukayi fuskokinsu da matuƙar tausayi suna mata sannu.
Ƙafar suka kallah, abin mamaki jinin dake zuba ya tsaya, wurin yayi wani irin green da baƙi.
Su kansu sun san nan da lokaci ƙanƙani itama zata zama Horror.
Allah sarki Jafar duk halin tsananin da suke ciki zuciyarshi tana wurin Biba kullum cikin tunaninta yake zuciyarshi tana hasko mashi hoton fuskar Biba.
Basma ta taimaka ma Mandiya sukaci gaba da tafiya har duhu ya farayi.
Ƙarƙashin wata itaciyar Kuka suka yada zango, daji Jafar ya shiga ya samo masu ƴa'ƴan itanuwa sukaci.
Fuskokin su duk cikin tashin hankali suke, kowa da irin tunanin dake cikin zuciyarshi.
Motsin da sukajine ya sanya su dawowa daga duniyar tunanin da suke.
Tamkar walƙiya haka sukaga wani farin abu ya gilma ta gabansu.
Basma da Mandiya rirriƙe juna sukayi ido ya raina fata.
Miƙewa Jafar yayi a hankali cikin sanda ya dudduba ko ina amma bai ga komi ba.
Dawowa yayi ya zauna zociyarshi cike da tunane_tunane.
"Jafar ka duba sosai kuwa?, ni fa kamar fatalwa nagani wallahi baka gani ta gifta tanan."
Basma ta ƙarashe maganar tana ƙara dudduba wurin.
"Tabbas nima ita na gani, amma komiye mu dage da addu'a babu abinda yafi ƙarfin Allah."
A ɗarare suke jininsu kan akaifa.
Dare yayi dare bakajin motsin komi sai kuka tsuntsaye da wani irin gurnani da suka rasa gane namiye.
Jafar gani yayi zaman zugum ɗin yayi yawa nan ya buƙaci jin miya fiddo da su daga gida.
Basma ta fara basu labarin abinda ya fito da ita, Jafar ya girgiza sosai dajin labarin yayi mamakin yadda ta bijirema umarnin miji ta taho biki, wai kuma bikin ma na ƙawa.
Nan itama Mandiya ta fara bada labarinta kamar haka;
"Kamar yadda kujaji da farko nidai sunana Mandiya, garinmu ɗaya daku wato gefen Kai kazo, na taso babu uwa babu uba, natsinci kaina a gidan karuwai hannun wata mata mai suna uwar daba, tun da na taso banida kunya ko kaɗan ga taka mutane da bi ta saman duk wanda ya so kawo mani raini, tun ina da shekara 20 uwar daba ta ɗorani a hanyar karuwanci, in da ni dana tashi sai karuwanci na yayi zarra saboda rashin kunyata nayi suna duk inda kashiga indai gidan karuwai ne to an san da zamana, abinda yayi sanadiyyar fitowata wannan tafiyar Magajiyar karuwai tai ta kwaɗaita mani inzo garin kai kazo zani tara dukiya mai tarinn yawa, domin chan karuwanci yafi tsada, kunji abinda ya fiddoni, har yanzu ina dana sanin fitowata da kasancewata karuwa ina nadamar rayuwar da na tsinci kaina ciki."
Kukan dayaci ƙarfinta ya sanyata kasa ida maganar.
Sun tausaya mata halinda ta tsinci kanta.
Nan Jafar ya ƙara jan hankalinta Allah gafurun rahimun ne, ta tuba har cikin zuciyarta Allah yana karbar tuban bawanshi madamar baizo gargara ba.
Nan shima Jafar Ya basu labarin abinda ya fito dashi gida, sun jajantama juna suna addu'ar Allah ya fitar dasu a wannan jejin.
Tsit! Wurin yayi kowa da abinda yake tunani, Jafar yana gefensu ya takure wuri ɗaya yana addu'a a zuciyarshi.
Dariya aka kece da ita wadda ta tilasta masu toshe kunnuwansu da duka hannayensu biyu.
"Hhh! Wane ganganci da ƙarar kwana yayi Sanadin kawoku cikin jejin nan, kamar yadda muka rasa rayuwarmu muka koma fatalwa haka kuma zaku rasa taku rayuwar bazaku taba fita a jejin nan ba."
Kawunansu suka ɗaga suna ƙarema halittar kallo, sanye take da farar riga da tayi face_face da jini, ilahirin jikin ta farine sol idanuwanta babu ɗugon baƙi ko kaɗan ga dogayen hannuwa masu ɗauke da farata dogaye masu tsananin tsini, doguwace sosai tsaye take saman iska kamar tsuntsu doguwar rigar dake jikinta dogowace har ƙasa shiyasa ko ƙafafunta baka iya hangowa.
Jikin su Mandiya da Basma tuni ya hau mazari.
Jafar ji yayi kamar an sanya sarƙoƙi an ɗaure bakinshi addu'ar ma ya kasa gurta koda kalma ɗaya.
Wannan damar Fatalwar ta samu ta nunasu da yatsa wani farin hayaƙi yafito ya zama guguwa yayi sama dasu Jafar.
Tamkar yadda fanka ke wulwulawa haka aka riƙa wulwula su Mandiya tun suna ihu har ƙarfinsu ya ƙare sukayi tsit iskar ta watsar da su wani bangare daga cikin jejin batare da sun san mike faruwa ba.
___________________
Kamar yunwa taccen zaki haka Audu yayo kan Salma da tayi mutuwar.
Tariga ta bada sadaƙar yau kwananta ya ƙare jira kawai take ya kasheta ta huta.
Kamar daga sama sukaji ƙarar wani abu kamar an buga bindiga.
Mace da namiji suka gani tsaye gabansu da wani abu kamar sanda a hannunsu.
Dubansu suka kai ga audu dake kwance ƙasa yanata bullayi da alamu ƙoƙarin tashi yake.
Mace tace dasu Biba mubar wurin nan kafin ya tashi domin gaf dake da miƙewa.
Su duka suka bar wurin suka yi wata siririyar hanya da guda.
Gudu suke ba ƙaƙƙautawa tamkar bazasu tsaya ba.
Ganin sunzo wurin wata gadar icce suka ja suka tsaya suna maida numfashi.
Rabson da sai yanzu hankalinshi ya dawo jikinshi ganin bakin fuska ya sanyashi yin tsalle ya koma gefe.
"Innahu min sulaimanu...., bayin Allah mutane ko aljannu, daga ina kuke mijya kawoku jejin nan?, ko dai kuma Horror ɗinne sukazo mana da taku salon yaudarar?."
Namijin daya gama ƙuluwa ya watsama Rabson kallon zaka gane kurenka.
Macen tayi ƙarfin halin fara magana.
"Tsautsayi ne da rabon wahala ya fiddomu daga gida har muka tsinci kanmu cikin Wannan halin, ni sunana Kulu amma ana kirana Kulu ganin ƙwam, sai abokin tafiyata sunanshi Nasir, sai kuma abokan tafiyar mu su biyu da suka bace mana Jamcy da Tukur muna kiranshi Tk, mun kasance masu son kallon abubuwar mamaki ne, Rannan malamin mu na mana lecture yake sanar damu wannan jajin da haɗarindake tattare dashi, da kuma abubuwan mamakin dake cikinshi tundaga lokacin muka yanke shawarar guduwa daga gidajenmu domin muzo ganin abubuwan Al ajabi, mu hudu haka muka shigo dajin nan bala in da muka shiga ya sanya muka rabu da abokan tafiyarmu batareda mun saniba.
Halin da suke ciki bai hana Rabson fashewa da dariya jin waɗan da suka fisu gantalewa, Nas a fusace ya taso ganin Rabson ya raina masu wayo, cikin hanzari kulu ta tareshi tana bashi haƙuri.
Rabson kallon Salma yayi gsnin yadda bakinta yayi Suntum ya haye ga goshinta daya yi ranƙwalele.
Sake fashewa yayi da dariya yana riƙe ciki, yana nuna Salma da hannu yanaci gaba da dariya.
Tamkar zata kai mashi bugu haka Salma tayo kan Rabson, Biba tayi saurin riƙeta tana bata haƙuri, ashar kawai take dannoma Rabson amma bai daina dariyar ba.
"Haba Rabi'u! Miye haka Kana ta taƙular mutane bakaga halin da muke cikiba amma har kuke ƙoƙarin fada?."
Bai daina dariyarba yaci gaba da magana"Habibalo kiyi haƙuri wallahi inna kalli bakin Salma yadda yayi tsawo kamar shantu bani iya danne dariyata, masoyiyita Salma kiyi haƙuri kinji nifa tunda muka shigo jejin nan nike jin ƙaunarki na ratsa jinin jikina."
Ya ƙarashe maganar yana dariya.
Salma kamar ana zugata haka ta riƙa zagin Rabson tana fadar tafi ƙarfin tayi soyayyah dashi, da Ƙyar Biba ta shawo kan Salma tayi shiru.
Gurnanin da sukaji bayansu ya sanya bashiri suka fara bi ta saman gadar katakon ba shiri.
Doguwar gadace wadda aka ƙerata da katako gefe da gefe kuma iggiyace wadda zaka riƙe hangu da dama, kasanta ramine mai tsananin zurfi baka iya hango ƙarshenshi.
Tafiya suke da sauri Rabson na taka wani katako ya balle yayi ƙasa , lokaci ɗaya gadar ta fara karairayewa ta yin ƙasa, hankulansu atashe wasu suka fara ihu, wasu suna addu'o'i.
Rabson atake ya fara bada wasiyyah yana;
"Salma masoyiyata inkin samu komawa gida kice ma Kaka na barmata ɗan bunsuru na duniya da lahira ta yafe mani , wayyoh kaka lokacin mutuwata yayi."
Igiyoyin gefen gadar suka rirriƙe suna gudu gadar na ƙara karairayewa.........
*COMMENT* ✅
*SHARE* ✅
*MEEN@RT...✍🏻*
08133562798
[10/11, 10:29 PM] Meen@t A Yandoma: 💀 *BAƘAR TAFIYA* 💀
( *HORROR STORY* )
*BY MEEN@T A YANDOMA*
*MARUBUCIYAR FATALWA*
🌍 *MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION*🌍🖊️
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
*SALONSHI NA DABAN NE 💃🏼*
*ALLAH KAJIƘAN MAHAIFINA DA DUKKN MUSULMU BAKI ƊAYA KASA YA HUTA, KA KAI RAHAMA A KABARINSHI, ALLAH KA GAFARTA MASHI ZUNUBBABSHI, ALLAH YAJI ƘANKA ABBANA*
*MASOYA INA MATUƘAR GODIYA DA SOYAYYAR DA KUKE NUNAMA LITTAFIN NAN, ALLAH YA BARMU TARE, INA MATUƘAR GODE MAKU MASOYA A DUK INDA KUKE*
🤸🏻♀️🤸🏻♀️🤸🏻♀️
*ƳAN BAƘAR TAFIYA FANS COMMENT ƊINKU YANA MATUƘAR TAFIYA DANI KUNA SANI NISHAƊI DA COMMENT ƊINKU, ALLAH YA BIYAKU INA MATUƘAR GODIYA*
🥰🥰🥰🥰
*WANNAN FEJIN SADAUKARWA NE GA DUK MASOYANA ADUK INDA KUKE, ALKHAIRIN ALLAH YA KAI MAKU, INA GODIYA*
*ALLAH YA BIYAKU MY PEOPLE, ALKHAIRIN ALLAH YA KAI MAKU HAR GADON BACCINKU, ƳAN BAƘAR TAFIYA FANS, KUNA SANI FARIN CIKI DA ADDU'O'INKU, ALLAH YA ƘARA DAƘON ZUMINCHI, KUMA BAZANI MANTA DAKUBA SAURAN MASOYA INA MATUƘAR GODIYA DA SOYAYYAR DA KUKE NUNAMA WANNAN NOVEL ƊIN ALLAH YA BARMANIKU MASOYA INA ALFAHARI DAKU.* 🤗🤗🥰
____________________
*PAGE 16_17*
........Sanyin da sukaji yana ratsa fatar jikinsu ya sanyasu fara bude idanunsu.
Jamcy da Tk dake tsaye kansu da wani icce ahannuwan su, suna jiran farkar warsu, a tunaninsu suma Horror ne lambo sukayi masu.
A firgice suka miƙe, Mandiya ganin mutane biyu saman kanta ya sanyata kwala ihu cikin tsananin kaɗuwa, kafin ta rufe baki Jamcy dake tsaye kanta atunaninta horror ce bata 6ata lokaci ta kwadama Mandiya sandar nan, a take Mandiya ta baje ƙasa a sume.
Sallallami su Jafar suka hauyi tare da yo kan Mandiya.
"Mutane ko Aljanu?, mikuke naima awajenmu da har kuka sumar da abokiyar tafiyarmu."
Tk da idanunsu suka raina fata cikin ƙarfin hali ya fara jawabi.
Nan ya kwashe komi ya fada masu har batan abokan tafiyarsu wato Kulu da Nas.
Sun yi matuƙar mamakin ƙarfin hali irin nasu Jamcy, kawai saboda ganin ƙwam irin nasu zasu baro gida.
Mandiya da ta samu ta farfaɗo buya tayi bayan Basma tana mai da numfashi.
Bata yarda dasu Jamcy ba sai da Jafar yayi da gaske sannan ta yadda su ɗin mutane ne.
(😂🤣 Niko nace Mandiya anji sambaɗebaɗe)
Wurin da suke wurine mai wuyar misaltawa, domin tunda suka fara tafiya basu taba tsintar kawunan su a irin wannan wurin ba.
Tsabar duhuwar dake wurin tamkar dare ya fara haka yanayin wurin yake.
Kallon_kallo suka shiga yi, tamkar yau suka fara ganin juna.
Da dai sukaga basu da wata mafita face su ci gaba da tafiya, miƙewa sukayi tare da kakka6e jikinsu suna makyarkyata saboda tsananin sanyin da ake zabgawa wurin.
Mandiya kai ko ɗan kwali babu ga kitson attach ansha ga kayan jikinta sun matseta, Basma riga da siket ne jikinta wanda suka sha ɗinki yayi rigar nan daga sama ta matse ƙasa kuma ta buɗe, ga siket ɗin irin wanda ƴan mata ke yayi wanda ake kira mai guiwa.
Uwa uba Jamcy da ta takesu wurin wayewa zamuce ko gantalewa, jikinta T.shirt ce ta ɗan kawo guiwa sai wandon ta jins wato crazy wanda matasanmu ke yayi.
(Wasu mutanen ganewace basuyiba wani fa inya kalleka bada halayenka zai duba ya gano kai waye ba, shigar jikinka ita zai fara kallo yayi maka hisabi, dan haka musan irin shigar da zamu riƙayi, in bakajin tsoron Allah to akwai lalatattun mutane in babu su akwai Shaiɗanun Aljanu.)
Tafiya suke suna bankar juna saboda sanyin da suke ji bakunan su har farin hayaƙi ke fita.
Tun suna tafiya iyakar ƙarfinsu har ƙarfin ya ƙare suka koma jan ƙafa.
Tsayawa suka yi da tafiyar tare da bajewa ƙasa suna huttai.
Ga yunwa ga ƙishirwa da basu iya tantance yaushe rabon da su kai wani abu bakinsu.
Fashewa da kuka Basma tayi tana faɗar;
"Wayyo mijina! Wayyo gidan aurena, shikenan a haka zani ƙare nayi bankwana da asuwaki da cinyoyin kaji gani nan abinda zanisa cikina yana gagarata,da gida nike da ina chan ina asuwaki da naman kaji abinci sai wanda naga damarci, amma yanzu ganinan na ƙare a daji,Ta gaban goshi Allah ya isa tsakanina dake da kika turani na bijiirema maganar Habib nafito damin halartar bikinki,