Showing 3001 words to 6000 words out of 39613 words

Chapter 2 - Yar Fulani 1 to End Book Complete by Aisha Aliyu Garkuwa .txt

02 Dec 2024

2317

suka shiga cikin gida.
Bayan sunyi sallan isha suka dawo gida sukasamu har an shiryamusu komai akan dining suna cin abicisu suna hira.karfe tara suka watse kowa yatafi mkon cinsa
Da safe hassan yayi shirin tfy office ko gda bai biya ba yatafi don yau yanada tiyata har 3 sai karfe 6: ya samu yadawo gidansa ya wuce sai da yyi wokka yyi alwala yatafi masallaci bayan sunyi sallah suka shiga cikin gda suka ci abinci.
Ya dauki phone dinsa ytfi parlon ammi ya kwanta kan kujera yanata danna woyarsa ammi Na zaune agefe tana kallon TV Zubaida ta zo wucewa yce ke kebaki iya sallama bane tace yaya nayifa baka jibane yce to koma ki sakeyi.ta koma tayi sallamar da karfi don ya bata haushi.ya tashi da sauri yana cwa ke ai zaki toshemanaπŸ‘‚πŸ»ke baki iya abu anitseba saikace maceba oya kauce kibamu wuri sokuwar banza ta wce ta tafi tanata kunkuni yace me kike cewa tace cewa nayi kyi hgri
Ta xauna kenan kuma taji yana kiranta tace nabonu da bala.i nibansan me yazoyiba yau kuma yayita takurawa mutane. taje tace gani..ya mikamata key din motarsa yce daukimin laptop dina takarba ta tfi tana mita .ammi tace wai nikam kai sarkine da komai sai ammaka yyi murmushi yce a a.to ammi don Na aiketa laifine.tace kai waya aikeka.yce mahaifiyata mana d Umma Na d baba Na tayi shiru bata sake cewa komaiba dama ya sani daya kirata da matsayin uwarshi to bazata sake mgnba
Aranshi yace kai fulaku baiyiba shi wlh bazaiwa dansa hakaba takawo masa laptop din suka shigo tare da Hussain suka yita klon pictures aciki...


By garkuwan Fulani
[4/12, 6:13 PM] Aisha Aliyu Garkuwa: πŸ“πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡
Y'ar Fulani part 5 Na Aysha Ali garkuwa.
πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡


Bari muje muga ya yar Fulani yata kaya Kuma ita wacce kuma a INA take.nima Aysha Ali garkuwa Na gaiyaci yan rakiya Na don nasan Fiji da son nono ga dalal maison garin dayake da sanyi to su halimancy sai anbimu ne gasu suwaiba harda su maman Dan baba kukam sauran kyi hpri Sai wani karon yenxukam motar ta cika😜 tafiyace mai Dan nisa kadan da kafita Gombe ka doshi hanyar dadin kowa xaka wuce kwadam kafin a isa baure akwai Forest atsakanin su a dai dai cikin forest din akwai wani Dan kauye Wanda ake kira da ardo yabani garin ardo yabani garine Na Fulani Allah yamusu ni ima kala kala agarin gasu cikin forest ga wani dutse a gefen garin Wanda yake xubda ruwa daga cikinsa ga yayan itatuwa iri daban daban fulanin wurin Allah yabasu arzikin dabbobi sosai.gidajan kauyen da duwasu suke ginasu yashin garin kamar kacisa Dan haske suna da dabbobi kama daga shanu rakuma dawakai tumaki akuyoyi xabbi kaji gaba daya Allah yabasu arzikinsu ardo yabani shine ardo wannan rigar matarshi daya hakanan yarsama daya itama saida sukayi shekara15 da aure kafin Allah ya basu ita ardo yabani dantijo ne mai tarin ilimin muham madiya ga tarin arziki da shi kanshi baisan adadin dabbobinsa ba Amman 'ya daya tilo Allah yabashi shida matarsa hari sunbaiwa yarsunnan bimbi tarbiya da ilimin Islama ba kadanba.yana da yara masu yimasa kiwo guda8 shi baya zuwa kiwo saidai yaje labbu da dere kuma yana karantar da manya da yara awoje cikin gida kuma bimbi Na karantar da yara mata hari kuma tana karantar da matan aure..
Randa su hassan sukayi musu barna awurin Gaini ya yanka duk shanun da yasan bazasu iya komawaba yabawa mutannen wurin sadaka.wannan dokar ardo ce yacemusu duk inda suke matukar dai sukaga wata dabba bata da lfy to su yankata awurin subaiwa mutannen wurin sadaka haka kuma sukayi suka kori sauran suka tfi gida. bimbi tun lokacin taketa mita tana
kado ya shusheni Allah ya isa kado banyafe makaba ita ba abinda yafi bata haushi harda Dan shannuta da tafiso aka yanka suna isa gida taje tazauna agefen hari tana bata lbrin yadda sukayi da masu mota. Hari tace kedai bakitada hkri wataran sai kije kinyi fada da Wanda xai karyaki.ta turabaki tace aradu yenxuma ya karyani.tunda ya karyamin buwana sunan da take kiran Dan shanunta dashine buwan.hari tace nikam kitashi kije kiyi sallah lokacin sallah yyi.ta idar da sallan isha kenan ardo ya shigo bayan yaje ya duba marasa lfyn.
Yace ke hari INA mamana tace gatacan tunda tayi sallah taki taci abici wae don an yanka mata buwanta yaje ya xauna agefenta kan wani dutse akusa da randunansu randunan Na tabone sai naso sukeyi alamar sanyi yana ratsasu..yace mamana waya taba minke kawai saita fashe da kuka.cikin yanayin lallashi yace kiyi hakuri mamana gaini ya gayamin abinda ya faru kidaina kuka gobe in Allah ya kaimu kishiga hoggo wato garke kixabin duk abinda kikeso kinji ko mamana.. Ta gyeda kai tana share hawayenta ya kamo hannunta ya zaunar da ita kan taburma yaje da kansa ya debo mata nono mai sanyi ya bata yace kisha xuciyarki zatayi sanyi kijiko.tace to Bappa kaima kasha mana yace nizanje kofar gida kinsa su siddi suna jirana lokacin karatu yayi kema kiyi sauri ki karantar da dalibanki tace to.
Da lokacin tashinsu ardo yakusa dama sukam tuni suntashi daliban nasu hari takira bimbi tace ke ina kike xoki kaywa bappanki abincisu kamar yadda suka saba dama kullum zata gasamusu kaji ko zabbi da madaran nono akaimusu insun kusa tashi da yan kananan kore da ludaya kowa yadibi abinda zai isheshi.shiyasa makarantar ardo tayi farinjini da suna akauyen nasu dama makobtansu ta kaimusu ta dawo tasha madaranta ta tafi dakinta takwanta
Da safe tana idar da sallah tafara shara tagama tayi wenke wenke sannan ta dauki tulunta ta tafi rafi basu da nisa tsaka ninsu da rafin daga cikin gidanma zakaji saukan ruwan gashi dutsen akasan bishiyar mankoro yake gaba data wurin yana xagaye da bishi yoyi masu tarin inuwa ga shuke shuke akasa sai yar siririyar hanyar da akabari don masu diban ruwa.......


By garkuwan Fulani
[4/12, 6:13 PM] Aisha Aliyu Garkuwa: πŸ“πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡
Y'ar Fulani part 6 Na Aysha Ali garkuwa
πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡


Ta cikamu su randunan duka taje ta juye wanda tadawo dashi yenzun a bandaki cikin wani Abu kamar daro saidai shidinma Na tabone ta hada daruwan zafi tayi wanka tafito tana tsane gashin kanta.ta tajeshi gashin har gadon bayan ta gashi bakikkirin gashi da santsin da sheki.taje bakin kitchen tace inna kizo kiyimin kitso.tajuyo tana cemata yau baxaki bisu kiwon bane?tace a a zanje mana inna kiyi sauri kizo kimin.to zama zasuyi sujiraki kenan tace a a basu ma fara kucce shanunba fa. inna tace to dauko kifiya.
Ki kawo suka fara duk yawan gashinan kitson kwaya 5 akayi 2 akazubo su gaban goshita 2kuma akayi baya dasu guda 1 kuma tufkeshi akayi atsakiyar kayin.Na gabannan har kan girjinta suke kwace.
Tasa kayanta irin nasu Na fulani rigar yar guntuwa bata karisa rufemata cibiyarta bama ta daura zani tasa takal minsunnan Na kiwo. da sauri sauri tasha madaran nono.ta dauki Dan sandanta tace inna midilli.inna tace allah yaba da Sa.a yakare ku.tace amen ta fita suka tfi.
Sungama fita cikin forest din sundauki hanyar hawa kandan wani dutse.gaini mai kiwo yace mata to bimbi kiyi sauri kitafi karki makara adakeki.tace to saikun juyo ko...jaaeh yace kedai tafi.tajuya ta gangara ta kasan dutsen naga tashiga kwadam ta nufi makarantasu ta yan mata tanazuwa tasamu duk sun shiga class tatsaya tabakin window tana lekensu tana tunanin shiga tasan wannan malamin mugune shi bashida tausayi..
Taji andafata tajuyo arazane sai taga yaya Sulaiman ne tace yawwa yaya shiga nake sonyi kuma inatsoron malaminnan yacemata kishiga bazai miki komaiba tace to taje tashiga.
Mutumin da yake tsaye kusa da Sulaiman yace wlh nikam mamaki nakeyi..sulaiman yace namefa.yace na yedda akayi iyayen yarinyar nansuka yerda takeyin karatun boko.kasanfa ba abida fulaninnan suka tsana kamar karatun boko.sufa gani suke bokon kafurcine..mutanneda ko hausa kayi saisuce maka kado.
Sulaiman yayi dry yace ai iyayenta basu san tana zuwaba.tace indai babanta yasan tana zuwa saiya kusan yankata..Adamu yace tokai asuwa kasata makaranta.yace amusulmi Dan uwan musulmi.yaci gaba dacewa.yarinyar tana da ra ayin yin karatun kuma tana da saurin fahimta..lokacin da tafara zuwanan.kullum insun fito kiwo sai tazo ta tsaya a window aji tanajin abinda akeyi.wata rana nakirata nace kekuma fillo me kikeyi anan sai tai dry tace karatun nake son koya.nace to kicewa baban ki ya kawaki mana ta zare ido ta buga hannu agirji tace ai den xaiyankani nacema ta tokeda suwaye kike zuwa?. Tace nida yayunane inzamuje kiwo sai in ce musu xanzo nakoyi krt.sukuma basa hanani kuma duk abinda akayi suma inakoya musu.shine nacemata kin iyane tace min eh.nace to fadamin abinda kika koya.
Hakika nayi mamaki lakacin da naji yariyarnan tana zaiya namin duk abi da ake koyawa yan pramary 6 gashi tana da ilimin addini sosai.to nikuma daga ranar nasata a school din.itakuma bata fashin xuwa kullum zata sallami iyayenta da zummar zata tafi kiwo.suna zuwa nan saita shigo tayi karatunta sukuma sutafi kiwo.garfe daya da rabi ake tashi.sukuma masu kiwon tun 1: suke juyowa..sai sutafi cikin forest dincan suci gaba da kiwonsu. Gashi yenzu har tana a s s3 sune masu gamawa bana kuma tunda ta shiga take daukan no 1 a ajinsu...
Adamu yace to menene sunanta.Sulaiman yyi dry yace nidai tacemin bimbi Amman da yar fillo ake kirantan.Adam yace gskya kasamu lada tunda karabata da jahilci..Sulaiman yace ai daman can ita ba jahila bace.tunda tana da ilimi Arabic.Adam yace gaskiya ne....
Toh muji lbrn bimbi bari mukoma muga ya doctor yerima Hassan Aliyu yake ciki......


By garkuwan Fulani
[4/12, 6:13 PM] Aisha Aliyu Garkuwa: πŸ“πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡Y'ar Fulani part 7 Na Aysha Ali garkuwa
πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡


Yau Sunday ana hutu shiyasa tunda akayi sallar asuba hassan yakoma bacci bai tashiba sai karfe 9:yana tashi yaga Hussain bayanan ya shiga toilet yayi wanka yana ftwa ya shirya cikin wani wando 3 quarter d wta yar Riga ma ra hannu mai hade da hula ya maida hular bayanshi ya kwanta kan kafadadunsa yadan fesa turare ya zira takal mansa.ya dauki key dinsa da lap top dinsa sai phone dinsa ya nufi gdan su yana shiga ya gaida Umma.tace kiyi breakfast kuwa yace sai anjima..yce ya baba tace ai yana tare da baki yace to bari Na gaida ammi.tace to.
Sau 3 yana sallam ba amsaba.parlor shiru bakowa sai yashiga kawai ya kwanta ka kujera ya dora laptop dishi kan cikinshi yanata danne danne..ammi tafito ta sameshi yana kwance.tace kaikuma yaushe kaxo yace daxu.tce o yagaishe to.daga nan ba wanda ya kara mgna a hankali ammi ta kira xubaida tace jeki hadamin tea tce to tajuya ta tafi Hussain yashugo tare da sallama suka gaisa da ammi.hassan yace brother INA kaje da sassafennan?.yace wlh babane ya aikeni inkira mai waxiri akwai taron gaggawan da xasuyi.kumafa harda su yaya Bashir kai dukan muma..hassan yace to Allah dai yasa lfy ammi tace amen.Zubaida nakawo tea din Hussain ya karbi cop din ya fara sha..tace yaya ammi nefa tace inkawo mata yace to hadomata wani harta tafi ya kirata yace .wai nikam Zubaida ban hanaki Sa kanana kayan nanbane? Tace kahana yce OK rashi tarbiya ce kenan tasa kike sawa tace a a kayi haquri baxan sakeba..hassan yace Dan Allah malam kabar yarinya tasake kai saishegen iyayi..ammi tace ai dama xakace haka tunda kaima bakada wata shiga sai ta kananan kaya.Abu ko tsari babu kafa sandal sandal awoje.yace ammi ai shan isakane..tce shan iska ko iskanci ba.tasake kawo tea din hassan ya karba yafara sha.xubaida ta tura baki tace wlh nikam Na gji ammi..Hussain yace da kikayi me oya jeki hadomata wani shayin .taju ta tafi tana qunquni. Hassan yace ammi tuwan shinkafa d miyar kubewa da man shanu nake so.tace ka gayawa mama.yace nidai kenake son kiyimin innace baxan yibafa yace xakiyima ammina....
Parlon yayi shiru bayan gaishe gaishen da skyi sarki yfra bayani kamar hka.yce Na gdwa Allah daya nunamin wannar ranar kuma ayau dinnan nakson insheda muku cewar zanyi murabus daga kan sarautar nan kuma zanbawa Babba danane mulkin.Bashir ya dgo kansa d sauri yce baba nikuma yace eh kai bashiru..yce baba Ku gafarceni wlh nikam banaso inda mai so acikin kannena to abashi.. Ibrahim yayi maza yce tonima dai bana buqata sai daiko in fawaz..fawaz din yyi dry yace kuji sonkai fa nikuma maiye hadini da sarauta ina sojo ina soja ina sarauta
Sarkin ransa yabaci sosai yace to nafisa kindai ji abin da yayanki sukace.wato ban isa inbasu umurniba.ko. ahankali waziri da galadima suka riqa bawa sarki hqri hardai ya Dan huce. ammi tace a gskya Bashir baka kyeuta minba ai babban wa shine magajin uba.don haka kyi hqri ka karbi wannanr sarutar.yce wlh ammi mulki baya ckin tsarin rywta..Umma tace Aysha barshi a yau da shikadai aka haifa a gdnna da sai muji haushi Amman ai suna da yawa..
Taci gba dcwa kai hassan inna neman alfarma daka zama mgjin ma haifinku.hassan ya dago kansa d sauri yce Umma nikuma tace eh kaifa hassan don wlh ninasan ba wanda zai iya riqe wannan sarautar sai kai Nina dade da sanin hakan..yce don Allah baba kaci gaba da riqe sarautarka inkuma ka gaji kbwa Bappa Ibrahim .sarki yce shima yaqi kuma kunqi ai duk randa Na mutu sai kusayar da sarautar ko.waziri yce baxa ayi hakaba haqiqa nafisa maganar gskyace tabbas hassan shine sarki kuma kaima kasan haka mai martaba don duk lkcin da akayi istihar inuwr hassan ke giftawa. Sarki yce to ke Aysha mkkace?ammi tce a gaskiya wannan tsarin baiyiba shidai Bashir din xa abawa.Bashir yce ammi kyi hqri wlh mulkinnan Na hassan ne.. Waziri yce Aysha ke muke sauraro fa..tce duk abinda kuka yanke ai shekennan Umma tce Na gode Aysha d kka fhimce mu.
Sarki yace to hassan nan da wata1 kafitar da mata don so nke randa xancika shekara 40 akan karagar mulki inyi murabus kuma randa za a nadaka aranar za adaura aurenka Kay da Hussain da naziru tunda shima naziru zaidawo cikin makonnan sai yanzu Hussain yyi mgna yce to baba nikuma me yahadani da yin aure.Umma tayi dry tce to haka xaku tabbata bakuyi auren bane? Hassan Wanda ya gama cika da takaici yce to ni wama nasan zan cewa xanyi aure nidinnan dai ace xanyi wani aure ai sai arei nani yacigaba dacewa haka kawai ya Bashir kasa xa ahadamin zafi 2 lkci 1 gskya ni baxan yi aureba.ammi tce tofa kunji irin tunanin da yakeyi kuma wai ahaka kuke son bashi shugabanci jiha gaba daya mutumin da bai masan abu mai kyeu ba..ahaka dai akayita masu fada da nasiha ..andai tashi taron da sharadin dukansu su fidda mata.fawaz yace tofa sarki hassan sai arege jin kai atsaya anemi aure.inko miskilancin ka ya hanaka wlh za ajajubo maka wata a hadaku kuma kasan gidanmu ba yaji bare saki.Ibrahim yce gayamsa dai Fawax.aka rufe taro da addu.a........


By garkuwan Fulani
[4/12, 6:13 PM] Aisha Aliyu Garkuwa: πŸ“πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡
Y'ar Fulani part 8 Na Aysha Ali garkuwa
πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡


Yau kwana 3 kenan bimbi bataje makarantaba sabida Bappa bashida lfy yana fama da ciwan kai mai tsanani har ya kwantar da shi hatta yawunsa iya tofar sai suga yakoma jini bimbi d hari sun rude sosai.to shiyasa bata samun damar binsu gaini kiwo sai dai taje lambu tadanyi aiyukan da Bappa yakeyi kamar dibo kwan xabbi d ciro banana da dai sauran yayan itatuwan.yau kam tayi niyar xuwa makarantar don haka tana xuwa labbun tayi abinda yakamata tayi da sauri sauri ta wuce school din. tana zuwa uncle Sulaiman yace yar fillo meya hanaki xuwa kwana 2 cikin sanyi murya ta gaya mishi abinda yake damun Bappanta ta qarisa maganar tana goge qwallah a idonta cikin tausayawa yce kun kashi asibiti ne tace a a yace to ko gobe kukaishi asibitin aduba kan nashi asan meyake damunshi kar abari ciwon yyita qaruwa.tce to xamu kawoshi ko wancan asibitin tanuna wani Dan karamin asibitin.yce a a Ku kaishi babban asibitin cikin gari don acan xa.afi gane meke damushi.tce to ai bamu san wurinba.yce to xan rubuta miki adireshin asibitin saikuje ko. Ya rubuta mata yabata yana dada jadda mata akansuje fa.tace to ta karba ta tafi gida
Haka kuwa sukayi washe gari ran jumma.a suka tafi cikin gombe .qarfe 9 dai dai tasame su cikin asibitin suka sayi kati sukaje suka kama layi ganin Dr itace take bin layin Bappa kam yana kwance kan benci.har layi ya iso Kansu wata Norse ta leqo tace ardo yabani Buba yashiga...lkcin kuma Bappa yasamu baci ya saceshi.sai ta tashi ita zataje tashiga tamusu bayin ciwan nappan nata to daga bude qofar tarasa yedda xata bude kawai sai tahau turawa da iya karfinta tayi tayi qofa taqi budawa kawai saita kama bugawa tana cewa kuzo kubu demini.cikin jin haushi da hatsala Dr ya dakawa Norse din tsawa yace ke Hafsat kije kiga wane Dan issakanne yake shirin ballamin qofar office tace sorry ser taje ta budemata qofar dai lkcin da shikuma Dr yerima hassan Aliyu yake cewa ai dama irin wannan bugun qofar sai masu suna ardo da jauro ne xasuyishi mutane kullum basa taba wayewa.yadago idonsa dai dai lkcin da ta xauna kan kujerar da aka tanada Dan majin yata da sauri yasake kallonta sama da qasa....


By garkuwan Fulani
[4/12, 6:13 PM] Aisha Aliyu Garkuwa: πŸ“πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡
Y'ar Fulani part 10 Na Aysha Ali garkuwa
πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡


Suna cikin mota ya juyo ya kalleta yace qanwata me sunanki.tce bimbi cikin mmki yce bimbi kuma tace eh yce to sabida me ake kiranki bimbi don dai nasan ba shine sunanki Na gaskiya ba.tce eh sunana fateema ana kirana bimbine don an ayfeni da safe yyi dry yce to wannan kitsonfa me sunansa tace kumbo bobini.yce to mesunasa da Hausa tce bansani ba nima
Dai dai lkcin suka shigo hospital ya bude mata ta fito ya dauki wasu kayan itama ta dauki wasu suka shiga.suna tafiya suka hadu da wata Norse tace oga a ina kasamu wannar kyekkyewar yariyar yce qanwata ce suna shiga ya ajiye kayan hannunsa yce to Bappa bari naje nayi sallah gashi yau jumma.a Bappa yamishi gdy.shikuma yce to Fatima sai nazo anjima ko ga Abicinku yana cikin ledanna ko tce to yayana mun gd sai kzo.
Bayan suntaso dga mallacin ya wuce gda suna zaune a parlor yce ammi adafa min abinci mai Dan sauqi zan kaiwa wasu Fulani tce INA yan uwasu.yace inaga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login