Showing 24001 words to 27000 words out of 42033 words

Chapter 9 - Zumuntar kenan book by Sumayya Abdulkadir Takori.txt

jini, koda an basun suce 'a’ah, inyaso ni sai ince a bani in karba da hakuri, don haka nayi furucin tana bin Yaya Aliyu B-Q, ko ince bata da kunya bata da kokari, kazama ce, kuma masifaffiya. Sai kuma tazo tana kazantar kowa ya gani hakan ya nuna ba kage nayi mata ba.
Nayi wauta da tazo ta zame min bala'i, ko ince alhaki ya zame min dan kwikwiyo. Wautar da ta jawo Fa'izah ta tsane ni fiye da kowa a duniya har take addu'ar ALLAH YA KASHE FA'EEZ BAMALLI IN HUTA!
Ni kuma Ya jarrabce ni da matsananin SO irin wanda ban ta ko gani ko cikin hikaya da labarun almara ba.
A zahiri na nunawa Fa'izah kiyayya domin SONTA da yayi min katutu, bani kuma da yadda zanyi dashi. Duk kiyayyar da na nunawa Fa'izah KISHI NE da PRETENDING. Amma da hankali ya zo min, na gane na kuma fahimci wannan ba hanya ce da ake nuna KISHI ba, ga wanda aka yimawa KIYAYYA NE. Bayan ni a wauta ta nayi ne don samarin A.B su ki Fa'izah baki dayansu. Da sun kammala sakandire ni in aureta, tunda ta rasa mai so. Na manta da cewa ma babu batun nagani ina so a cikin A.B, a ganina koda an basun dai suce basa so. Tunda babu wanda zai so mace mai wadannan halaye da na kaga mata, har shi Aliyun, don dai yana da wata irin zuciya ne data sha bamban da ta sauran 'yan Adam.
Ashe ni ban san wannan na nufin gina kiyayyata mara iyaka a zuciyar wadda na yiwa KIYAYYA DON SO. Ban tashi jin son Fa'izah na neman hallaka ni ba sai da nayi nisa da ita. Na kasa karatu na kasa ci, na kasa sha, barci ya kaurace min fau-fau. Da hoton ta na 'teddy bear' nake kwana nake tashi.
Nayi kuka domin son Fa'izah, abinda ban taba yi akan mace ba: Nayi abinda ban taba yi ba a rayuwata domin SON FA'IZAH, wato "NADAMA".
A shekarun karatuna, baki daya, kowanne sakan, kowanne minti, kowanne dakika da kowanne awa son Fa’izah da kaunarta ke kara habaka a tare dani.
Ba komai ya hana ni yiwa Fa'izah aike tamkar su Ummi ba illa TUNA BAYA... Yadda Fa'izah ta tsane ni, yadda ta ki jinina, na tabbata ba zata amshi abin hannu na ba ko za'a kasheta. Tsammani ma zata yi wata cutar na kunso zanyi mata.
To amma nayi mata aike da abu mai daraja a gareni, nake kwana nake stashi tare da shi. Nayi mata aike da HANKICI na, wanda ke nufin sakon kaunata zuwa gareta, domin na sanya anyi rubutu da harshen Larabci a jiki, an rubuta 'AHUBBIK' wato ina sonki da dukkan zuciyata!
Daga ranar da aka daura aurenmu da Fa'izah na tabbatar Fa'izah alkhairi ce a gareni, kuma wani bangare ce ta cigaban rayuwata. Daga ranar na soma ganin budi takowanne bangare, aikina, nasara da cigaba cikin duk abinda na sanya hannu, mutunci da martabata a idanun iyayena suka karu.
A dalilin aurena da Fa'izah ne mahaifiyata ta dawo da soyayyar ta gareni wadda ada ta haramta mini saboda na ki karatu kuma na takurawa Fa'izarta. Ta kuma fifitani a tsakanin sauran 'yan uwana.
Kiyayyar da Fa'izah ke nuna mini tana kara min kaunarta ne a koda yaushe, tana nuna min ta san ciwon kanta, tasan mutuncin mahaifiyarta, tasan makiyinta, ta san masoyinta (in comparison to yaya Aliyu!). Tana hangen abinda ka je ya zo, tana hangowa kanta dacewa da rayuwa da wanda soyayya ce ta hadasu ba kamar ni data rika a matsayin makiyi ba, tunda (that's the way I proved myself to her). Kuma masu iya mmagana sunce "Makiyinka baya taba dawowa ya zama masoyinka". Wannan ne dalilin da yasa nake yi mata 'UZURI'.
A hakikanin gaskiya ba kin Fa'izah nake ba, WAUTA ce ta KURUCIYA domin in samu ABINDA NAKE SO, wato ita FA'IZAH. Idan kowa yace baya so.
Ni kaina nasan mutum ne miskili da akan rasa gane inda yasa gaba, mutane irina ba sa karantuwa (from every perspective). Ubangijin da Ya halicci zuciya Shi Ya sirrantata, Ya sanya ta zamo HIJABI a tsakanin 'yan Adam da abinda ke zuciyar su. Don su sirrinta al'amuran da Ya boye cikin zukatansu. Ina kaunar Fa'izah da dukkan ruhi, zuciya da bargon jikina 'but I cant express, neither explain.
Bakin da ya furta sharri, zalunci da rashin kirki, ya dawo yana furta SO (will never be trusted) don haka Allah Yayi zamu cigaba da rayuwa ni da Fa'izah. Burina ya cika tunda ta zamo mata agareni kuma wani babban JIGO na rayuwata, kuma wani BANGARE na jin dadin rayuwata tunda mallaki na ce ko da har abada ba zata yarda da ni ba. Zaman mu tare a hakan ya fiye min zaman kuncin da na dandana a Ukrain ina azabtuwa daga soyayyarta.

THE ISSUE OF MOMIN ABU
Sha'ani na da Momin ABU kamar yadda Fa'izah bata fahimce shi ba ko ince bata sani ba. Babu kuma wanda ya taba tararta ya gaya mata, Momin ABU bata daga cikin Zuri'ar Abubakar Bamalli.
Kamar yadda ya faru tun muna kanana, an tura Baban ABU bautar kasa Jihar Taraba, kamar yadda Baban Kaduna yake bamu labari, yana (service) din ne a gidan marayu na Jihar Taraba (Taraba State Orphanage Home).
Maimunatu marainiya ce, da ta tashi ba uwa ba uba, ba dangi a gidan marayu. Kamar yadda Baban ABU ya baiwa su Baban Kaduna labari, ni kuma a lokacin bani da wayo da nayi wayo ne naji labarin a bakin Hajjah.
An tura Ahmadu A.B bautar kasa Jihar Taraba, acan yaga Maimunatu, inda yake (serving) wato Taraba State Orphanage Home. Tana daga cikin 'yan mata goma a gidan marayun da suka kai minzalin aure, sannan mafi nutsuwa da kamalar cikinsu.
Ya je ne a matsayin malamin (secondary school) dinsu, yana koyar dasu kimiyyar noma, wato (Agricultural Science).
Maimunatu hazikar yarinya ce wadda Allah Ya yiwa baiwar kwakwalwar fahimtar karatu.
Kamar yadda yake a cikin (psychological nature) na kowanne malamin makaranta. Wato kaunar hazikin dalibi da girmama shi hakan ce ta faru tsakanin Baban ABU da Momin ABU har kuma ya rikide zuwa soyayya mai tsafta da inganci. Wadda tausayi da kauna, shi ne tubali da ginshikinta.
Kamar yadda Hajjah ke bamu labari, ta ko'ina Ahmadu A.B ya hanga ya tauna baiga ta inda marigayi mahaifinsa A.B zai amince masa auren Maimuna ba.
Bar ta auren zumuncin gidansu da suka maida shi farillah, kuma shika-shikan rayuwarsu, rashin ASALI wani babban abu ne domin kashi tamanin cikin dari na yaran dake gidan marayu har abada ba'a sanin asalinsu ko ganin wani nasu. A haka suke zuwa duniya su koma, cikin kiyayewar Ubangiji.
Wannan yasa Ahmadu A.B cikin tsaka mai wuya da tunanin abin yi. Na farko ba zai iya barin Maimunatu ba, maganar ma ace ya hakura da ita bata taso ba, domin ba karamin sonta yake ba, kuma shakuwar dake tsakanin su ta wuce tunanin kowa.
Sai ya yi tunanin wadda yake ganin zata fisshe shi saboda KURUCIYA irin wadda ta faru dani akan Fa'izah!
Ahmadu yaje kotun Musulunci an daura musu aure da Maimuna ta yin amfani da malaman shi na Jami'ar Ahmad Bello. Ya dauko Maimunatu ta kawowa Hajjah, a lokacin da cikin Fa'izah wata bakwai.
Mafari kenan dana tashi cikin nunawa Momin Fa'izah wariya da kabilanci a tsakanin su Mama, Aunty Hauwa da tsararrakinta. Shi din ma na fatar baki ne, ko kallon banza ban taba yi mata ba, sannan a bayan idonta musamman idan Fa'izah ta bani haushi.
Hali ne na zuri'armu baki daya (kabilanci) da 'ethnocentrism' duk wanda ba daga zuri'ar A.B ya fito ba, to fa ba cikakken mutum bane.
Da Hajjah da marigayi suka ji kowacece Maimunatu hankalinsu ya tashi kwarai, sunyi fushi da Baban ABU fushi mai tsanani, sannan 'punishment' dinsa shi ne 'suspension' daga duk wani abu da ya shafi zuri'ar A.B zuwa wani lokaci da basu kayyade ba. Duk Ahmadu ya ce yaji ya gani, indai zasu barshi ya cigaba da rayuwa da ita.
A lokacin hatta zuwa daurin auren cikin gida an dakatar dashi, haka itama, zuwa wani sha'ani na mata kamar biki ko suna duk ba’a bukatar su.
Zance ko da Baban ABU ya damu to kadan ne tunda gogaggen dan boko ne wadanda (time matters a lot for them) wato lokaci abu ne mai matukar muhimmanci a garesu. Sai ya yi amfani da lokacin 'suspension' din nasu ya koma makaranta ya nemi (degree) na biyu. Ita kuma ya sanyaata a (school of Nursing and Midwifery).
Ba da bata lokaci ba yana kammalawa A.B.U suka dauke shi 'lecturing' ya kuma samu gida a cikin makaranta, domin ada a gidan haya suke domin gidansa na A.B Quaters an hana shi mukullin an rufe. A lokacin tuni an haifi fa’izah har tayi wayo.
Kafin A.B ya rasu ya yafewa dansa Ahmadu, ya kuma karbi Maimunatu a matsayin surukar kaddara, bayan haihuwar danta na biyu, wato Abdallah, saboda kyawawan halayenta da zuri'a da tazo musu da ita mai albarka mai kama da nasu 'ya'yan. Domin Abdallah sak mahaifinsa, Fa'izah kuma Aunty Rabi ta debo, sai dai ta dauko duhun Maimunatu. Dama kuma abinda basa so kenan na auren bare, domin zai haifar da sauyin kamanni a cikinsu. Amma tabbas da Maimunatu na da iyaye, da sun maida ta ga iyayenta ko Ahmadu zai mutu, sun karbeta ne saboda MARAICIN ta.
Nayi nadama, nadama mai yawa akan duk abinda na yiwa Fa'izah! Nadamar da bani da tabbacin akwai ranar da Fa'izah zata karbeta, tunda ba zata taba tsayawa ta saurari kalaman bakina ba. Fatana Allah Ya bani iko da damar nunawa Fa'izah kuskurena da karbarsa kafin na kwanta dama... Ya yaye min wannan ginshiran, domin ni kaina yana wahalar dani...".

Da na kawo nan kuka na rikice da shi sosai, na kasa ci gaba da karatun, na ya da littafin. A guje nayi daki na ina kuka wiwi, na fada tsakiyar gadona na ci gaba da rasgar kuka.
Nayi kuka-nayi kuka har naji babu dadi. Wannan shaukin ke kara mamayar zuciyata yana kara habaka. Wanda da nayi tsai da zuciyata na fahimci abinda bana so in fahimta da gangan. Wato SON FA'IZ ne yake mamayata cikin kowanne dakika na bayan da ya barni. Wani irin so mai cin rai, da tafarfasa zuciya.

***
[1/4, 12:24 am] Takori: ***
Washegari haka na tashi sukukui! Babu kuzari ko yaya a cikin jikina. A wannan lokacin, babu abinda nake tunani illa hanyar da zan bi na gyara girgidadden aurena tun lokaci bai kure min ba.
Kaunar Fa'iz da soyayyar sa ke lallasa ni ta duk hanyar da suka ga dama. A duk lokacin da na daga ido na dubi tangamemen hotonmu (window size) da aka manna a (main-palour) kamar za muyi magana, sannan tsananin kamar mu da juna ta fito sosai a hotunan. Kyau ne ke bugun kyau na mallawan usili, sai kwarjini da ya dara mini da wasu ilhamomi na daban da aka halicci Fa'izun dasu da ban taba ganinsu a tare da wani da namiji ba.
Nakan tuno abubuwa da dama na irin cin kashi da rashin arzikin da na shekara yiwa iyayena da 'yan uwana akan auren mutumin da na tabbatar ban dace da kowa ba cikin duniyar nan face shi, sai inji na tsani kaina da mata masu irin halina na kafiya da taurin zuciya, riko da zuciyar rashin afuwa da yafiya, bayan dukkaninmu da Allah ba Ya hakuri damu, Yana afuwa a garemu albarkacin mai albarka, da bamu kawo yanzu ba.
Hakika da Allah Baya afuwa ga al'ummar Annabi Muhammadu (S.A.W) da tuni an shafemu a doron kasa kamar yadda aka shafe al'ummar sauran Annabawa da suka gabacemu saboda kura-kuran da muke tafkawa Ubangijinmu da tsakanin mu kanmu 'yan Adam.
Misalin karfe uku na yamma na dauki waya na bugawa Momi, jikina a matukar sanyaye, kamar yadda zuciyata ta mace, babu karsashi ko kankani a tare dani.
Jin muryar Momi tana yi min sallama wani matsanancin tausayinta yazo ya lullubeni. Kenan ita bata da kowa a duniya da zata kalla ta ce nata ne, bayan mijinta. Baiwar Allah koda wasa bata taba gaya min ba don kar hankalina ya tashi.
Ni Allah Ya bani dangin kamar ruwa masu kaunata da son yiwa rayuwata gata amma nake wulakanta su ina bata musu rai akan abinda sunyi ne amma sai nafi kowa cin ribar sa. Wato zaba min miji daya da daya a cikin 'ya'yansu wanda sun tabbata ko bayan ransu zai rikeni amana kamar rikon da uwa da ubana za suyi min.
Momi taji nayi shiru, bayan ta jima da amsa wayar, ta ce.
"Lafiya?"
Na ce, "Lafiya".
"Kin kirani kuma kinyi min shiru".
Na sharce hawaye da suka yo wani irin ambaliya akan kuncina, sai naji ba zan iya tambayarta komi akan rayuwarta ba, kada in tado mata abinda ta riga ta manta dashi, tana cikin rayuwarta mai tsafta. 'And a total submission to ALLAH' da yadda Ya kaddara mata rayuwar. Na kasa 'controlling' kaina da tausayin Momi, kawai sai na fashe da kuka gaba daya.
Kuka kawai nake ta rusa mata a wayar har na gaji don kaina bata katse ba, kamar yadda bata nemi taji dalilinsa ba, balle ta lallashe ni akansa. Sai da nayi mai isata sannan naji muryarta cikin sanyi tana magana.
"Na rasa ke wace irin yarinya ce, na rasa a cikin mutane ke wacce iri ce, na rasa abinda yake damunki, ba mamaki gata ne yayi miki yawa.
Menene aibun Fa'izu? Me kika fishi? Dame kike takama nayin butulci da irin wannan miji da Allah Ya baki? Har sai yaushe zaki shiga hankalin ki kisanAnnabi Ya faku? Duk sa'o'inki da tsararrakin ki kowanne na dakinshi cikin kwanciyar hankali, ga albarkar aure, sai ke don dai ki tabbatarwa da danginku da cewa uwarki bare ce abinda suke gudu a bare dai-dai ne.
To ni dai wannan hali naki ba a wurina kika gado ba (kafiya da taurin kai na rashin tunani) ke kadai kika san inda kika kwaso abinki. Yanzu da kika ki kwantar da kai kibi Fa'izu ribar me kika ci? Meye ribar zaman da kike yi? Ke ba ga ladar aure ba, ke ba kwanciyar hankali ba, ke ba ga komawa karatun ba, ba wan ba kanin wai karatun dan kama... Saboda ke shashasha ce kuma dabba, wadda bata san ciwon kanta ba ko?"
Hawaye ya ci gaba da wanke min fuska, ita bata san cewa tausayinta da nake ji ya rinjayi tasirin fadan da take yi min.
Muryata cikin sanyi da shasshekar kuka mai yawa, na ce.
"Don Allah Momi kiyi hakuri, ni yanzu babu abinda yake damuna. Hakuri zan baiwa Fa'iz din ma in ya dawo. Insha Allahu nayi alkawarin daga yau ba zaku sake jin wani abin assha daga gareni ba. Shima Baba zanzo in bashi hakuri.
Walida nake so ki taimaka min tunda sauran sati biyu su koma wannan hutu, ba wanda ke zuwa min daga Giwa har Jabi Road, ni kadai cikin wannan katon gidan... Don Allah Momi...".
Na rushe da kuka sosai wanda ya tayar da hankalin Momi, maimakon kalamaina su sanyaya mata domin kukan nawa mai zafi ne irin na kauna da tausayin DA ga MAHAIFIYARSA, yafi karfin ace akan fadan da tayi min nake yinsa.
Wani irin kuka ne mai fitowa tun daga karkashin zuciya na wani abu mai nauyi da ya taba rayuwar mahaifanka.
"Don Allah don Annabi Momi kiyi hakuri, ba zan kara ba... ba zan sake ba... Na tuba na bi Allah na bi ku... Zan bi Fa'iz sau da kafa kamar yadda kike bin Baba, ba zan sake tada muku hankali ba... Ni kaina na gaji, na gaji da wahalar da kaina, ina son mijina yanzu. INA SON SHI Momi...".
Banga Momi ba, amma nasan murmushi tayi, (a very deep smile) kasancewarta mai yin murmushi mai fidda sauti. Ta jima bata yi magana ba, daga baya kuma ta yin.
"Ki yiwa Abubakar waya, ki nuna nadamarki gareshi. Wannan zai sa shi watakila dawowa nan kurkusa. Amma in ba haka ba, mawuyaci ne yasan hakan, har ya yi marmarin dawowa gareki. Babu kunya tsakanin mace da mijinta, akwai inda ya dace aji kunyar, amma ba a irin nan ba, musamman idan baya ganin ki".
Na ce, "Ba zan iya ba Momi, wallahi bazan iya ba, ina jin kunya, ina jin nauyinshi sosai domin sai a yanzu na fahimci abubuwa da yawa wadanda ada ban fahimta ba. Tsiyar dana tsula tana da yawa, tijarata gareshi mai yawa ce, da kyar in zai yarda ya kara hada rayuwa dani...".
Na ci gaba da kuka mai tada tsigar jikin mai kaunar ka, musamman UWA!
A sanyaye Momi ta ce, "Ai sai kiyi tayi, tunda kinga shi zai fisshe ki. Ki tsaya jin kunya ya dawo da matar dake son shi, ina ce shi kenan ko? 'It's not too late for you to correct your misdeed' ba'a tsufa da tuba muddin ana raye. Mutuwa ce kadai shinge ga tuba da nadamar bawa. 'Atleast ya san kinyi, koda ba zai karba ba... Walida da Kausar duka na nan zuwa".
Jikina duka ya saki a yayin da Momi ta kashe wayar. Na kifa kaina cikin kujera na rasa me yake min dadi. A yinin ranar baki daya, na kare shi ne cikin tunanin ceto kima ta a idon Fa'iz da sauran son, in akwai.
Yamma lis misalin karfe shidda na yamma, direban Bababn ABU ya sauke Walida da Kausar a harabar gidan. Walida tayi sallama ta aje (trolly) dinsu, ta dube ni duk nayi firgai-firgai dani, tun safe banyi wanka ba ga yunwa, tun kofin ruwan lipton dana zuba ma cikina da safe. Da yake yarinya ce mai hankali bata yi magana ba, gaisheni kawai tayi ta aje mayafinta ta shige (kitchen) ita kuwa Kausar wai wanka zata yi.
Uffan na kasa ce masu, ashe Walida girki take yi, sai bala'i kamshi mai tada tsohuwar yunwa naji yana bugun hanci na kafin ince wannan ta aje min (tray) a gabana, (fried-rice) da taji kayan lambu tayi sharr da farfesun koda na tiriri da tashin kamshi.
Nayi ajiyar zuciya na dubeta cike da kauna a raina, na ce.
"Dan uwa rabin jiki".
Na sa cokali na soma ci hannu baka hannu kwarya. Rabona da su tun ranar da Fa'iz ya kore su.
Kausar ta fito ta dau wanka ta dau gayu da tirare dai-dai sanda na kammala cin abincin. Ta samu kujera ta hakimce ta kunna t.v tashar 'Bollywood' na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login