Showing 12001 words to 15000 words out of 42033 words

Chapter 5 - Zumuntar kenan book by Sumayya Abdulkadir Takori.txt

da nake yi na fito zuwa (kitchen) din. Ashe kallo na sama, babu irin na'urar girkin da iyayenmu basu jera min ba, komi na cikin (kitchen) din (orange) ne (freezer) da (cooker) sune (lemon-green). Na ba da ajiyar kallon zuwa gobe da safe na fara abinda ya shigo dani.
Cikin minti goma sha biyar na gama da yake dankalin ma a (fryer) na soye shi bai dauki lokaci ba. Na jera a (tray) yana zaune na dora a (dinning).
Naga mamaki a fuskarsa da na juyo zan koma daki sai na tuna ban ajiye ruwa da lemu ba, kada inci gaba da aikina ya kara taso ni. Na koma firjin dake dab da (dining) na ciro masa (Pepsi) da ruwan Faro.
Har na kai bakin kofar daki na, ya ce.
"Aunty Fa'izah saura ruwa da lemo".
Na cuno baki na harari tebirin sai shima ya kalle shi. Dariya yayi.
"Aunty Fa'izah ta soma zama (full-house wife): It's a job weldone!".
Da sauri na shige daki bana son zuciyata taji yabon da yayi mata.

Wani gashin kaza yake ci yau da bai taba cin mai dadi da taushinsa ba, koko santin hannun daya sarrafa shi ne, bai sani ba. Kunnensa har motsi yake musamman da abin ya hada da yunwar wuni guda. Tun barowar mu Minna bai ci wani kwakkwaran abinci ba, sai ruwa da lemo yake daddaka. Tunda ya fara bai yi motsin kirki ko magana ba, sai da ya zuge kasusuwan katuwar kazar nan gaba daya.
Da ya kammala kasa jurewa yayi sai da ya dangana da kofar dakina. Ya rausayar da kai yana rike da kofar.
"Aunty Fa'izah, daga yau, a duk inda muke, zaki gasa min kaza da (chips) da wadannan yatsun naki, a kowanne dare matsayin (dinner) dina. Zan samu Fa'izah na?"
Ban amsa ba, sannan ban kalle shi ba, na ci gaba da jera kaya cikin (wardrove) kamar bada ni yake magana ba.
Ya gaji da sauraron amsata, ya aro (extra) hakuri ya kara akan wanda yake da shi, murmushi ya karawa zuciyarsa. Wani bangare na zuciyarsa na cewa, "There's alot of improvement. Is a matter of time!".
Washegari ban tashi da wuri ba sai misalin karfe tara na safe. Badon komai ba sai don sanin babu nauyin sallah akaina. Nayi wanka ba tare da wata kwalliya ta kuzo ku gani ba. Babbar rigar shadda mai aikin surfani na sanya, nayi daurin kai sassauka da kallabinta, na fesa turare 'Escada sentiment' na nufi (kitchen).
Ruwan tea na fara dorawa a (water heater) sannan na debi dankali dai-dai cikin mutum biyu na soma ferewa. A haka ya cimmani cikin madafin. Ya hade cikin bakar shaddar rini mai ratsin ruwan makuba, yayi sharr yayi (fresh) kamar sabon ango sai fesa kamshin '212' yake.
Ya saki murmushi mai kayatarwa cikin fadin, "Good morning Aunty Fa'izah".
Na ci gaba da firar da nake yi, ban kalleshi ba sai ta gefen ido, haka bai samu amsar gaisuwarsa ba. Bana son wannan kulanin da yake yi, na fi son tunda zama tare ya zama dole, to kowa ya ci gashin kansa kamar yadda ya ce a farko kamin in shigo gidan kowa yayi wadda zata fisshe shi, koko rayuwar da yayi amanna da ita.
Ya dauki wata wukar cikin fadin, "Bari in tayaki ba don halinki ba".
Ya fara ferewa da gani bai iya ba, sai zaftare tsokar dankalin yake. A haka aka yi firar aka zo wajen daddatsawa, nan ma ba iyawa yayi ba sai yanka su yake ba fasali, wani kudi wani bashi. Bai ankara ba ya sharce dan alinsa da wukar. Nan da nan jini yayo ambaliya. Ya yi saurin ya da wukar ya tara danyatsan a famfo jinin na bin ruwa.
Sai naji tsigar jikina na tashi ganin yawan jinin dake fita. Kamar yadda ya ce din ne idan babu soyayya akwai kauna ta 'yan uwantaka. Ban san sanda na wuce daki na dauko turaren dana fesa ba na dawo na kashe famfon (sink) din da ya kunna na soma fesa turaren akan yankar. Ban fasa ba sai da gudun jinin ya tsaya. Na gutsiro (tissue) na danne yatsar, duk kokarin da zan iya nayi wurin ganin bamu hada ido ba. Shima bai takura da sai mun hada din ba, kawai cewa yayi.
"Thank you!".
Na bi na tattare fuska na hade wuri guda cikin raina cewa nake, " Ni bana son wani tayin aiki, a barni da likitancin da ban karanta ba". Amma a fili aikina na ci gaba da yi bance komai ba.
Sai ya jingina da kabinet din (kitchen) din yana kallon yadda nake ayyukana cikin nutsuwa da hada hankali guri guda.
Na bude firji na debo kwai ina fasawa sai ya baro jikin (cabinet) din ya iso gareni. Cikin murmushi ya ce.
"Let me help you".
Na ce ciki-ciki, "Barshi nagode".
Bai karbi godewar da nayi ba ya dauki daya, maimakon ya hada shi da uwansa ya fasa ko ya fasashi da wuka, sai ya hada shi da goshina ya juye a fadi ka mutun da nake juyewa. Ya sake daukar daya, ya hada shi da tsinin karan hancina shima ya juye ya yar da bawon a (dusbin).
Nan da nan ya fashe su duka guda takwas din a goshi da hanci na, ko a ina ya koyo wannan fashin kwan oho! Nan take na soye shi tas na gama duk abinda nake yi yana tayani. Amma cikin raina bana godewa, a kyaleni yafi mun.
Karar kararrawar shigowa tasa na samu yadda nake so, wato ya fita ya barni. Can na jiyo tashin sautin su shi da Surajo ne.
"Na dauka tuni ka kama hanya?" Cewar Fa'iz.
"Ni na isa in tafi, ban zo naga dakin Madam rikici na sayi baki ba?"
Tare suka zauna kujerun falon rike da hannun juna.
Kai sai yaushe zaka wuce? Ko kazo kenan".
Ya ce, "Two weeks off gareni, yau kuma kwana na hudu, saura kwana goma inaga".
"Tare zaku wuce amma?" Surajo ya tambaya.
"Don Allah ka rufa min asiri kada ka ballo min liki irin wanda ka saba ballowa, na samu an daina yi min hayagaga ko ba'a bini ba na gode".
[1/4, 12:23 am] Takori: Abin ya baiwa Surajo dariya, in wani ne ya bashi labarin Abubakar Mukhtar (sunan da suke kiranshi) zai koma haka akan mace karyatawa zai yi. Soyayya ba karya bace, a yau ya kara yarda da hakan. Ya shiga girgida kai kamar kadangare.
"Tana ina ne? Ban ji motsinta ba. Ga hotunan (cocktail) din ku fa na wanko".
Ya amsa ya aje gefe ba tare da ya bude ba yayi mai nuni da (kitchen) da girar shi.
Dariya Surajo yayi, "Kace har girki ake mana!".
Shima dariyar yayi, "Mai dadi kuwa".
Suka yi ta dariya kamar wasu shashashan madina, sai da suka yi mai isarsu tukunna.
Surajo ya ce, "To yanzu yaya za'ayi batun tafiya UK?"
"Sai yanda ta yiwu Surajo, bani da sauran dabara, duk abinda zan iya nayi, na bada hakuri, nayi fada, nayi wa'azi, nayi nasiha. Zan iya cewa (there are lots of improvements) sai dai bata yi min magana, sannan in nayi bata amsa min da baki, sai dai tayi a aikace. Kuma ba musu, ba rashin kunya, duk abinda nasa ta daga jiya zuwa yau tana yi".
Surajo ya ce, "To Alhamdulillahi, hakuri (still) ba abinda baya bayarwa. Kuma ina ganin inta bar kasar zuwa inda bata da kowa komai zai tafi (normal)".
Ya ce, "Nima tunanin da nake kenan, amma Surajo (how easy is that)?"
Dai-dai lokacin da na fito daga (kitchen) dauke da fadi ka mutu ina jerawa akan (dining). Duk suka yi shiru kamar ruwa ya cinye su. Jikina ya bani zancena suke yi. Zan koma (kitchen) Suraj yayi gyaran murya.
"Madam ba gaisuwa yau ma?"
Ina tafiya ban tsaya ba na ce, "Ina kwana?"
Ya ce, "Lafiya lau, sannu da aiki".
Na ce, "Yauwa".
Na shigo don dauko filas din ruwan zafi. Suka dubi juna suka yi murmushi.
Tare suka karya kumallon shi da Surajo yana tambayarsa abinda yaji masa ciwo. Ga ammakin Fa'iz sai ya kasa gaya masa kada yayi masa dariya don a hakan ma bai daina mamakin canzawarsa da rauninsa ba, gani yake yayi min sako-sako da yawa. To abin ne shima yazo amsa 'beyond comment' (sunan wani ganyen shayi), idan yana gaban Fa'izah manta kansa yake da (identity) dinsa.
Cewa yayi yankewa yayi da reza ya ce.
"Kai me ya hadaka da reza kamar wani wanzami?"
Ya ce, "Don Allah ka kyaleni haka Surajo, kwakkwafin ka ya isheni".
Wata irin dariya Surajo yayi wadda ke nuna ko dai bai gano ba to ya kusa ganowar. Ni kyale su nayi na koma daki na kwanta don rama bacci.

***
Ban jima da kwanciya ba bacci ya dauke ni, ba ni na farka ba sai azahar. Nayi wanka nayi (brush) ba don banyi na safe ba sai don inji dadin cin wani abu. Domin da mahaukaciyar yunwa na tashi. Na fito falo na duba (dining) na tarar da (plate) daya da basu taba ba, na hada 'tea' mai kauri na fara warware hanji na dashi sannan na zauna na soma ci. Na kammala na kwashe komi na hada da wadanda nayi amfani dasu a (kitchen) na wanke. Na adana komi wurinsa.
Dana kammala sai kadaicin ya isheni, na kasa zama wuri daya. Tunanina ya bani in zagaye gidan cikinsa da wajensa in gani, sai na sanya mayafi da (slippers) na fito harabar gidan na zagaya baya.
Dawisu ne guda biyar (peacock) mata da maza, wasu a kasa, wasu akan katanga sun bude kyawawan jelunansu abin gwanin ban sha'awa. Sai na gane sune ake maganar su jiya sun kwanta da wuri. Na debi dawar da na gani cikin buhu a kofi ina cilla musu da dai-daya. Sai ga wani saurayi ya bullo yayi min sallama, na amsa muka gaisa. Jiya ban kalle shi ba balle in san kamanninsa, da yayi magana ne na gane shi.
"Kai ne Ya'u?"
"Eh, ni ne Madam. Wannan aikina ne, don Allah ki bari zanyi, basu dade da cin abinci ba".
Nayi murmushi na ce, "Ka dinga share kashinsu daga yau kawai Ya'u. Ina so na karbi ragamar ciyar dasu da hannuna, ina son Dawisu Ya'u".
Sai yayi dariya ya ce, "Hakan ba zai zama matsala gareni ba wurin Yallabai?"
Nayi murmushi nima, "Ba zai ji ba insha Allahu".
Ya ce, "To Allah Ya ba da lada Aunty".
Na amsa, "Amin Ya'u".
Ya wuce ya barmu, na ci gaba da jefa musu dawa duk suka yo gabana suna dauka da bakunansu masu kyau suna kara baza bindi.

***
Cikin wannan yanayin kwanaki suka ci gaba da mirgina mana har muka kwana goma, ranar Juma'a da yamma naji kugin mota, sai dai ba irin na motar Fa'iz bane. Na mike na daga labulen falo, sai na hangosu Walida, Shu'aib, Yahya, Junior, Abdallah, Kausar da sauransu suna fitowa daga mota, direban Mama Malam Sani ya kawo su, kowanne da 'yar karamar 'troller' din dana tabbata kayan sanyawarsu ne a ciki, yadda dai na gansu a gidan Ummi.
Wani irin farin ciki naji ya rufeni don dama ina fama da kadaici da kewar su. Har da hadawa da gudu wurin bude musu kofa, kowanne yabi lafiyar kujera yana wash-wash, 'ya'yan hutu malam. Manyan su Shu'aib ne kawai basa cewa wash din, sai gaisheni cikin girmamawa.
Na nunawa Junior dakin dake kusa dana Fa'iz shima (bedroom) ne (single) ba falo, ba abinda babu na ce su mazan su kai kayansu can, matan suzo mu hadu a nawa dakin sai ina-naka-saka nake dasu.
Kausar ta kwantar da kanta a cinyata kasancewarta shiru-shiru ba kasafai ta fiya magana ba.
Na ce, "Wai daga ina kuke ne?" Walida ta ce, "Gidan Aunty Ummi".
Na ce, "Tun (last week) dana baro ku kuna can?"
Suka ce, "Eh".
Kausar ta dago kanta daga cinyata ta ce, "Koro mu fa suka yi ita da Yaya Bashir, yau ya dawo bayan hutun mu bai kare ba".
Abdallah ya ce, "Kora da hali dai ba kora ta ku tashi ku tafi ba".
Nayi musu kallon son jin karin bayani, dariya na son kama ni. Walida ta dora bayani.
"Saboda Yaya Bashir ya dawo ta barmu a falo tun safe, sannan bata dora mana (break) da wuri ba, suka kyalemu yunwa na cinmu. Da ta fito bata hada mana ruwan wanka ba, ta ce kowa yayi da ruwan sanyi wai hitar (toilet) din gidan duka ta lalace. Ki dubi sanyin nan da ake.
Shi kuwa Yaya Bashir din kai tsaye daya fito ya ce mu hada kayanmu mu koma gida, wai mun cika mishi kunne".
Dariya nake kamar cikina zai fashe, Walid ya karasa.
"Tunda dama hutun sati biyu muka je sai yaya Junior ya ce muzo nan kawai mu karasa kwana biyun mu sai mu koma gida, don dama Monday duk zamu koma (school) ke kam mun san ba za kiyi mana abinda Aunty Ummi tayi mana yau ba".
Na janyo autan Momi jikina ina dariya, "Ina kuwa zanyi muku Walid? Ni farin ciki nake da zuwan ku, inma kun dawo gidan kwata-kwata ne (you are most welcome) dakunan gidan zasu ishemu".
Duk suka hau murna sosai.
Na ce, "Yanzu me zaku ci?"
Abdallah ya ce, "Chicken burger?".
Yahya da Junior suka ce, "Shinkafa da salad".
Shu'aib ya ce, "Quaker oat kawai zansha da 'peak' ta ruwa".
Kausar da Walid suka ce, "Wake da shinkafa da mai da yajin tafarnuwa".
Taashin hankali gobarar gemu, (inji hawwa lawan meturare) tawa ta sameni ni Fa'izah. Na fada cikin raina, naja numfashi.
"Uhm! Gaskiya abin naku (is too much). Dankari! Sunan wata jarida, dole Ummi tayi muku kora da hali har da sandan ma in tana dashi, in haka kuke kullum to tayi bala'in kokarin rike ku har kwana goma. 70% na abubuwan da ku ka lissafo bani da kayan hadinsu, kuma ko inada su jikina akwai jini da bargo ba zan iya ba. Chicken burger da Indomie kawai zan yi muku dukkan ku. Shi kenan?"
Gaba daya suka ce, "Eh, ya isa".
Banda Yaya babba (Shu'aib) shi harar su ma yake, ya ce.
"Ai basu da hankali ne".
Na ce, "Naga alama Yaya Shu'aib".
Gaba dayanmu muka shiga (kitchen) banda Shu'aib, aka zage ana aikin hada burger, mai yanka tumatir da salad daban, mai baking da blending tsokar kazar da za'ayi amfani da ita shima daban. Haka mai tsaga biredin da shafa masa mayonnaise da salad cream shima daban. Nan da nan aiki ya kammalu kowa da (plate) dinsa ina ta rabo Fa'iz yayi sallama ya shigo. Sai kuma ya tsaya turus! A bakin kofa yana kallonmu, hannunsa dafe da habarsa. Yake fadi cikin kidayawa da dan alinsa.
"1,2,3,4,5,6,7... duk a dan gidana? Ina zamu kaiku? Gaskiya ba zai yiwu ba, ba kuma zata sabu ba wai bindiga a ruwa. Banda dukkan ku taron mahaukata ne ana zuwa gidan mutane ba (notice in this century?) Kuma wai kwana? Ba daya ba har biyu? (Look at you all with your noses like hippopotamus's". (Dube ku duka hancinanku kamar na bauna).
Suka aje lomar burger hankali tashe, rai bace. Ya samu kujera ya rage tsawo, ya dora kafa daya kan daya yana karkada 'yan mukullayen motarshi, ya sake fadin.
"Wai da ba gidan Ummi na ganku ba?" Walida tayi rau-rau da ido, "Ai sun koromu...".
"Au, shi ne ni aka zo aka tare min? Ga gidan dan iska ko? Abokin wasan ku?" Suka yi shiru tsuru-tsuru dasu abin tausayi, da alama wani abu ya bato masa rai a waje yazo ya huce a kansu.
"To kuje kuci abincin duk kuzo in kaiku Jabi Road, ba mai kwanar min a gida".
Kausar ta sha mur, Abdallah ya turbune, Junior ne mai karfin halin musantawa.
"Haba don Allah Ya Fa'iz! Ka barmu mana? Don kwana biyu kawai?"
Yahya ya yi kicin-kicin da fuska, "Kaima in kaje gidanmu ai Mama bata korar ka, daki ma take baka".
Fa'iz ya fiddo ido waje saura kadan dariya kufce mana ni da Shu'aib, ya ce.
"Kuji min marasa kunyan yara, ina fade kuna fade? To wallahi ba zaku kwana ba, ko ana dole? Bana son bakuntar, aje na gode. In ba wuni ba kada wanda ya kara zuwar min gida kwana, OK?"
Tsit suka yi, sannan suka karasa cinye abinda suke ci. Duka suka mike cikin sanyin jiki suka dauko jakunkunansu suna ja a hankali duk suka bani tausayi. Wato mai hali baya fasa halinsa. In ka jima baka hadu da mutum ba, tambaye shi wani abin amma banda halinsa. Shi kuma irin tasa ZUMUNTAR KENAN!
Idanuna suka cicciko da kwalla amma na rantse ba zanyi magana ba tunda nasan don inyi maganar ne kawai da bashi da alfarmar samunta haka kawai shi ne yake neman dalili.
Suka yi waje, ya tashi ya bisu yana, "Oya! Kuyi sauri ku shige muje".
Kamar ya samu wasu tumaki, haushi da takaici ya sake kamani. Na kudurta a raina duk yadda za'ayi yau ba zan gasa kazar da (chips) ba ladan korar min kanne. Sai dai nima ya kore ni.
Anan kan kujerar da nake zaune ina sakawa da kwancewa barci ya kwasheni, har ya dawo ya rufe ko'ina ya kashe kayan wuta ban sani ba. Sai ji nayi yana tashina ta hanyar kiran sunana da jan babban yatsan kafata.
"Yaya banga (chicken) akan (dining) ba?"
Na mike na kalle shi cikin matukar fushi amma na kasa magana, na mike tsam kawai na shige dakina na rufo kofa, garam!
Da safe ma kin fitowa nayi in dora karin kumallo duk da jiya ya ce in dora da wuri zai je Abuja da sassafe kan visar sa. Har bakwai da rabi ban bar gadona ba, duk da ba barci nake yi ba.
Ya tabbatar bazan fito din ba balle in bashi ko ruwan zafi, sai ya iso kofar dakina yana balle 'links' din hannun rigar shaddar 'hilton' dake jikinsa fara sol.
A bakin kofar ya tsaya yana fafin.
"Ran Aunty Fa'izah ya dade, an tashi lafiya?" Shiru babu amsa, don haka ya dora gundarin bayaninsa.
"Jiya nasan ban kyauta ba dana kori su Junior. Ina da dalilai na nayin hakan (which are all for our own goodness: Na farko kin sani Allah bai halicce ni da son hayaniyar yara ba. Na biyu ke ba kirki ne dake ba abubuwan da kike aikatawa ba lissafi a cikinsu, yaran nan kuma suna da fahimta sannan basu da mantuwa, gasu da daukar zance komi aka yi akan idanunsu sai ya koma kunnen Mama da Baba. Hatta rotsen da kika yi min a (Area One) Yahya ya gayawa Mama Junior ya gayawa Baba na kuma rasa ta inda suka jiyo. Haka kike so suje suce kina hararata, ba kya kulani wani zubin har tsaki kike mini komai da ya kamata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login