Showing 30001 words to 33000 words out of 42033 words

Chapter 11 - Zumuntar kenan book by Sumayya Abdulkadir Takori.txt

dashi din. Koda cikin mafarkin ne. Sai kuma na soma jin motsi cikin kaina, mai cewa in tashi in taka rawa, inyi juyi, in kuma rungume 'yar uwa shakikiya da ta kawo labarin, in bata tukuici da duk abinda na mallaka.
Maimakon hakan, sai na mike na sanya hijabin sallah ta dake bisa darduma, wanda nayi sallar subhi dashi dama da alwalata, na sauko na dungura goshina gaban Subhana, na tsarkake shi, na tsarkake tsarkin mulki da iyawarsa!
Duka walidar da Kausar suna kallona, sai suka kama yi min dariya suna tambaya.
"Duka farin ciki ne Yaya Fa'izah?"
Ban iya na tanka musu ba. Na lula a wata sabuwar duniyar ta daban, ta tunanin wacce irin tarba zan shiryawa Hafizin Hajjah? Fa'izun gidan Baban Kaduna? 'The one that is always hunting my dream?' Wanda tunanin ranar dawowar tasa ke zuwa min a farke, wato (ido biyu), cikin barci, ranaku da darare guda casa'in da nayi ba tare da na sanya shi cikin idanuna ba? A yau ga ranar tazo, 'so it will be a hectic and busy day; that needs planning and coordination'.
Na daga ido a hankali na dube su ina murmushi wannan karon, wani irin murmushi da bana jin na taba yin ni'imtaccen sa a rayuwata.
"To ai tafiya bata ganku ba, ajiye mayafin za kuyi ku tayani aiki ko? Mu gyara gidan, mu yiwa maishi girkin sannu da zuwa. Kuyi min kwalliya irin wannan da kuka caba, mai 'eye-shadow' da mascara, jambaki da lip gloss, ko 'yan matana?"
Walida ta saki dariya, Kausar kuwa zumburo baki tayi da ya sha AVON lipstick yayi jajawur, Walida na fadin.
"Kin burgeni Yayata, baki taba sa ni farin ciki irin na yau ba. Allah Yasa ki dore da hakan, Yasa ki cigaba da hakan har zuwa karshen rayuwar ku, ko mu ma 'yan baya ma yi koyi dake ko?"
Murmushi nayi cikin matsanancin nishadi, "Sai kuyi ta addu'a ya yarda ya amshi tuban nawa, ba kwa ganin yadda yayi 'deleting' dina 'from the screen of his sight and mind?"
Walida murmushin tayi itama, “Ni na gaya miki zai yafe miki, yana sonki yadda ba kya zato. Idan daso kuma ba aibi, sai dai 'FUSHI' wanda ba inda yake zuwa. DOn baki san me ya ce min dazu ba".
Na kamo hannunta da sauri na zaunar a kusa dani.
"Me ya ce miki Walida? Eye, gaya min? ".
"Cewa yayi "Gyara mata bargon rufar garin da sanyi, tunda ruwa ake". Da na duba sai naga da gaske bargonki ya yaye daga kafafunki, na gyara miki. Ya ce, "Kin gyara?" Na ce, "Eh". Sannan muka yi sallama. Don haka zai fi kowa farin ciki da kika gane kuskurenki, ki ka amshi laifinki. Ki ka kuma yi dammarar gyarawa.
Na lumshe ido a hankali ina mai gasgata kowace kalma dake fita daga bakinta.

***
Muna (kitchen), abinda zamu karya kumallo dashi muka fara hadawa, sai dai nasan ko naman Dawisu na ne na gidan nan yau aka soya, aka farfesa min ba zan iya ci ba, farin cikin da nake ciki, doki da kuzarin da har yayi min yawa ba zasu barni in iya kai komai baki na ba, bayan ruwan lipton, shima don ya warware min hanji, ba don ina da 'appetite' akanshi ba.
Kausar dake firar dankali ta ce, "UHm! Yaya Fa'izah in miki wani tsegumi mana?" Walida ta sanya bawon kwai da ta fasa cikin 'dustbin' ta ce.
"Uwar tsegumi, yau kuma gulmar wa za'ayi?"
Kausar tayi dariya, "Ba na kowa bane, naki ne. Don ni bana gulmar mutum sai dai in fadi akan idonshi don nasan illar yi da mutum".
Cikin matsanancin nishadi nake wanda har baya kwatantuwa, don haka dariya suka bani.
"Ina jinki Kausar, me ya faru?"
Ta dubi Walida tana dariya alamar akanta zata yi maganar kuma Walidar bata sonta.
Ta ce, "Kwanaki ko? Na ji Baban Kaduna yana gayawa Baban ABU a dakin Hajjah, an yiwa Yaya Walida miji".
Duka Walida ta kai mata nayi hanzarin boyeta na riketa.
"Wallahi ba zaki dake ta ba, ai ba ke take baiwa labarin ba ni take baiwa. In ba zaki iya ji ba ga hanya ki fita. Ina jinki Kausar, wane ne mijin?"
Kausar dake tuntsira dariya ta ce, "Ki canka".
"In canka Kausar?"
"Eh, ki canka".
"A cikin A.B ne?" "Eh mana".
"Mus'ab?"
"Gaba dai".
"Abba?" "Can gaba dai".
"Sani?"
Ta ce, "Saura kiris".
Na ce, "Shu'aib?"
Tayi dariya, "Wannan ya mata nisa, yafi karfinta".
Na harareta na ce, "Badar?"
Tayi dariya, "Lallai kin manta magajin Ya Fa'iz wajen ginshira irin na 'ya'yan A.B".
Ta fara kular dani, na ce, Ke na baki gari wane ne?"
"A nawa zan fada miki?"
"Au, sai mun tsadance?"
"Eh Mana!".
Na ce, "To #500 zan baki cash ba cheque ba".
Ta mere baki, "Allah Wallahi yayi kdan".
Da yake a zake nake da son jin abinda zata gaya min, na ce.
"To #1,000".
Murmushi tayi, "Shi kenan sai mun gama aiki".
Walida dai na jinmu bata kara tofawa ba sai anan ne tayi tsaki, muka ci gaba da aiki duk na kosa a gama ta gaya min don Kausar miskilar yarinya ce, na san ko na ci gaba da na ci ba gaya min zata yi ba sai sanda ta ga dama".
Muka kammala muka baje a kasa kan ledar cin abinci muka fara karyawa, ko ince suka fara don ni abinda na ci din ba wani na azo a gani bane.
Ganin Kausar bata da niyyar gaya min har suka gama na kwada mata duka a baya, na ce.
"Ke don Allah ki gaya min mana, ko so kike sai jini na ya hau?"
Ta tintsire da dariya, ta kai kofi mug bakinta mai cike da kunun farar shinkafa ta kurba ta hadiye, ta ce.
"Gaskiya sai naci na koshi Ya Fa'izah".
Don haka nayi zuciya na kyaleta.
Amma da suka gama ta shiga wata sabgar haushi ya kume ni, na ce (kamar zanyi kuka).
"Uhm! Ke nake sauraro fa Kausar".
Ta ce, "Kai don Allah Ya Fa'izah, kya bari abincin da naci ya tsirga mini mana".
Ta sha toka abinta muna haka wayata tayi kabbara (call tune) din kenan. Na mika hannu zan dau wayar ina fadin.
"Ke don Allah kada ki fada min in kina kaunar Annabi, ko ba dade-ko ba jima zanji ne ai".
Kamin in dauka Walida dayake tafi kusa da wayar ta daga, ta ce.
"Hello Yaya!.."
"Eh ta tashi, abinci muke ci ma yanzun".
"O.k toh". Ta kashe.
Cikin zabura nake tambayarta, "Wane ne?"
"Yaya Fa'iz ne. Ya ce in kin gama cin abincin ya sake kira".
Kamar in maketa don takaici, muryata kamar ta wadda ta sha duka.
"Amma ai kina ganin mun gama ko? Tun dazu muka gama ci fa!".
Na karasa cikin karkarwar murya kukan takaicin Walida na neman kubce min ba da niyya ba. Ga idona ya ciko da kwalla. 'Yan banzan yaran nan sai suka kyalkyale da dariya.
Karfe goma sha biyu da rabi na rana sai ga Shu'aib, Ya'u ya biyo bayansa niki-niki da kaya, jakunkuna saiti biyu samfurin (Argos).
Na mike ina yiwa Shu'aib sannu da zuwa, Ya'u na shigo da jakunkunan falo. Ya zauna yana satar kallon Walida, ita kuma yana shigowa sai naga ta bar falon bata gaishe shi ba kamar yadda Kausar tayi, sai yasa murya yana kiranta amma bata dawo ba.
"Ke 'yar kauyen ABU... Ina Yaya Sa'id Na'ibi A.B Giwa?"
Cikin mamaki na ce, "Au, dama Yaya Sa'id ne mijin da Kausar ke fadi tun safe take ja min rai ta ki gaya min?"
Yayi dariya, "Nima haka naji ana fada, ni na ce a bani an hana ni wai tunda ni na furta ba za'a bani ba. Yaya Sa'idu za'a baiwa, amma ai munga wanda ya furta aka bashi ba tare da an tuna cewa shi ne ya furta din ba, saboda mu ne ba'a so kawai sai Yaya Fa'iz".
Murmushi nayi ya kuma matukar bani dariya da maganarsa. Ashe dai ba ni kadai nasan Hajjah tafi son Fa'iz akan kowa ba kowa ma ya ganeta ayi magana ta ce shima yafi kowa sonta, mu bama mata sai dai ta mana, Hafizinta fa? Komai nashi nata ne, komai ya samo ita yake fara tunowa kafin iyayen da suka haife shi.
Ban kai karshen zancen-zucin nawa ba Shu'aib na tsinkaya yana fadin.
"Ga kayan mijinki nan sun riga shi isowa, yanzu haka daga Airport din Malam Aminu nake, shi sai yamma zai iso wai sai biyar jirginsu zai sauka. Yaya Bashir zai je ya taho dashi ni yanzu haka Giwa zan wuce".
"Allah Ya kiyaye hanya Yaya Shu'aibu".
Na fada ina shiga (kitchen) don kawo mishi abinda zai ci a hanya ko da ba abinci bane ya samu na motsawa a baki.
Ya'u ya shigo da kayyakin cefane har da buhunhunan kayan abinci ya shiga (store) dasu wanda hade yake da (kitchen), sai nama nau'i-nau'i, nasa Kausar ta adana kowanne daban a (freezer).
Shu'aib ya mike zai tafi yana godiyar 'snacks' da dambun naman da na zuba masa a leda, ya ce.
"Af! KInga ko na manta da sakon Mama a mota, bari inje in dauko".
Ya koma ya dauko ya dawo ya miko min.
"Ta ce kowanne akwai takarda a cikinsa, yana dauke da yadda za'ayi amfani da shi".
Na amsa da hannu bibbiyu ina zabga godiya kamar shi ne Maman.
Na ce, "Ka turo min Malam Isah (direban gidan Baban Kaduna) ko ta waya ne zai maida su Walida Zaria anjima".
Murmushi Shu'aib yayi, "Ai yayarmu, haka za'a kora su 'so early' don maigidan ya dawo har an gama cin amfaninsu za'ayi (dumping) dinsu?"
Na harare shi cikin wasa, "NI ban kore su ba, su suka kori kansu. Tun safe suka hada kaya za su tafi da kyar na samu suka kai yanzu".
Shi dai ya fice yana min dariya, ya barni da guntuwar kunyata a katara. Cewa yake.
"'Yau Mama zata sha labari idan na dawo daga Giwa, zata yi murna da farin ciki kwatan-kwacin na a zuba ruwa a kasa a sha. Fa'izah, ta sauke tata GINSHIRAR ta Bamalli, saura Pilot Fa'eez Giwa".
Na ce, "Lala! Shu'aib ba ma haka da kai kada mu soma, kada kayi min sharri. Su Walida su suka nemi tafiya ni ban kore su ba".
Ya ja motarshi kowannenmu cikin matsanancin nishadi marar misali.
Ni da Walida muka share ko'ina na gidan nan kal-kal, muka goge, muka kade, musamman (side) din Fa'eez, da kaina na wanke (toilet) din shi na kawata da (toiletries) da turaren bandaki ko ina sai tashin kamshi da (atmosphere) mai dadi.
Na canza (bedsheet) din dakin da wani (light-blue) mai hade da (duvet) da Baban Kaduna ya bamu tsarabar Umrah ni, Ummi da Zanirah. Na feshe (bedroom) din da (room-freshner) na 'HARAMAIN'. Na kunna na'urar sanyaya daki duk da sanyin da garin ke dashi, nasan daga 'Europe' zai fito, don haka zai bukaci sanyin.
Sannan muka yi sallar azahar muka fada (kitchen). Da taimakon su Walida komai ya tafi dai-dai cikin dan lokaci, munyi faten acca da bushasshen kifi, baked moi-moi, tuwon shinkafa da miyar yakuwa da alayyahu da kabewa da tantakwashi zallah. Sai gashin 'Turkey' wato tolo-tolo.
A fannin abin sha munyi coconut and milk shake, carrot drink, sai zobo mai abarba da pinaplple flavour. Dukkansu fresh da na sarrafa da kaina.
Na ce a raina, "Yau babu 'chips', babu 'chicken', 'you need change HAFIZIN HAJJAH, as everything around us would completely change. Babu abinda LOKACI baya canzawa. 'With TIME change is possible in everything we do". (Lokaci yana canza komai).
Sannan na koma 'snacks', ba tun yau ba, ba tun jiya ba na sha jin Hajjah na ba da umarnin a yiwa Fa'iz (samosa) 'best snacks' dinshi kenan. Don haka shi kadai muka yi, muka adana komai inda ya dace.
Walida da Kausar suka gyara min komai suka goge min (kitchen) tas suka wanke duk kayan da muka bata, sannan suka shiga wanka.
Karfe hudu Isa direba yazo suka tafi muna cike da kewar juna, sai da Walida tayi hawaye.
[1/4, 12:25 am] Takori: Wankan da nake ninkaya ina yi cikin kwami yau (unexpressable) ne. Wani irin wanka (slow-slow) da ban taba yin irinsa a rayuwata ba. Fatar jikina ta wanku har santsi take da silki tamkar mai canza launin fata...
"Kazo ga jikin nan FA'EEZ, zan baka abinka, ba na yawon dandi bane naka ne, mallakinka ne, a yau sai yadda kayi dashi... Nayi kuskure Yaya Fa'iz, kuskuren da nayi farin cikin amsar shi tun a duniya na kuma yi dammarar gyara shi tun a duniya kafin Mahalicci ya tambaye ni shi".
Karar wayata ne ya katse min sambatun da nake yi, na mika hannu na daga. Mama ce.
"Yaya magungunan da na aiko miki dasu dazun Fa'izah? Kin shanye ko?" Cikin jin kunya irin wanda bai taba faruwa tsakaninmu ba, na ce.
"A'ah!".
"Dalili?" Ta tambaya.
"Aiki nake tun safe Mama, su Walida sunce yau Yaya zai dawo".
Wata matsananciyar kunya tazo ta lullube ni, na kuma kasa fadin wane yayan? Tunda yayun namu yawa gare su.
Tayi murmushi na manyance, "Shi bai gaya miki da kansa ba sai su Walida?"
Nasa hannu na kautar da zirin gashina dake disar da ruwa a jikina, na ce a hankali.
"Ya yo waya ina bacci, ya sake yowa ina cin abinci, daga nan bai sake yowa ba. Kuma laifin Walida ne da bata bani wayar ba, sai ta ce wai ina bacci, ko ta ce abinci nake ci don shirme irin nata".
Mama ta ce, "Ai shi kenan. DOn Allah kiyi amfani da kayan lefenki kinji Fa'izah! Ya gaya min baki taba amfani da duk abinda ya dauka ya baki ba. Sakon da Shu'aib ya kawo kuwa kada kiyi wasa da yadda na ce a cikin takarda kinji Fa'izah na?"
Tausayin Mama da wani bala'in son danta ya kara kamani, na kara kwantar da kai a cinyoyina na kasa magana. SHin ita din wacce irin UWA ce mai maida nata ba nata bane?
Ta ce, "Ba abinda kike bukata ta fannin kayan girki?"
Na ce, "Ba abinda Shu'aib bai kawo min ba Mama, har da wanda bana bukata duka ya kawo".
"Yayi kyau". Inji Mama.
Muka yi sallama cikin girmama juna. Ni na fara aiwatar da umarninta.
Wata irin kwalliya na soma da Voyal din Hilton pitch and maroun, kasancewata wankan tarwada sai kalar ta wani irin kwanta ta bi fatar jikina. Na dauki voyel din ne cikin kayan da Mama ta kira da lefe na a dinkensa na ganshi, dinki mai kayatarwa da daukar ido na doguwar riga budaddiya, sai dai daga sama ta kama jikin tsam. Na nada dankwalin a kaina ya kwanta lambam.
(Make up) dina bai yi yawa ba, (very cool and sexy). Don karawa aya zaki na dauko takalmi cikin kayan, (flat) ne pitch dan Italy na zura siraran kafafuna. Turaruka kala-kala nayi amfani da su, duk dakin ya dumame da kanshi mai sanyi da sanyaya zuciya.
Na karashe shanye romon kazar Mama, na shiga (toilet) nayi (brush) na fito na dawo falo na kishingide cikin (three seater) ina kallon tashar ALJEZEERAH. Dai dai lokacin da agogon bangon dake 'main palour' yua buga karfe hudu da minti talatin. A lokaci daya na murdo radio daga I-pad dina ina sauraron sashen Hausa na BBC, ni kaina ban san wanne nake sauraro ba tsakanin Radio da talbijin.
Sai dai babu wanda hankalina ke kansa cikinsu, hankalina ya karkasu ne. Wani ya tafi ga tunanin wace irin tarba zan yiwa Fa'izun in ya shigo? Sannu da zuwa ko sannu da hanya? Sannu da hanya ko ina wuni? Ni kaina ban sani ba.
Wata mutum ce ni din a yau dake ninkaya cikin maliyar SO, take neman a karbeta ko yaya ne a zuciyar da bata da tabbaci a kanta.
Daya kashin kuma ya lula ne cikin tunanin tarbar da shi zai yi min. 'Will I be accepted? Appreciated? Trusted? Believed? Ignored or abandoned???
Karfe biyar ta buga na soma waiwaye ina duban kofa, haka duk motsin da masu karanta labaran Aljezeera da na BBC suka yi tsammani nake shigowar mota ne, ko kararrawar shigowa falo.
Biyar da rabi... shida na yamma babu Fa'eez babu mai kama da shi. Bakwai na dare ta shude babu labarin Fa'eez Bamalli balle sallamarsa.
Na soma karaya, kwalliyar ta soma gushewa da kanta, Gwiwata ta soma sagewa da kagara da zakuwa. Mutumin da akace zai zo biyar na yamma, shi ne har karfe takwas na dare, babu shi babu alamarsa.
Da kyar na iya mikewa na bada faralin magariba da isha. Takwas da rabi na samu wayar Mama, ina dagawa ta dora da tamabayar da ta girgiza ni ko ince ta firgita ni.
"Fa'eez Malali ya soma isowa kenan? Ni ina nan ina ta zuba ido shiru, to kice da shi in ya huta Babanku na son ganinsa da safe kafin yaje ko'ina...".
Ban san sanda hawaye ya barke min ba, na soma shasshekkar kuka da ma kiris nake jira. Hankalin Mama ya tashi.
"Ke lafiya? Babu lafiya yazo ko kuwa?"
Cikin kuka na ce, "Bai fa dawo ba kwata-kwata, kuma babu wayarshi babu ta Yaya Bashir. Nayi (trying) ta Yaya Bashir din a rufe take. Shi kuma wadda ya kira da ita dazu da na duba sai naga ashe anyi (hidden No.) din".
Mama tayi dan jim! Kafin ta ce, "Ya isa! Nan da karfe tara in bai iso ba zan turo Malam Isa ya dauke ki, Babanku sai ya bi sawun su Kanon shi da Shu'aib, idan yayi tafiya irin wannan ba inda yake fara sauka sai nan Jabi Road, daina kukan hakanan, watakila suna Kanon".
Nayi shiru ina goge hawayena tana bani hakuri, da cewa kukana yana tayar mata da hankali.
Jikina a matukar sanyaye na aje wayar gefe, lokaci guda hankalina ya kai ga abinda ake fade a tashar ALJEZEERAH, tare da wanda BBC ke fadi duk a lokaci daya, wato;
"JIRGIN BRITISH DA YA TASO DAGA HAVERFORDWEST AIRPORT DA KARFE GOMA NA SAFE, YA FADI A SYCHELLS ISLAND TSAUNIN DAKE HADAKAR KASAR SINGAPORE DA......
Ihu da kururuwa na saka, wanda ya tafi tare da yin fatali da I-pad din da kafata ta kwankwatse a kasa, na mike tsaye ina ta kururuwa hade da INNALILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'OUN. Na dora hannuna duka biyar a kaina, wani irin azababben kuka na saka dake ketowa tun daga cikin hanji da koda ta, cewa nake.
"Noooooo!".
Na yunkura na doshi kofa hannuwana aka, juwa ta kwasheni ta kayar. Ban daddara ba na sake yunkurawa, burina in bar gidan zuwa inda za'a ce min ba dai dai naji ba, ko kuskuren hanyoyin sadarwa ne. Juwar ma bata yi kasa a gwiwa ba wajen sake kayar dani. Sai na soma rarrafe akan gwiwoyina dai-dai lokacin da wayar da ta fashe a kasa ke nata kuwwar duk da tsagewarta.
Da rarrafen na isa gareta na sata a 'handsfree' dukkan hannuwana da jikina baki daya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login