Showing 3001 words to 6000 words out of 42033 words
Chapter 2 - Zumuntar kenan book by Sumayya Abdulkadir Takori.txt
ya ja motar a hankali suka fita daga gate din gidan nasu.
Ummi ce ta fara hango shi ta tagar (kitchen) din wadda ke santar harabar adana motar su. Tayi ihu harda dan tsalle ta ce.
"Ya Fa'iz in town".
Suka fito da sauri ita da Bashir suka game dashi a main falonsu. Daga matar har mijin bakin su yaki rufo sai jera masa sannu da zuwa da yaya hanya suke yi yana amsawa da ka, yana dan yatsine fuska. Ya bi daya daga cikin lafiyayyun kujerun falon ya nitse. Takaici ko kishin yadda yaga Ummi da Bashir ne suna rayuwarsu babu abinda ya dame su duk sunyi haske sunyi kiba, koko tunanin tashi 'yar bala'in amaryar ne yasa shi yatsine fuska oho! Da irin tarbar da shi zata masa? Allah kadai Yasan ZUCIYAR MUTUM (sunan wani littafin TAKORI).
Suka zauna kusa da shi suna manne da juna. Ya dube su sai ya saki fuska.
"Mr. and Mrs.".
Suka hada baki wurin cewa, "Allah Ya taimaki angon Fa'izah!".
Ummi har da jinjina da hannunta.
Bashir dariyar shegantaka yake mishi ganin yadda ya zabge amma ba zai fasa halinsa na rainawa mutane wayau ba da ginshirar babu gaira babu dalili ya ce.
"Shin Pilot Giwa yayi ciwo ne?"
Ya ce, "Lafiyata kalau, me ka gani?"
Tare da cin laya kada su kawo mishi shegantakar da ba zai dauka ba, amma sai da Ummi ta ce.
"Kaima dai dear! Fa'izah's calamity mana! 'Yar banza Bakin Bunu Bata Baibaya...".
Ji yayi kamar shi ta zaga, kuma dai shi baya son a dinga shigar masa rigimarsa da Fa'izah ko ace tayi ba dai-dai ba, zai fi son ka zauna a gaban sa kayi ta yabonta kana bashi labarin rayuwarta fiye da nuna kana taya shi takaicin abinda take yi akansa. Ya share zancen da cewa.
"Shin kuna lafiya? Na same ku lafiya?"
Bashir ya ce, "Gani ya kori ji".
A yayin da yake tuttula mishi (fresh milk) din Peak cikin tambulan din dake hannun Ummi, ta mika mishi ya daga mata hannu.
"Barshi, bana tare da yunwa, Mama ta bani abinci na ci".
Ummi cikin rashin jin dadi ta ce, "Amma ta yaya zaka shigo gidanmu ka fita ko ruwa baka kurba ba?"
Kamar zata fashe da kuka, sai ya mika hannu ya karba ya shanye ya dire kofin bisa (center table).
"Na yaba da tsarin gidanku, Allah Ya ba da zaman lafiya. Ni zan wuce". Ya mike.
Dan uwa rabin jiki, Yaya Bashir sai yaji tausayin Fa'iz ya kama shi duk da basu cika shiri ba ya gano damuwar dake tare dashi da halin da ya shiga ganin irin rayuwar da suke yi shi da Ummi suka mike suka fito tare da shi.
Bashir ya ce, "Wai ina Fa'izar ne?"
Ba tare da ya juyo ba, kamar yadda bai fasa tafiya ba ya ce.
"Tana nan".
Ummi da Bashir suka hada ido suka yi murmuishi, shi kuma ya sake hade rai da fuska har da tsuke baki kada su kara tambayarsa game da Fa'izah, kowa yayi (minding business) dinsa. Ita kuma Ummi bata fahimci hakan ba, sai ta ce.
"Don Allah ka kawo min ita mu wuni yaya Fa'iz, na matsu in ganta, nayi-nayi tayi hakuri ta ki saurarona...".
Sai kawai ya samu bakinsa da furta, "Me kika yi mata?" Alhali bai yi niyyar yin furucin ba.
Ummi ta ce, "Matsalar mu ce, amma ka tambaye ta mana, ai kunfi kusa".
Sai yaji kamar shaguben da yake gudu suka yi masa. Ita kuwa Ummi tsakaninta da Allah ta fada, ta kara da cewa.
"Sai yaushe za ku tare mu zo rakiya?"
Ji yayi kamar Ummi ta zage shi, ya ce.
"Ummi, ina wasa dake? To babu rana babu wata!".
Dai-dai sanda suka kawo inda ya yi (parking), Shu'aib na zaune bencin megadi suna hira yana jiransa. Ya bude boot din motar yasa Shu'aib ya fitar musu da tsarabar da ya kawo musu. Electronics ne na amfanin (kitchen) cikin kwalayen su guda biyar samfurin 'Binatone' microwave, juicer, mixer da 'rice boiler' sai 'blander masu karshen (quality).
Shu'aib ya shigar musu da su gida ya dawo suka shiga motar suka tafi, Ummi da Bashir na godiya suna daga musu hannu har suka fice daga harabar gidansu suka hau titi.
Yana tukin ya dan juyo ya dubi Shu'aib ya ce.
"Yo kai in haka ne ai zaka yi min amfani wajen sauke kaya, shige muje Zaria kawai".
[1/4, 12:22 am] Takori: ***
Ban tashi kaduwa da al'amarin Fa'iz ba sai da na ganni cikin jihar Niger (Minna). Ya samu gefen wani titi yayi (parking) ya doshi wasu masu kirar wukake da ludaya na garin Minna ya yi cinikin wata sharbebiyar wuka gayawa jini na wuce, irin ta yankan shanu, suka yi 'yar magana da makerin, sai naga an fara rubutu a jikin wukar. Ya kunso wukarshi cikin takarda ya biya kudi ya shigo ya ajeta a gefenshi ya kunna mota. A raina na ce.
"Eh, gara kayi min yankan rago ya fiye mini da hada rayuwa da kai. Mugu, azzalumi, munafiki, mara imani. Ko kuma kayi min yankan kifi gunduwa-gunduwa zai fiye min kwanciyar hankali fiye da in karashe rayuwata matsayin matar Fa'iz Bamalli Giwa.
Uhh! Daga wurin masu wuka kun san ina Fa'iz ya dosa? Fa'iz shahararren kogin Nigeria da nake ji cikin tarihi da 'Geography' sanda nake sakandire, wato 'RIVER NIGER' ya nufa damu wanda an tabbatar yanki ne daga kogin Nilu (Nile). Can ya dosa damu gadan-gadan ya zagaye masu kamun kifi zuwa can inda babu mutane ko daya. Ya danna wani madanni jikin motar glassai bakake suka maye gurbin farare (tinc) suka rufemu ruf. Ya kwantar da kujerarshi baya sosai ya bita ya kwanta yayi matashi da hannayensa ya yi 'facing' dina (fuskantata) sai kuma ya yunkuro ya taso ya dauko wukar nan ya cireta daga cikin takardarta tana walwali da walkiya.
Duk da abinda na ce a baya na gara min ya kashe nin, yayi min yankan rago ko na kifi gunduwa-gunduwa amma a wannan lokacin da matuwar ta iso muraran sai na samu kaina da matsawa gefe na soma marmasa kalmar shahada tare da duk irin addu'ar da tazo bakina. Walwali take da walkiya inba za'a ce idona bane yake min gizo da sai ince har huci wukar take yi.
Sunan Allah nake kira a halshena da zuciyata, idanuna sun kankance sunyi wuri-wuri, amma babu hawaye a cikinsu sai firgita da razana.
Na tabbata yanzu Fa'iz ya fini hauka, na dubi rubutun da aka yiwa wukar a sace, "FA'EEZAH". Na fiddo ido kuru-kuru na sake makurewa jikin kofa. Fa'iz ya cillo mini wuka akan cinyata ya tube riga baki daya, har singiletin jikinsa itama ya cire yayi kira da kakkausar murya.
"Fa'izah!".
Subhanallahi-subhanallahi, Hasbunallahu wani'imal wakeel kawai na shiga furtawa, na runtse idanuna. Ban taba ganin namiji a tube ba balle kato mai girma irin Fa'iz, yayinda haiba da kwarjini na Fa'iz Giwa yayi min lullubi, ya kara fuskantata ya ce.
"Dauki wukar nan ki caka mini ko ki yanka ni karewar kiyayya kenan, ko kya huce bakin cikin zamowa na miji a gareki, ko kya yafe laifin da kike ikirarin na miki, wanda kika kasa yafewa! Kika kuma ki saurarona inyi miki bayaninsa. Idan kika yi hakan na tabbata zaki huce ba karya...".
Nayi salati na dire ba tare da na kai karshen sa ba na dauko sabo. Na ture wukar daga cinyata ta fadi kasan kujera, na soma murda murfin motar ko na samu ya bude in san inda dare yayi min amma ko gezau kofa bata yi ba, yasa (lock) ya kulle ta gaba daya. Cikin dakiya da tsare gida ya ce.
"Haba Fa'izah, (be brave) mana! Babu wanda zai sani, babu wanda zai ganki. Na tabbata in kin yankani zaki huce kiyi rayuwa mai dadi da nagarta. Ki samu rangwamen kullaci na dake zuciyarki na zagin Momi, mugunta da azabar dana kwashe shekaru ina yi miki, takardar saki dana hanaki, tare da huta auren direban tasha tunda ni dai hannuna ba zai iya rubuta saki ga Fa'izah ba ko da ace na iya rubutu!!!".
Idona rufe na ce, "Fa'iz ka bude min kofa in fita, naga alama ka haukace. Wallahi ba don komai na yarda na sanyo kafata a motar ka ba sai don furucin Babana, na yafeni da ya ce zai yi". Na fashe da kuka.
Ya sake matsowa ya dauki wukar dana yasar, ya ce cikin taushin murya.
"Fa'izah, ki kwantar da hankalinki ki yanka ni, kinga in ba hakan kika yi ba baki huce haushi na ba, baki kuma ci nasarar kiyayyarki ba. Kamar yadda bakin cikina ba zai kyale zuciyarki ta samu sassauci ba don kuwa ni ba sakinki zanyi ba...".
A yayin da ya zura min kotar wukar cikin hannuna, nayi maza na yi baya da hannuna na kwalla kara tun karfina. Ihun da ake kira kunu a makota babu wanda yasan ina yi. Ihu nake ina karawa ko Allah Zai kawo wani giftawa yaji ya kawo min dauki. Sai dai ga dukkan alamu ihu na ya tsaya ne cikin motar kadai ko ta taga baya fita.
Ya ce (in subdued) wato cikin raunin murya.
"Ki yiwa Allah ki aikata abinda na umarce ki, sai ki jani ki tura cikin kogin nan. Babu wanda zai ganki, wukar ma ki jefata cikin ruwan. In yaso ki samu wani ki roke shi ga kudi zan bar miki ya tuka ki zuwa Kaduna ko Giwa tunda baban ABU yasan tare muka fita...".
Na girgiza kai da sauri, "Ko da nake kinka babu yadda za'ayi in kashe ka da hannuna tunda ba ni nayi maka ran ba. Sai dai na kasance cikin addu'ar Allah Ya kashe ka in huta wannan bala'i".
Wannan karon murmushi ya yi, sannan ya cira ido a hankali ya dube ni.
"Kin kasa gane abinda nake ankarar dake har yanzu, wato babu wanda zai ganki, ki kashe ki tura RIVER NIGER shi ne maganin kiyayyarki ga Fa'iz. To tunda kina tsoron kama wukar taki...".
"Ka daina cewa wukata, ba tawa bace, kai ka san inda ka samo abarka...".
"Ai don ke aka yi ta. Ko baki ga sunanki ne a jiki ba? Wai ma shin, ina haukanki da rashin imaninki yaje ne da kike yin baya-baya dani yanzu ba kamar dazu da wannan bakin ke gartsa min cizo ba?"
"Na rantse da Allah ka isheni, ka maida ni inda ka dauko ni, ko kuma ka bude min na fita".
Ya sha mur sosai, "Ki fita kije ina? Wajen 'yan daudu da 'yan ashana? Fa'izah babu wannan damar in har kin barni da rai. Baya ga wannan kyakkyawar dama da na baki, (remember that opportunity comes only once in life!) Muddin kika bar wannan damar ta subuce miki, to kiyayyarki ta karya ce... Kina son FA'IZ BAMALLI.
Ba kuma zaki iya kaiwa 'yan bariki, 'yan daudu da 'yan ashana jikin da ya zam mallakin Fa'iz ba! Za ki bar mishi abinsa ne ya yi yadda yaga dama da shi daga yanzu har gaban abada! Muddin baki aikata abinda na umarce ki ba kina son rayuwar Fa'iz Bamalli Giwa ta ci gaba da wanzuwa a doron kasa...!".
Ai jin hakan da ya fada, ya sani daukar wukar na riketa gam-gam cikin yatsuna amma na kasa motsa hannuna ko kadan. Sai Fa'iz ya matso gaba gareni sosai har hucin numfashinsa na dukan fuskata tare da sassanyan kamshin 212 dake tashi sannu a hankali daga jikinsa. Ya daga gira, tare da dan ware ido, ya kuma buda hannuwansa.
"Uhm? Ina jiranki, (I'am ready)".
Na runtse ido tamau, yayin da hawaye suka shigo kwaranya babu kakkautawa, a kundukukina, fadar Ubangiji (S.W.T) ke zuwa mini cikin kunnuwa na ta "WANDA YA KASHE A KASHE SHI" haka wanda ya kashe kansa ya mutu kafiri da sai in kashe nawa kan kowa ya huta, shi ya huta ni in huta, iyayenmu su huta. Sannan muddin na kashe Fa'iz dukkan dunguma-dunguman zunuban da na tabbatar ya wanzu yana dauka a rayuwarsa rubdugowa za suyi kaina. Baya ga haka in Baba ya nemi bayanin inda Fa'iz ya shiga bani da hujjar kare kaina. Ga wuka an rubuta sunana a jiki, idan ma na cilla ta cikin ruwan wani ya tsintota fa, ko masu kamun kifin nan?
A hankali na saki wukar kasa, na sanya kaina cikin cinyoyina na shiga shakar kuka. Fa'iz murmushi yayi.
"I achieve what I want to achieve, ... all of a sudden... it's obvious that you LOVE ME! (A fili ya ke kina so na, na cimma abinda nake son cimmawa)".
Ya dauki wukar ya sauke (glass) ya cillata waje, ya mayar dashi yadda yake. Ya dauki farar (singletinsa ya maida, ya kuma maida shaddarsa. Ya tsallako ya dawo kusa dani ya zauna kafadunmu na gugar juna, ya shiga wakar 'YAN ASHANA' wadda marigayi Dr. Mamman Shata ya rera.
Iyakar zuwa wuya na zo, ga yunwa dake cina kamar me. Babu abinda na iya baya ga rufe ido da yin shiru. Na kuma saddakar na saduda duk iskancina Fa'iz ya dameni ya shanye. Da Aunty Rabi na nan da ta kada mishi tutar da tayi alkawarin kadawa WINNER, ya tabba ni ce na fadi 'game' din, (I'am the LOSER!!!)
Wasu hawaye masu zafi suka shiga biyo kuncina.
A lokacin ne naji ni cikin danshi sosai a inda nake zaune, alamu ne na isowar (period) dina wanda ban zata a wannan lokacin ba. Na tabbata tashin hankali ne ya kawo shi ba wani abu ba, don lokacina bai karasa ba. Na jike sharkaf kamar wadda tayi fitsarin zaune. Don haka ko wani kwakkwaran motsi na kasa, nayi fiki-fiki dani idanuna sunyi ciki sun zurma don bala'i da kaduwa. Na kai idona ga agogon motar ya nuna karfe shidda na yamma. Shin yaushe zamu kai gida in mun fita jihar Neja yanzu? Gani da shegen tsoron 'yan fashi, bansan sanda na sake tsandarewa da kuka ba.
Duk dai ni na jawowa kaina, da na kama Fa'iz na kulle a dakin Walida. Da na barshi ya wuce abinsa tun shigowarsa da ya nemi tafiya da duk hakan bata faru ba.
Akuyar cikina ta sake yin kukan yunwa da karfi, ji kake farrr! Fa'iz ya dan saurara kana ya yi dariya, ya ja kujerarsa ta koma dai-dai ya yi tsalle ya haure ya koma mazauninsa ya tashi motar. Bai tsaya ko'ina ba sai tsakiyar birnin Minna.
Ya karya kan motar ya shiga wani katafaren gidan saukar baki, a samansa an rubuta (MINNA GUEST INN). Ya yi (parking) a wuri na musamman da aka tanada don adana motoci cikin wata rumfa kamar tanti
Hankalina ya kara tashi, me Faiz yake nufi? Hotel ya kawoni? Ni karuwa ce?
Tunanina ya kasa boyuwa cikin raina sai da ya bayyana a kunnensa.
"Ni karuwa ce da zaka kawo ni hotel?"
Wani irin kallon biyu ahu yayi mini bai ce komai ba. Ya kashe motar ya soma tattara 'yan shirginsa dake cikin motar ya ce.
"In zaki fito, ki fito. Gara da na kawo ki hotel ki zama babbar karuwa mai (class) ban kaiki matattarar 'yan daudu da 'yan asahana ba, ki zama (low level or classless prostitute)".
Na kara tsananta kuka na, baki shi ke yanka wuya, da na sani banyi furucin nan ba da Fa'iz ya mayar garkuwarsa a komai. A wannan lokacin (I'm speechless) kalma ta kare a bakina.
Alal hakika ina tsoron kwana cikin motar ni kadai saboda ina da labarin garin Minna cike yake da mayu tare da tunanin koda na kulle motar ba za'a rasa masu (master key) ba.
Ya ce, "Ke kina bata min lokaci fa, abinda kike tunani ba shi bane, dube ki don Allah, me zan dauka anan kayan najasa? Dubi yadda ki ka batawa Baba motarsa, ni taimakon ki zanyi, a kuma wankewa Baba motarsa...".
Idan na ce banji kunya ba kema kin san nayi karya. Eh, Fa'iz na da damar fada min duk abinda yaga dama. Nayi Allah Ya isa tafi cikin carbi, amma a zuciyata.
Na mike da kyar, duk kafafuna sun kumbura suntum saboda zama, ya zaro ido sanda na idasa fita a motar, ya ce.
"Kai-kai-kai! Ke tsaya nan, koma ki zauna kada ki bata masu (tiles) ki jawo min idon mutane, sai nayi (booking) daki tukunna zan dawo".
Ban yi musu ba na koma na zauna, ko ni naso hakan sai dai babu wani alamun sassauci a fuskata.
Na koma inda na tashi na zauna nayi tagumi, na gama saki da al'amarin Fa'iz ni yanzu tsoron shi nake ji ma. Tunanina na ya gangaro yadda zai yiwu in kwana daki daya da Fa'iz? Na kama kaina da hannuwa na biyu na rike, saboda barazanar tsage min da yake yi. kaina sarawa yake ta ko ina, ga kugin da cikina ke yi min babu sassautawa. Kuka ya kafe daga kwayar idona, nayi amanna babu yadda zanyi da Fa'iz yafi karfina a wannan lokacin duk ma wani yunkurin hauka ko tashin hankali da zanyi akaina zai kare don haka na alkawartawa kaina kunshe bakina don mu wanye lafiya.
Nayi zama na kamar awa daya, in saka wannan in kwance kamin ya dawo ya bani zani na bakin yadi da ake kira kofilin ko (plain yard) ya dora bisa cinyata ya ce.
"In kinga dama kina iya fitowa".
Ban yi musu ba na fito na daura, na kwanto dankwalina na daura daga wuya. Sai a wannan lokacin ne Fa'iz ya lura ko takalmi babu a kafata balle mayafi. Ina kallon sanda ya kada kai, ya saci kallona ta gefen ido.
Haka nake tafe tamkar mai tafiya bisa fasassun kwalabe saboda hardewar da kafata ke yi, duk da babu mutane sosai ko ince sunyi nesa damu a harabar (guest inn) din ji nake tamkar idanun kowa akaina yake. A lokacin duhu ya shigo, hasken fitilu ya wadata ko ina, haske ne kamar rana. Dadi daya naji da na lura babu wanda ya damu da harkar wani a wajen. Ganin irin tafiyar da nake, sai ya rage taku duk da bai tsaya mun jera tare ba.
Wata sabuwa inji 'yan caca! Ganin mu nayi a bakin matattakala wanda ke nufin bene zamu hau.
Nayi tsaye jimm! Rike da kafar benen ina tunanin ta yaadda zan hau shi. Ban yi aune ba naji Fa'iz ya sunkuce ni ni da kazantata ya soma taka matattakalar dani dauke a hannayensa cikin sassarfa, bai tsaya ba sai a hawa na biyu, daki mai lamba (82) yasa mukulli ya bude sannan ya dire ni, ya ce.
"Ga daki nan, ki kintsa ki huta. Duk yadda naso mu koma gida a yau ba zai yiwu ba sai sanda Allah Yayi. Duk wanda ya buga in ba muryata kika ji ba kada ki