Showing 6001 words to 9000 words out of 42033 words

Chapter 3 - Zumuntar kenan book by Sumayya Abdulkadir Takori.txt

bude, ko da yake 'yan ashana ne ba damuwa".
Ban tsaya sauraron kalolin rashin mutuncinsa ba na nufi (toilet), shi kuma ya ja kofar ya fita yana murmushi.
Kai Fa'iz sai a barshi, duk abinda zan iya nema dama wanda banyi zato ba na gani a (toilet) din, sinkin (always pad) (pantis) har shidda, dogayen riguna guda hudu, body lotion, brush da macleans har da mouth-wash, da saitin kayan wanka na 'suddenly' har da abin tazar kai, ga towels kala-kala a (toilet) din. Nan da nan ban bata lokaci ba na hada ruwan wanka cikin kwami na wanke ko'ina na jikina da ya yi tsami ya warware. Na gasa kumburarrun kafafuna da suka suntume saboda zaman mota. Sannan ne na fito daga kwamin na bude ruwan ya tafi na zura daya daga cikin dogayen rigunan da ya aje mani kalar kofi. Na wanke wadanda na tube na shanya. Na dauki brush da maclean ina goge hakorana kenan naji bugun kofa. Tare da cewa.
"Zo ki bude ni ne".
Ban san abinda ya ruda ni ba na kasa tsayawa in wanke kumfar baki na ko duk sabon tsoron Fa'iz daya shigeni ne oho! Da burushin a bakina da kumfar duka nazo na bude kofar.
Fa'iz ya shigo rike da manyan ledoji, ban yarda mun hada ido ba na juya na koma na kuskure bakina. Na dubi kaina a madubin bandakin inda na tabbatarwa kaiwa na karamin ramewa nayi ba rana daya kacal da Fa'iz ya sanyani a duniyarsa. Duniyar bala'i da masifa.
Haka na fito ina ciccin magani, inda kamshin wani hadadden gashasshen nama ya bugi hanci na. Miyau na yayi bala'in tsinkewa, na hango shi bisa (three seater) ya ja (centre table) ya dora ledar (foil-paper) mai cike da gasasshen naman mai ruwa-ruwa da yaji tumatiri da albasa yana ci yana korawa da lemon (7Alive).
Na hadiyi miyau, ji kake mukut! Na samu daya kujerar na zauna ina kau da kai.
Ya yi murmushi ya dauko wata ledar ya ja (table) irin nasa ya dora mini, ya mike ya shige (toilet) ya barni ina kintsa hanjin cikina wanda baya yarda aja masa aji. Bayan gashasshen naman akwai (fried sphagetti) da hadin salad.
Na kusa tashi da duk abinda ke cikin ledar nan sannan na mike na isa ga dan firjin dake dakin na bude. Ya cika shi da nau'in lemuka kala-kala (squash juice) da (fruit cocktails), na dauki kwali daya na kwankwadi iya yadda zan iya nayi wata katuwar gyatsa, sannan nayi hamdala ga Allah. Sai naji bude kofarsa daga (toilet) da alama wanka yayi ya sanya ruwan madarar jallabiyya yayi sharr yayi (fresh) (very handsome) da shi.
Nayi maza na dauke kaina bayan da muka hada ido. Shima cin magani yayi kada in kawo masa wargi, bai san nayi rantsuwa cikin zuciyata har ya maida ni inda ya dauko ni ba zai ji wani furuci ko wata kalma daga baki na ba.
Ban zauna a kujera ba bisa carpet na zauna na mike kafafuna na dauki (remote) ina canza tasoshi har saida nazo (Bollywood) na tsaya ina kallon shirin da suke yi a lokacin mai suna (Baabul). Shi kuma sai ya dasa sallah bisa dardumar da ya sayo.
A raina na ce, "Lallai direban tasha ya canza, da can mutum ne wanda baya wasa da sallah, amma yau sai da ya zauna ya take ciki yayi wanka sannan zai yi sallolin dake kansa.
Ya jima yana sallar da ban san la'asar ce ko magariba ko isha ba, kamin ya yi sallama ya kunna sautin Abdurrahman Sudaith cikin wayarsa yana saurare cikin Suratul An'ami. Ya kuma shiga gyaran akaifarshi da ‘nail cutter’ yana bin karatun da wani irin sauti mai dadi da na kasa tantance Fa'iz ko Sudaith wane ne hafizin gaskiya? Dole na rage sautin talbijin tunda dai ni ba shaidan bace. A hakan wani irin barci yan soma fisgata, barci mai dadin gaske wanda na tabbata gajiya da samun nutsuwa ne suka saukar dashi.
Ni dai sai juyi nayi na jini bisa tsakiyar ni'imtaccen gado, lalluve da lallausar bargo. Ban farka ba sai washegari misalin karfe goma na safe. Nayi mika, nayi salati, nayi tasbihi ga Ubangijina na nufi (toilet) na cika baho nayi wanka. Na tarar kayana da na tube na wanke jiya sun bushe don haka maimakon daya daga cikin dogayen rigunan su na mayar. Atampha ce (exclusive Sheraton) riga, zane da kallabin su. A (toilet) din na shafa (lotion) din E45 cream da ya sayo nayi daurin kallabina tsaf, sannan na fita ina cin magani ina harbin iska.
Zaune yake cikin kujerar zaman mutum daya, ya daura kafa daya kan daya, yayi kyau har ya gaji cikin (light blue) din jeans, na tabbata suma siyo su yayi jiya tare da nawa kayan. Don dogayen rigunan daya sayo min ma kalar makuba maroon, milk da black daga gani sayen (boutique) ne. Rike da 'yar karamar radio yana sauraren harshen Hausa na Rediyo Najeriya Kaduna. Na samu wuri can nesa dashi na zauna na zuba tagumi. Da alama Fa'iz bai da niyyar tafiya ma kwata-kwata, na dai ja bakina na kara tsukewa cikina ya soma kiran ciroman garinmu Giwa.
Ya rage sautin rediyon cikin sassaucin kallo.
"Madam, babu gaisuwa?"
Kokari yake mu hada idanu amma na ki. Ya yi murmushi .
"Kiyi hakuri, na canza miki wurin kwanciya ne jiya saboda kada wuyanki ya kage". Ya sake yin shiru.
Ya tabbata ba zai samu amsa ba. Hakan bai hana shi karawa ba.
"Me kike son kiyi (break-fast) da shi?" Ya dan canza fuska, wato ya dan sha mur.
"Fa'izah ba zaki magana ba?"
Na sunkuyar da kaina hawaye suka soma mirginowa a hankali ta kasan idanuna. Ya aje rediyon ya taso ya iso har inda nake, ya kama hannuna na dama ya rike cikin nasa, nayi kokarin janye hannuna amma ya rike tamau, gam-gam.
"Me zaki ci eye Fa'izah na?"
Da wani irin karyayyen sauti, mai kassara gabban jiki da sanyaya zuciya.
Da hanzari na mike na nufi (toilet), duk da nasan bani da abinda zanyi a ciki. Gaba daya jikina rawa yake yi, haduwar fatar jikimmu wani 'chemistry' ne da bazan iya fassarawa ba, mai dauke da wani irin (shock) tamkar (electrical shock). Na maida kofar bayin na rufe, na jingina da ita, na lumshe ido a hankali cikin kokarin (regaining consciousness) wanda ya yi min wahalar dawowa.
Sai da na samu nutsuwa sannan na fito. Wannan karon bashi a falon. Na dauki takarda da biro nayi rubutu layi biyu kacal, ina kokarin ajeta a inda ya tashi ya bude kofar ya shigo da sallama ciki-ciki. Nima ciki-cikin na amsa, ko kadan bai ji ta ba, don dai amsawar ta zama farillah ne.
Ina kokarin dagowa ya dafa ni, "Me ki ke rubutawa?"
Kamshin '212' dinshi da kamshin bakinsa na (mouthfreshner) mai karfi da yayi amfani dashi ya cika hanci na. Ban son irin wannan kusantar da yake son assasawa a tsakaninmu ko kadan kuma ba zan lamunta ba. Nayi saurin aje takardar na ja da baya da zafin nama. Ya yi murmushi ya dauki takardar ya bude ya soma karantawa a fili.
"Don Allah don Annabi Yaya Fa'iz ka kaini Kaduna wajen Mama. In kuma ba yanzu zaka tafi ba, to don Allah bani kudin mota in tafi, ina da abinda zanyi da yawa".
Ya aje takardar ya dube ni da shanyayyun idanunsa.
"Kina da wani abin yi ne dama wanda yafi mijin ki muhimmanci? Na duaka miji shi ne (foremost) a rayuwar kowacce diya mace indai tagari ce. Nima ina da abin yin na tattara na watsar saboda matata Fa'izah, ko bance ita tafi komai muhimmanci cikin rayuwata ba tana da hakki cikin lokuta na, wani neman duniya ko sabgogin duniya wadanda ba sa karewa basu isa su sa nayi watsi da wannan hakkin ba. Ko da yake nasan ke baki dauke ni a matsayin mijin ba, balle ki bani wannan muhimmancin.
Zamu tafi, amma sai kinyi min magana cikin dadin rai, irin wadda macen da ke son mijinta take masa. Son samu kice I LOVE YOU YAYA FA'EEZ!!! Har sau uku. In ba haka ba, mu karashe sati biyun hutuna anan, daga nan mu wuce Birtaniya, ke da gida sai kinzo haihuwa. Kin san dai ba mai nemanki don an san muna tare. Don haka zabi na gareki".
Ya juya ya soma fiddo abinciccikan daya sayo a ledar su, yana dorawa a (centre-table). Ya ci abinshi cikin kwanciyar hankali ya dora da Gahwah mai zafi (Coffee). Ya shige uwar dakin ya bi lafiyar gado da yake dakin ciki da falo ne. Amma ya sauke kafafunshi a kasa. Ni fa na kammala, ke nake jira.
Na zauna na ci son raina na koshi, har da kara tea bayan na shanye kofi guda. Naji ni dai-dai, nayi hamdala ga Allah. Na kwance daurin da nayi na dankwalin atamfata na yafa da yake dankwalin babba ne sai ya rufeni ruf. Na nufi kofa na tsaya. Ya mike ya fito falon ya jingina da kofar da ta raba uwar dakin da falon, ya ce.
"Au, baki ji abinda na ce ba ko? Tunda kunya kike ji dauki biro da takarda ki rubuta min kinji sabuwar kurma?"
[1/4, 12:22 am] Takori: Ban musa ba, sai dai a raina na ce, "Inji kunyar ka? Amma da nayi asara. Kunyar maras kunya ai asara ce!".
Na dawo na dau takarda da biro na jingina da bango na soma rubutu.
Da na kammala na aje nan, na sake komawa bakin kofa na lafe. Ya dauki takardar ba tare da ya bude ba ya sanya a aljihu ya taho yana fadin.
"Kin manta da guzurinki". (Yana nufin sanitary pard).
Ban bashi amsa ba ya shiga (toilet) din ya kullo duka kayan a ledar da ya shigo dasu ya fito ina ta manna masa harara kamar kwayan idanuna sa fado. Ya yi murmushin sa (broad smile) ya ce cikin rada.
"Wannan hararar, wata rana kallon so zai koma, wannan hararan, wata rana in wata tayi min Fa'izah dukan tsiya zata yi mata, sai inda karfinta ya kare akan duk wanda yayi min ita. Wannan hararan, ni a ganina 'I love you ne, I can't do without you ne'. Ba abinda lokaci baya magani".
Ni dai bance komai ba, kulawa ma yabawa ce koko Hausawa sunce sai an kula kashi yake doyi.
"Saura ki sake batawa Baba mota, wannan karon Shu'aib zansa ya wanke. In yaso in ya tambayi na mene ne? Sai in turo miki shi kiyi masa bayani".
Kokari yake mu hada ido, na ki. Na koma na sanyo (slippers) din bandakin don bai sayo da takalmi ba. Muka sauka kasa ya basu mukullin su muka wuce, 'parking lot'.
Nayi-nayi in bude kofar gidan baya, na kasa ban sani ba ko kulleta yayi, dole na hakura na shiga gaba, shima ya shiga mazauninsa ganin naki rufe kofar daga inda yake ya sunkuyo har muna gugar juna ya rufo kofar ruf. Maimakon ya ja motar, sai ya bude takarda ta ya soma karantawa a fili.
"I hate you. And I would never love you forever... In mafarki kake, ka farka...!!!"
Ya zuba min shanyayyun idanunshi masu cike da wata irin fitina, maimakon kalamaina suyi tasiri mara dadi a kansa. Sai naga kamar dadi sukai masa. Na juyar da kai domin ba zan iya jure kalon abubuwan da ke cikin idanunshi ba masu kama da (magnet) mai jan zuciya tamkar jan wutar lantarki, wadanda a fakaice wasu irin sakonni ne suke bayyanawamasu nuna matukar bukatar miji zuwa ga matarsa ta sunnah. Sai naji wasu bangarori na jikina suna kokarin karbar wannan sako, idan har banyi da gaske na zama jajirtacciyata ba kamar yadda nake wannan mutumin zaiyi saurin cin galabata dole in kara jajircewa. Wanda ba komi bane illa kokarin ganin ban yarda mun sake kadaicewa ba. Domin nima din 'adolscent' ce mai bukatar mahadin rayuwa, don dai auren ya zo ba a yadda na so ya kasance bane. Ya kasance ya zo min tareda wani mutum da ba abinda zai yi ya burgeni a rayuwata, ko ya wanke dattinsa dake raina.
Ya yi murmushin da yafi kama da takaici ya tada motar. Bai sake magana ba har muka fita garin Minna. Yayin da ni kuma na tsayar da idanuna gefen da bishiyoyi suke zuciyata cike da farin cikin ko yaya ne dai kalamaina sunyi tasiri.

***
Wajejen karfe uku sai gamu cikin garin Kaduna. Ya karya kan motar ya dauki hanyar anguwar Kabala Custain. Ni sam bam ma san nan gidan Ummi yake ba. Yayi (parking) bayan maigadin gidan ya bude get din gaba daya. Su Yahya ne suka fito ashe duk suna gidan sunzo musu wuni, abin mamaki har da su Walida, Abdallah, Kausar da Walid autanmu. Nan gidan ya rude da sowar kannen mu kamar zasu hadiye mu.
A sannan ne na gane gidan Ummi da Yaya Bashir ne ganin tangamemen hoton su (window size) ranar (cocktail) din (Indoor sport hall) kafe a kayataccen falon.
Sai na wuce kai tsaye zuwa uwar dakin matar gidan babu wanda na kula a cikinsu sai cika nake ina batsewa. Na zauna a gefen gadonta ina kallon dakin kallon kurilla, na jiyo alamar tana (toilet) ne wanda ke makale da dakin nata tana wanka.
Ummi tunda taji ana oyoyo Yaya Fa'izah, oyoyo Yaya Fa'iz tayiwa wankan baja-baja ta fito a guje duk rabin jikinta kumfa ta fado mini.
Na ture ta na ce, "Ke baki da hankali ne za ki jikani? Don kawai nazo gidanki? Ba tambayar mutum ya yake? Ko wane hali yake ciki?"
Ta daga ni tana dariya, ta rasa inda zata sa kanta don farin ciki. Na bita da kallo har cikin ta ya tasa. Na kama baki cikin tsananin mamaki domin na dauka da da wasa take kamar a bakin kofa ake tuntube da cikin?
Ta sunkuya ta zauna a gefena hannuwanta duka biyu tallabe da fuskarta tana murmushi, ta ce.
"Fa'izah matar Yaya Fa'iz! Sai kyallin amarci kuke don na hango shi ta taga, daga ina kuke haka? Naji labarin Baba ya kore ku, tsammanin mu kun bar kasar babu sallama ga kowa".
Na hade girar sama da na kasa, na ce.
"Kin san Allah ki fita daga harkata, wane irin an kore ni kamar wata shegiya? Maras kunya fitsararriya, kyallin amarcin uban wa? Amarcin yaci ta kaza-kazan sa". Na mirgino ashariya.
Ummi ta dafe baki, sai kuma ta fashe da dariya.
"Oho dai! Mun gane kiyayya taci uwatar, Pilot yayi fari yayi kiba, Fa'izah ta rame saboda wuyar amarci amma ta zama kyakkyawa. Shin wai a ina aka yada zango ne?"
Ganin tana neman maishe ni mahaukaciya na mike nayi (toilet) don inyi wanka in sauya kunzugu na ko naji dadin jikina. Na fito daure da tawul tana make-up a (dressing mirrow) fuska kamar jikakken kwaki don turbunewa na ce.
"Bani kaya in sauya, ko ba hali?"
Tayi dariya kawai, ta dauko min atamfa Vlisko mai ruwan ganye mai karamin dinki na karba na saka nayi kwalliyata sosai nayi sharr, tuni kuma tausayin 'yar uwata ya kamani ganin yadda take ta rawar jiki dani cike da kauna. Sai na ware nima muka shiga hirar arziki.
Duk sanda ta sako zancen Fa'iz cikin hirarmu bana yarda ince mata komai, dolenta ta kyale, muka koma hirar makaranta da dakace iri-iri na cewa yanzu an shiga zangon karatu na farko na sabuwar shekara babu mu, Haulatu na can tana ta (missing).
Ko da wasa Ummi bata yi zancen marigayi N.S ba, nima banyi ba. Na ce.
"Wai ina Yaya Bashir ne?"
Ta ce, "Ya koma Russia zai harhado kan takardunshi don na ce ni ban yarda yayi aiki a can ba, sai dai ya je, ni in zauna anan duk sanda ya samu dama ya neme ni, dalilin komawar shi amso takardun kenan ya dawo nan ya nemi aiki".
Nayi dariya na ce, "Kin hadu, wai kema mai tsarawa miji rayuwa ko?"
Ta ce, "Ba wani tsarin rayuwa ko dai gaskiya. Na rantse miki shashanci yake a can ba aikin da yake yi. Ya jima da gama karatu babu yadda Mama bata yi ba ya dawo yaki, wai jiran Yaya Fa'iz yake ya kammala da yake karatun Fa'iz yafi nashi nisa. Gara Fa'iz idan ya ce zai yi aiki a waje yana da hujja a Nigeria bamu da wasu Airlines na arziki, kuma ba zaki hada albashinsu da nagartarsu da 'Internationals’ ba.
Shi kuwa Yaya Bashir su Nigeria ke bukata suzo su amfanar da al'ummar su yafi, (Global; security) ya karanta.
Na samu da dabara da taimakon Allah da na addu'a na tsayar da hankalin Yaya Bashir a kaina, anan bai fita ko'ina sai tare da ni, don kar in zarge shi. Firinji kuwa (fridge) duk gidan daya ne na (kitchen) don kar ince yana boye (gulder) wani wuri. Don haka ko ya dawo ya samu aiki zan ci gaba da sa masa ido sosai duk da cewa na tabbata a yanzu yaya Bashir ya bar shashanci 90%".
Na jinjinawa Ummi a fili da zuci, kaga mace duk gabuntarta a fannin mu'amala da miji kada ka rainata. Ban taba zaton Ummi na da hankalin da yau na sameta da shi ba.
Na ce, "Bani abinci Ummi, yunwa nake ji, tun karin kumallon safe rabona da abinci, kin san kuma ba iya jure yunwa nake ba".
Ummi ta dafe kirji, kai Fa'izah, amma kin iya rashin mutunci, kin shagaltar dani ko ki tuna mani da dan uwa na dake waje cikin yara ko ruwa ban bashi ba, kanki kawai kika sani, (selfish!)".
Ummi ta fita falo da fara'arta sai taga wayam!
"Ku! Ina Yaya Fa'iz?"
Ta tambayi Walida.
"Ai tun dazu ya debi Shu'aib, Junior da Yahya suka wuce wai Zaria za su raka shi.
Haushi ya kashe Ummi ta harari Walida.
"Shi ne baku gaya min ba? Ban bashi ruwa ba, ban bashi abinci ba". Ta fada kamar ta fashe da kuka.
Abdallah ya ce, "Shi ne ya ce mu kyale ki hira ku ke, kun jima baku hadu ba. In ya dawo daukan Yaya Fa'izah gobe ko jibi kun gaisa".
Ba haka ta so ba, sai dai tayi farin cikin jin cewa ya bar mata 'yar uwarta barin rayuwarta su kwana su hantse tare, wani abu da suka rabu da samu tun barowar su Kano gidan Yaya Rabi.
Da kuzarinta ta fada (kitchen) don dora sanwar dare. Ta dawo ta ci gaba da yi min sababi, ta gaji ta koma wa'azi na hakkin miji akan matarsa da girmama shi da kula da cin shi da shansa da shimfidarsa. Amma ga mamakina na kasa tanka mata duk da nasan gaskiya take fada ban dai furta komai ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login