Showing 15001 words to 18000 words out of 42033 words
Chapter 6 - Zumuntar kenan book by Sumayya Abdulkadir Takori.txt
ace mata na yiwa mijinta ni sai na roka sannan a hagunce ake yi min...".
Tsakin da baya so na sake saki na juya masa keya na ba banza a ajiyarsa. Kai ni surutan da yake yi ma sun isheni nasa hannu na toshe kunnuwana.
"Ina (breakfast) dina? Na gaya miki Abuja zan tafi".
"Banga damar girkawa ba".
Ya ce, "To Allah Ya bamu rai da lafiya".
Na ce, "Amin Ya Rabbi".
Ya juya ya fita ya janyo min kofar a fili, na ce.
"Umma ta gaida Assha".
Bai jima da fita ba na mike nayi bayan gida wurin Dawisu don basu abincin safe. Ina watsa musu hatsi daga nesa suna kara matsowa gareni cikin alamun nuna sabo, wato sun fara ganeni. Ya'u ya iso ya gaida ni ya ce.
"Aunty na kawo cefane yana can kofar falo".
Na ce, "Ina godiya Ya'u, anjima a sake musu ruwa, wannan ka gani duk yayi kura".
Dariya abin ya baiwa Ya'u, amma sai ya ce.
"Aunty kina son 'yan gidan nan naki, zan kara himma wurin kulawa dasu".
Na ce, "In kayi hakan kaima Allah zai kula da kai".
Na koma na kwashe cefanen da ya aje dokin kofa na shiga (kitchen) na adana kowanne a muhallinsa.
Fa'iz bai dawo ba sai dare, sanda ya shigo gidanma bacci nake, ban san ya shigo ba. Na fito ne da daren don samawa cikina abinda zai ci naji yana kwalamin kira kamar tashin duniya. Duk da na firgita da irin kiran amma na share na shige kicin sai gashi ya biyo ni (kitchen) din a sukwane hannayensa rike da tulin hotuna. Fusatar dake fuskarsa ba zan iya bayyanata ba.
Ta gefen ido nake kallonsa ina ci gaba da abinda nake yi, sai ji nayi ya finciko ni ta baya, saura kadan in fadi Allah Ya taimakeni na dafa (cabinet) na mike a lokacin na lura hotunan da Surajo ya kawo ne rike a hannunsa, fuskarsa a murtuke, idanunsa sun kada sunyi jajir yake magana harshensa na sarkewa.
"Meye na daukar hoto da Suraj haka (very so close) har jikinku na gugar juna?
Meye na tsayawa kusa da shi haka kusa da kusa a bainar jama'a? Da na ce yazo ya tsaya min cewa nayi kuyi hoto?
Shi kuma Ya'u da kullum kike bare baki kina hira dashi da izinin uban waye? Ina ruwanki da duk namijin da na kawo na aje cikin gidan nan da har kike dafa musu abinci? Cewa nayi dake bana basu kudin da zasu ci abinci ko me?"
Wani matsanancin haushi da takaici suka taru suka rufe ni, naji in ba rushewa nayi da kuka ba bazan huce wannan cin mutuncin da rainin hankalin na Fa'iz ba. Na kasa cewa komai sai ido dana zuba masa cikin matsanancin haushi.
"Ina magana kin zuba min wadannan kwala-kwalan idanun naki, ba zaki amsa ba? Na ce shi kuma Ya'u ina ruwanki da shi har yake gaya min kince masa kaza da kaza? Na kirashi na aje domin baiwa tsintsaye abinci hirar da kike yi da shi ta mece ce? In hirar kike so kiyi dani mana? (Am I not applicable to meaningful talks than him?) Ni baki yi hirar dani ba sai da wani gardin kauye can daban. Ba zai yiwu ba to! Daga yau Ya'u ya bar gidan nan. Shima buzun in kika sake kula shi wallahi tafiya zai yi, ki zauna ke kadai ba zaki kasheni da raina ba... Akwai masu bukatar rayuwata ba don ke kadai aka halicceni ba!!!".
Bayan takaici da haushi da buyaginshi ya bani, sai ya dawo bani dariya saboda da iyakacin gaskiyarshi yake wannan hargagin, akwai (gesture) a tare dashi mai nuna abinda yake fadin, haka yake har zuciyarsa.
Dariya ta cika min ciki ban san sanda nayi murmushi ba irin murmushin nan na tura haushi da maida kai shashasha domin na rantse da fari na firgita, matukar firgita kuwa. Ko da kwartaye biyar aka kamani yanayin da ya zo min dashi sai haka!
Ko ni nace a daukemu hoto da wani Surajo oho! Balle kuma bawan Allah Ya'u. Naga idan na kula shi ma (is a waste of time) don haka da sauri nabi ta gefensa zan fice daga (kitchen) din, sai jin hannuna nayi rike cikin nasa, cikin wani irin riko mai tsauri dana kasa fincikewa kamar ba mutum ne ya rike ni ba.
"Ina magana kin maidani dan iska?"
Yanayin da yayi maganar muryar kamar ba tasa ba kuma cikin wani irin 'tune' da ban taba jin wani mahaluki yayi magana dashi ba. Abubuwa biyu sautin da yayi amfani dashi din ya haifar a gareni.
Faduwar gaba da wani irin bugun zuciya, hannun nasa da jikinsa duka rawa suke yi yana wani irin tsuma. Wani matsanancin tsoro ya shigeni. Na daga kai a hankali na dube shi don tantance ko dai wani ne ya rikide yazo min da suffarsa don ya cutar dani. Daga idon dana zo ina dakacensa, domin kamar jira yake na dago idon yayi hanzarin ya sanya bakinsa cikin nawa ya soma 'kissing' ba ji ba gani kamar wani mahaukacin zaki.
"Na tuba Fa'izah, na bi Allah na biki. Kiyi min duk abinda kike ganin in kinyi shi zaki huce bacin-ranki, amma ki barni in rayu dake muddin rayuwata...".
Kalaman da yake maimaitawa kenan ba adadi, babu 'comma' ba 'full-stop'. Saura al'amuran da yake kokarin bijiro dasu masu nauyin fada ko misaltawa ne, kuma ban shirya karbarsu ba daga nan har gaban abada. Don haka na tattara karfina da Allah Ya hore min a wannan lokacin wanda ya kasance fiye da nashi na angaje shi na taka da gudu nayi dakina na shige na rufe da 'key' ban kuma yarda na zare key din daga jikin kofar ba har safiyar washegari.
Kwana nayi jinyar tsallake rijiya da bayan da nayi jiya wanda ko a mafarki ban kawo shi cikin rayuwar dolen da nake yi da Fa'iz ba. Wanda ya hankaltar dani ga cewa in sauya taku. Hanyar dana dauka ta yin sako-sako ga rayuwar da muke yin bisa tilas ba zata bille dani ba, ba kuma mai billewa bace ba. Idan kuma na ci gaba da binta, la-shakka ina cikin hatsarin da bazan iya maganinsa ba idan ya sameni.
Nayi kuka har na gode Allah. Daga baya bacci mai nauyi ya dauke ni. Can cikin barci na naji yana buga kofar ba da karfi ba. Na bude ido na ga hasken rana ya ratso ta labulen taga nayi mamaki matuka, sallar asuba ta kufce min cikin shagala! Ina rokon Allah Ya yafe mini.
Na fada (toilet) da sauri nayi alwala, saida nayi sallah sannan na koma nayi wanka. Sannan na shiga (kitchen) don kwana nayi da bakar yunwa.
Har kicin din ya biyoni ya tsaya daga kofa yana sanye da kayan wanka na 'versace' da alama fitowarshi kenan daga wanka. Daga inda nake ina iya jiyo kamshin 'bathrobb' din da yayi amfani dashi na 'desire dunhill’.
"In kin kammala ki shirya muje Jabi, Area One (Zaria) da Giwa kiyi musu sallama don jibi zamu tafi".
Na wani irin juyo nayi masa kallon kayi hauka ka warke, na juya na ci gaba da aikina. Ya girgiza kai ya juya ya kyaleni.
Duk yunwar da nake ji sai naji ba zan iya cin abincin ba ma saboda tashin hankali. Amma sai wata zuciyar ta ce bishi kawai kuje wajen Maman, wannan ce kawai mafitarki sai kiyi amfani da damar ta inda bai zata ba.
Sai kawai na aje komi na fito na sauya kaya, kwalliya sosai nayi da 'pitch swiss-lace’ mai ratsin baki, na yafa bakin gyale na rufo dakina. A falo na cimmasa yayi nasa shirin cikin riga da wandon shadda getzner dark-green dinkin tazarce kanshi ba hula. Sai 212 ke tashi a falon. Ya hadu ya cakude da 'escada sentiment' da nayi amfani dashi wani sanyin ni'ima ya baibaye dukkanin mu, da ganinmu kasan ango da amarya ne ba karya. Ko kallona baiyi ba yayi waje, na bishi a baya naki rufo falon na shige mota. Ina kallon yadda yayi kwafa, ya fito ya rufe ya dawo, sannan ya tada motar muka fita harabar gidan buzu na daga mana hannu muka nufi gidan Baban Kaduna.
Su Yahya dake ball a harabar gidan babu wanda ya taremu da murna ko tsalle kamar yadda suke yi da, tabbacin haushin yayan nasu da abinda yayi musu bai sake su ba. Sun dai yi mana sannu da zuwa suka ci gaba da 'ball' dinsu.
Ya kalle su ya gyada kai yayi murmushi bai ce dasu komai ba, muka wuce kai tsaye falon Mama.
Mama waya take sanda muka shiga kafarta daya kan daya a hamshakin falonta. Ta daga ido ta dube mu muna shigowa, fara'arta ta karu, ta ce.
"Kinga 'yan halak, gasu nan sun zo".
Ta miko min wayar tana fadin, "Rabi ce daga Kano".
Na karba sannan na zauna a kusa da ita daga gefe na kara a kunena na ce.
"Hello Ya Rabi".
Kafin in karasa ta fasa min guda aka mai barazanar tarwatsa min dodon kunne. Da sauri na dubi Mama da danta don tsammani nake suma sun jiyo mahaukaciyar gudarta Ya Rabi, sai naga hankalinsu baya kaina sam, gaisawa suke.
Yaya Rabi ta ce, "Diyata 'yar albarka, ya aka kare da BOXING? WHO IS THE WINNER?"
Nayi tsaki, "Tsiyarki kenan Ya Rabi, ba a maganar arziki dake".
[1/4, 12:23 am] Takori: Tayi dariya sosai, "Ni kuwa ake maganar arziki dani, ‘yar Abubakar uwar Abubakar da Fa'izah, uwa ga Zanira uwa ga Ummi, sha lelen Muftahu autar Hajjah. Kirarina kenan, na zama duwawu dole a zauna dani.
Tafiya ta tashi ko? Birtaniya ko Murtaniya? Na so ace nazo rakiya Allah bai yi ba, naji tafiyar taku ne ba shiri, a tabbatar in za a dawo da baby aka taho min sai inzo in zauna zaman dabaro mai dalili...".
Nayi tsaki na katse wayar don nasan in ta Ya Rabi ne sai mu kwana muna yi bata gaji ba. Ga haushin da take kara kuma mini ta barni inji da wanda nake fama dashi.
Mama ta dubemu duka tana murmushi bayan ta karbi wayarta.
"Komai lafiya ko?" Tana duban Fa'iz.
Ya hade gira ya ce, "Tambayeta mana Mama!".
Mama ta ce, "Fa'izah ta ina Fa'iz ya kuskuro ki ko ince yake bata miki?"
Na girgiza kai kaina a sunkuye.
"Babu Mama".
Ta dube shi, "Fa'iz Giwa fa?"
Ya ce, "Mama ba sharri ba, tunda dai gatanan a zaune a gabanta zan fada. Da abinda take yi min na kisan mummuke gara min ta bude baki tayi ta zagina kamar da, ko ta ware hannu tayi ta dukana kamar yadda ta faro.
Bata yi min magana, bata shiga sabgata, ba ruwanta dani ko rayuwar da nake yi cikin gidan. Bata yi min biyayya sam, ta maida kanta kurma domina".
Na dago idanuna da suka yi jawur na ce.
"Wallahi Mama ina iyaka yina, ina masa girki duk abinda ya ce dani bana musawa nake masa, to ban san kuma wace irin biyayya yake nufi ba...".
Ya katse ni tare fidda ido, "Girkin banza! Mama baya ga girki me take yi min na hakkin maza akan matansu? Fa'izah bata kula ni, bata taba zuwa shimfidata ba, bata gaida ni, ga tsaki da harara kamar wani sa'an wasanta".
Maganar ta dan girme mu ni da Mama, amma dukkanin mu sai muka yi kamar bamu ji ta ba. Na kawo wata daban.
"Saboda Allah Mama ya yake so nayi? Ya zo ya sani gaba da bala'in wai don me zanke kula Ya'u leburanshi? Bayan a karkashinmu yake, dole ne ko gaisuwa ta hada mu, wai kuma don me zan ke basu abinci bayan ciyarda barori wani abu ne da muka taso muka tarar a gidanmu a matsayin kyakkyawan koyi koda ana basu albashi. Ban kula shi ba sai ya koma wai don me nayi hoto da Surajo ranar Cocktail? Bayan bani na gayyato shi ba, ban kuma je fatin nan don kowa ba sai don kaina ko ku baku san zan je ba.
Ban san ma sanda aka dauki hoton ba da abinshi ya zo. Sannan kannena suka zo min zumunci ya kore su, yanzu duk haushina suke ji kamar yadda suka kullaci Ummi. Sannan ya kawo wata magana wai wani tafiya, ko ina oho! Ni kam kiyi masa magana ya fita harkata, babu inda zani gaskiya in har ba so yake ya kuntata rayuwata ba (by all means from every angle).
Na yarda na amince zan zauna a can Malali ko ni kadai ce yaje duk ranar daya samu dama ya kawo min ziyara babu damuwa".
Ya fiddo ido cikin kidima, "Baki isa ba, Allah kinyi dan kadan, duk abinda kike ji dashi ina shirye da dauka amma banda wannan".
Fada yake yi sosai har jijiyar kansa na mikewa kamar ma ya manta da Mama a wurin.
Mama tasa masa ido tana kallo sai da yayi mai isarsa tukunna, daga ni har ita babu wanda ya tanka, sai dai jikina naji ya soma rawa, kuka na son kece mini.
Ya yi shiru ganin na soma sharar hawaye da mayafi na. Sannan ne Mama ta nisa cikin bacin rai ta soma magana.
"To tunda zuwa kayi ka kare mana tanadi ni da ita, to tattara iyalinka ku tafi ka fini iko dasu. Ni dama ban kirawo ku ba balle kuzo ku daga min hankali".
Ya soma bata hakuri tana kaucewa, daga karshe ta ce.
"Laifi duk naka ne Fa'iz. Meye don Fa'izah tayi magana da yaron gidanta tunda kana da tabbacin ba zata yi maganar banza dashi ba? Don ta girka abinci ta basu domin kyautatawa bai kamata ka nuna jin zafin ka ba, sai ma kayi alfahari da ta zamo mai kyautar abinci ga na kasa da kai ba kace ta daina ba.
Hoto kuwa duk muna tsaye aka yi shi, kasan baka so ayi hoto dashi don me ka turo shi? Suraj ya rufa maka asiri babu wanda yayi zaton ba kaine a wurin ba, meye laifi anan?
Magana da kace bata yi maka ina ce komai sai ta dauro za'ayi? Ka sani Fa'izah ba mai son yawan magana bace tun tuni. Tunda har da bakin ka ka furta bata yi maka musu, sannan tana girka maka abinci, sai me ya saura? Dan Adam da ba'a iya maka har kana fadin gara maka zagi da duka da wannan. Yau da Fa'izah zagin naka take da duka da rashin kunya, ko kuma bata baka abinci dole ne in tsawatar mata.
Don Allah ka koyi hakuri Fa'izu, zafin zuciyar nan baya da amfani ko kadan, kabi komai a sannu, a baya ka zaci wannan din da kake rainawa cikin kankanin lokaci haka? Har kullum addu'armu na tare da ku, komi zai yi dai-dai a gaba insha Allahu".
Da alama jikinsa yayi sanyi, amma ba duka ba.
Ya ce, "To amma Mama tsaki da harara fa? Gaskiya ba zan jure ba, don ban taso naga kuna yi ba ga su Baba ko wani cikin A.B baki daya. Wannan ai raini ne. Ko don Fa'izah ana sonta kowa na tsoron masifarta?"
Abin ya bawa Mama dariya, amma ta gimtse.
"In ma hakan ne bamu yi laifi ba tunda ai amarya ce, amarya kuwa kowa yasan bata laifi. Kuma ka dinga tausaya mata tunda dai auren nan kasan ba da saninta akayi shi ba, zuwar mata yayi kamar saukar aradu. Don haka ni yadda ta dawo yanzun naji dadi, ta fara nuna mana ta haifu, bata fi karfinmu ba kamar yadda muke zato, huce bacin ranta take yi kuma ta fara hucewar to ka bimu a sannu in kana son mu ci gaba da hucewa".
Yayi kwafa ya ce, "Me nayi mata? In zaki yankata ta fadi laifin da take ikirarin nayi mata bashi da yawan hukuncin da nake karba. Banda ni din nine Fa'izun Hajjah Abubakar-Saddiqu, na Baban Kaduna da ABU wa zai yi hakurin dana yi? Ko anan aka tsaya an san ni jarumi ne wanda mace bata isa ta girgiza ba ko ta sani abinda ban yi niyya ba. Don haka nayi niyyar mu tafi tare wajen neman abincina, kinyi kadan ki canza min ra'ayi.
Wallahi Mama yarinyar nan ba abar tausayi bace, ki daina jin tausayinta kina ganinta haka kamar wata mumina. Musa ce a baki Fir'auna a zuci, rashin mutuncin dake cikin bakinta da zuciyarta yafi bakinta girma".
Mama tayi dariya tana mamakin yaushe bakin Fa'iz ya bude yake zaro Hausa haka? Abar da ada sai dai kaji yana yi mata baragada in ya jima yana magana, lallai Fa'iza bata kama kurwarsa da wasa ba.
Ta gyada kai ta ce, "To ke Fa'izah kinji wannan?"
Na ce, "To Mama tunda ya ce tsaki nake masa to yayi tafiyar sa shi kadai mana ya huta da jin tsakin? Maimakon inje ina yi mai ranshi na baci? Tunda cikin hutu su Junior suke sai muyi zaman mu tare a gidan har su Walida a karo, amma ni ba inda zan iya matsawa inbar iyayena da 'yan uwana zuwa inda ban san kowa ba tunda duk abinda nake yi masa baya gode ko daya, haka idan na bishi rai zai yi ta baci gara inyi zamana".
Mama ta ce, "Kwarai kuwa, ba inda Fa'izah zata, zata zauna har ka samu hutu. Ni dama bana son yawon jirgin nan, tukunna ma kai da baka zama wuri guda, a tafe kake kwana a tafe kake wuni, meye amfanin bin naka da kake so tayi?"
Kamar zai yi kuka ya ce, "Amma ba kullum nake kwana a tafe ba ko Mama? Abin cikin tsari ne, (we have breaks!)".
Mama ta ce, "Oho maka! Na gama magana, ku tashi ku tafi don Allah. Allah Ya yi muku maganin abinda ke damun ku, Ya yaye muku shaidanun dake yawo akanku. Duk 'yan uwanku kowanne na zaune lafiya da abokin zamansa ba mai jin kanshi da dan uwansa sai ku. Ku taka a sannu, duniya ba'a yi mata gaggawa".
Mun mike kenan Baba ya shigo, zuciyata kamar farar takarda nake gaishe shi. Fa'iz bai bari na dire gaisuwar dana debo ba tun kamin Baba ya zauna ya soma karanto masa yadda akayi, da hukuncin rashin adalcin Mama.
Shi dai Baba da dadin ganinmu tare har ana zancen tafiya Birtaniya sai ya hau hamdala ga Allah a zuci, a fili kuma ya ce.
"Tunda bata so a kyaleta man Fa'iz? Ba a son tilastawa cikin zamantakewar aure, watarana da kanta zata ce zata bika ne".
Tun daga ranar da aka yi mana aure Fa'iz bai ji na bashi bakin ciki da takaici irin yau ba. Ya mike cikin fushi ya zari mukullin motarshi ya yi hanyar waje. Baba da karin