Showing 36001 words to 39000 words out of 42033 words
Chapter 13 - Zumuntar kenan book by Sumayya Abdulkadir Takori.txt
tabbacin duk sun tafi gida. Mukullin motar Baba yana hannunsa, don haka shi ke janmu zuwa Malali.
Tafiya sosai mikakkiya, don asibitin yana unguwar Rimi ne. Ina gefensa yana tukin cikin sukuni da kwarewa. Na lalace a kallonsa tamkar wani furen fulawa don kyau. Ubangijin da ya halicce shi ya suranta shi, ya kyautata halittarsa da haiba da kamala. Idan na dube shi kallo daya kaga nitsatstsen mumini mai kiyaye iyakokin Ubangijinsa. Wanda kuma ya dama, ya kutsa cikin ilmin zamani mai tsada da daraja. A goshinsa tabon Sujjadah ne, ya taru yayi baki sidik cikin nuna babu ranar Allah da zata fito ta fadi bai russuna ga Ubangijinsa ba, Ma'abocin wata iri tsafta bayyananniya da ko cikin faratansa ya nuna. Komai nashi garai-garai kuma tsaf-tsaf kamar a lashe.
Babu abinda nake yi cikin zuciyata sai tasbihi ga Ubangiji na da Ya mallaka min wannan ‘giant-handsome’ a matsayin miji a gareni mai so na da kaunata ba. Idan bance nafi sauran mata sa'a ba to hakika ina cikin sahun masu sa'ar ta kowanne bangare a rayuwa.
Sautin Sheikh Mahmoud Khaleel Al-khusairi ke tashi a rediyon motar cikin Suratul-Ankabut.
Watakila jikinsa ne ya bashi kallonsa nake yi kamar zan cinyeshi, ya juyo a gicciye ya saci kallona. Murmushi yayi, wanda ya fadada shi har fararen hakoransa suka fito.
"Da yanzu wata na nan da lullubi aka, ta fara takaba".
Na galla masa harara wadda ta fito ne hakikatan daga zuciyata, na dauke kai na mayar gefen titi.
"Na matsu mu isa gida, (am running at a speedly level) amma motar bata sauri. Na matsu inji dalilin da yasa makiyinka yake kokomawa mutuwarka, har ya sume dominta".
Juyowa nayi na kalleshi na 'yan sakanni, na sake maida kaina a titi cikin jin zafin maganganunsa. Na sadda kaina kasa, sai hawaye suka fito, suna diga akan tafukana.
Sanyin na'urar motar yayi min yawa domin har raba ke naso daga kofofin A.Cn. Ga sanyin da jikina yayi da kalamansa, suka hadu suka haifar min da zazzabi-zazzabi, na soma jin kaina a sama, ban bari mun hada ido ba, don bana so yaga hawayena.
Ya karya kan motar ya shiga layinmu, wannan karon yana tafiya ne cikin (slow-motion). Tamkar baya so mu karasa gidan.
"I'm hungry, yaya za'ayi kenan? Gashi nayi alkawarin bazan sake cewa ki dafe min wani abu ba, 'above all' kema din baki da cikakkiyar lafiya, kin jigata kin wujijjiga da mutuwar maigida ba zaki iya girkin ba ko na janye alkawarin nawa. ‘I still wonder’ dalilinki na damuwa da mutuwata maimakon kiyi farin ciki na baki duniyar ki sha sharafinki...".
Wannan karon ma shiru nayi, banyi magana ba, hawayen ne dai suka ninka na baya.
"Insha sharafina, ko in shiga uku na?" Zancen zuci nake, ban san cewa ya subuto fili ya shiga kunnensa ba.
Yi yayi kamar bai ji ni ba, ko da gasken ne bai ji ni ba bazan iya sani ba. Domin cewa yayi.
"Kina jina? Na ce don mene kika damu da mutuwa ta?"
Har tsakar kaina naji shock, cikin kwanyar kaina naji kunya, wata irin kunya da ban taba jin irinta a rayuwata ba. Wadda ta haifar min da dabarbarcewa.
Ya sake maimaita tambayarsa. Wannan karon, tambayar tasa tana dauke da 'intonation' na ba da umarni kuma da gaske amsata yake bida, ko rai ya baci.
CIkin karkarwar murya da in-ina na ce.
"Uhm... uhm abincin yana... yana gida, na riga na dafa... ba sai ka sayo ba!".
Dariya yayi mai hade da kallo daga can kasan ido.
"Shi kluma cefanen fa?"
Nima sai abin ya bani dariya, ganin ya saki daga daure fuskar da yayi.
"Tambayar da nayi miki daban take da amsar da kika bani Fa'eezah!. 'Anyway' jikina ya bani kinyi kewana, idanuwanki sun nuna, kwayar idonki ta fada, kazalika kasusuwan da suka yiwa cikakken wuyanki ado, suka kuma maida dara-daran idanunki lungu. Don haka ne na zamo 'curious' wajen son jin dalili? Dalilin da ya sumar dake don NA MUTU! Alhalin sanin kowa ne mutum yana murna ne da mutuwar makiyinshi...".
Na katse shi cikin kosawa, "Indai cefane ne ai Shu'aib ya kawo, Ya'u ya sanya su a (kitchen) da (store) da firinji, don Allah ka rabu dani haka!". Sai hawaye.
Dai-dai sanda ya sanya hancin motar cikin gate din gidanmu. Buzu ya bude bakin shi yaki rufuwa don murnar isowar Ubangidan shi lafiya. Ya sanya motar a ma'adanarta, ya kashe fitilunta amma ita motar bai kasheta ba.
Na murda mabudin motar don in fita, ko motsi ya ki yi. Na juyo a hankali na dube shi, da idanun bidar dalili. Har yanzun murmushi yake, ya ce.
"Cefanen? Guda nawa ne?"
Na ce cikin kauda kai, "To bude min kofar mana tukunna muje ciki kaga yawan cefanen da idanunka?"
[1/4, 12:25 am] Takori: Rausayar da kai yayi, a cikin kallona, ya lumshe idanunsa ya bude.
"Yaya akayi kika sauya haka? 'What a sudden and awkward change! I need an explanation if you want to go out".
Idanuna suka wani irin lumshe da kansu, na debo karfin zuciya na bude su tangararau akanshi.
"Allah Ya hana bincike, kaga Allah Yaya Fa'iz yunwa nake ji... ka bude min kofa".
"Allah Ya hana bincike, amma ke kika yi?"
Na fiddo ido na ce, "Binciken me nayi maka?"
Murmushi yayi (again), "Za ki rantse da Allah baki shiga dakina ba?"
"Na shiga mana, amma ban bincika komai ba wallahi, gyarawa kawai nayi".
Ya miko min hannun shi na dama na alamar karbar abu.
"Bani DIARY dina!'.
Na kai tafukana na rufe fuskata cikin matsananciyar kunya.
"Koda na gani, ba lallai ne ya zamo na karanta ba. Kuma ma ai duk rabi Larabci ne ba iyawa nayi ba".
Ya girgiza kai, "Fa'eezah! Kin dauka ban san cewa tun kina 'yar ficikar ki kike yara Larabci ba? Kin zaci ban san cewa (B.A Arabic) kike karantawa a BUK ba???"
Baki na saki galala! Ina kallonsa.
"Rufe bakin kada kuda ya fada".
Dariya nayi na juya masa keya.
"Duk wani motsi na rayuwarki nasan dashi, haka duk wani abu da kike aiwatarwa a kan wadannan fitinannun idanun ne, ko ba haka kuke cewa ba keda 'yan uwanki Ummi da Zaneerah?"
"To mai yasa kake sa min idon? Ko kasan sa min idon da kake yana daga cikin abubuwan da suka sa na ki jininka a lokacin? Ina ganin kana sa min ido ne domin ka kuntaci rayuwata".
"Kina so ki ji dalili?"
"Eh".
"To amsa min tambayata, ta shin kin karanta min DIARY bada izinina ba ko?"
"Eh, na karanta, shi kenan? Amma wallahi ba bincike nayi don na samo shi ba, tuntube nayi dashi a dokin kofa".
Murmushi yayi, "...Fa'izah matar Fa'iz! Insha Allahu jirgi ba zai zamo ajalina ba sai SON FA'IZAH!".
Na dago cikin (slow) na dube shi, kwayan idanunmu suka hadu, suka sarke da juna. Babu komai cikin kwayar idanunshi sai 'gesture' wato motsi mai nuna zahirin abinda ke zuciya.
Tsigar jikina ya tashi yarrr! Jikina yayi bala'in sanyi, ban san yaushe kalaman ke fitowa a hankali daga baki na ba.
"Balle ma in Allah Ya yarda tare zamu mutu, tare za'a binnemu, kuma ba ta hadarin jirgi ba. Tukin-jirgi, hanyar abincin mu kenan ba hanyar ajalinmu ba, yanzu muka fara tukashi muna saukewa daga kuruciya har tsufa, ranar da ba zamu iya ba 'ya'yanmu su karba, haka har jikoki".
Ni kadai nasan abinda naji... da na tsammaci mutuwarka! Da ka mutu a wannan lokacin Yaya Fa'iz I'll no longer be in existence. Na tabbata in 'so' bai kasheni ba kewa da 'kauna' za su kasheni...'
Wata irin runguma Fa'eez yayi min da saida kasusuwana suka amsa. Hawayen dake makale tun dazu suka balle mini suka shiga shan sharafinsu a kundukukina zuwa gadon bayan sa.
Ya kai hannu ya shafo hawayen, "Daina zubar dasu haka nan Fa'izah. Na tabbata ba ni ne baki so ba HALINA NE. Wanda a zahiri ba halina bane KISHI NE. Ba ke nake sanyawa ido ba, SOYAYYAR DA KIKE YIWA YAYA ALIYU NE!
Ina kishin Aliyu Fa'izah, yadda bakya zato, har gobe ba zan daina ba. Domin wani mutum ne shi da kika so da zuciya daya saboda HALINSA! Na yarda na amince halin mutum jarinsa ne daga yau nima na zama dan kirki, dama ke kadai nakewa rashin kirkin, kema kuma don kina son ALI NA'IBI ne! Tunda kin maido son gareni na miki alkawarin zama mai kirki fiye da Yayanki ALIYU HAIDAR NA'IB A.B GIWA!"
Na dago kaina ido sharkaf da hawaye.
"Ko baka canza ba INA SON KA HAKA!
I go along with the people I love da halinsu...".
Dariya yayi, "Da can dinma bakya ki na, bacin ranki kike expressing' na bakanta miki da nayi. Da kina ki na da kinbi shawarar dana baki a RIVER NIGER".
Na dunkule hannu na bugi kirjinshi da shi.
"Kai ne baka iya kishin ba ai, kishi na mugunta?"
Na sake bugunshi, "Ba'a nuna KISHI da KIYAYYAH... Ga wanda aka yimawa KIYAYYAH NE. Ka daina kishi da Yaya Aliyu don Allah, dan uwanka ne, kuma surukinka.
Na so yaya Aliyu, kasancewar shi wani mutum da ya wahalta mini, da gangar jikinsa, da zuciyarsa, da aljihunsa da lokacin shi a kaina. Ya shiga kunci a lokacin da ya rasa ni. Kai da ka samu bai yi kishinka ba ya bada kyakkyawar gudunmawa wurin ganin na hakura na rungumi aurenka Yaya Fa'iz.
Aliyu ne ya sani yin zuciyar da na tsaya nayi karatu na shiga sahun dalibai nagartattu a lokacin da nake cikin shagaltattu. Don me ba zan so shi ba a wancan lokacin tunda an halicci zuciya ne da soyayyar mai kyautata mata? Ina son shi ne a lokacin, amma wani irin so irin wanda nake yiwa BABA NA ban taba kimsawa zuciyata sha'awar tarayya a tare dashi ba sai so na 'KAUNA' da mutuntawa hadi da ganin kimar juna.
Amma wannan son da nake ji a yanzu akan Hafizin Hajjah? Wani iri ne da harshe ba zai iya bayyanawa ba, kwakwalwa ba zata iya fassarawa ba, da ya gagari fahimtar mutum sai dai zuciya ta jishi amma ba zata iya bayyanawa ba.
Haka nan zuciya da kwakwalwa basa iya daukar shi ba tare da sun nuna gazawa ba saboda GIRMANSA! Daban yake dana YAYA ALIYU kazalika NAZIR SANI GALADANCI. A kansu duka, banji irin wannan lullubabben son da nake yiwa FA'EEZ MUKHTAR ABUBAKAR BAMALLI GIWA BA!!!".
"Barni haka... kada ki kasheni da raina".
"Ya fadi ne a galabaice, cikin tsananta rungumar da yayi min.
"Allah Ya bani tsawon ran da zan ninka farantawar da Aliyu yayi miki, Allah Ya bani tsawon ran da zan nuna miki bakiyi asarar Yaya Aliyu ba! Nayi alkawari Fa'izah zan nuna miki so da kulawa fiye dana Yaya Aliyu. Ko da can din ban samu dama bane, babu kuma hanyar da zan samu damar. Sai dai kisa a ranki, na rantse ALIYU BAI FINI SONKI BA... DAMA YA FINI SAMU!"
Ni kadai nasan halin rudun da na shiga a lokacin da kike neman hallaka kanki don kiyayyata, sai ko abokina Maajid. Kada ki kara sawa a ranki wai bana son ki. Kisa a ranki Fa'eez naki ne KE KADAI".
Shudewar mintuna masu tsayi cikin wasu al'amura masu tsayawa a rai, da zuciyar wanda ake mawa. Na nemi ji na da ganina na wucin gadi na rasa.
Fa'eez ya daukeni ya kai wata duniya ta daban irin ta Adamu da Hauwa'u da ma'aurata kadai ke zuwa kwatankwacinta. Ya manta da yunwar cikinsa na manta da tawa, da kyar muka rarrafa zuwa cikin gidanmu muka dangana ga dakin baccinmu.
A can komai ya kwance, al'amuran suka sauya taku, baga Fa'iz ba, ba ga Fa'izar ba, kowanne so yake ya nunawa dan uwansa ya fishi so da kaunar kansa. Ina rokon Allah Ya tsawaita rayuwarmu, Ya kara soyayyar junanmu cikin zukatanmu, ya bamu 'ya'ya masu albarka da biyayya ga iyaye.
Bana burin in haifi da mai irin halina na kafiya, riko da taurin zuciya. Addu'a nake, Allah Ya bani Da ko 'YA mai hali irin na Ubansa/ubanta, mai yakanah irin ta Ubana da Baban Kaduna, mai son zumunci da kyautatashi irin HAJJAH. Mai tsaftattar zuciya irin ta MOMI na ma'abociyar rungumar kaddarorin UBANGIJI.
(Ku ce Ameen, makarantan TAKORI).
* * *
Kwanaki bakwai da suka biyo baya, babu abinda ke wanzuwa a gidan sai amarci zallah, na a buga a jarida. Babu inda Fa'iz ke zuwa daga gida sai masallacin wani gida makwabtanmu, sai gidansu a Jabi Road shima duk dadewarsa baya wuce rabin awa.
Ranar da ya cika kwana goma sha hudu ya ce in shirya zamu je zaga dangi daga nan mu wuce Giwa wajen Hajjah, sun dawo daga Jeddah ita da Baba Na'ibi da Aunty Zainab inda aka kaita asibiti tsayin sati biyu.
'Yan uwa dake kewayen Kaduna muka fara zagewa, su Aunty Hauwa Maman Ummi, sai Jabi Road. Mama dai hadiyeni ne kawai bata yi kullum sai zuba mana albarka, haka Baban Kaduna albarka suke saka mana babu kakkautawa a duk lokacin da kafafun mu suka taka gidajensu. Da kara jan hankalinmu kan riko da ZUMUNCI. Su kan ce. "Ko babu aure mu 'yan uwan juna ne, don haka hakuri da junanmu ya zama dole don cigaba da (maintaining) burin Abubakar Bamalli, ya cigaba da ganin abinsa can inda yake, suna rokonmu ko bayan ransu...kada mu warware wadannan igiyoyi da suke kukkullawa a tsakaninmu kan kannenmu da 'ya'yayenmu, jikoki da tattaba-kunne.
Mun dauko hanyar Zaria bayan mun baro Kaduna, bayan motarmu shake da tsarabar su Walida (trolly) guda da Fa'iz yayo musu. Amma cikin rashin sa'a bamu same su a gidan ba. Walida tana makarantar WTC Soba tana shirin zana jarrabawar fita (SSCE) yayin da Abdallah ke makarantar horas da sojoji a Jaji (National Defence Academy). Kausar na S.S I a Sarauniya Amina, inda Walid autan Momi ya shiga shekararsa ta farko a karamar sakandire.
Babana Prof. Ahmadu A.B da Momina Maimunatu A.B, sun rasa ina suka-saka-ina-suka aje damu don farin ciki. A fili Baba ya daga hannu yana yiwa Allah godiya a cewarsa da Ya nuna masa wannan rana, wadda Hajjah har kullum ke ce da su tana zuwa! Yayi addu'a Allah Ya karawa Hajjah lafiya da tsawon kwana., Ya jikan ABUBAKAR BAMALLI. Gaba daya muka shafa da amsawa da
"Ameen".
Fa'eez ya tafi cikin city ya barni, ya ce zai je yaga Surajo ya dawo.
Bayan fitarsa ne Baba ya dubeni yana murmushi yake fadin.
"Yo ko ke fa Fa'izata?"
Na dago kai na dube shi nina murmushin nake yi. Rabon da inga yana walwala irin haka tun muna kanana sanda yake kaimu (Nursery) 'staff school'. Yana tuki yana mana tatsuniya har muje makaranta.
Idan ya debo mu akan hanya zai tsaya ne ya sai mana dafaffen kwai da gishiri ni da Walida da Abdallah. Kullum ne ranar Allah sai ya sai mana dafaffen kwai da zuma wai suna kara kwanyar karatu.
Idona ya ciko da kwallah da na tuno wahalar da na bashi 'in return'
"Na ce ko kefa? Dubi yadda kika yi kyau, kika ciko, da kika kwantar da hankalin ki. Amma watannin baya baki ga irin takaicin da kike sanya ni ba. Kullum idan na daga ido na dubeki a gidan nan wai na kasa lankwasa ki, wani abu ne ke tokareni a kahon zuci. Kullum tunanina wai 'yar da na haifa tafi karfina, tafi karfin UWATA da yayye na, a duk sanda nayi tunanin haka, na duba na hanga naga cewa babu wanda keda irin wannan dan cikin A.B ... sai inyi dakacen dama ba ni na haife ki ba!!!'.
Da rarrafe na isa ga Babana, kuka sosai nake har da majina.
"Ka yafe min Babana, ka dubi Allah kayi min afuwa, kuskure ne da aikin shaidan ina rokon Allah Ya kara nisantani da shi.
Duk abinda nayi nayi ne a bisa kuskure da rashin fahimta. Na roki afuwar yaya Fa'iz tuni ya yafe mini... Ina rokon ku kuma ku dubi Allah da nadamata ku yafe mini ko na cigaba da ganin haske a rayuwata... Ku taya ni rokon Hajjaty ta yafe mini...".
Baba yasa hannu ya dago ni, "Tuni na yafe miki Fa'izah, ina gaya miki halin da na shiga a baya ne ba don ban yafe miki ba. Allah Yayi muku albarka, Ya kyautata gabanku da bayanku, Ya baku zuri'a masu albarka!!!".
Ya sanya hannu ya janyo 'brief-case' dinshi ya fiddo wasu takardu, ya duba sannan ya miko mini.
"(Share) ne na banki na saya muku dukkanin ku, ke kuma na hada da bude miki 'account' da bankin JA'IZ don saukakawa mijinki wasu daga cikin lalurorinki. Na kuma bude shi ne da niyyar duk wata idan na dau albashi zan sanya miki wani abu a ciki, haka kason ku na wata-wata da ake baiwa duk wani da na A.B shi kuma na bude mishi 'account' daban da Bankin 'Fidelity' ga (details) dinnan ki adana a wurinki ko ki bawa mijinki ya adana miki".
Hannu biyu nasa na karba ina godiya. Na kare da cewa.
"Baba Allah Ya bar min kai!".
Murmushi yayi, "Nima Allah Ya bar min ke".
Momin tayi dariya tana jinmu bata ce komai ba, dana juya gareta sai naga ta sunkuyar da kai hawaye na diga daga idanunta.
Wato wannan din wata irin soyayya ce ta da da mahaifi da ita bata samu ba!
Kaico da iyayen dake haifar 'ya'yan su zubda su ko masu sacewa su raba su da iyayensu, saboda cimma wata manufa ta duniya. Ya Allah ka barmu da iyayenmu har karshen rayuwarmu, Ka kara musu lafiya da tsawon kwana, Ka basu ikon kula da hakkokinmu, muma Ka bamu iko da zuciyar yi musu BIYAYYAH don gamawa da duniya lafiya (Ameenm summa Ameen).
Dai-dai lokacin da Fa'eez yayi sallama shi da Surajo, Surajo ya gaida Baba da Momi ya koma tsokanata.
"Yau sati biyu kacal cikin takaba amma aka rangada kwalliya?"
Na galla masa harara Baba kuwa dariya yayi suka shiga hira na abinda ya shafi aikin Surajon (Banking), tashin zabuwar 'Doller' da 'sterling pounds' abin babu dadin ji. Sun dade suna hirar, tare da yiwa kasar mu addu'a. Muka yi sallama dasu muka dauko hanyar Giwa, shi kuma Surajo suka yi hannu ya shige motarsa ya koma cikin city inda gidan iyayensa yake. Har zuwa yanzun bai yi auren fari ba, na dai ji jiya Fa'iz na fadin ya kai kudin aure.
Muna tafe akan hanyar Giwa, sanyin na'urar sanyaya mota na ratsa kasusuwa zuwa bargon mu, sautin Abdurrahman Sudaith na tashi cikin Suratul Tagabun, Nake gayawa Fa'iz.
"Ko kasan rabon da kalami mai dadi ya hadani da Momi da Baba irin na yau, tun ranar da tsinkayi labarin daurin aurenmu? Na rasa wane irin so kafatanin A.B ke maka, kana da wata ilhama ta musamman da duk cikin zuri'armu babu mai ita. 'I salute!"
Na kai