Showing 1 words to 3000 words out of 42033 words
Chapter 1 - Zumuntar kenan book by Sumayya Abdulkadir Takori.txt
[1/4, 12:21 am] Takori: Shin wace ce Fa'izah? Me take takama da shi da take neman haukatar mana da Fa'iz haka? I dare you (Ina baka karfin gwiwa) kafin Fa'izah ta haukata ka, ko ta maida kai Fa'izah ta koma Fa'izun".
Su da basu san dawar garin ba sai abin ya basu dariya da yake da Turanci yake maganar.
Fa'iz ya kufula, a fusace ya ce.
"Uban waye ya ce da kai tsoron Fa'izah ne ya hana ni tahowa da ita?"
Maajid ya ce, "Yo in ba tsoro bane mene ne wannan? Yarinya tana matarka, karkashin ikonka amma ka tsaya kana shayinta? Anya kuwa zaka iya lankwasa Fa'izah Fa'iz? Ni wannan so ya yi yawa, ka bata (power) sosai ko da ace laifin naka ne kamar yadda kake ikirari. Muna da sati biyu kwarara na kintsawa kafin mu fara aiki da British Airlines, kayi amfani da su kaje ka dauko Fa'izah ta zauna a damanka zuwa duk inda ka cilla kafa cikin duniya ko ma samu nutsuwar ka, ko da ace haukan gaske zata yi ba na karya ba, a Turai akwai (psychiatrics) da (Asylums) iri-iri (gidan mahaukata).
Fa'iz kam tsiyar Maajid ta ishe shi, yana neman tona masa asiri gaban abokan su bayan ya kasance mutum mai son sirri a rayuwarsa, musamman idan abin ya hada ne da (personal-life) dinshi ba harkar karatu ko aiki ba.
Sai ya mike ya dauko robar ruwa ya kuskure bakinshi ya furzar. Amma bai daina mishi azabar yajin da yake mishi ba,.
Maajid ya ciro karan sigarin dake bakinshi ya mika mishi.
"Sha wannan, zai kashe 'shatter' (yaji)".
Ya dalla mishi harara, sai Javed Saddyqy ya tsiyaya sanyayyen lemun 'shany' cikin tanbulan ya mika mishi. Ya karba ya kwankwade ya dire kofin Javed ya kara bincire hancin 'Rany' ya cika tambulan again ya sake mika mishi. Wannan karon ma ba musu ya amsa ya kwankwade ya dire kofin. Sunyi haka har sau hudu, sannan Fa'iz yaji dai dai, ya ce.
"Shukran Yaa Siddiqy" wato (thank you Saddyqy).
Ya wuce su ya nufi (lifter) da zata kaishi dakinsa dake hawa na goma sha uku. Ya bude dakin ya shiga ya maida ya rufe. Kai tsaye na'ura mai kwakwalwa ya nufa, yana duba tsarin tashin jiragen su cikin satin inda ya samu akwai jirgin British da zai tashi zuwa Abujar Nijeriya a safiyar gobe. Kuma a goben ne hutun kintsawarsa zai fara. Kafin ya dawo ya kama aikin da aka dauke shi cikin nasarar da dukkaninsu basu zata ba.
Ya tabbatar aurensa da Fa'izah alheri ne a gareshi, domin daga ranar da ya furtawa Hajjah yana son Fa'izah a aura masa ita don ya gyara zumuncinsu da ya bata yake ta ganin fatahi wato budi ta kowanne bangare cikin hanyar samun abincinsa, kai har ma da wata irin nutsuwa cikin zuciyarsa.
Zama yayi a bakin kayataccen gadon dakin yayi shiru, ya rasa abinda ke masa dadi, haka ya rasa abinda ke cunkushe masa zuciya. Baya farin ciki da komai kamar yadda ya rasa walwalar sa dungurungum.
Kada dai zancen Maajid ya kasance gaskiya ya zama FA'IZAH maimakon FA'EEZ. Tabbas yana tsoron haduwarsa da Fa'izah a karo na biyu, amma haduwar (is something inevitable) wato wani abu da ba makawa sai ya faru, don haka ya zama dole ya aro jarumtar dake neman kufce masa ya koma ya kawo karshen kalubalen da suke ciki shi da Fa'izar da gidansu baki daya da kowa cikin zuri'arsu da suka zame musu wake daya mai shegen doyi. Don haka cike da karsashi ya shigar da kanshi cikin jerin fasinjojin da jirgin British zai kwasa a safiyar gobe zuwa kasar haihuwarshi Najeriya.
Da ya kammala ya janyo jakar tafiye-tafiyen shi ya soma shirya kayansa, cikin tarin nutsuwa da Ubangiji Ya halicce shi da ita. A karo na farko yayi tunanin gwada daya cikin (theories) din Maajid na lallashi ga Fa'izah duk da ya san ba wani tasiri zata yi ga Fa'izah ba.
Rufe jakar yayi ya mike ya sauya kayan jikinsa, ya dauki wayoyinsa da (mastercard) dinsa ya fito daga dakin ya rufe. Mota ya dauka a harabar adana motocin dake cikin hotel din wadda ta kasance ta haya ce kirar 'camry' ya hau bisa kwalta a hankali. Bai tsaya ba sai a bakin wani (Jewellery shop) a tsakiyar birnin Wales ya fito cikin wandon jeans ruwan kasa-kasa da riga ARMANI itama ruwan kasar ce amma mai haske, yayin da wandon ya ciza sosai, saye a idanunshi gilashi ne 'prada' baki mai duhu wanda bai faya amfani dashi ba in ba a lokacin aiki ba.
Ya tabbatar ajiyar da yake da ita cikin (mastercard) dinsa sun isa da ya shiga wannan kantin domin ba kantin (fashion jewellery) bane, kanti ne na duwatsu masu madaukakiyar daraja (diamond, sapphire, gold, emirald) kadai. Kamin ya isa ga kofar shagon wadda ta kasance ta gilashi tuni ta bude kanta. Ya tsaya yana nazarin siraran sarkokin farin 'diamond' a wani bangare dake cikin shagon, ya zabi wadda yake ganin zata yi dai-dai da siririn wuyan Fa'izarsa, haka zoben dake hade da ita yayi bala'in dacewa da zara-zaran yatsunta daya gani ranar da suka kantara masa kwalba...
Ya yi murmushi shi kadai, ya kai hannu ya shafo lallausar sumar kansa daidai inda kwalbar ta huda, ya kame yazama tabo, ya dauka ya biya. Aka sanya su cikin gidansu mai martaba aka bashi tare da risidi (reciept) bayan an ciri kudin daga (credit-card) dinnasa.
Akan hanyarsa ta komawa hotel din da suke, ya shiga shagon "NEXT” ya yiwa Fa'izah sayayyar sutturun NEXT samfuri daban-daban, riga ne, siket ne, wando ne, jacket ne, sweater ne duka 'yan gidan 'NEXT' masu daraja ko daga kallon su a ido ba sai an tambaya ba.
Daga nan shagon turaruka ya tsaya ya daukar mata gigitattun turarukan ESCADA (sentiment and magnetism) sannan ya dawo hotel ya hada cikin kayansa.
A daren ya hada komai nasa cikin jakunkuna manya har uku, daya sayayyar Fa'izah ne taf, daya na Mama da kannensa, sai ta kayansa. Washegari ya biyo jirgin British mai zuwa Abuja.
****
Da ya sauka a Abuja waya ya yiwa Yaya Sa'id yaje (airport) ya dauko shi, kasancewar Yaya Sa'idu Na'ibi kani ga Yaya Aliyu aiki yake a Abuja da (Federal Ministry of Agriculture) zuwa gidansa. Ya kwana ya huta suka sha hirarsu ta zumunci duka akan 'yan uwa washegari ta kama asabar dama Sa'idun zashi gida Giwa, sai suka taho tare. Ya sauke shi Kaduna (Jabi Road) shi kuma ya wuce Giwa.
Ba zato Mama ta ga Fa'iz yana sallama a kofar falonta. Wani dogo kuma katon saurayi (giant and gentle) ma'abocin kwarjini, cikar zati da kamala da ya gama zama mutum, wanda in ka kalle shi dole ka sake, mace ne kai ko namiji saboda wasu ilhamomi da Allah Ya yi masa da ba duk maza Allah Ya mallakawa ba.
Abubakar Mukhtar Abubakar (Fa’iz), kamar yadda cikakken sunansa yake, mutum ne (extraordinary) tun yana kankaninsa har girmansa, komai nasa daban yake da na sauran maza tsararrakinsa cikin A.B Bamalli House. Mutum ne mai matukar kyau da kwarjinin da idan ya shigo wuri sai kowa dake wurin ya ji shi (inferior) wato kasa dashi, ko da ya girme shi da shekaru, sai an san ya shigo saboda haibarsa, sai an san yana wuri saboda zatinsa. Sai an san namiji ne saboda kamalarsa.
Duk da ya kasance mai kin ji da kiriniya a lokacin kuruciyarsa, shi ne da mafi soyuwa a zuciyarta cikin ‘ya’yanta guda tara, wanda kuma tafi shan wahala akansa kafin ya tsaya ya ginawa kanshi (future), wanda sai da ya shekara goma bai iya rubutu ba, ya kuma yi karatu ba tare da rubutu ba.
Idan ta hada rayuwar Fa'iz gaba daya, daga yarinta zuwa girma, akwai baiwarwaki masu yawa a ciki. Ya kuma ci ace tun yana yaro sun gane yana da karama a fannin sarrafa abin hawa da (passion) akan duk wani al'amari da ya shafi injin hawa. Kai dai barshi da kabilanci da wariyar launin fata ga wanda ba ahalinsa ba ko ba jinin sa ba.
Ta sauke idonta cikin nasa a hankali tana murmushi, shi kuma sai ya zarce da dariya yana fadin.
"Ga bakon Mama babu sanarwa".
Ta amsa, "Ina maraba da wannan bako nawa duk da nasan wannan zuwan ba nawa bane".
Sai ya yi dariya cikin bagararwa ya zauna kasan kafafunta suka shiga gaisawa.
Mama ta kasa zaune ta kasa tsaye da hidimar saukar (unexpected) bakonta, Abubakar-Fa'iz. Fitinannen danta (a da) amma dan lele a yanzu tunda ya auri abin sonta Fa'izah, ya kuma tsaya ya fuskanci rayuwa ya gina kansa irin yadda, ko ma fiye da yadda suke so ya fuskanta.
Kalolin abinci har biyar da ta jere a gabansa sai da suka bashi dariya cikin jin dadin kulawar mahaifiyarsa gareshi yake fadin.
"Duk ni kadai, ni Abubakar dan gatan Mama!".
Ta harare shi idanunta cike da kauna.
"Ko kunya baka ji ba da abinda kake fada wai dan gata na, ina ruwana da kai, (after all) nasan ba wajena kazo ba. Amfani nayi da Hadisin Manzo da ya ce, "Bakonka-Annabinka..." da kuma kasancewar mai yin bata kusa da ina ruwana da hidimar ka?" Dariya yake yi wadda ya manta rabonshi da yin irinta, watakila tun kafin Fa'izah ta shigo tayi sallama cikin sabuwar rayuwarsa ta baya.
Ya ce, "ya yi min yawa ne Mama".
Ta yarfar da kai, "Ko da baka cinye duka ba dai ka daure ka dan tsakura, don wadda kake rawar jiki da dokin ganin ba baka zata yi ba".
Murmushi ya yi, ya dauki (spring roll) mai taushi ya sanya a bakinsa ya gutsira yana ci. 'Yan kannenshi su Junior duk sun zagaye shi suna tambayar shi yadda sama take.
Ya ce, "Kuje ku tambayi malamin 'Geography' dinku (I'am not an astronomist)".
Shu'aib ya ce, "Yaya Fa'iz nine planet suna yi muku magana a sama?" Shi kuwa Yahya cewa yayi, "Wai Yaya ta saman su kuke bi ko ta kasansu?"
Junior ya ce, "Yaya bakwa take su?"
Ya zuba lemu 'Don-simon' cikin tambulan ya ce.
"Kai don Allah ku saurara mini, na ce (I'm not a geographer, neither an astronomist) amma ku bari na muku alkawari ranar dana shiga duniyar wata (journey to the moon) na dawo zan amsa muku wadannan tambayoyin naku".
Sai Yahya ya ce, "Amman da Fa'izan gidan Baban ABU ce ta tambaye ka da ka gaya mata ko Yaya?"
Fa'iz ya dauke wuta, cikin mamakin kalaman yaron, dariya ta kama Mama amma bata yin ba sai a zuci. Ya tsurawa yaron ido yana kallo cikin hada amsar da ya kamata ya bashi, kafin ya samu ya harhada sai Shu'aib ya ce.
"Kasan ko tun ranar da Fa'izah suka zo da Aunty Ummi daga Kano muna gyaran dakinka ta zo ta leka dakin ta tambaye ni na ce mata ku za ku dawo, bata kara zuwa gidan nan ba".
Yahya ya ce, "Ai bata son sa, kaga wannan tabon na goshinsa ma ance ita ta ji masa".
Junior ya ce, "Kai ya akayi ka sani?"
Ya ce, "Rannan ina dakin Aunty Zainab (Maman su Yaya Aliyu) naji Ummi na gaya mata har tana cewa tayi asara...".
Da sauri Mama ta cira ido ta dubi goshin Fa'iz a hanzarce, Fa'iz bai san sanda yasa kafa ya kaiwa Yahya wani mugun hauri ba, Mama tayi sauri ta rike kafar gam, ta ce.
"Kada ka karya min yaro, ba shi ya kar zomon ba balle ka rataya masa, ba a bakinsa na fara ji ba. Waye bai san Fa'izah ta kwada maka kwalba ba? Ni dai rokona akan ka duk rintsi kada ka biye mata domin ka cancanci hakan daga gareta ko ma fiye. Ka ringa yi kana TUNA BAYA... domin TAKORI ta ce "TUNA BAYA SHI NE ROKO" sai dai ina da yakinin yadda komai a rayuwa ke zuwa ya wuce (with time) kiyayyar Fa'izah mai wucewa ce tunda kaima sanda kake kinta baka kayyade lokacin daina kin nata ba. Zuwa ya yi da kansa, don ma anfi karfinta ne amma da ko kusa baka cancanci auren Fa'izah ba, Aliyu shi ne mutum mafi dacewa da auren Fa'izah ba kai ba Fa'iz!".
Banda Mama ce, UWA! Wa ya isa ya dubi tsabar idonsa ya gaya mishi haka
Ya yi kwafa kamar zai hadiyi zuciya ya mutu don takaicin kalaman Mama, ya yi shiru yana gwama numfashi kamin ya dubi Mama cikin sanyin jiki.
"Wa yafi karfin nata? Gaba daya cikin ku wa yafi karfin nata a yanzu Mama? Cikin ku duka an rasa mai sanya baki a bani matata kamar yadda aka baiwa kowa tasa, saboda ita ishasshiya ce kowa yana tsoronta. To ni kam na zo daukar aurena ne (dead or alive)!"
Mama tayi dariyar da ta kara kular dashi, ta ce.
"Kofar hanyar Zaria a bude take ai kullum Fa'iz, kai da baka tsoronta sai ka je ka dauki abarka, munji mu tsoron ta muke ji kada muje ta fasa mana kai kamar yadda ta fasawa jarumi Fa'izu Abubakar".
Haushin maganganun Mama koko ya ce shagube ko gugar zana yasa shi mikewa ya nufi dakinsa ba tare da ya kara tofawa ba.
Yayi wanka, ya zuba shaddah 'getzner' koriya sharr. Ya bi jikinshi da turaren (212). Bai dauki sanya hula da muhimmanci ba kasancewar sa mai tara sumar kai da bata (extra) kulawa, don haka yau din ma bai sa ba. Ya zura lafiyayyun takalma budaddu bakake sidik kirar Thailand. Ya jawo kayanshi da ya zo dasu ya ware tsarabar da yayowa Fa'izah wadda dama ya wareta cikin (troller) guda.
Ya daga ido ya dubi jerin akwatunan dake girke a gefe masu suna lefen Fa'izah wanda har yau babu wanda yace ya kawo a kai mata duk da an kai na Yaya Bash da alama ma da baya nan anzo an bude an zari wasu.
Ya kwalawa su Shu'aib kira, ya ce su fidda akwatunan su zuba mashi a 'Roll-Royce' din Baba da ita zai fita. Suka kwashe har ta tsarabar, ya fito ya nufo dakin ya isa sashin Mama ya shiga ya zauna cikin lumtsuma-luntsuman (leathers) dinta.
Tana jera kayanta a sif ta amsa mishi sallamar kafin ta juyo. Tayi murmushi ganin yadda ya hade kamar wani angon so, nan kuwa angon ki ne, shi kuma sai ya fara sakin tsaki.
Ta ce, "Ya akayi? Sai ina kuma ango sha kamshi? Ko sai Zariyan?"
Ya ce, "No Mama, ina son zuwa gidan yaya Bashir ne, bana nan suka tare".
Ya sha mur sosai ya ja fasali ya ce.
"Yanzu Mama da ita mutuniyar kirki ce da bamu je tare ba?"
Tayi dariya ciki-ciki kamar bata gane wa yake nufi ba, ta ce.
"Ita wa?"
"Fa'izah mana!".
Tayi 'yar dariya, "Mutuniyar kirki ce mana".
Ya yi tsaki, "Ban ga alama ba. Yanzu don Allah Mama da gaske kike ba zaki sa baki Fa'izah ta sakko mu tafi tare ba? Na gaya miki British Airlines sun dauke ni aiki, zan fara sati biyu masu zuwa don haka (most of my stay now will be in Wales, London and Scotland) ba zan iya zaryar zuwa gida akai-akai ba sai bayan watanni uku-uku.
Zai fi sauki idan muna tare a duk inda nake don samun cikakkiyar nutsuwa da kwanciyar hankalin gudanar da aikina yadda ya kamata. Ki taimaka min Mama, ni kadai ba zan iya ba, kunyi min aure amma kun barni ni kadai da yakin kwatar sa, baku cika ladar ku ba".
Mama ta ce, "Kaga babu ruwana cikin rigimar ku, can muku. Wanda ya jawo ruwa shi kadai zai doka. Yadda Fa'izah ke ganin bakin kowa kan maganar auren nan banda ni, sannan kazo ka tsoma ni ciki, salon ta ce na bi bayanka don ba ita na haifa ba? Bayan sanda kake tsula mata tsiyar ka baka nemi taimakona ba idan kuma na hana ka ba ka ji. Kowa ya debo da zafi, bakinsa".
Kamar zai fashe da kuka, "Amma Mama haka za'a zuba mata ido tana yin abinda taga dama, ni me na yi mata da zafi haka? Don kawai ina cewa ta dinga tsafta kamar su Zanirah? Ni ba dukanta nake ba, ba zaginta nake ba...".
Ta tare shi, "... in ita baka zageta ba, ai ka zagi uwarta, kana tsammanin 'ya'ya mata suna yafe wa in an taba musu uwa?"
"To ba na ce ayi hakuri ba? Waye kuruciya bata sa shi yin kuskure? Babba ma yana aikata kuskure balle yaro karami kamar Hafizin Hajjah!".
Sai ya bata dariya a yanayin yadda ya yi maganar, ya kuma bata tausayi duka a lokaci daya. Ta dan dube shi tayi murmushi, da gaske cikin damuwa yake, duk jarumtakarsa damuwar ta kasa buya.
Lallai ta yarda SOYAYYAH halitta ce mai zaman kanta, kuma (reality of man's existance)... sannan bata shawara da kai idan ta shirya yin awon gaba da kai, da ta tabbata bai barta tayi wannan tasirin mai yawa a kansa ba, kasancewarsa namiji daya da daya mai ra'ayi da akidu da 'principles’ masu zafi.
A yanayin yadda tayi magana yanzu ya fahimci ta fara jin tausayinsa ta kuma fara fahimtarsa amma bata so ya gane hakan. Cewa tayi.
"Kai da baka tsorontan me ya hana ka yin maganar? Ba matarka bace? Ko ko zaman dadiro ka nema ba hakkin ka ba?"
Ya yi wani irin murmushi, yanzun kam ya fuskanto inda Maman ta sa gaba, wato itama zaman Fa'izar a gidansu ya dameta illa alkunya da kara irin ta mallawan usli don haka ba zata bari aji daga gareta ba sai dai shi din. Ya mike zai fita, wannan karon cike da kuzari, sai ta ce.
"Akwai kudi a aljihunka ne? Motar babu mai, naji Hadi yana fade dazu".
Ya shafa aljihunshi akwai kudi, amma 'pounds sterling'.
Ya ce, "Ban je canji ba sai zuwa gobe insha Allah".
Ta bude jakarta ta fiddo bandirin 'yar Sardauna dauri uku ta mika masa, bai yi musu ba ya sanya hannu biyu ya amsa yayi godiya. Ita kuma tayi hakan ne don sanin halin sa, ya gwammace ya zauna baya da ko sisi da ya tambaye su ko kwandala.
Ummi da angonta Yaya Bashir suna cikin (kitchen) suna hadin (burger) da suke so su ci. Da ya fito sashen Mama a bakin kofa suka yi karo da Shu'aib ya tambaye shi kwatancen gidan Yaya Bashir.
Ya ce, "Yaya Fa'iz muje mana in raka ka, nan ne Kabala Custain ba nisa".
Ya ce, "Amma da kanka za ka dawo? Don ni daga can ba gida zan dawo ba".
Shu'aib ya daga mishi kai suka jera suka fito suka shiga motar Baba, Fa'iz