Showing 15001 words to 18000 words out of 42757 words
Chapter 6 - AISHA-SIDDIQAH-Book 2 Complete original by Takori Kabara.txt
Kiki-Ruqayyat a lokacin ta gama sakandire ta nada shekaru goma sha takwas.
Zamu iya kiran Kiki sa’ar Siddiqah amma ta bata wajen watanni tara, saidai Kiki tayi biyun Siddiqah a girman jiki. Ko don yadda Abdulrasheed ke sakar ma Kiki kudi tana wadaqa yasa ta zama irin (first class ‘yammatan nan), kaunar Kiki da Uncle dinta Prince har girmanta bata canza ba.
Dade ya kira Nenne a daren ranar da suka sauka a Gombe yace da ita suna Gombe shi da ‘yan uwansa su Dan Iyan, Malami Uban Doma da Turaki da Mutawalli, gobe Juma’ah zasu daura auren Abdulrasheed da Aisha a garinsu mahaifinta wato (Kumo) in Allah yaso ya kuma yarda, bayan masallaci.
Ya tabbatar mata komai na neman auren ya kankama Emir bai sa wasa cikin lamarin ba ranar da yaje masa da zancen, a take ya bada sadaki da dukiyar aure yace suje suyi komai da ya dace, ya gaya mata Baban Aisha-Siddiqah wato Malam Yunus da dan uwansa basu kawo kowanne uzuri ba don sun riga sun warware maganar aurenta da yaron da yake neman nata.
Ya roketa kada ta gayawa su Taiwo komai don zata bata musu shiri. “Lets’ take all of them by surprise”. Inji Dade. Kunnen Taiwo na Abdulrasheed ne, baya so Abdulraheed ya kawo musu kowanne cikas ko da kuwa na cewa a dakata ne sai yazo ko makamancin haka, yace duk wata dama sun gama bashi ita yanzun hukunci yana hannunsu, don haka sai an daura ya ji daga baya, ya gaya mata cewa Emir yace kada a sanar dashi sai ranar da yazo gida dan kansa don a lokacin ma baya Qatar, ya halarci wani shahararren ‘tournament’ a yankin kasar Rasha.
Nenne a wurin da take zaune ta fadi tayi sujjadah da wayar a kunnuwanta.
Albishir ne irin wanda Dade bai taba yi mata mai dadinsa ba. Alas! Burinta yau ya cika, akan damuwarta ta rashin auren Prince Abdulrasheed (Kehinde), ko yau rayuwarta ta kare (wadda take da tabbacin ba mai tsayi bace) ta tafi cike da farin cikin cikar buri, ta tabbatar Aisha-Siddiqah data zaba masa bata yi masa zaben tumun dare ba, tana fatan ta zame masa matar rufin asiri kuma uwar ‘ya’yansa kamar ita da Dade, Nenne tace a fili “ko yau Allah ya katse tafiyar, ta gode masa.
Don ta san Kehinde zai rike Siddiqah muddin ta bashi hujjarta ta hada su aure haka da gaggawa, zai riketa albarkacinta, koda baya son ta.
Ita bata aura masa Siddiqah don ya so ta ba, ta aura masa ita ne don ya cika mutum! Mai kamala. Rayuwarsa ta zama cikakka kuma mai ma’ana kamar ta kowa, kuma ya samu zuri’a shima. Tana cikin damuwa da bakin cikin rayuwar da yake yi shikadai. duk da a yanzu bata zarginsa da rayuwar ashararanci face rashin auren wata jarrabawa ce a gareshi. Tana da yaqinin AbdulRasheed zai rike Aisha-Siddiqah a gidansa irin rikon da Dade yake mata don barewa bata gudu danta yayi rarrafe, zai shiga da ita duk inda ya shiga cikin duniya albarkacin cewa ita Nenne ce ta aura masa ita, ba don kasancewarta ‘yar wasu masu mulji ko dukiya ba sai don kasancewarta zabin Nennensa.
Nenne ta kwana da sanin cewa babu gurbin soyayya a zuciyarAbdulrasheed dinta, ya dade da konewa kurmus daga kowanne sako na zuciyarsa, akan dalilin da har gobe ita bata sani ba. Amma ta shinshini cewa koma dai menene kin auren Kehinde yanada dalili in tayi la’akari da irin kalaman dake fita bakinsa akan mata.
Koyaushe tayi masa maganar aure cewa yake “Nenne…they are nothing but gold-diggers… true love does naver exist. I am a hopeless romantic… And I want true love!”
A ganin Nenne Sappa shi aure ba a yadda Abdulrasheed yake kallonsa yake ba a zahiri. Abdulrasheed yana kallon aure ne a matsayin wani abu mai girma wanda sai da sahihiyar soyayya yake yiwuwa (sai zukata biyu sun hadu akan son juna, sai yana son mace zai aure ta, itama sai tana matukar sonsa zai yarda da ita, alhalin kuma ya kasa son kowacce din balle ya bata dama) har gashi yayi sallama da shekarun kuruciya. Bai kamata yayiwa matan duniya duka hukunci akan laifin mace daya ba.
Ita Nenne ta yarda cewa ba lallai sai da soyayya ake yin aure ba; circumstances yana kawota (along the way) ga ma’aurata. Nenne tafi yarda da cewa ana yin aure ne don dalilai masu karfi na addini dana al’ada, muhimmi shine don raya sunnahr Annabi SAW da cikar kamala da addinin mutum, da neman zurri’a saliha. A al’adance kuma sai dashi kake cika mutum, kima da martabarka ke cika a idon al’ummar da kake tare dasu. Amma ba don soyayyahr da yake ikirarin shi bashi da ita akan diya mace ba.
Nenne bata san cewa abinda ya hana shi sake soyayya tun daga incidence dinsa da Ex dinsa Haseenah ne, ya zama cewa he lacked his trust and feelings on women akan Haseenah Ambursa, al’amarin daya kwashe shekaru kusan goma sha biyu yana dawainiya da shi yana haunting dinsa, yana lalata yardarsa da bukatuwarshi akan mata bakidayansu. Shikuma ba aboki na jiki gareshi ba, tunda ya rasa Bello Birnin Kebbi, wanda zai zaunar da shi ya gaya masa gaskiyar cewa ba’a yiwa duka mata hukunci da laifin mutum daya.
**** **** ****
WAIWAYE
“
Nenne Sappa has been battling with kidney stones for some years, ba tareda ita kanta ko wani cikin ‘ya’yanta ko mijinta Dade ya sani ba. Tana dai ‘yan ciwuwwukanta a tsaitsaye wadanda basu kwantar da ita ko sau daya ba, har zuwa shekarun baya da ya fara nuna alamu har ta kwanta a asibiti a Morocco.
A shekarun baya tana yawan tafiya kasar Morocco da sunan ziyartar kaninta da iyalansa a rashin sanin kowa medical check-up take zuwa akan treatment din da ake mata don a lokacin kanana ne stones din likita na tunanin zai iya treatment dinsu ba tareda surgery ba.
Daga baya ta manta da zancen don bata fama da kowanne ciwo ga yawan sabgogin iyali dana al’umma dake kanta.
A check-up na karshe da Hajiya Sappa ta je Morocco aka tabbatar stones tana bukatar surgery don a ciresu gabadaya ta huta. Kaninta Abdulmajid baisa was aba yajaddada mata cewa da zarar ta dawo ta yi shiri ta sake dawowa ayi aikin. Amma Nenne tunda ta dawo kuma tanacikin koshi lafiyarta sai bata sake bi ta kan lalurarta ba.
Daga ita sai Dr. Abdulmajeed Ahmadu Jalloh Omar, suka rike da wannan zancen na kidney stones dinta a tsakanin junansu, wato kaninta mai binta a haihuwa wanda likitan Koda ne dake aiki a babban asibitin Koda na kasar Morocco, su biyu kadai suka san da wannan al’amarin.
A can baya da take yawan zuwa Morocco da sunan ziyarar Abdulmajid da iyalinsa a rashin sanin Dade da yaranta ana treating dinta ne, don samun lafiyarta.
Daidai lokacin data dago daga sujjadarta, jikinta ya soma dan bari da karkarwa na shigar zazzafan zazzabi, bata taba jin zazzabi irin na wannan lokacin ba tun saninta da ciwon nata. Zafin jikin Nenne ya karu, har ta kai ga ta bar abinda take yi a kitchen ta koma dakin mijinta ta kwanta a gadon su na alfarma.
Nenne ta dauki waya ta kira Abdulmajid, yana jin muryarta sanda suke gaisawa ya san jikin ya tashi sosai, yace “Adda kiyiwa Allah ki yarda ayi miki aikinnan kowa ya huta, ina amfanin zama da ciwo? Kuma kin hanai fadawa kowannensu har yau” Nenne tace “Abdul tsoron aikin nake ji, gara idan tafiya ce in tafi salin alin ba tare da an farke ni ba, ina rokon ka kara rike min sirri na, ban yarda Dade da Hammansu da Nani Oummana su ji wannan maganar ba…”. Abdulmajeed ya katseta cikin damuwa “Adda na gaji! Na gaji da wannan boye-boyen da muke yi, mara amfani, Adda boyewar nan bata da wani amfani, su dinnan duka musulmi ne Adda, musamman miji da mahaifiyarki, koba komai zasu yi miki addu’a ayi aikin nan a sa’a. shikuwa Abdul ai namiji ne shi yafi kowa dacewa ya san halin da kike ciki, ki sanar da ko Abdulrasheed da Murjanatu ne kadai su rako ki ayi aikin, in har bazaki bari Dade dinsu ya sani ba saboda hawan jininsa, su ya kamata su sani”.
Nenne tace “ko zan sanar dasu ba yanzu ba sai na shirya, akwai abinda ke gabana yanzu, zan cigaba da shan magungunana da na bar sha kwana biyu. Tunda na samu cikar burina da raina akan Hammansu (Abdulrasheed) to Alhamdulillah!”
Abdulmajeed Yace cikin damuwa da hukuncin ganganci na ‘yar uwarsa, “amma Adda idan kika mutu kina musu wannan boye-boyen ba tareda sun san jinyar da kika dade kina yi ba, suka kuma ji da hadin bakina, na rantse daga ni har ke bazasu taba yafe mana ba!”.
Nenne tace “bazan taba saka sunanka cikin maganar nan ba Abdulmajeed, amma zan duba yuwuwar na sanar da Abdulrasheed shikadai, amma dai don Allah ka kara min lokaci Abdul, har Abdulrasheed ya karbi matar dana aura masa daga hannuna”.
Abdulmajeed ya rasa me zai ce mata da zai sa ta dauki al’amarin lafiyarta da muhimmanci sama da zancen auren danta. Yace a hankali “Adda!” Nenne Sappa ta katse kanin nata cikin kulawa.
“Abdul, Ko Allah hoddiri fe’an be tagu fe’an!”.
(Abinda Allah ya riga ya rubuta zai faru ga bawa ba makawa sai ya faru)!”
***** **** *****
ROUQAYYAT-KIKI
K
iki (Ruqayyat) zuwa yanzu an zama manyan ‘yanmata, shekafun ta zasu kai sha bakwai da watanni tara. A bana ne ta kammala karatun sakandire. Can na hangota cikin shiga ta alfarma ta ‘ya’yan gayu amma kuma wadda bata nuna tsiraici a tare da itaba, irin dai shiga ta yaran musulman Yoruba, rashin saka lullubi ko a kafada aka ya nuna ita din ba cikakkiyar bahaushiya bace, cikin wani hamshakin supermarket take shawagi a (Santa Monica) din birnin Los Angeles.
Dana leka kwandon da Kiki take sayayya a ciki sai na ga cewa kanta take zabar ma ‘brazier’ da ‘panties’ da ‘undies’ da kuma ‘nighties’ ‘yan ubansu-ubansu, kasancewar a gobe ne zata koma hutu na farko gida Ilorin, tun bayan zuwanta kwas din Computing a Los- Angeles, sai wani tunani ya fado mata, kasancewar kome take yi Uncle AK baya barin ranta.
Mai zai hana tayiwa Kawunnata gudunmuwa dasu shima idan aurensa ya tashi ya baiwa matarsa? Sabida a idanunta nighties dinnan da undies din duka unique ne, da kyawunsu da tsadarsu ya kai ya kawo. Kiki na nan ‘yar lukuta haka duma-duma kamar buloras, doguwa mai garin jiki kamar na mahaifiyarta, Taiwo.
Da ‘yan yatsunta da suka sha adon bangles da zobban zinare ta latsa tsadaddiyar wayar hannunta wadda Uncle AK dinne ya mallaka mata (yadda take kiran Prince har inda yau ke motsi watau Uncle Abdulrasheed Kehinde) a ranar da yazo bikin graduation dinta na sakandire daga ‘Greensprings School’ dake jihar Lagos, alkawari ne da ya dade da yi mata cewa sai ta kammala secondary school da kyakkyawan sakamako sannan zai mallaka mata wayar hannu kuma a ranar ya samu ta cika shi. Musamman kasancewar Kiki tayi kokari sosai a jarrabawarta.
Yana kwance cikin ‘sofa’ a ranch house dinsa atsakiyar babban birnin kasar Argentina, a jiya yazo kasar daga Qatar wani babban tournament.
Dawowarsa kenan a matukar gajiye ko Polo Helmet din kansa da chukka boots din kafarsa da socks bai samu ya cire ba. Da chukka boots da safa da komai dake jikinsa ya fada akan Sofa-bed din, yana matukar son zuwan su Nenne a satinnan kafin lokacin tafiyarta aikin Hajjin bana yayi, don ya jima shi bai je ba. Idan kuwa har yayi irin wannan jimawar bai je gida ba irin haka Nenne kan tarkato kan kannensa Princess Fatima da Princess Firdausi, da ‘ya’yansa Hakeem da Kiki su zo su yi masa sati.
Daidai lokacin yana tunanin mikewa don wucewa bedroom dinsa yayi sallah, ko ya samu yayi barci sosai, ya huta gajiya don rabonsa da barci tun daren shekaranjiya wato kafin su fara tournament din da ya kawo shi, wayar ‘yar rigimarsa Kiki ta shigo masa.
Da kyar ya mika hannu ya daga idanunsa a lumshe saboda gajiya. Amsawar kawai yayi cikin dushewar murya ba tareda yace mata komai ba.
Tace “Uncle AK size nawa zan daukar mata na backward da frontward?”
Abdulrasheed ya yunkura ya mike zaune cikin yamutsa fuska yace “Kiki! Where are you now? What sheet are you talking about?”
Kiki ta rangwadar da kai gefe irin na yaran da ke jin duniya akan tafin hannunsu tace “Uncle AK, lefe zan fara hada maka, in duba wata hadaddiyar Baby haka anan ajinmu in yi mata tallanka, Uncle nagaji da ganin ka kai kadai a gida, Uncle nagaji da ganin ka a cikin Dawakai ba ‘ya’yan ka ba”.
Idanun Abdulrasheed suka dan bude kadan don mamaki, har an kawo wannan lokacin da ‘yar cikinsa ma ta damu da rayuwarsa har haka, da kyar ya iya ya hadiyi miyau, yace.
“Kiki are you alright? Ko kin fara shaye-shayen zamani ne?”
“Allah ya sani ban sha komai ba. Mamana ta hanani sauraron samari saboda kai, ina dalili? Akwai BF dina dana ke matukar so Mama ta hana ni ko magana dashi wai sai kayi aure, rannan fa cewa tayi wai bana jin kunya in shige gidan miji in barka a zaure?” Kiki ta karasa harda kirkiro ajiyar zuciyar damuwa, yadda take maganar kadai zaka san bilhaqqi take yinta cikin gabunta.
Wata ajiyar zuciyata subucewa Prince, shikansa bazai iya tuna rabonsa da yin irinta ba, in ba yana magana da Kiki ba baya tuna yawan shekarunsa. Ita kadai ke iya saka shi dariya a kowanne lokaci koda bai shirya ba.
“Idan na fahimceki daidai Kiki, kina so in yi aure ne don a baki dama kema kiyi aure?”
Kiki tasa hannu daya ta rufe ido daya tana dariya don kunya, kamar Abdulrasheed na ganinta, shikuwa kallon mamaki yakewa kan wayarsa, har yaushe ‘yar cikinsa Kikin da yake sawa ‘diaper’ ta girma haka?
“Alright Kiki, nina tsufa da aure, zan wa Taiwo magana kada ta kara fadin haka gareki. Ta baiwa mai kaunarki dama ya iso gida. Kiki har kayan dakinki na gama hadawa suna nan kulle a gidana na Qatar.
Kuma ni zaki fara kawowa boyfriend dinki din kafin kowa. Sai nayi na’am dashi zaki kaishi ga Daddynki. Yaya sunanshi?”
Don farin ciki Kiki kamar bakinta ya yage don murmushi tace “You know I love ko Uncle AK? Nayi alkawarin bazan taba sauraron saurayi ba sai kayi aure? Sunansa “Abdul-Nasir Oluwatosin”.
A kwance Prince yake amma bai san yaushe ya tashi zaune ba. ya rike wayar hannunsa sosai yace “Tosin Abdulnasir, a footballer?”
Kiki ta gyada kai tana jin kunya, kamar Uncle AK yana kallon idonta. Shi kuma yace “Kiki iyayenmu bazasu taba bari ki auri footballer ba, sai dan sarauta, ni nasan iyayenmu sarai, ki cire ni a gefe kan batun aure. Maybe your Uncle is not destined to marry in his life. Amma akwai mata fal a aljannah ai kin sani ko Kiki? They are called hurul’eeni, who knows ko mata na hudu suna cikinsu?
Don haka ki daina damun kanki a kaina kinji. If you really-truly love this Guy, I will stand by you Kiki. AbdulNasir was a football celebrity. Me ya hada ki da dan ball? A ina kika hadu dashi?”
Kiki ta labarta masa haduwarta Tosin AbdulNasir sun je kallon wasan da Inter-Miami tayi da LA Galaxy a California itada kawarta Badriyya.
“Amma Kiki ban hanaki bin kawaye yawo ba? Ban ce daga makaranta sai makaranta ba? wato har kallon ball kike zuwa?”
“Kayi hakuri Uncle AK, wallahi ba inda nake zuwa banda shopping, ranar ma Badriyyah ta matsa muje ne don taga AbdulNasir a fili, tana matukar son wasansa, na gaya mata ka hanani zuwa ko’ina, tace daga ranar bazasu kara zuwa yin wasa Los-Angeles ba, and she don’t want to miss seeing her favourite footballer in reality (bataso ta rasa ganin dan ball din data fi so a fili), sai na yarda muka je, tun a ranar ya nuna kaunarshi gareni muke waya, ban taba gayawa kowa ba sai Mama, shine ta bani waccan amsar cewa bazan taba sauraron kowa ba sai kayi aure”.
Abdulrasheed yayi ajiyar zuciya ya ce “Kiki count me out kinji? Bani lambar yaron kuma ki bar ni da Taiwo”.
Kiki ta dage itafa bata so itama, in Abdulrasheed