Showing 36001 words to 39000 words out of 42757 words
Chapter 13 - AISHA-SIDDIQAH-Book 2 Complete original by Takori Kabara.txt
Zai kuwa ga iya shege albarka Annabijo (da albarkar Annabi).
Sai kawai ta bi shi da adduar data saba yi masa wato.
“Allah hokku sa’a Hammansu ko a yahi dabuttugo albarka Annabijo”.
Kuma ko a fuskarta babu bacin rai. Watakila Prince harda auren aljana a tare da shi ta ke gayawa kanta.
Namijin da zai ga mace tamkar Aisha-Siddiqah a matsayin halalinsa amma zuciyarsa bata ko motsa ba, manhood bai motsa masa ba.
Sannan bai yi wani action ko kankani da zai nuna cewa ya san da wanzuwarta ba, alhalin ko jiya tana jin yadda Dade ya zaunar da shi kusan awanni uku yana labarta masa yadda aurensa da Siddiqah ya wakana, tun daga haduwar Nenne da Hajiya Zainab a filin Munna ya dauko masa labarin har kawo zuwa yau.
Har Dade yayi yagama tana jin su daga kwancen da take uffan wannan Prince Abdulrasheed Kehinde bai ce ba.
Dade da saurin hassala a lokacin taji yace da shi “ka samu lalurar ji ne ko Kehinde?”
Dan murmushi ya yi cikin kasaitarsa yace “Dade, kunnena ras suke. Banida abin cewa ne, banda Allah yasa hakan shi yafi alkhairi a gareni daku da yarinyar bakidaya”.
Wannan ne yasa Nenne bata kara yi masa zancen Aisha ba ita, koba komai he is now aware of it. His I don’t care attitude ne ya bata mata rai ta fasa ce masa ya tafi tare da Aisha. Aisha tafi karfin ta cusa ta wajen namiji, ta barwa Allah wannan ikon nasa. Su dai sun sauke nauyin dake kansu da addini da al’ada suka dora musu sauran ya rage nasa.
Yarinya dai data dauko daga gaban uwarta da ubanta zata kula da ita kamar koma fiyeda tana gabansu.
Don haka bayan barin sa wurin Nenne ta cigaba da yiwa Aunty Taiwo ciwon bakin tayi rabon tsaraba ta manta da ‘yar uwarta.
Murjanatu-Taiwo, nan ta hau babbaka dariyar shakiyanci nan ta maida Nenne Kakarta, tana cewa “Nenne mai ‘yar fingi-fingi, kamar kazar mayu, ina ganin sai kin hada da addu’a fa, naga Kehinde yarinyar nan bata masa ba”. Ta kara babbako dariya tace.
“Allah na tuba Nenne, wadanne irin matane Kehinde bai gani a kasashen duniya? Wadanne irin mata ne basa bibiyarsa kamar su bashi ransu har gida da ofis, Kehinde da in mata dari yakeso a rana zai aura, sai kece mai idon gano masa macen aure Nennenmu?
Nenne a shawarce ki maida yarinyar nan ga iyayenta, ki basu hakuri kawai. An daina irin wannan auren yanzu”.
Nenne tace da kakkausan lafazi, “Murjanatu! Shin ke kika haifa min yaron nan ko ni na haife shi?
To in har ba ke kika haife shi ba, baki kuma shayar dashi ba, sannan baki tayani jegonsa da rainon cikinsa ba daga yau na cire ki daga sha’anin auren sa.
Shiyasa dama tun farko ni ban saka ki ba don nasan dama tunaninki akan Abdulrasheed ragagge ne sai abinda yakeso kike bi, ba abinda zaifi masa alkhairi ba. Shiyasa tun farko kika biye masa akan waccan yarinyar.
Na yarda har yanzu da sauranki Murjanatu a sanin baiwar da Allah yayiwa 'ya'ya mata, yawan shekaru da zurfin ilmi ko cikar jiki basu ne ba. Haka naki shekarun basu yi miki amfani ba, tunda har kike tunani akwai namijin da yafi karfin wata bafullatar mace don kawai bata da wayewa irin ta kabilunku.
Murjanatu ta rage dariya ganin Nenne ta hassala sosai, gashi bata da lafiya, tace “Nenne ni dai ba ruwana fa kiyi hakuri, I rest my case akan maganar nan, shawara ce dama na bayar sabida saninda na yiwa Kehinde, amma kiyi hakuri ga ku ga Kehinde”.
Nenne tace "ki yi fatan alkhairi ko ki fita daga sabgar da ba'a saka ki ba tun farko".
Ai kuwa a washegari tunda asubah Prince ya tashi zuwa Qatar ko Dade sai a masallaci sukayi sallama da shi.
Dade yaso yace dashi Siddiqah fa? Yaga cewa wannan ba wurin da ya dace suyi maganarta bane, amma ya sha mamaki da cikin daren Nenne tace masa gobe AbdulRasheed zai koma har yayi mata Sallama, ta rokeshi kada ya takura masa kan tafiya da Aisha wato yace sai sun koma tare, ya zuba masa Ido, ita bazata cusa masa ita ba don saya mata martaba a wurinsa don ta lura kawai shida Taiwo basuyi na'am da zabinsu ba. Dama kullum bakinsu daya.
Kasancewar bata da koshin lafiya sai bai cikata da magana ba kawai ya gyada kai. Sukayi sallama da Dan nasa yadda suka saba yasa masa albarka ya kuma yi masa addu’ar da ya saba yi masa. Seun, ya wuce dashi zuwa filin jirgi.
Kwanansa daya da tafiya itama Murjanatu ta koma gidanta a Ilorin.
Gidan ya koma yadda yake wato su ya su. Sai lokacin da Firdausi ta tabbatar mata Hamma ya koma, Auntynsu Murja ma ta wuce gidan mijinta, sannan Siddiqah ta soma fitowa falo cikin su yadda ta saba ta sake.
Nenne ta yankewa kanta shawarar bazata sawa ranta damuwar komai ba, cututtukan nan na zamani na zuciya da hawan jini ba karya bane. Ta samu ta sha da kyar daga cyst and renal stones. Bari ta maida hakali kan abinda zai fishsheta da ibadarta ta gama da damuwar Abdulrasheed kuma.
Ya rage nasa ya gama da yazo ya dauki matarsa a sanda ya shirya ko ya cigaba da rayuwarsa a jirkice yadda yake yinta.
Ita dai ta san ba zata kwari yarinya ba idan ya shekara bai dauketa ba, zata mayarwa iyayenta dake ganin mutuncinta ta ce musu ta gane bashi da lafiyar iya yin aure, wanda mutuncin ne yasa aka bashi ba wani abu nasa ba. Bazata yi sanadin da zumuncin ta da Haj. Zainab wanda sun ginashi ne saboda Allah zai lalace akan ‘ya’ya ba.
Allah ya gani wahalar da ta sha a baya akan damuwar rashin auren Abdulrasheed, bazata kara maimaitata a yanzu ba. Ta cimma shekaru na girma da take bukatar tattalin lafiyarta.
Kehinde ba shikadai ta haifa ba. Amma shikadai matsalarsa ke wahalar da ita, bazata taba lafiyarta dake reto saboda shi ba, alhalin shi yana can cikin jin dadin rayuwarsa. Tunda ta wanke masa ‘labelling’ na rashin aure (tambari) wanda addini da al'ada ya dora musu sauran hukuncin na rayuwa da matar ko a'ah nasa ne ba nata ba.
Nenne ta sha mamaki da Aisha Siddiqah ta koma rayuwar walwalarta cikin gidan bayan barin Taiwo da Kehinde gidan. Wato itama ta gane Taiwo bata yin ta kenan. Allah sarki! Yo aka ce shimfidar fuska tafi ta tabarma, sannan ido ba mudu ba amma ya san mai maraba dashi, kai tsaye Aunty Murjanatu bata boyewa kowa ba matar Kehinde bata yi mata ba, including iyayennasu da suka hada auren bata yi musu alkunya ko Karar ganin ido ba wajen nuna musu basu yi zabin da ya dace ba.
A wurin Siddiqah gidan har wani fili ya kara da iska mai dadi da Hamman su Firdausi ya bar shi. Wanda iya hangenta na kushe dan adam ko kabilan da ba nata ba data saba kushewa ta kasa hango ta ina zata iya kushe Prince Abdulrasheed (Kehinde) Idris Akanni.
He's perfect, duk da ana cewa duk mutum tara yake bai cika goma ba.
Gani uku ko hudu ta yi masa cikin gidan kuma ba wai ta masa kallon kurilla bane ko a asibitin. Amma tashin farko ta gane shi din ko cikin mazan Yoruba kyakkyawa ne na gaske ashe. Classique. Jinin fulanin Gombe ya wanke shi tas! Akwai abinda ya burgeta guda daya a tare dashi wanda shi kadai ta rike a kamanninsa, “Tabon Sallah_shaidar Sujjadah” wanda ke shimfide can farkon saman goshinsa.
He didn’t give her a second look either… Iya abinda ta hango a tare dashi kenan, bata hango maraba ko rashin maraba da ita a tare Abdulrasheed ba. Kai ko kai ne Sigmund Freud ko Wilhelm Wundt wurin karantar dan adam bazaka karanci komai akan Siddiqah a tare da shi ba.
Nenne na kara jin karfin jikinta, ta koma harkokinta na cikin gida, aka maida Aisha makarantar su Kiki ta jeka ka dawo.
***** **** ****
Malamar da aka daukowa Siddiqa ma Bayerabiya ce mai suna Mrs Yemisi.
Ana saura kwana biyu ta fara zuwa makaranta wato asabar malamar ta fara zuwa suka soma karatun bita. Muhimmin abinda zata koya mata shine Lissafi da Ingilishi.
Siddiqah ta fara karatu daga takardar transfer da Babanta ya karbo mata daga FGC Billiri, ya aikowa Dade, ta fara ne daga (first term) na aji shidda inda daga shi sai zango na biyu sai zana jarrabawa
Ranar data fara zuwa a darare take, ba abinda take tsammani a makarantar sai yaran yarabawa zasu yi mata “Atule bahaushiya!” Irin wanda take yiwa Bisola. Tunda ta gama saddaqarwa alhaki kwikwiyo na Bisola keta walagigi da ita a cikin Yarbawa.
Amma akasi ga tunaninta daliban kowacce harkar gabanta take yi babu wadda ta lura da ita balle su kula cewa ita din bahaushiya ce, har saida form master din ajin ya gabatar da ita ga sauran dalibai a matsayin sabuwar daliba daga Gombe suka ji sunanta na hausawa ne.
Tun yinin rana ta farko a makaranta Siddiqah ta san cewa makaranta tazo, wadda ta amsa sunan makaranta, ta ko’ina ta zarta Billiri zafin karatu, ba hadi ko kusa. Turancin makarantar har yaso yafi karfinta.
Don haka Siddiqah ta dan ture kabilancin nata a gefe ta soma karatu tareda ‘yammata Yarabawa da sauran kabilu, amma yorubawa sun fi yawa. Har bada jimawa ba ta soma tsinttar wasu kalmomi na yarbanci irin su “Zo” (Wa) “Jeka” “bari” “good morning” (Ekaaro) da sauransu.
Ta ga cewa ma akwai hausawa tsilli-tsilli a ajinnasu, wadanda galiban aiki ya kawo iyayensu jihar Lagos, don taji ana kiran jakadiyar ajin (class monitress) din da suna Maijidda Sulaiman Yabo.
Cikin sati daya Aisha Siddiqah ta saki jikin ta a makaranta. Mrs Yemisi kuma na kokari da ita a gida, don ganin cewa ta haye Ingilishi daa Lissafi a yayin zana jarrabawarta ta kammala sakandire.
**** ***** ****
KIKI
A karshen wannan watan da ake ciki ne Kiki ta kusa kammala course din da take yi a LA tazo Lagos hutu don gaida Kakanninta.
Da shigowarta babban falon gidan ba wanda idonta yayi tozali da shi sai Aisha-Siddiqah, a lokacin tana zanawa Firdausi lalle a kafafunta.
Sha’awar abun ya kama Kiki ba kadan ba, don Kiki akwai son abubuwan hausawa amma bata da kawaye hausawa, Aisha sai kallon Kiki take tana admiring komai na Kiki a ranta; ga tsayi, ga kiba kamar Aunty Murja, don ita Siddiqah duk wani mutum mai cikakken jiki sha’awa yake bata, ta kasa gane cewa jikin ta ma abinso ne musamman ga wadanda ke neman weight loss. A shirye suke dasu biya makudan kudade in zasu samu irin jikin ta.
A ganinta Kiki komai ta hada, ga iya ado sannan ga kibar, ga hutu yabi jikinta, ya hadu da iyayi da rawar kan wayewar 'yammatan zamani masu yawo a duniya, duk wannan ya nuna a tare da Kiki.
Ita kadai amma duk ta ishi gidan da karadi.
“Nenne bakuwa kukayi ne, halan daga Gombe? So Pretty and Georgeous!”
Nenne ta sha mamaki da Taiwo bata gayawa Kiki maganar Siddiqah ba, sannan shima duk yadda yake da Kikin ace bai mata zancen ba. wannan kadai zai nuna maka (how uncared they are) da zancen Aisha daga Taiwo din har Kehinde dinnata.
“Umh!” in ji Nenne cikin takaicin Murjanatu, tafi takaicinta fiye da Kehinde saboda da ace ta karbi Aisha 100% da kyakkyawar fahimta akan zabin da ita Nenne tayi da komai zai zo da sauki, don ita kadai ce zata iya convincing din shi ya kalli Aisha da idanun rahma, har ya fahimci alkhairin dake tare da ita don da farko shi da bakinsa ya yabe ta kafin yaji maganar aure a tsakaninsu, Taiwo da taga dama zata iya taimakawa kwarai Kehinde ya bude zuciyarsa ya samar ma Aisha gurbi ko yaya, ya manta da komai da ya jima da sakawa ransa a kan mata.
Amma har gobe tana kan bakanta na bazata cusa Aisha ga Prince ba, ta ma fara tunanin da Aisha ta gama karatun data sa aka katse mata a garinsu ta karbi sakamakonta na WAEC sai ta maida ita Gombe hannun iyayenta cikin salama.
Ta san Aisha akan dole take zaune tare dasu don ba yadda zata yi ne amma zuciyarta tun fil azal bata son mu’amala da yarbawa balle alaqa mai girma ta aure.
Fin karfinta iyayenta suka yi, sai kuma kirki da karamcinsu iyayen Abdulrasheed din a gareta ya taimaka wajen kwantar mata da hankali ta zauna. Amma Prince da al’amarinshi basa gabanta. Har Nenne ta soma ganin laifin kanta ta dinga tunanin anya bata dauki alhakin Aisha ba, data hada wannan auren? Ita dai tasan manufarta kyakkyawa ce akai, ta kwadaitu da hada tsatso da kyakkyawan iri ne, mai addini mai albarka, sauran kuma Allah shine shaida amma bata da wata manufa cikin hada auren Siddiqah da Prince. Bata san ya zata yi ta fahimtar da Taiwo da Kehide hakan ba. Idan Taiwo bata yi na’am ba, mawuyaci ne ya zama Kehinde zai taba yin na’am, because they share each others’ feelings.
A tunanin Nenne Taiwo da Kehinde sun hada baki ne akan su yi wa Aisha kora da hali, wanda aka ce yafi kora da sanda, akan wannnan gallafirar Haseenah din rainon Taiwo.
Ita kuma zata kyale su suyi abinda suka ga dama. A rayuwarta bata matsawa kowa yayi abinda ba ra’ayinsa ba, ta dauka farat daya Murjanatu in taga Aisha zata karbeta da hannu bibbiyu da zuciya daya, ta zamar mata uwar daki a cikin su, shikenan ta Kehinde zai zamo mai sauki, amma har gara shi din, bai kushe ba amma bai ce komai ba.
Ita kuwa Taiwo muraran ta kushe Aisha har tace a mayar da ita ga iyayenta kai tsaye. ‘Ya’yan yanzu ne ba’a tuka su, musamman a shekaru irin nasu shida Murjanatun, babu karamin yaro a cikin su da zata tankwara ta karfi akan dole yayi abunda take so, musamman Abdulrasheed yadda yake gudun bacin ranta da gudun zuciyarta yake iya kokarinsa wajen kyautata mata da ‘yan uwansa, itama bazata yi abinda zai takura shi ba, duk da cewa in ta takura din zai bi, tunda ta lura da gaske bashi da lafiyar yin aure duk da ya musanta hakan ita yanzu ta yarda da hakan, ta kuma barwa Allah ikonsa, tana addu’ar Allah ya bata ladan kyakkyawar niyyarta na dabbaqa Sunnah a tsakanin Siddiqah da Prince, ya bata karfin zuciyar fuskantar iyayen Siddiqah ranar ta mayar da ita su yarda da hujjarta na Prince baida lafiyar auratayya koda bai fadi ba.
Amma namijin duk da za’a baiwa lafiyayyar mace kamar Siddiqah a gaya masa matarsa ce ta Sunnah ba tareda ya kashe ko kwabonsa ba, zuciyarsa ta kasa motsuwa to ba namiji bane mai lafiyar mazantaka. Don in babu SO to akwai SHA’AWA a tareda kowanne Da namiji.
Ita bata kin Haseenah din da Taiwo take so dashi, kawai tsatsonta ne tace bata yarda ya gauraya a cikin tsabtataccen jininta ba, ba kuma don komai ba sai don babu tabbacin halaccin haihuwarta.
Amma tunda daga Taiwo har Kehinde su suna ganin abinda a wurinsu ita bata gani kalas! Yaje ya auri Haseenan dama duk matan gidan marayun Ambursa masu wayewar kai da iya rangwada in har yanada lafiya, don yanzu ita uwarsa ma tana tababa akan ingancin lafiyarsa.
Sai suyi mai fishshesu ta maida Siddiqah ga iyayenta ko ba takardar saki, don bazata iya cewa ayi abinda Allah ya halatta amma baya so ba (saki). Dama Siddiqah din ba kwantai tayi ba kuma ba wani girma tayi da iyayenta suka gaji dashi ba. Mutunci ne da sanin yakamata da alkhairi yasa aka bashi ita.
To amma ina mafita? Aisha zata dauwama ne da auren Kehinde da bashi da gurbin ajiyeta cikin rayuwarsa ko lafiyar da zai iya ijjema bukatar aurenta. A rayuwarta kuma bata ko son jin kalmar “saki” balle gittawarsa a aure, watakila ko don babu ita a kamus din gidan sarauta gabadaya daga nasu gidan sarautar har na mijinta.
Sai taji ta kasa ce da Kiki Aisha matar Uncle