Showing 42001 words to 42757 words out of 42757 words
Chapter 15 - AISHA-SIDDIQAH-Book 2 Complete original by Takori Kabara.txt
yace “tayi hakuri Dade zai dauka. Suna isa ta hango dade a nesa yana jiransu, sai ya karaso jikin motar tana kokarin fitowa cikin girmamawa don ta gayar dashi, yace ta biyoshi zuwa ciki.
Tare suka shiga ciki yasa aka mata hoto da finger-print. Seun ya dauko su zuwa gida gabadaya. A kan hanya Dade na tambayarta yaya jarrabawar tana gaya masa ita bata da matsala har suka iso gida.
**** **** ****
BAYAN SATI HUDU
MURFIN LITTAFI NA BIYU
“Dade har ka kwanta ne?”
Nenne dake karasowa gabansa ta tambaya, ganin shi a kwance, ido a lumshe kamar baya jin dadi, sai ta zauna gefensa ta dora hannu akan goshinsa, zafi rau.
Dade ya bude ido da suka kada yayi mata murmushi, kafin yace “masassara ke son rufe ni tun dazu” “sannu Dade, to tashi ka sha magani”. Ya yunkura ya mike zaune akan gadon ita kuma jiki na rawa ta doshi (first aid box) dinsu don dauko maganin.
Dattijan biyu na matukar kula da junansu, kullum kamar sabon aure haka suke mu’amalarsu, ta ballo maganin kan hannayenta ta bashi ya kora da ruwa sai ya koma ya sake kishingida. Nenne ta yi amfani da wannan damar ta zauna a jikinshi ta soma magana.
“Dade nace dama gobe ne Aisha zata zana final paper, ina so jibi in maida ita Gombe in Allah ya kaimu”.
A kishingide Dade yake, amma bai san lokacin da ya taso zaune ba, yace “zata je ganin gida ne? Har yaushe aka yi auren Hajiya Sappa? Ko dai Nani Ummana zaku je ganowa?” Girgiza kai Nenne tayi, tace “Dade, in ta tafi ta tafi kenan, Allah ya gani na yi nadamar hada wannan auren, na bata muhimmin lokacina a kansa, don zuwa yanzu na yarda da gaske Abdulrasheed baya bukatar mace a rayuwarsa.
Na yi nadamar rabo yarinya da iyayenta. Da na san in ya ganta bazai karbeta ba da koda wasa ban fara ba”.
“Dama ana nadamar aikata alkhairi ne ga haularka Hajiya Sappa?”
Dade ya tambaya idonsa a kanta. Ba tareda ya jira amsarta ba ya cigaba.
“Kada ki karaya, kada ki sare tun yanzu kada ki maida alkhairinki baya. Wanda zashi sama ya taka tsauni ai yayi kokarin azo a yaba.
You truly made it my dear. Tunda har kin aura masa ya san da zancenta ya kuma ganta ganin idanunsa, ya kuma san tana zamansa. To kin gama naki, ki barni inyi nawa nikuma.
Da wannan Dade ya lallashi Nenne kan kada ta mayar da Aisha gida, ya soma yi mata bayanin abinda ya dade yana shiryawa wanda shima Emir ne ya bashi idea din hakan.
“Yana hutun karshen shekara (Annual Leave) a gidan sa na kasar Argentina currently”.
Mu karasa a littafi na uku.
Tare suke.
Taku har abada SUMAYYAH ABDULKADIR (TAKORIN TAKORITES).
10/04/2024
(MASOYA LITTAFAN TAKORI INA FARIN CIKIN TALLATA MUKU JAKADIYAR KAYAN KAMSHI NA ORIGLAME HAJIYA AISHA LAME (ORIGINAL ORIFLAME AMBASSADOR)
Kina neman jakadiyar oriflame ta kwarai? Kinason mayuka da zasu dace da launin fatarki a wannan lokacin na zafi kona sanyi? Kinason kamshi na alfarma? Kinason supplements ingantattu na wellness and meal replacement ga masu bukatar weight loss and weight control? Kayan kwalliya na kerewa sa’a? Kina bukatar zama Dawisu sarkin ado? Kawai tuntubi AISHA LAME a lambar waya 07036662633 zaki samu duka wadannan cikin farashi mai inganci da kyakkyawar mu’amala. Aisha lame karshe ce wajen baiwa faat hakkinta ku tuntubi Aisha ku zo ku bani labari.
-Takori Sumayyah Abdulkadir
April, 2024