Showing 30001 words to 33000 words out of 42757 words
Chapter 11 - AISHA-SIDDIQAH-Book 2 Complete original by Takori Kabara.txt
jikinta har daukar ido yake.
Madallah da kulawar uwar miji irin Nenne Sappa, madallah da kyawun abincin yarbawa mai inganci da gina jiki (freshy Yoruba food), ga kamun gero da cukwi din Nenne, tabbas yana aiki ba kakkautawa a jikin Aisha-Siddiqah.
**** **** ****
CIKA ALKAWARI
Yau dai Nenne ta cika alkawarin data daukarwa mahaifin Siddiqah, domin kuwa ta shigo dakinnta ta sameta ne tana gyaran kumba, sai ta mika mata littafai da uniform harda takalmi da jakar makaranta, ta gaya mata gobe in Allah ya kaimu zata fara zuwa makarantar da Kiki tayi.
Har ila yau, ta sanar da Siddiqah cewa ta shirya an daukar mata malama da zata dinga yi mata lesson Asabar da Lahadi akan jarrabawar WAEC din dake gabanta.
Hakan yasa Siddiqah ta kwana cikin zullumin wayewar garin, maimakon farin ciki, wanda shi ya kamata ace tayi, don samun damar karasa karatunta data yi cikin sauki kamar yadda Nenne ta dauki alkawari tuntuni ga iyayenta, ba kuma don komai ta shiga zullumin ba sai wani tunani daya tsirga mata babu gaira babu dalili.
Wai gata dai yanzu ta tsinci kanta dumu-dumu a garin Yarbawa ta dalilin auren da bata shiryawa ba, duk wannan bai isa ba, yanzu gashi gobe zata fara cudanya da dalibai suma yarbawa, ta tabbata duka daliban makarantar Yarbawa ne tunda su suka fi yawa a garin Lagos, kuma cikinsu za’a kaita tsundum a barota suyi tayi mata yaren da bata son ji dinnan, in a gida ana ragewa sabida ita. Shin ko yaushe hakkin Bisola Akanbi zai barta ta huta? Ta tabbata shiyake ta bibiyarta har yau.
Kabilanci yaki sakin ranta ta sarara, kullum tana tunanin ko ta koma Gombe. Gabadaya rayuwarta ta dawo cikin yarbawan data raina matukar rainawa, takewa shagube da mockery yadda ranta yake so, Allah kenan. Yau dai gata tsundum a cikinsu da sunan zama na dindindin har inda bata taba mafarkin shigowa koda ziyara ba (masarautar yarbawa).
Babu ko shakka alhakin Bisola ne ya tsundumota cikin kabilar yarbawa, ya hanata samun rayuwar fulani yadda ta yi mafarkin samu, ta kuma yi burin samu tareda wanda takeso, saurayin bafillace dan uwanta, wanda ya san ciwonta da darajarta, suke harshe da yare guda (Ishaq Nafada).
Sai Allah ya jefo ta duniyar yarbawa data ke yiwa wani kallo-kallo da shagube. Yanzu idan taje makarantar itama daliban suka yi mata irin abinda take yiwa Bisola fa a matsayinta na bahaushiya ita kadai?
Duk sai taji zancen karasa makaranta ya fice mata aka, gara ta cigaba da zamanta a gidan tunda su suna raga mata, Fatima ce kadai bata raga mata in taga ba iyayensu a wuri ma da gayya ma take suburbuda yarbanci, da zata iya da tace da Nenne bata so kawai a kyaleta. Ta hakura da zana WAEC din don dam aba wani jami’a take son zuwa ba. Dan ilmin data samu na karatu da rubutun hausa ya isheta ya wadaceta Allah ya amfana. Don ko turanci ba wani iyawa tayi can acan ba, tana dai ji in an yi mai sauki amma ko na su Fatima ba duka take ganewa ba.
Da wannan damuwar Aisha-Siddiqa ta kwana yau, wadda ta saka mata kewar FGC Billiri, ta hadu da kewar Umma data gang members dinta su Amintako, Ramatu da sauransu.
Ga Ishaq dinta masoyi na hakika data kwallafawa burin rayuwa tare dashi ya mata nisa yanzu, ta tambayi kanta ko zuwa yanzu Ishaq ya gama NYSC? Rabon ta dashi har ta manta.
Kowa nada wayar hannu a gidan nan banda ita, don Nenne tace makaranta zata fara, nan kuwa bata so Siddiqah ta dinga yiwa Ummanta kuka a waya ne, don kusan kullum ta hada su waya a gabanta sai Siddiqah tayi kuka da ta ji muryar Umma, saidai ta kai yanzu Nenne ta dade bata hadasu gaisawa da Haj. Zainab ba.
Yau kam da yake cikin tension da takurar zuciya take, saita nutsu, tana sauraron zuciyarta, shiga tunane-tunanen abubuwan da suka dace suka kuma shafeta, ciki har da tunanin wai shin ma wanene shi wannan Hammansu Firdausi din da ake kira Hamma Prince???
Ko meye matching dinta dashi da har yasa iyayensa suka ga kamatar su katse mata rayuwa a kansa, ta hanyar hadasu wannan makalallen aure haka bagatatan bata shirya ba, kawai daga haduwar Umma da Nenne a hanyar Munna, alhalin sun san ba sonta yake yi ba shanyata zai yi a garin yarbawa?
Ai ko ba'a fada ba zuwa yanzu ta gane kamar ma baisan da auren ba, don kusan duk wayarshi da Nenne dasu Firdausi ta kan ji jefi-jefi, bata taba jin wani cikinsu yayi masa zancenta koda da subutar baki ne ba.
Kamar ma boye masa suke, me hakan ke nufi? Anya Umma ta san zaman kashe wando da take yi a Lagos ba a gidan Prince din takde ba?
Haka kawai an raba ta da mai sonta bayan shi ba son ta yake ba baima da lokacin zuwa kasar Nigeria, me yasa iyayenta zasu takurata a yi aurennan don kawai su farantawa Nenne dake cikin damuwa akan danta. Ita ba'a damu da nata feeling din akan kabilar yarbawa ba. da gaske take tanada kabilanci da ethnocentrism ba da gangan gtake yi ba. amma aka tashi aka aura mata Bayerabe da bata ko taba gai ba shima kuma baya sonta.
Ta tabbata da yana son ta, da tuni ya zo, ko bai zo ba, da wani cikinsu ya gaya masa batun auren su da zaman jiransa data ke yi. Gashi har ana neman fita watanni uku. Shi wanda aka ce zaman shi take yi a gidannan bai zo ba, bazai wuce shima bakin bayerabe bane kamar kowanne bayeraben mutum data sani, kuma irin katoto dinnan ya tsa tsagu ba kamar Ishaq ba. Kodayake taga cewa Dade baida tsagu, kuma indai irin kalar su Fatima ne kuma Nenne ce ta haife shi da gaske to ba lallai yayi muni ba.
Ai kawai data rasa takamaimai tunanin daya dace tayi, ta kuma ga cewa tunaninta ya fara fita daga saiti, sannan ta kuma ji ta na dokin ganin Prince Abdulrasheed (just to quench her curiousity about him) sai ta karkace ta cusa kai a kasan pillow ta tsinke da kuka ita kadai, irin kukannan na banida tsumi bani da dabara. Ba tareda ta san mawuyacin halin da al’ummar gidan suka kwana a ciki ba.
Ashe ita kukan samun wuri takeyi.
Kwana sukayi Nenne na suma tana farfadowa cikin murmukususu na azabar ciwon ciki. Don haka cikin daren akayi asibiti da ita. Sai da asubahi taji ana buga mata kofa, dama barcin nata ba wani nisa yayi ba, ba kuma dadinsa take ji bat un bayan daya sureta, tana dai kwance ne kawai, nan da nan ta bude ido tana mutstsika shi sai taji ya kumbure suntum. Ta mike ta bude, sai taga Femi tsaye cikin damuwa.
“Aisha ki sauko falo Dade na kiranki”.
Gabanta saida ya tsinke ya fadi, amma bata tambayi Femi komai ba ta dauko hijab ta dora akan kayan barcin ta cikin kidimewa tabi bayanta zuwa downstairs.
A falon kasa ta tadda Dade a tsaye yana jiranta, Fatima da Firdausi basa gidan suna Ilorin bikin cousin sister dinsu ‘yar wajen Malami Uban Doma. Da girmamawa ta hau kokarin gaisar da shi, amma ko daga fuskarsa ta ga damuwa, Dade yace mata cikin Hausa
“Aisha biyoni, Nennenku ce babu lafiya tun cikin dare muna asibiti, and she’s calling you”.
Iyakar firgita da rudewa Siddiqa ta shigesu. Ta bi bayan Dade zuwa mota a sukwane, Seun direba ya ja suka tafi asibitin da Nenne ke zuwa wato Lagoon.
Suna tafe a hanya Siddiqah na jan hasbunallahu wani’imal wakeel saboda ko daga damuwar da Dade ya nuna a fuskarsa ka san jikin na Nnnne ya matsa, ta na jin sa yana waya da Hammansu Firdausi, akan hanyarsu ta isa Lagoon Hospital. Dade na magana kamar cikin hassala yana cewa.
“Kehinde na rantse maka zaka hadu da fushi na, na ga alama baka san zuru ba, na rantse in ban ganka gobe ko jibi ba zaka sha mamaki na, aiki da hawa doki yafi ahalinka ko? Yau watan ka nawa rabon ka da gida saboda Baffanninka? To in kaga dama yanzu ai ka zo, in kana da rabon ganawa da mahaifiyarka dake kwance rai kwakwai, mutu kwakwai tun jiya.
Gata nan kwance rai a hannun Allah amma da yake har kullum kana ranta bata fasa kiran sunanka ba.
Ka tabbatar ka bar duk abinda kake yi ka nemi jirgi mafi kusa ka taho Lagos”.
Ya danyi shiru, da alama rokonsa Prince yake ta daya bangaren, kan ya fadi masa ko me ya faru da mahaifiyarsu Nenne?
Dade sai da ya nisa kafin yace.
“Wai ashe Hajiya Sappa ta jima da 'renal stones' har 'cyst' ya fito a ‘kidney’ dinta, tana treating ni ban taba sani ba saboda zurfin ciki irinnata?”
Da haka Dade ya kashe wayarsa, ba tareda ya jira amsar Hamma Abdulrasheed Prince ba, ya koma ya jingina da allon kujerar motar, ya lumshe ido yana maida numfashi a hankali yana kiran sunan Allah As-Sattaru, yana rokonsa ya tashi kafadar matarsa abar son sa uwar ‘ya’yansa Nenne Sappa.
Itama Siddiqah ta tsorata sosai da jin halin da Nenne ke ciki. Tuni ta fara mata addu’ar duk da tazo bakinta.
Sanda suka isa asibitin Nenne ta sha allurai ta samu barci mai nauyi amma bata san wanda ke kanta ba, motsin da bakinta ke yi ya nuna salati take yi da hailala wanda daman baya rabo da bakinta koyaushe.
Gari na kara wayewa likitoci sun gama shirinsu na shigar da Nenne tiyata. Dade yayi shahada kan ba yadda zai yi yasa hannu, aka wuce da ita dakin tiyata.
Shi da Siddiqah suka koma suka zauna a dakin da aka bata, kowannensu yayi tagumi da hannu bibbiyu yana kissima irin girman rashin da zaiyi, it will be (irreplaceable loss) rashin Nenne a tare dasu.
Idan Nenne bata fito da rai ba, dukkansu rayuwarsu ta durkushe suna addu’a suna kuma hawaye, Siddiqah har da kuka wiwi amma Dade ko umh bai iya yace mat aba balle ya lallasheta shima fama yake da kansa, da zai iya shima fashewa da nasa kukan zaiyi yadda ta yi ba kananan hawaye ba amma dai ya jure yanata hailala da carbinsa yana tsane ruwan ido.
**** **** ****
Koda Dade ya kashe masa waya. The Prince was shocked, hankali a tashe ya zubar da komai da yake yi a lokacin, yanada tournament din da zai halarta swannan satin a Argentina amma ya kansile shi nan take, haka yayi ta kansile duka scheules dinsa na sati yana bada excuse, ya soma neman jirgin da zai kawo shi Lagos ido rufe.
**** **** ****
Sosai Siddiqah kewa Nenne addu’a kafin fitowarta dakin tiyata da carbin da da Dade ya ciro a aljihunsa ya mika mata, yace tayi masa shiru haka, kafin isowar Femi da kayan karin kumallon su.
Amma ko kallon kwandon abincin babu wanda ya iya yi a cikinsu, kuma Dade ya ki kiran kowa nashi daga Ilorin ko nata daga Gombe don ya sanar da su, don yasan da ya fada za azo a cika asibitin. Ya dai kira Fatima da Firdausi yace su bar bikin su dawo gida maza-maza.
Bai kuma basu damar tambayar ba’asi ba ya kashe wayarsa amma sun tsinkayi damuwa a muryarsa.
Wajen karfe sha biyu na rana aka fito da Nenne daga theatre room. Cikin ikon Allah an yi aikin lafiya, an cire stones and cyst, aka kawo abubuwanda aka ciro din aka nuna wa Dade, Dade sai hamdala yake yana godewa Allah, Siddiqah ta rungume hannu a gefe tana hamdallah, aka fito da ita tana barci akan gado aka gungurata zuwa dakin hutu.
Sai lokacin Dade ya samu ya fita ya tafi gida don ya dan kintsa, ya bar Siddiqah tana jiran farkawar Nenne. Ta sakata a gaba, motsi kadan ta gyara mata rufa. Amma an tabbatar musu komai lafiya lau, nan da mintuna talatin zata iya farkawa.
Kona minti daya Siddiqah bata dauke ido akan Nenne, fatanta dai Nenne Sappa uwar alkhairi ga al’umma ta farka cikin koshin lafiya don ita tafi yarda zaman Nenne take a gidan, ba zaman kowa ba. Wato ta fi yarda cewa ta zowa Nenne hutu ne gidan ta a Lagos, kamar yadda aka fara tun farko. Ita kadai ta sani, da ita kadai ta saba a cikinsu. Bata san wani Hamma, bata addu’ar ta san shi nan gaba.
Ta kuma yarda cewa Nenne Sappa mai kaunarta ce, ba saboda dan ta ba sai saboda amincinta da mahaifiyarta. Ita da Haj. Zainab Allah ne kawai yaga dama ya hadasu zumunci a dakinsa mai alfarma, don su abokantaki juna ba don ajin rayuwarsu ya zo day aba, sai don halayensu da suke kusan daya, na kaskantar da kai, tsoron Allah da yawan tawali’u (down to earthiness).
Don haka lokaci-lokaci inta kalli Nenne ta tuno abubuwanda aka ciro a cikinta wadanda aka ce sun dade suna wahalar da ita har share hawaye take sake yi da gefen hijabinta.
Aka turo kofar cikin wata irin nutsuwa kamar ansan mara lafiyar barcin allurar anaesthesia take yi.
Wani dogon ingarman mutum ya bayyana a gaban Siddiqah. Shi ba fari bane ba kuma za’a kira shi baki ba. In fact, kalar fatar jikinsa rarely kaga mai irinta a kusa, domin mai wuyar samu ce a cikin al’ummar Afrika ta yamma.
Gashinan dai ingarman gaske, ma’abocin fadin kirji da kasaitar tafiya. Sannan akwai kamala da nutuwa ta ban mamaki. Sallamarsa cikin wani accent mai dadin ji da zakin sauraro. Kai tsaye bazaka iya gane ko wane yare ne hakikanin harshensa ba. Domin accent din sallamar yafi kama dana Fulanin da basu kware da Hausa ba tsantsa.
Yana sanye da ‘casual wears’ na wani tsadadden yadin Filtex ruwan makuba, wadanda da gani babu tambaya zaka fahimci masu matukar daraja ne a inda ake amfani dasu. A kafarsa bakin takalmi ne sau ciki samfurin Raul Burgundy (Black Italian Leather Loafers).
Idan kana neman perfection na rayuwa to ka gama samunsa a wannan mutum mai shigowa, dauke da sassanyar sallama a siririyar fatar bakinshi, wadda gashin bakin nan na (man’s pride) yabi ya zagaye har kasan habarsa inda ya kwanta sosai akan habarsa.
**** **** ****
Siddiqah bata dauke ido a kansa ba har ya zo daidai kan Nenne ya tsaya, hancin ta ya shako mata wani ni'imtaccen turaren maza na “Boss Intense” har bata san lokacin da ta ja numfashi ta aje ba. Ko lura da ita bai yi ba, don gabadaya hankalinsa yana kan Mamansa.
“Here comes THE PRINCE!” Zuciyar Siddiqah ta ta gaya mata cikin whisper. Alhalin har yatsun kafarta kakkauran takalminsa ya dan taka mata kuma ta ji zafi da radadi, amma da yake hankalinsa baya jikinsa bai lura ba, kacokam hankalinsa ya dauku kan mahaifiyarsa dake kwance saman gado, baima kula da ya dan taka yatsun mutum ba, yama dauka inuwar daya cikin twins ce a zaune gaban Nenne.
Sai ga Nenne ta bude ido a hankali bayan ta shaki turarensa, kamar tana jiran isowarsa kafin ta bude ido, sai idanunta cikin na Abdulrasheed.
Prince yasa tausasan yatsunshi ya damke hannun Nennensa sosai, yana fadin "Nenne please don’t leave us..... gani nazo. My Nenne get well soon I beg you, duk abinda kikeso zan yi, koda barin Polo ne dungurungum, na rantse in har yanzu ba kya so daga yau na daina! Na kuma dawo gida kenan!!".
Nenne ta lumshe ido ta bude, ta tabbatar Abdulrasheed ne a gabanta, ba cikin mafarkinsa take ba, yadda yayi ya zo haka cikin gaggawa shikadai ya sani. Ta damke hannunsa itama cikin nata, ta nemi ciwon da take ji ta rasa, tana kokarin juyawa idanunta suka fada kan Aisha-Siddiqah.
Wadda ta ja can gefe ta tsaya duk ta sha jinin jikinta cewa Prince Abdulrasheed ne.