Showing 39001 words to 42000 words out of 42757 words
Chapter 14 - AISHA-SIDDIQAH-Book 2 Complete original by Takori Kabara.txt
dinta ce, in tayi hakan tamkar ta cusa Aisha ne a inda bata da kwarjini, tace da Kiki Aisha diyar kawarta ne kawai ta zo mata hutu daga Gombe.
Ai kuwa tashin farko Kiki ta makalewa Siddiqah tana rokon itama tayi mata lallen, Firdausi tace “na kudi ne malama?” Kiki tace “Ke kudin kika biya Aunty Feedy? Imma na kudin ne kinsan Uncle dina zai biya mun ayi mun” Ta fada cikin tsananin shagwaba irin tata, Aisha na dariyar shagwabar Kiki katuwa da ita sai sokonci, tace.
“Wasa Anti Feedy take miki kinji Kiki, zan miki lalle wanda yafi na Aunty kyau kin ji?” Kiki ta hau murna tace “kuma zaki na koya min hausa?” (kasancewar maganar Kiki duk rabi yarbanci ne sai kuma turanci da yafi yawa), Siddiqah ta ce “zan koya miki hausa har sai kin ce ta isheki”.
To dama a dakin Kikin Aisha Siddiqah take zaune, sai ga Kiki na shigo da jakunkunanta jikake keeeyyy! Tana jansu a kasa cikin dakin cikin dokin zama tareda Aisha.
“Pretty, tare zamu dinga kwana har in koma gida, yaushe zaki koma Gombe zan biki in ga gidanku?”
Aisha ta rasa me zata cewa kiki, ita kanta batasan sunan zamanta a gidan Engnr. Idris Akanni ba, haka bata san matsayinta ba. Don haka a karshe sai tayi kundumbala kamar tasan shirin da Nenne ke yi tace,
“Sai na gama WAEC zan koma gida”.
A daren Kiki bata bar Aisha tayi barci da wuri ba sabida hira, Nenne taji dadin irin reception din da Aisha ta samu a gurin Kiki, ko dama bata jin ta, indai wajen son mutane ne da saukin kai a gaskiya Kiki ba’ayi halin Anti Murja ba.
Ita daga nata sai nata, sai kuma wanda zuciyarta taga damar so, kamar Haseenah Ambursa kenan da suka dade tare.
Kiki akwai surutu, sa'annan akwai kirki da manyance, sannan ga hannun kyauta. A take ta hau daukan kayan kwalliyarta tsadaddu tana baiwa Aisha, don taga bata da kayan gyaran jiki, wadanda ta sayo tun daga Santa Monica din Los Angeles. Ta kwana tana zuba mata labarin da ya shafeta ko wakafi Kiki bata sakawa.
“Ni dinnan da kike gani nice ‘yar gatan Hamma, I mean Hamma Prince na gidannan, ai kin san shi ko?”
Murmushi Aisha tayi, tace “naga alama Kiki, ko daga wannan uwar sayayya da kika jido, kamar zaki kwaso kasar da kika dawo bakidaya ai sai dan gatan”.
Kiki ta kyalkyale da dariya tace “ai Uncle dina bashi da wayau in dai a kaina ne, ya manta da canjinsa a wurina basu kare ba, da nace zan yi shopping a “Santa Monica” sai kawai ya karo min. Har sayayyar matar shi mai zuwa nan gaba a kudinsa nayi mishi ya dauka kudi nane, to wa yake bani kudi in bashi ba?
Mum (Taiwo) ba’a cin kudinta ko zaka yi yaya. Kinsan likitoci akwai rowa, Dad kuwa ina na ganshi ma ko abu zai turo mana saidai ita ya tura mata yace ta saya mana.
Allah ya gani ina yiwa Uncle dina sha’awar kyakkyawar yarinya kamar ki. Inama zai yarda da an yi ‘yar gida tunda Nenne tace Mamanki kawarta ce”.
Kiki ta dan yi shiru kafin cikin damuwa tace “to bazai yiwu ba, don naji ance aljana ta auri Uncle dinane shiyasa yake gudun mata, ko zancen aure baya so ayi masa.
Yanzu gashi lamarinsa ya shafeni, Mum ta saka min takunkumin kin kula BoyFriend dina, tace sai ranar da Uncle yayi aure don bazata yarda yayi jika bai yi aure ba.
Sabida Allah Aisha Uncle AK fa har furfura ya fara (clicking to 43 years), jiran gawon shanu Mama take yi, da zai yi aure da tuni yayi, don ba irin matan da baya tare dasu a kasashen ketare”.
Aisha taji ta kara tsorata da lamarin Prince Abdulrasheed, jin abinda Kiki ke cewa a kansa, har a cikin idanunta da Kiki ta lura da taga tsagwaron tsoro tsantsa, wai har ya fara furfura, sai ta tuno Ishaq din ta dan shekaru 28 National Youth Cervice Corp Member (dan hidimar kasa).
"Banza bata kai zomo kasuwa tabbas", inji hausawa, akwai dai abinda ya hana Hamman su Firdausi yin aure ba haka kawai ba, har sai da aka zabo masa aka kuma yi masa bada saninsa ba.
Komai kuma yazo ya kare a kanta, poor her! Saboda anga iyayenta masu karamin karfi ne aka bata tsoho.
Can anjima kuma Kiki ta saki zancen Prince ta koma bata labarin footballer dinta, apple of her eyes; TosinAbdulNasir.
Labarin soyayyar Kiki da dan ball gwanin burgewa da ban kaye, domin soyayya ce suke yi mai tsafta ba tareda suna ganin juna ba sai a hoto da vedio call da Imo. Har lokacin sau daya Tosin ya ganta, itama sau daya ta ganshi a LA (Los Angeles). Kiki ko shafa labari shuni ce ita sai haka wurin bada labari. Ga saurin sabo. Koda yake zamu iya kiran al’amarinta da Aisha da haduwar jini na farat daya.
Haka itama Siddiqah Kiki ta shiga ranta from day 1 ta ji ta kamar kanwarta ciki daya. Don Kiki irin yarannan ne frank da basu da munafurci ko nunkufurci. In tana son mutum kawai tana fara son shi ne daga sanda ta fara ganinsa ba tareda wani dalili ba. Kiki is innocent, kwatakwata bata dauko tsauraran halayen yarbawa na Aunty Murja ba.
Washegari Kiki har makaranta ta raka Aisha suka dawo tare da Seun, tace “Aisha kiyi karatu da kyau kinji, ki fito da 9 credits, in kika yi wannan kokarin, ni kuma zan sa Uncle dina ya kai ki makarantarmu kiyi irin course dina.
Yayi sponsoring karatun ‘ya’yan marayu ma balle ke diyar kawar Nenne? Uncle AK is a philanthropher. Yana daukar nauyin karatun marayu da yawa a wurare da dama a ciki da wajen kasar nan. Kinsan hatta Ex-dinshi Haseenah Mum ta taba bani labarin cewa a irin yawon shi na a gidan marayu ya daukota”.
Aisha dai haka take ta biyewa surutun Kiki, da murmushi da gyada kai, ba don duka take ganewa ba. In fact, tana yi tana hadawa da yarbanci ko turanci. Daga jiya zuwa yau Kiki ta ambaci Uncle dinta yakai sau malala gashin tunkiya. Wannan kadai ya nuna (how close) karfin kusancin da take dashi da Hamma din. Wani mutum da tun bayan komawarshi, ko na minti daya Aishah, bata taba zama ta ware muhimmin lokaci ta zauna tayi tunaninshi ba.
Da shi da wanzuwarshi da rashin wanzuwarshi cikin rayuwarta duka sammakal. Karshen yankan kauna an gama mata itakam tunda an rabota da mai sonta da ya san darajar soyayyarta (Ishaq Nafada).
Amma tasa a ranta komai ma zai zo ya wuce ne kamar ba’ayi ba cikin hukuncin Ubangiji, don bata ga ta ina rayuwarta data Prince ta zo daya ba. Iyayenta zasu hakura su maidata ga Ishaq komai daren dadewa, ranar da suka gaji da jiran gawon shanun basarake Hamman da baya da tabbas. Ta jinjinawa (down to earthiness) din Nenne (halin tawali’un Nenne) da har tayi tunanin mace kamarta marar zurfin ilmi, mara nasabar sarauta, marar ajin rayuwa irin nasu zata iya zama mata ga Hammansu Fatima.
Ya Allah kanwarsa Fatima da ‘yar uwarsa Taiwo ma ya aka cika dasu wajen kasaita balle kuma shi kansa? Ita sau dubu gara mata Ishaq da yake bahaushe/bafillace ba dan kowa ba akan Bayeraben Prince din. Darajar idon Nenne kadai ya hanata cewa don Allah in ya tafi kada ya kara dawowa.
Tafi jin dadin rayuwa cikinsu da ya bar gidan. Don a dan zuwan Prince gidan hatta numfashi wuyar shaqa ya koma yi mata. Kwarjininsa ya bi ya cika kowanne sako na gidan Engnr. Idris Akanni.
Dade kadai ne ya san cewa Siddiqah murna take da komawar Prince, don yafi kowa lura da reactions dinsu ita da shi, don lokacin Nenne bata gama samun kanta ba, so bata ta tasu ta lafiyarta take, amma shi yana hankalce da motsin kowannensu, shi kansa Prince ya takaitawa kansa magana cikin ‘yan uwansa a wannan zuwan da yayi ba kamar yadda ya saba ba.
Daga irin kalaman bakin Nenne na yanzu Dade ya fahimci ta fidda rai akan al’amarin, wato ta fidda ranta akan auren Prince da Aisha. Jira take, Allah-Allah take Siddiqah ta gama WAEC ta maidata Gombe, akalla zata cigaba da rayuwa da mahaifiyarta a gefenta. Ita kuma ta fita zargin kanta na cewa bata kyautawa Siddiqah ba.
Don haka Dade ya fara nasa shirin shima don ruguza na Nenne. A wurinsa Aisha tazo cikin ahalinsa kenan. Aure tsakaninta da Abdulrasheed anyi kenan, ko yace yanzu aka fara daga nan har gaban abada, bazai yi saken da Siddiqah zata bar Abdulrasheed ba no matter ho worst things are becoming.
Hasalima bada sanin ita Nenne ba shi da mahaifinsa maimartaba sarki sun riga sun yi shawara, ji da Emir yayi Abdulrasheed yazo har ya tafi bai nuna bukatar daukar Siddiqah ba yace lallai jikan nasa sai an fito masa ta bayan gida, Emir ya gayawa dansa Engnr. Idris yadda za’ayi da Prince, yace in ma aljanar ce tare dashi da macen aure ta shiga gidansa alkadarinta ya gama karyewa, wato sunada yadda zasuyi maganinta cikin sauki.
Don haka yasa Dade ya fara shirin abinda ya dace akan Prince da Siddiqah.
Satin Kiki biyu tare dasu ta koma gidan iyayenta a Ilorin, bata tafi ba sai da tayiwa Nenne dadin bakin da yasa ta baiwa Aisha kan waya don a baya tace sai ta gama WAEC zata bata. A cewar Kiki ta yaba da hankalin Aisha tana so zata dinga kiranta akai-akai don neman shawara. Kuma bai dace a dinga hadata waya da Ummanta ta wayar Nenne ba a barta ta dinga kwana tana hira da Ummanta tunda yanzu bata kukan. Kuma dai Aisha bata da `BF’ a cewar Kiki da zai ke distracting karatunta da zancen soyayya.
Nenne ta kalli Kiki tana hararar ta wai bata da kunya, amma maganganun Kiki suka sa dole ta baiwa Aisha waya tsadadda, ta yarda Kiki na son Aisha.
Su Siddiqah sun fara jarrabawar gwaji wato mock kusan kullum suna waya da Ummanta da Abbanta suna binta da addu’ar samun nasara (albarkar Annabi).
**** **** ****
Watarana Kiki ta kirata tsakar dare daga Ilorin.
“Siddiqah ko kin san addu’ar rufe bakin mutum ya kasa magantuwa akan wani abu?” Dariya sosai Aisha tayi tace “Kiki wa kuma za’a rufewa baki dungurungum? Wane mai tsautsayinne ya shiga komar yar gatan Uncle dinta?” Kai tsaye Kiki tace
“Mamana! My Mum. Oh! My Mum is annoying.
Aisha tayi maza tace “akul! Kiki daina fadin haka gareta tun kafin mala’iku su rubuta” Kiki tace “To ya zanyi da Mum dina? Tosin yace zai zo Ilorin, musamman don ya gabatar da kansa gareta ya gaisheta ya kuma gaida Emir, amma ina tsoron gaya mata, don nasan bazata yarda ba, yanzu zata hau cewa sai Uncle AK yayi aure, bayan Uncle da kansa ya bani go ahead, har Tosin yaje ya sameshi a Qatar ya ganshi ya kuma amince da shi.
Amma ita sarkin tagwaitaka ta nace sai yayi aure zanyi, sabida Allah Aisha Mum bata kwareni ba idan ta janyomin na rasa Tosin? Abinda na sani ina son AbdulNasir sosai. Kuma Uncle din nawa ya amince dashi. Haka kawai Mum zata yimin sakiyar da babu ruwa. Bata san yawan ‘yammatan dake son Tosin bane”. Muryar ta yanzu gwanin ban tausayi cikin damuwa. Aisha ta san bayan wauta da gata da suka yiwa Kiki yawa, still da gaske tana neman shawara da mai hankalin da zai sa ta a hanya.
Ta san ko ta girmi Kiki to da kadan ne, amma hankalinsu da wayonsu ba iri daya bane. She’s so much infatuated akan Tosin AbdulNasir. Har tana ganin laifin mahaifiyarta akan saurayi.
Irin Kiki duk abinda wada suka yarda dashi ya fada musu dashi zasu yi amfani ba tareda wani dogon tunani ba. Siddiqah ta nisa, a hankali tace da Kiki cikin kwantar da murya.
“Kiki ki dinga addu’ar neman zabin Allah kin ji? Don’t be obsessed with him, ki bi mahaifiyarki akan duk abinda takeso wallahi zaki ga alfanu a gaba.
Kuma ko a kan son da kika ce min Uncle dinki na yi miki zaki iya yi masa solidarity ki jikirta baiwa zuciyarki abinda take so kamar yadda Mum take so sabida shi, da gaske baza taso ki yi aure ki haihu alhalin shi bai yi ba, baki son soyayyar twins ga junansu bane musamman in opposite sex ne (mace da namiji).
Nima bana son zaman gidannan, bana son zaman Lagos at all, amma yana iya? Dole na yiwa iyayena biyayya kuma ina kan yi. Na san ko bajima ko ba dade zan tsinci wannan biyayyar dana yi musu a gaba ko a kan ‘ya’yana ne.
Ke kinji dadi ma kina tare da ita har gobe (mahaifiyarki) an kuma barki kin gama karatu kafin ayi miki aure kuma ga dukkan alamu wanda kikeso za’a barki ki aura …..”.
Sai bayan ta fadi hakan ta tuno cewa ta saki layi. Kiki bata san wacece itaba har yau a gidannan. Bai kamata Kiki taji daga gareta cewa tana da auren Uncle dinta daga bakin ta ba, idan har Nenne da Aunties dinta babu wanda ya ga dacewar ta sani din ita akan me zata fada?
Amma ina! Aka ce magana zarar bunu ce ta riga ta fita, ta kuma shiga kunnen Kiki-Ruqayyat.
Kiki tayi dan jim, kafin tace.
“Kina nufin kina da aure? Ko kin taba yi kenan sister Aisha?”
Ta girgiza kai da sauri tana cewa “Kiki chapter closed, kiyi ta istikhara kina addu’a idan Tosin rabonki ne, kuma akwai alkhairi a tarayyarku, Allah ya kawo auren Uncle dinki kurkusa kamar yadda Mum keso, idan hakan ne kwanciyar hankalinta. Kada kimanta kullum tafi Tosin muhimmanci agareki”.
Kiki ta ja numfashi tace “Sister Aisha, my Mum is annoying, wadda take so Uncle ya aura fa ba wata bace Aunty Haseenah ce, his ex Haseenah Ambursa, koda yake ya so ta acan baya, amma wallahi yanzu baya sonta, ban dai san abinda ya raba su ba amma anfi ten years da rabuwarsu, rana daya naga ta dawo jikin Mum dina sun koma shiri, ni nafi Mum sanin Uncle dina, bakina da nasa yace min shi matansa Hurul eeni ne suna aljannah, me Uncle zai yi da Haseenah yanzu? Don kawai ya taimaketa?
Tsintacciya ce fa as in ‘yar gidan marayu bata da iyaye shiyasa Nenne bata so.
“Ho Kiki! Shafa labari Shuni!”
Duk da Kiki bata san me kalmar shafa labari shuni ke nufi ba, ta san yana nufin dai kamar ta faye surutu ko fadi ba’a tambayeki ba. Ta hau dariya tana cewa “da gaske nake duk abinda na gaya miki ni bana karya, ke nafi ganin dacewar Uncle ya aura kuma zan je har Qatar in sameshi akan hakan”.
Siddiqah tace da karfi “Kiki! Ni nace miki banida wanda nake so toh? Ba kyau cin naman mutane ki daina zancen wata budurwarsu. Is better you mind your business Kiki, ki rabu da sa damuwar kowa a ranki. In Allah yayi matarsa ce tunda Mum naso, sai kiga anyi”.
Kiki tayi maza tace “ba amin ba! Because my Uncle has a pure heart, I assure you he’s pure and clean, with a golden heart! Allah bazai bashi mace wadda ba mai tsarkin nasaba ba. Bazai taba auren mara asali ko lalatacciya ba in sha Allah”.
Amma ko bayan gama wayar su da Kiki, Aisha sai tayi jimm! Tana jin maganganun a ranta. Ashe shiyasa bata samu reception a wurin Aunty Taiwo ba, akwai wadda ta dade da yiwa dan uwanta tanadi.
Banda haka bata ga me tayi mata ba da ko gaisuwarta sama-sama ta amsa kuma a shaqare.
“Umh! Su suka sani” inji Aisha. Babu wani Bayerabe data saka a ranta balle damuwarsu ta dameta.
Sati biyu bayan nan su Aisha suka fara zana WAEC, wadda zata dauke su tsayi sati hudu suna zanawa.
Watarana Siddiqah ta fito dakin jarrabawa ta tadda Seun yana jiranta zai dauketa zuwa gida, suka kamo hanyar gida, sai taga Seun ya karkace kan motarsa ya tafi wani wurin da ita. Saida suka isa wurin ta fahimci ko’ina ne, wata ma’aikata ce ta shige da fice a jihar Lagos (immigration office).
Da ta tambayeshi ko’ina zasu je