Showing 12001 words to 15000 words out of 42757 words

Chapter 5 - AISHA-SIDDIQAH-Book 2 Complete original by Takori Kabara.txt

mai ran karfe Emir Abdulrasheed Akanni na zaune a kan karagar mulkinsa sun saka shi a tsakiya hagu da dama, a gefen sa mutum biyar a hagu mutum biyar a damansa, kowa ya sunkuya ya kawo gaisuwa ta al’ada Sarki na amsawa daki-daki da harshen Yoruba, kafin ya yi musu addu’a ta hadin kai a tsakaninsu kamar yadda ya saba sannan ya shafa kan kowanne in ya sunkuya a gabansa kamar yadda suka saba, duk sanda akayi irin wannan zaman haka yake yi musu tare da nasiha akan su guji duk abinda zai raba kansu, yak an fadakar dasu akan cewa kada su taba bari ‘ya’ya su shiga tsakanin su, Sarki yace ‘ya’ya da daukiya fitina ne, sune manyan abubuwanda ke farraqa zumunci, a karshe ya shaida musu abinda yasa ya kirasu akan auren dan su Prince AbdulRasheed ne.
Mahaifiyarsa Hajiya Sappa ta samo masa mata a Gombe, amma ba ‘yar sarauta ba.
Shiru ya dan gifta. Kafin su balle da yarbanci a junansu na resentment. Kowa da irin abinda yake fadi a falon ganawar na Sarki, mafi yawan ‘yan uwan Dade sun ce ne ta yaya AbdulRasheed zai kasa samun mace a gidan sarautar Ilorin, dama duka masarautun kasar Najeriya sai a cikin ‘ya’yan talakawan garin Gombe?
Uncle Abdulfatahi yace. “Kamar ance ‘ya’yan sarauta dana manyan attajirai da suke hada auratayyar abota (family friends’ marriage) da ‘ya’yansu sun kare?”
Abu daya da zai burgeka a wannan zaman shine cikinsu babu wanda yayi magana akan banbancin yare dana al’ada dake tsakanin Yoruba da Fulani. Musulman Yarbawan Ilorin nada kyakkyawar alaqa da Fulanin Najeriya. Sun fi karkata sukar tasu da cewa iyayen Aisha basu da sarauta (ko ta mai unguwa). Kamar yadda na fada a baya, masarautar Ilorin (is a Yoruba-Speaking Fulani Emirate) hakan yasa ko kusa basa kin auren Fulani a tare dasu.
Babban abinda ya kara wanke Fulanin Gombe a idon zuria’ar Sarki AbdulRasheed Akanni shine auren Gimbiyar Gombe wato Nenne Sappa da akayi da jimawa kuma aure na farko a zuri’ar Akannis, wadda har gobe alkhairinta kadai suke gani a tare da zuri’arsu, kodayake ita ta fito ne daga babban gida irin nasu, duk da haka baka rasa korafin matansu da ‘ya’yansu akan Hajiya Sappa din na cewa ta mallake Engnr. Idris da surkullensu na Fulani. Idris Akanni bai kara kallon kowacce mace ba da sunan kara aure har zuwa yanzu da ya fara tsufa bayan ita, yan uwansa kuwa daga mai uku sai mai hudu. Korafi dai da kananan maganganu irin na mata wanda baka rasa shi cikin kowanne gidan yawa, na talakawa ko na masu dashi ko na sarauta.
Uncle din Abdulrasheed na hudu wato Mutawalle ya dage a kan bakansa na cewa a baiwa Abdulrasheed mace cikin ‘ya’yansu kawai, ko yana so ko baya so, a wuce maganar aurensa haka. Su basu yarda ya auri diyar talakkawa ba. Emir yace dashi cikin lallashi da harshen Yoruba (kasancewar Mutawalle baya jin kowanne yare sai harshensa na yoruba).
“Oloruko mi o fe ni nkankan se pelu oye gege bi Baba e na. Mi o fe ke fi tipa je kanse nkanti won o ni ife si”.
Ma’ana; ku cire takwarana a cikin lissafin sha’anin SARAUTA sabida shi da ubansa babu tunanin gadon sarauta a cikin rayuwarsu, to ku cire musu abinda basa ra’ayi daga zama dolen su”.
Da kansa Emir ya mike ya taka da kyar ta hanyar dogara sandar girmansa zuwa kuryar turakarsa, ya dauko wata akwati ya kawo gabansu ya ajiye. Yace “Ga dukiyar aure da duk abinda za’a nema wajen gudanar da auren (Kehinde), na daukewa kowannenku wannan nauyin, a matsayinsa na jikana na farko, kuma wanda bai taba yin aure a cikin jikokina ba. na dauki nauyin komai da za’a kashe wurin aurensa.
Na umarceku da ku amince da zabin da mahaifiyarsa tayi masa, ita kadai ta san dalilinta, a matsayin ta na wadda tafi kowa kusanci dashi, don haka ta fi ku sanin matar data yi masa daidai”.
Da wannan magana ta karshe Sarki ya kashe korafin kowannensu akan auren Prince da diyar da bata sarauta ba, don a karshe bai ma kara bada wata dama ta wani cikin su ya kara fadin ra’ayin sa ba, yace umarni yayi musu su tafi su auro ma takwaransa zabin mahaifiyarsa, bai yarda ma a tuntube shi ba (Abdulrasheed din) sai bayan an daura auren.
Abu idan Ubangiji ya rubuta faruwarsa shi shine sai kaga in lokacin faruwarsa ya zo ya faru nan da nan bagatatan, kodayake shi aure lokaci ne kuma kamar habo yake sai sanda Allah ya nufa kadai yake tabbata. Abu kamar wasa hausawa suka ce sai ga karamar magana ta zama babba. Aisha-Siddiqa da Nenne na ta zaryar ganin likita a Legas, a can Ilorin da Gombe kuma ana shirin daurin aure, shiri ake sosai babu kama hannun yaro daga dukkan bangarorin guda biyu ba tare da Siddiqah ko Prince dake can matatar man Fetur a birnin Qatar sun san ana yi ba.
Akanni’s (‘ya’yan Emir) duka sun bi umarnin mahaifinsu babu wanda ya kira Prince ya gaya ma an karba masa aure. Dade yana Ilorin suka yi gangami da ‘yan ’uwansa da wakilan Sarki suka sauka a fadar Gombe ana sauran kwana biyu daurin aure wanda akasa za’ayi ranar Juma’ah bayan sakkowa sallahr juma’ah.
Likitan su Nenne ya gama baiwa Siddiqah kyakkyawan treatment yadda ya kamata saida ta kwana uku a asibitin, ya sabunta mata inhaler. Yace da Nenne, Siddiqah tayi babbar sa’a asthma dinta ba mai tsanani bace kamar ta Firdausi (mild asthma) ce wadda in an guji allergy dinta zata dade bata tashi ba.
Ita kanta Nenne Dade bai gaya mata me ake ciki akan maganar auren ba saida suka kama hanyar Gombe shi da sauran ‘yan uwansa daga Ilorin. Ya kuma ce ta kame bakinta har a daura baya so ko Taiwo ta samu labari.
A ‘yan kwanakin nan da Aisha-Siddiqah Yunus ke tare da ahalin kawar mahaifiyarta Hajiya Nenne Sappa, tunaninta mara kyau akan Yarbawa sai ya fara canzawa gradually. Ta fasa bude zuciyarta tana gane su waye ‘yan kabilar Yoruba. Mutanene masu matukar tsafta a gidan ba kamar yadda take hasashe ba. Nenne kuma ta fahimci cewa Siddiqah a ‘yar kankanuwar rayuwarta mara exposure wadda iyakacinta kauyen Billiri da zagayen Kumo da Gombe, bata taba jin wani abu positive (mai kyau) akan Yarbawa ba, ko me take ji akan su is ridiculous (na habaici da ba’a) ne tun tana yarinya, shiyasa ta girma tana ma bayeraben mutum wani kallo na dabam da bahaushe ko bafillace. Aisha-Siddiqah bata san cewa su din, kabilar yarbawa wata babbar kabilar Najeriya bace mai martaba da daraja da kima da rikon addini (ga musulman cikinsu) kamar koma fiyeda kabilun hausa-fulani, sai da ta fara zama da ahalin Nenne Sappa ne ta soma gane hakan, ta fahimci ashe bayarabun ma suna suka tara.
Dabi’un Nenne da ‘ya’yanta (Fatima da Firdausi) dana sauran jama’ar gidan, har ma da hadiman gidan su (Chief Cook Femi) da masu share-share da goge-goge kai har da masu kula da shukoki wadanda duk sun kasance kabilar Yarbawa ne, wasu ‘yan Lagos dinne wasu daga Ilorin aaka debo su, bakidaya suka taru suna narkar da wannan negative perception din na Aisha-Siddiqah wanda ta girma dashi a ranta akan kabilar Yoruba. Domin zuwa yanzu data saki ranta kadan a cikinsu, sai ta soma ganin abubuwa sabani ga tunaninta.
Ta ga cewa Princess Firdausi da Princes Fatima ‘yan gayun ‘yammata ne na karshe masu ajin daya take nata, a bana suka kammala karatun jami’a, a irin tsarin kwalliyarsu ma kadai da tsaftarsu wadda ta take tata, Siddiqah ta gane ashe Bayeraben ma suna ya tara.
Bayan an sallamosu sun dawo gida saboda ganin yadda yunwa ta kusan lahantata dole ta yarda take cin abinci, shima Nenne ta bata damar ta dinga fadin abinda take son ci, har tace ita da kanta zata dinga shiga kitchen ta girka mata, ba masu aikinta zata sa ba.
Sanda Nenne ta fadi haka sai da Siddiqah taji kunya sosai, tayi duba ga girman shekarun Nenne da matsayinta da mukaminta a cikin gidanta, hadimai sai sun fadi kasa sunyi gaisuwa in zasu fadiwa Nenne sako. Dade da kansa yana girmama Nenne. Amma tace zata shiga kitchen saboda ita, alhalin mijinta kadai take yiwa girki da kanta, ta rasa wace irin kauna wannan baiwar Allah ke yi mata. A rashin saninta damshin son danta Prince ne ya nasheta. Siddiqah don kunya da nadamar abinda take yi sai ta sunkuyar da kai tace “Nenne ki bar ni in dinga yi da kaina, ko a gida nina ke yiwa Ummata girki”.
“Lallai zaku shiryawa keda tawa Nanin (Nani Oummana) tana son mace mai yin girkin gidanta da kanta”. Ta shiga bata labarin Nani Oummana dake Gombe. Da yawan shekarunta amma bata fasa shiga kitchen ta yiwa iyalita girki ba musamman idan Prince Kehinde ya je wurinta. To kuwa har ya tafi Oummana da kanta take bashi abinci mai kyau na alfarma.
Siddiqah tace “sunan mutum ne KEHINDE?” murmushi Nenne tayitana duban kyakkyawar fuskar Siddiqah with affection na Kehinde din akan fuskarta. Tace “shine Hammansu Firdausi. Amma shekaru masu yawa ya basu. Kehinde ba sunan yanka bane sunansu ne na yaren Yoruba me nufin Hassan da Hussaini ko Hassana da Hussaini. Sunansa na yanka Prince Abdulrasheed”. Da murmushi Siddiqah tace “Nenne shima ‘yan biyu ne kenan?” Nenne ta gyada mata kai “yes-yes. Shi da ‘yar uwarsa Taiwo”. Sai Siddiqah ta hau dariya tana cewa “Nenne uwar biyu sau biyu”.
Suka fara hira tiryan-tiryan gwanin ban sha’awa. Ita kanta Siddiqah daga ranar ne ta fara sakewa da Nenne ta kuma fara jinta a ranta a kamar Ummanta.
Nenne ta baiwa Femi Agbode Chief cook tagidan umarnin ta bar Siddiqah ta dinga girki da kanta, ta kuma dinga taimaka mata da duk abinda take bukata.
Siddiqah aka shiga kitchen din Nenne aka sanya apron kamar gaske tafi awanni biyu tana aiki kuma ta sallami Femi. Kai saika rantse wani special abu take dafawa yadda ta tara hankalinta da nutsuwarta akan girkin. Can a jima sai ga kamshin suyar manja ya karade madafin Nenne.
Daidai lokacin Nenne ta taso daga barcin rana tana mai jin yunwa sosai, ta zauna a karamin falonta kafarta daya kan daya ta kwalawa Femi kira.
“Femi me kuke dashi mai sauki zan iya ci?” Femi ta amsa da yarbanci cikin damuwa cewa bata dora komi ba, bakuwar nan Aisha tana kitchen tun dazu ta hanata nata aikin komai, tace sai ta gama nata “Hausa food”.
Dariya Nenne tayi tace “shine nake ta jiyo kaurin manja kuma maimakon kamshin girki? Siddiqah manya rigimammiya’yar Ummanta”. Ta dau waya ta kira Haj. Zainab suna gaisawa tana bata labarin cigaban da aka samu yau na cewa Siddiqah ta saki ranta har ta shiga kitchen tana girki da kanta kuma tana shan magungunanta. Suna cikin hirar nan Umma na cewa “ai na gaya miki zata ware, don bata saba zuwa ko’ina ta kwana bane bayan makaranta. Tace kuma dai dama Petel uwar makon gida ce ina tausayin ta ranar auren ta. in aka koma hutu koyaushe da kuka take komawa makarantar sai daga baya ne take warewa ta shiga sabgoginta”. Sun jima suna hirar Petel din kafin suyi sallama.
Femi na tsaye Nenne na ce da ita tayi hakuri da Siddiqah. Amma ta sani ba bakuwa bace daga yau ba kuma ta zo ne don ta tafi ba a’ah ta zo kenan, ki kirata daya daga cikin yaran gidannan ki girmama sha’aninta kamar Firdausi da Fatima”.
Sai ga Siddiqah an fito daga kitchen, da katoton tray a hannunta ta isa ga tebirin cin abinci ta dora. Da murmushi tace “Nene barka da tashi barci” Nenne tace “ba jiya naji na gyara miki ba? Nenne ne ba Nene ba?” Siddiqah tayi murmushi ta ja kujerar dining daya ta zauna a rashin saninta kujerar Prince Abdulrasheed ce har sai da Nenne taji gabanta ya fadi. Siddiqah tace “afuwan Nene, ni nafi so ince Nene” sai Nenne tayi dariya tace “Petel din Nene me aka dafa mana haka ya sha manja da yaji?” Femi ta leka tana son gane ko menene wannan abun da Siddiqah ta dafo amma ta kasa gane ko meye. Tana dariya don a zatonta Nenne bazata iya ko tabawa ba balle ta kai ga ci, tace da Nenne cikin yamutsa fuska “you are having delicious meal Ma”.
Nenne ta kai idonta ga farantin Siddiqah taga ta shaqoshi ne da “danmalele” wanda akasari abincin ‘yammatan hausawa ne da yaji manja da uban yaji (borkono) tace “shagali wan dinner, to bari in zauna mu kwashi wannan garar tare”. Siddiqah na dariya daga tsaye ta dauka Nenne wasa take yi, bazata iya cin Danmalele ba, sai ga Nenne ta saka cokali tana kai loma cikin sukuni, ta zauna a kusa da ita suna ci tare suna hirar duniya abinda ya baiwa Femi mamaki.
Ire-iren hakan da Nenne ke yi mata kullum, na janta a jiki da nuna mata cewa itama uwarta ce kuma kawarta ce kamar Haj. Zainab ya koya ma Siddiqah sakin jiki da ita, ya taimaka wajen da cire mata kabilancin dake damunta, yasa damuwar data ke ji a baya akan zaman gidan da kewar su Ummanta yanzu ya ragu hamsin cikin dari. Nenne da Siddiqah sun zama kamar uwa da autarta, kai sai ka dauka Gambon su Fatima ce. Tunda Dade ya tafi Ilorin kullum suna tare itada Aisha.
Musamman da ya kasance Firdausi da Fatima basu cika zaman falon gidansu ba, ita Fatima bama ta dawowa gidan da wuri yanzu sabida haushin Siddiqah. Don haka Nenne da Siddiqa kadai take harkarta cikin gidan. Princesses koyaushe zaka samesu a daki suna waya da mazan da aka yi musu baiko wadanda duk family friends suke da zuri’ar Akanni, kuma ’ya’yan manyan sarakuna ne a yammacin kasar Najeriya, mijin Fatima Abdussalam Kayode dan Ohinoyi of Ebiraland ne, mijin Princess Firdausi kuma Prince Adesina, Da yake ga Oba of Ibadan.
Ranar yau Firdausi ta dawo kasuwa ta tadda Aisha da Nenne a dakin Nennen, Aishah na kitse kan Nenne suna hirar kawayenta na makaranta wato ‘yan gang dinta su Amintako, Firdausi ta sha mamaki sabida a sanin ta Nenne ta yarda Nenne da bata son kitso, kai bata yarda ma kowa ya taba mata kai ita da kanta take gyara gashin kanta ta kitse ko ta fake shi, amma tun da ta fahimci Siddiqah ta iya kalba mai kyau don taga tana yiwa kanta yau tace ta yi mata.
Princess Firdausi tace cikin tsokanar Aisha “Nenne I am jealous, kin yi auta kin ture ni gefe, yau tun safe baki neme ni ba sai Siddiqah” Saddiqah ta sunkuyar da kai tana murmushin jin nauyi. Nenne tace ma Firdausi “ai tuni na yaye ki kam!”.
Aunty Taiwo ma tayi korafin Nenne bata kiranta a waya a dan tsakanin nan ko lafiya? Don in ta kira itama ba koyaushe take samun ta ba. Hankalin Nenne yanzu yana kan koyawa Siddiqah girkin data san shi Prince Abdulrasheed yake son ci, kullum suna kitchen tare. Ga Toufeeq yana gari ba damar ta zo Lagos har sai ya koma UK.
Fatima sarkin korafi ta shiga tunawa Taiwo “Aunty Murja kin manta da zancen da nayi maki kwanaki na wata yarinya da Nenne tazo da ita wai Siddiqah?” Nan ta shiga labartawa Aunty Taiwo cikakken bayani cewa wata ‘yar farar yarinya da Nenne ta dauko daga Gombe a wannan zuwan data yi gida, tana nan mai ruwan fulanin kauye da rashin koshin lafiya kamar ba nutrition a jikinta, sai iyayi da kidifiri”, ta kara da cewa “amma kuma yarinyar mai kyauce fa, ko ni da bata yimin ba saboda abinda na gaya miki naji tana fadiwa Nenne kwanaki akan yorubas, na sallama kyawunta, daga haduwa da Mamanta a Saudi ta shige sukuf jikin Nenne. Nenne yanzu bata da lokacin kowa a gidannan sai nata, tunda Dade yayi tafiya”.
Aunty Taiwo bata yi mamaki ba don tasan halin uwarsu da son kyautatawa mutanen dake kasa da ita, wadanda wata alaqa mai kyau ko yaya ta hadasu, amma bata daukosu ta ajiye a gidanta, don haka Siddiqah ma bazasu barta tare da uwarsu ba in taimako take son yi mata tayi mata daga nesa, amma ba’a cikin gidansu a dakin Kiki ba, duk wani taimako da Hajiya Nenne Sappa zata yi maka tana yi ne daga inda kake zaune, to why zata taho da Siddiqah?
Taiwo tace “ha’an, na tuna zancenta”.
Sun hada baki itada Fatima kan cewa duk yadda zasuyi su sa Nenne ta maida yarinyar Gombe zasu yi, a bisa dalilinsu na rashin son bare a cikin gidansu. Sun gama magana akan cewa su Taiwo zasu taho Lagos dinma in Toufeeq ya koma don ta kwana biyu bata zo ba, zata jira har ya koma, inyaso lokacin Kiki ta dawo daga Los-Angeles sai su taho gabadayansu (Kiki ta tafi yin wani gajeren kwas na ilmin na’ura mai kwakwalwa na watanni shidda a wata shahararriyar Institute dake Los Angeles) bayan kammala karatun sakandirenta a wannan shekarar. Ta shiga Institute dinne kafin ta fara jami’a.
A lokacin Taiwo tana gidanta na Ilorin, an maida ta aiki asibitin koyarwa na jihar Kwara/Ilorin daga Lagos State Teaching Hospital da jimawa.
A halin yanzu Taiwo Murjantu na matsayin Consultant a gyanaecology

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login