Showing 3001 words to 6000 words out of 42757 words
Chapter 2 - AISHA-SIDDIQAH-Book 2 Complete original by Takori Kabara.txt
cikin yanayi na I don’t care attitude dinsa na halitta yace da Nenne “diyar wanene kika samo masa din? ‘Yar wace masarauta ce? Kinada tabbacin Abdulrasheed zai karbi zabin ki tunda ba wai mata ne baya gani ba a duniya? Me kika gano haka har ke da kanki yau kika zabi ki tafi nemo masa aure alhalin ina raye haka kannena maza?
Amsar da Nenne ta bashi yai matukar saka shi bude ido sosai yana kallonta da mamaki don tace yarinyar bata da alaqa da sarauta.
Har ila yau ya dauka ne zata ce a cikin danginta ta samowa Prince mata, tunda an zaga ta bayan fagge ance dashi Nenne ce ta daure gindin kada Abdulrasheed ya karbi mace a ‘ya’yan ‘yan uwansa wato jikokin Emir.
Lokacin da akayi wancan zaman dashi yayi kuskuren cewa zai fadawa Nenne amsa ta zo ta fada musu. Daga lokacin ya gudu Qatar bai kara zuwa gida ba, sunata jira Nenne ta zo musu da gamsashshen bayani daga bakin Abdulrasheed akan zabin da suka bashi har gobe shiru.
Baiwar Allah Nenne, bata ma san Abdulrasheed ya saka sunanta cikin maganarsa da kannen mahaifinsa ba a lokacin ta tafi aikin Hajji.
Nenne ta kwantar da kai da murya a gaban Dade, ganin kamar cikin gatse yake mata magana. Mai bi masa wato Turaki ya masa famfo ba jimawa cewa Nenne ce ta hana danta Abdulrasheed karbar ‘ya’yansu. Sabida ta fi so ya auro daga nata dangin.
Nenne bata san an yi haka ba. Tana zaune daidai kafafun maigidanta shikuma yana bisa kujera. Ta tankwashe kafafunta ta duka a gabansa (yadda take yi masa in zata yi masa magana mai muhimmanci), cikin girmamawa ta ce da shi.
“Ba komai na gano ba Your Highness, ban ga sarauta ba, kuma ban ga tarin arziki ba.
Na gano ma Abdulrasheed mace daya cikin dubu da na dade ina roka masa wurin Allah, irin wadda ta dace dashi ne, wadda zai matukar so fiye da komai na jin dadin rayuwarsa duk da gudun matan da yake yi. Yarinya karama wadda ta fito daga tsatson mutanen kwarai masu tarin halin kirki da nagarta.
Na samo masa mace wadda ta samu tarbiyyar Uwa da Uba a tare, kwarai da gaske mai tarbiyya ce, wadda nake da yaqinin zata zauna da shi da zuciya daya ta taiamaka masa wajen gyara duniyarsa da lahirar sa. Zai zama cewa ta raba gardandamin auren zumunci da aketa so yayi daga kowanne bangare nawa da naka. Inada tabbacin Aisha Siddiqah ce kadai ta dace da zama (first wife) kuma uwar iyali ga Abdulrasheed ba tareda yawan shekarunsa ya dameta ko yayi sanadin kawo mishkila a aurensu ba. Sannan in akayi duba da kankantar nata shekarun sai naga cewa zata iya da halinsa da yi masa kowacce irin biyayya.
Iyayen Siddiqah mutane ne dana dade banga irinsu ba, warin gudun duniya da tsoron Allah da tsayawa a matsayinsu. A takaice Dade naga duk abinda nake nema a suruka da surukai daga Siddiqah da iyayen da suka haifeta wanda shi yasanya ni kwadaitarwa Abdulrasheed aurenta, da fatan Barewa bazatayi gudu dan ta yayi rarrafe ba”.
Nan ta kwashe komai na haduwarta da Haj. Zainab a filin Munna, da yadda ta tsinci Dollars din guzurinta ta kuma maido mata su cas a yadda ta tsince su, tace wanna shine babban abinda ya burge ni da mahaifiyarta, sannan kamanni na halitta da halayyar Siddiqah bakidaya yayi mata irin na mahaifiyarta, tana kwadaitarwa Prince samun wannan tsatson mai albarka.
Sannan a surar Aisha ma bata jin AbdulRasheed zai kushe ta matsayin matarsa, tace saboda Aisha kyakkyawace shikuma aduniya yana son abu mai kyau. Duk da ake masa kallon wanda baya son mata tace zata gwada sa’arta akan Siddiqah. Tace saidai idan dansu Prince Abdulrasheed ba namiji banemai cikakkiyar lafiya.
Nenne tace daga ganinta na farko da Siddiqah taji a jikinta ga matar Prince Abdulrasheed Allah ya nuna mata yau a zahiri, tace komai na yarinyar yayi mata shige dana yarinyar datake gani a istikhararta ta koyaushe, fuskar Siddiqah ta dade tana gani a cikin mafarkin ta, a matsayin matar Prince AbdulRasheed. Diyar dattaku da mutunci”.
Haka dai Nenne tabi ko ta ina ta daddaure Babansu Taiwo, ya ji shi da kan shi yana son ahalin Haj. Zainab dinnan, wannan halin amana data nuna wa matarsa a wannan zamanin da muke ciki yayi matukar impressing dinsa. Ya dade bai ji hakan a kan mutanen arewa ba, kowa dai yaki halak-yaki haram saboda talauci. Dade Engnr. duk da haka bai amsa mata dari bisa dari ba, yace ne ta bashi lokaci yayi nazari sannan yayi shawara da Emir da sauran ‘yan uwansa. Ita kanta ta san Dade shikadai bai isa ya zartar da komai akan auren AbdulRasheed ba tareda amincewar Sarki da sauran ‘yan uwansa ba. ta gaya masa ta taho da yarinyar zata yi mata hutun sati daya, sai Dade yace da Nenne ta raka shi ya ga yarinyar da kansa.
Baba da Nenne suka taho dakin Princess Fatima, inda Nenne ta baro Aisha-Siddiqah tun shigowarsu gidan.
Siddiqah tayi tagumi a gefen gadon Princess Fatima (looking uneasy), cikin damuwa take sosai jin ‘yammatan gidan na Yarbanci, wani yare data tsana kuma bata son ji ko a makaranta, Yarbanci shine yaren data tsana fiyeda kowanne yaren al’ummar Najeriya sabida jinsa take a kunnenta kamar fada, ita kuma bata son fada da hayaniya ko kadan. Ko Ummanta ta sani Siddiqah bata shiri da bayeraben mutum a duk inda ta ganshi. Kai ita ko a makaranta bata kawance da ‘ya’yan yarbawa.
A yau sai ta tuno da BISOLA! Akan kunnenta Princess Firdausi tace da Princess Fatima “Mi o mo ibi ti Nenne ti ri omo Fulani to rewa bayi. O ma’n fi oju kekere wo eyan”. (I don’t know where Nenne got this beautiful Fulani girl, she keeps looking at people with her small eyes - ma’ana; bansan ina Nenne ta samo wannan ‘yar kykkyawar bafulatanar ba, sai kallon mutane take da kananan idanunta masu kyau kamar almond)”.
Princess Fatima ta dan saci kallon Siddiqah daga kwance, cikin ginshira irin ta ‘ya’yan sarakuna tana daga kwance akan gado tace “O jo ora oko ti ko ri itoju gidi (she looks local and unhealthy) wato da ganin ta mara lafiya ce kuma ‘yar kauye”.
Aisha-Siddiqah taji hawaye ya surnano a idonta, tace a ranta “Oh ni Siddiqah! Umma ta san gidan Yarbawa ta turo ni? Ina zaune suna zazzagina da Yarbancinsu…… Wallahi bazan zauna ba sai an maida ni gida.” Sai hawaye data keta rikewa ya digo, dis-dis a saman kundukukinta tayi kasa da kai tana tsanewa da gefen mayafinta.
Kyawun gidan, da alatun data gani cikinsa, da irin daular dake cikin sa wanda ko a talbijin bata taba gani balle a zahiri bai ko dadata da kasa ba, hasalima bata lura da komai ba hankalin ta yayi mugun tashi ya tattara ya koma gidansu a Jeka da Fari.
Damuwarta yafi karkata ga yaren yarbanci da taji a bakin jama’ar gidan ba babba ba yaro, kowa da kowa, har ma'aikatan gidan, wanda tun farko ba shi ta ji a bakin mahaifiyarsu Haj. Sappa ba ai da kome Umma zatayi mata da bata yarda ta biyo Nenne Sappa ba
Ga Siddiqah da dan banzan kabilanci a zuci. Ko bahaushen mutum bai cika mutum a idanun ta ba, balle Bayerabe, in dai kai ba bafullatani bane Siddiqah wani ganin daban take maka.
Tun suna yara da ta ji ana waka ana cewa “Yarbawa masu kashi a kwano" to fa tun daga lokacin Siddiqah tasa a ranta duk Bayeraben mutum kazami ne.
Ita a duniyarta da zuciyarta tana da kabilanci, data dade da gina zuciyar ta akai, na jin cewa kabilarta ta Fulani tafi kowacce kabila, tana ganin Bayeraben mutum kamar wani ‘alien’ ko wani na daban a cikin mutane sabida yarensa.
Princess Firdausi ce ta lura da tsurewa da tsoron da ya samu Aisha a idanunta, amma bata san me ya kawo shi a tareda Siddiqa ba, sai taga jikinta na 'yar kyarma wanda bata ga dalilin sa ba.
Ita kam Aisha-Siddiqah kawai yaren da suke yarawa ne ya tayar da hankalinta ya dugunzuma ta don ta gama sawa a ranta zaginta suke faman yi da yarbanci suna mata kallon raini wanda a zahiri ba haka bane yanayin kallon Firdausi da Fatima ne haka kaga suna kallonka daga kasan ido kamar suna harararka kasancewar sunada dara-daran idanu.
Inda Allah ya taimaketa kafin su sake yin yarbancin dake barazanar saka ta ciwon kai, sai ga Nenne ta shigo tareda Babansu Taiwo wato da Dade Engnr. biye a bayanta.
Nan Siddiqa ta ga ‘yan matannan biyu duk sun nutsu matuka, itama sai ta fara kokarin nutsar da kanta daga firgicewar ta. Amma idonta yayi kozai-kozai. Nenne da murmushin kaunar ta da Siddiqa tace “Aishan Nenne mutanen Lagos, yaya bakunta? Ga Babanku yazo don ya ganki”.
Hawayen sabon tashin hankali ya kara digowa daga idon Siddiqah data gane Bayerabe ne mijin Hajiya Sappah shima. Kenan ita Nenne din kadai ce ba bayerabiyar ba a gidan? Haka zata zauna cikin Yarbawa kwana da kwanaki? Sai ta cije lebenta kamar 'yar goye, tana binsu da Ido ta kasa cewa komai. Amma tayi tunanin yakamata ta gaida Dade ko da ba zai gane nata yaren ba. Ta duka tana gaisheshi cikin Fulatanci, da matukar girmamawa cikin dari-dari don ta dauka baya jin ko alif a nata yaren, kamar yadda itama bata jin nasa ba kuma ta fatan ta koya. 'Yar dariya ta kama Engnr. Akanni. Kasancewar yana jin fulatanci suwayya-suwayya (kadan-kadan), ya kuma gane yanayin data ke ciki na kin sakin jiki dasu kamar ace kyat! Ta zuria da gudu zuwa Gombe, suka yi mata dariya gabadayansu ganin irin tsugunon data yi a gaban Dade ta kasa dagowa, dariyar su ta kara dugunzumata, don dai ita bata ga me ta fada abun dariya ba bayan gaisuwa. Ga mamakin Siddiqah sai taji Engnr. Idris Akanni yace “Calm down Aishah, feel at home kinji, zan hana su yin yare in kina zaune, ya kika sauka a Ikko kuma ya kika baro mutanen gida a Gombe?” Ya Karasa da Hausa.
Wata wawuyar ajiyar zuciya Siddiqah ta ajiye, at least Uwar da Uban su sun iya Hausa. Kuma zasu hana a yi mata yaren oduduwa a kunne.
Ta sakko daga gefen gadon tana gaida Baba da ‘yar karamar muryarta. Gaisuwa irin ta al'adar mutanen Gombe. Nenne ta dago ta daga gaisuwar “ina wuni?” Don ba haka ake gaisuwar al’adar Ilorin a gidan ba. tace a ranta coaching na musamman zata soma yiwa Siddiqah akan ala’adun gidan.
Baba Engnr. na observing komai na Aisha a fakaice, sai ya tuna da sanda aka kawo masa Nenne Sappa gidan sa a matsayin matarsa, haka take ‘yar tsurut kamar Aishah duk ta rikice a cikin danginsa Yarbawa, lokacin itama bata wuce girman Aisha din ba sai tsantsar kyau irin wanda mazan Yarbawa ke matukar so daga matan Fulani (kyau da farar fata).
Dade ya tambayeta makaranta, ajinta nawa? A hankali cikin nutsuwa da sanyin murya Siddiqah ta gaya masa aji shidda wato ajin karshe zata shiga da zarar an koma hutun nan. Dade bai jima tare dasu ba yayi musu sallama cewa zai fita kuma zai kai dare bai dawo ba kada su jira shi cin abincin dare. Waziri Idrisu ya fita da gamsuwa sosai da zabin da Nenne Sappa ta yiwa Prince Abdulrasheed. Zai iya cewa shigen nasa zabin ne da mahaifinsa Sarki Abdulrasheed yayi masa. Banbancin shine Siddiqa ba ‘yar sarauta bace ba ‘yar kowa ba. Bai san yaya akayi ba zuciyarsa dari bisa dari tayi na’am da zabin matarsa “Aishah-Siddiqah Yunus”, ta zamo musu suruka, mata ga tauraron zuciyar zuri’ar Akanni’s kuma tilon Dan sa namiji a duniya Prince Abdulrasheed (Kehinde).
Firdausi ce tayi waya kitchen wa Femi, shugabar kukun gidan bakidaya, inda ta ce mata maza a shirya abinci yanzu, Nenne nada bakuwa daga Gombe tun zuwansu bata ci abinci ba, Nenne ta raka Dade har ma’adanar motocinsa ya fita, sannan ta dawo ta tarar Firdausi ta saka an shirya musu abincin rana a dining. Don haka ta hutar da ita wucewa kitchen wajen su Femi, ta dawo ta samesu a ‘dining area’.
Princess Firdausi ita ta jagoranci Siddiqa zuwa ‘dining room’ dinsu. Bayan ta fito daga wankan data sata tayi. Ta bata sabuwar doguwar riga cikin kayan da niece dinsu Kiki ta bari a gidan tace ta saka kafin a wanko nata, ganin cewa Siddiqah bata fice sa'ar Kikin ba, tsayinsu ma zai zo daya da Kiki, kiba kawai Kiki Ruqayyat ta fita.
A idon Firdaus sai taga kamar duk kayan Siddiqa masu datti ne. Don haka ta hada duk kayan da Siddiqah ta zo dasu tace Femi ta tafi dasu BQ ta wanke ta goge mata kayan bakidaya sannan ta dawo dasu, tace da ita da fulatanci “duka kayan naki ba guga ba saiti”. Wannan abu bai yiwa Aisha-Siddiqa dadi ba, don harda kayan sallahnta na bana a ciki, sauran kuwa duk kure adakarta ne atamfofine masu kyau da daraja daidai karfin Ummanta, cote d’voire ce da glitter da kuma atamfa ‘yar Ghana, amma sarkin fi'ilin gidan wato Princess Firdausi tace basu da saiti ba karin guga bayan sunfi wata uku a wanke a goge a kasan akwatinta na gida, tana makaranta shiyasa ba wani sawa take yi ba. Amma maganar da Firdausi tayi da fulatanci maimakon Yarbanci yasa taji dadi bat ace komai ba tunda Dade ya hana Firdausi da Fatima yin Yarbanci a gaban Siddiqah ganin yadda take muzanta in ana yi, sai suke yin turanci ko fulatanci, don da gaske Hausa bata wani zauna a bakinsu ba, don haka taji sanda Firdausi ta ce da Femi a kaisu BQ a wanke a goge, sai akayi sa'a ‘yan maganar Siddiqah basa kusa bata ce abar mata kayanta ba yadda taso fada tayi shiru, suka wuce zuwa dining tana bin bayan Firdausi.
Nenne ta nuna mata kujerar gefen damanta tace ta zauna, haka ta zauna a dofane, ta ga ma’aikatan kitchen din wadanda duk mata ne dake kai kawo a gabansu suna aje akusan abinci duk tumatuman yarbawan Lagos ne, suna aje abubuwa suna juyawa suna kada bombom suna badeta da warin jikin yarbawa. Ko motsi wannan da kyar Aishah ke yinsa a ‘dining room’ din, don ita kam tasha jin ance jikin yarbawa body odour dinsu daban ne dana hausawa ba tun yau ba, ga Nenne ta cika gida dasu sune duka hadimanta ba bahaushe ko bafillace ko daya, ta riga ta saka ma ranta duk Bayerabe nada warin jiki daya banbanta dana hausawa da fulani, shiyasa har zuwa lokacin a darare take dasu kuma a kyankyame, ita dai a ranta kawai so take ta bude ido ta ganta a dakin Ummanta a lungun Jeka da fari, amma abu ya gagara, don haka ta zama rakumi da akala sai yadda Princess Firdausi tace tayi kawai take yi bata umh bata umh umh. Duk bakin nan na Aisha ya kama kansa a gidan Engnr. Idris Akanni musamman data lura babu hayaniya a gidan sam.
Wannan abincin dai da aka zauna cinsa tare da Siddiqah, wadda a rashin saninta ta zauna ne a kujerar da Prince Abdulrasheed ke zama gefen a Nenne, kasancewar kujerun dining din a kirge suke iya jama’ar gidan kacal, sai ko ta Hakeem da Kiki ‘ya’yan Taiwo, wadanda suna cikin iyalin gidan, ko kwakkwarar loma uku Siddiqah bata yi ba, ta fada a ranta ita bazata iya cin abincin da tumatuman Yarbawan nan suka girka ba. dama dai Nenne ce tayi shine zata ci. Ta san yarbawa suna cin dodon Kodi da Qaguwa (shrimps). Duk yunwar data ke ji haka ta hadiye abarta, data tuno Dodon kodi da Qaguwar da yarbawa ke ci a cikin abincinsu, ta na juyawa kuwa ta yi ido biyu da Fatima ta cako katuwar shrimp da fork ta kai bakinta, tana shirin kurbar ruwa a tambulan don toshe yunwar dake addabarta wanda ba abinda yake mata sai kara kulle mata ciki, duk idanunta sun fada cikin lungu, Fatima na tauna ‘shrimps’ dinnan cikin taunarta ta gayu da yanga Siddiqah ta ji ta kware jikake “kat!” Da ruwan data ke sha, amai kuma ya zo mata gabagadi. Da sauri ta kai tafin hannunta ta toshe bakinta, idanunta fal! Kwallah!
Dukkansu ba wanda ya lura cewa bata cin komai sai Nenne, ba kuma kowa ya lura da halin takura data ke ciki a a baka da zuci ba sai Nenne, wadda duk wani motsinta tana ankare ta gefen idonta har aman data kunso ta cika bakinta dashi. Kasancewarta Uwa mai tsananin kula da mood din ‘ya’yanta. Abincin da Siddiqah ta tsana a duniya (bakar Amala) ne aka yi da kuma lafiyayyar sakwara dakan hannu (pounded yam) da taji kirbin tabaryar Femi tayi laushi lubus da miyar ganyen Ugu da taji kaguwa da ganda zuqu-zuqu da naman Tolo-tolo wannan shine (favourite food din Dade) kuma don shi aka yi, in har yana gida to abincinsa kenan, duk da yace ba zai dawo da wuri ba a fitar da ya dan yi sun zuba a ma’adanan abinci (food warmers) sun ajiye masa nasa.
Amma Siddiqah ko loma uku kwarara ta kasa, kuma ko sha'awa abincin bai bata ba, duk haduwar abincin da bajintar Femi wajen iya abincin yarbawa na alfarma, itafa komai na bayerabe