Showing 24001 words to 25578 words out of 25578 words
Chapter 9 - Bagidajiya Book 2 Complete hausa novel by Haseena Muhammad .txt
'yan gulma 'kus”
“Lallai ne farouk anje honk Kong and'ibi 'dabiun 'yan can...kun zauna kun tarun ma autata kaida matarka,ko ?”
Nok'e kai yayi yana Sosa keya.ya dan babban yatsan kafarta tad'ago tana kallon sa signal yayi mata,kan sutafi yaduba lafiyar babynsa.aiko zaraf tamike tayi kamar ta gaji da zaman ne ,tana barin wajen shima ya mik'e yabi bayanta...
“Nashiga aljannah mom binta yayifa”
“Kedai bari kawai 'yan tselan k'wa,inaganin sanda yake mata signal”
Dariya 'yan dakin sukayi,Anty faty uwar miskilanci,murmushi kawai tayi ta mike,tana gyara mayafi
“Mom twins badai tafiya ba?”
“Eh mana tafiya tunda munga saukan bak'i lafiya, sai fatan a haife kuma lafiya”yanda tayi maganan saida ya baiwa kowa dariya.itako ko ajikinta tayi masu sallama tafita.....
*★★BAGIDAJIYACE★★*
•★
By Hassenart bamalli
•★
09065990265
★
★
*One of the five Za6a66u of 2020*
★
★
_~Mashaallah ,alhamdulillah wannan page din sadaukarwa ne d'ungurgun gareku masoyan littafin bagidajiyace ,wa'inda suka biya kud'i dama masu dan raruma a groups ,ina sonku dukkan Ku,shi yasa nabaku fajin nan kushana,kuyi duk yanda kukaso dashi~_
_____________________________
50
🔚🔚🔚🔚🔚
Ina mik'a d'imbin godiya ta ,ga tarin masoyana wa'inda suka bani lokutan su da aljihunsu suka Bini har zuwa yau da nakawo k'arshen littafin nan,naji dad'i Allah yabarmu tare cikin so da yardan juna Ammen.
*💓💓Kuna raina💓💓*
*Maman janan*
*Ummi minnah*
*Maman Fareeda*
*Aisha (Nanah)*
*Maman husna*
*Ruky*
*Mrs najeeb*
*Kune kuke biye dani tundaga littafina na rayuwar afredarh, Ramuwar gayyah,har zuwa yau a bagidajiyace, kai wasunkuma har kun fara biyo ni a sabuwar littafina dake tafe...wato LAILAEH! I Salute your efforts much of tncu❣️*
Koise Darling...kekam bazance komai ba tukun😊
_Son so fisabilillah my fans💯_
A section d'in farouk suka yada zango mom ke jigilar hidimta ma aisha ,cangal bata barin ta tayi,farouk kam kullum yana d'aki baiya ko fitowa ,maryam na shigowa zai koreta wai taje wajen mijinta ,tana takurasu .
Cikin wata Daren jumu'a ne Aisha ta tashi da nakuda,zufa ya hau keto masa ta ko'ina, dasauri ya dauki wayarsa yakira mom d'insa ringing biyu ta d'auka, dama itakam tunda suka dawo bata barci kullum cikin saurare take....tana d'anka tafara da tambayarsa
“Yaro ,haihuwar ne?”
“...Mom gadai tanan tana kuka wai cikinta ke mata ciwo,mom kizo dai please kawai”ya k'arasa maganan a rud'e.
Tuni tazura hijab d'inta dama major baya gida ,yina jaji .
Tana tafiya tana cigaba da receiving kiransa,har taje k'ofar su
“Son Ku bud'e mun section d'in inshigo”
“Mom it is opened ”
A falo sukayi kici6is dasu ya taitayota zasu fito ,jiki na 6ari ta taitayeta
“Son jeka a fito da mota ,kira maryam tazo ta rakamu”
Suna shiga harabar asibitin ,nurses suka fito da keken tura pt,suka sakata daga motar, aka wuce da ita labour room.
Saida ta kwashe sa'oi biyar sannan haihuwar tazo ta sosai a lokacin har safe tayi ,farouk kam ganin yanda ta fita a hayyacinta haka yake shar6an kuka ,kamar ba sojaba.
Ganin haka,yasa doctors suka fita dashi ,wai karya idasa kashe mata jiki ,taji bazata iyaba.masallaci yawuce yashiga nafilfili bai fitoba saida aka shaida wa su mom ta haihu,Nan fa aka shiga rige-rigen kiran wayarsa,maryam taci nasaran samun sa ,nan ta kyankyasa masa ai a sittin yashigo yana jaddada godiyarsa,
Da ita da sunkucecen yaronta jajir sak mahaifinsa mulmul dashi,d'akin Hutu aka wuce da su,saida sukayi 24hrs kafin aka sallamesu suka dawo gida.
A gida kam tuni gida yadinke da 'yan uwa ana jiran dawowarsu,sosai farouk yayi ma likitocin yayyafin naira kafin suka wuce.
Hassana najin labari tafara kintsa kaya kwana biyu da haihuwa ta iso Zaria,ko hutawa batayiba ta fara gayawa Aisha shirye² bikin sunan da zasuyi.
Ashobe suka fitar ta rantsatsen swiss les purple da takalmi da clutch pitch ,sosai suka gama shawarinsu su uku anty faty taba k'awarta kwangilar kayan kano akafara waya ganin za'a samu matsala kawai tafita waje tayo order takalma da jakunkunan ,taturawa customer dinta na Dubai sample din less din kwana biyu kaya sukazo na mutum hamsin kacal.
Oya -oya anty faty da momyn su farouk sukayi suka ciccirewa 'yan uwa na jiki-jiki da abokan arzuk'a sauran kuma en karere aka basu pieces sunema akasuwa.kwana shida da haihuwa saiga Hussaina itama da nata dan sagarin cikinta.
Tana zuwa ko hutawa batayiba tace abata ankonta tagwada dinkin kar yazo asamu matsala don ita kanta tasan tayi shigegiya.
Ranar suna kam lafiyayyen liyafa aka shirya a cikin gida mai jego da angon karni suka shashha ankonsu iri daya,yamma nayi aka tafi dinner dafa d'an la6u6un jariri 🙄 ,duk Wanda yaso daka tar dasu saisuce ai ba ayi masu na bikinsuba don haka abarsu su Shana.
Taro kam alhamdulillah ya watse aisha da baby mai sunan dadyn farouk ana kiransa jawwad sun sama gift ta ban girma.washenkari aka wuce dasu katafaren gidansu a gonar ganyen tukur-tukur.nidai fans wash mezan fad'a.... Infact komai mashaallah don harta dakin baby an ware masa ankuma k'awatashi.
Haka kowa ya watse yabar su cikeda farinciki dafatan gama jego lafiya...wai inji tsoffi asauke garwa lafiya,nikam hassenart nace indodo karki yarda da laftawa jikinki haukan ruwan zafi kije ki kamu da yawan jini ,sannan ki komawa farouk duk kinyi bak'i jiki ya nuna da ruwan zafi,😁 ayi wankan saffa-saffa amma fa aci romon dadi asha tea mai kauri dasauransu.
Yaya kuluwa kam anzubarda makaman yakinta sosai takejin Aisha indo a rai ,tunda tabiyo 'yan suna tazauna agidan ta,tace itakam da zuntu sai angon ta yayi wata shidda yafara zama yana karya k'afa tompa.......keda farouk ai kila da rabon yakorakine.
Bayan shekaru biyar
A zuwa wannan lokacin al'amura da dama sun faru masu dad'i da akasin haka ciki ko harda,rasuwar Abban aisha Mal Abdullahi, bayan share makoki yaran mama binta suka sa aka sau yawa gidan baban nasu nanan Zaria salo akasiya fili tabaya sukatankasa masu gida suka dawo Zaria ,kancankam da zama suda fallanki saidai zumunci.
Yaya kam na alfahari da mama binta zaman ta na abokiyar zama tagari yau gashi sanadiyyar ta sun fito sarari ,sunbar karkara,acewarta....
Sanusi ma Haidar yasa an Neman masa makaranta yana karantan computer science.yakuma bude masa business center yana samun 'yan kudadensa, yazama dan burni abinsa....
B'angaren Aisha kuwa k'alk'alawa gidan nayi dagudu saidai me inasamu nawuce get din farko da kyar,sakamakon mugayen sojojin da suka kabbaro mun kamar sun sama nama,wai nadamesu da sunturi... Hakuri nabasu in sunyi hakurima daga yau bazasu kuma gani naba.
burki naci a compound din hango wani hamshakin mutum da 'Yar kyakyawar matarsa agefensa sanye cikin danyar geznar da yaransu uku dan namijin dazai kai shekaru biyar agefensa sai macenda bazata wuce shekaru ukuba a jikinsa sai er jaririyar wata uku ajikin momyn ta....wato Aisha.
Mamakine Yakama ni to wai me akeyi ne agidan naga zaratan maza da matayensu zazzaune a tantinan gidan akan kujerun roba kowanne gaban su da table dauke da shawarma,burger da lemunan gwangwani biyu da roban ruwa faro.
Jingina nayi dajikin get din ina raku6e Ina hango bidiri.
Mr.mc ne yakar6i mike din yana taunan cinyar kaza“uhmmm...muma kam lallai mun shaida,don haka muna tayaku murnr zagayowar ranar aurenku ,Allah ya kawo 'yan uku sau uku,muzo mu kwashi rawan shoki...ahhh, yanzu dai muna son ganin hajiya Aisha tareda mai gidanta afili...yau kam ranar kine kijuye mana galon gallon mukuma mu k'yatta ashanar DJ.... ”
Mik'ewa sukayi suka fito filin dake daukar walwali,maryam ce taketo filin tabar haidar Da yaransu biyu a table dinsu taje takar6an masu baby janan,
Cake suka fara zuwa suka yanka ,yasaka mata cake din a baki shi kuma ta kafa masa kofin juice a baki ,kur6a yayi with full of rejoice
“Happy anniversary my hubby”
Kyakyawar hugging,yayi mata sannan bata lafiyayyen French kiss ta koyi lif a jikinsa tareda rufe ido,'dif wajen ya dauke wuta,kafin mc dake sake da baki sagaga yafara magana
“Uhmmmuuhmhumm ni kam master of ceremony... ,ai dama yau d'in ranar kune ,don Allah Ku basu hannu. RAF...RAF...RAF...DJ abamu sauti”
Tuni waje ya d'auki kid'i a kacashe da lik'in daloli da 1-1k
Daga k'arshe farouk ya amsa mike yayiwa kowa dasuka samu halartan taron anniversary d'insu godiya.... Sannan yafad'a achievement dasuka samu da eassshhh dinsa tundaga kan mallakar companoni biyar dasukayi,filling station takwas,gidaje ak'asashen duniya sha biyu ,uku a Nigeria, asibitoci biyu Wanda duk suke dauke da tambarin sunansu wato ASHMAER Wanda su kad'ai suke juya abunsu sai wa'inda suka jawo. sai kuma arzik'in yara uku dasuka samu ,jawwad,Teemah janan .
Sun kar6a prizes naban girma daganan taro ya fashe,anan ne na hango Hassana da tulelen cikinta mijinta munnir na lallaminta dayaranta kyawawa su biyu mace da namiji suka shige motarsu wai zai kaita gidan kakus ne mama binta acan zasu kwana kafin washenkari suwuce gida
Aikam Hussaina najin haka itama ta taso nata tawagar tace ,gidan kakus din zata suci shinkafar manja da wake mai daddawa ta tsoffi.
Maryam ne ta narke fuska uwa junior yaronta
“Habiby zani nima”
“Sowie qalby a matse nake,kinga su Hassana da ciki waincan su Romeo d'in kinsan muna watsewa duty zasu tafi ,nima a agaza mun ko mayiwa junior k'anwa”.
Dallaro masa sexy eyes d'inta tayi
“Allah habiyby?”
“Sosaima...kedai muyi oya-oya kar hassenart tabiyo mu nad'an sirrikanmu,hope dai kin shirya,don yau inajin kat zamu karye gado...”
TAMMAT!.
Alhamdulillah ala ni'imaty hatha.....
Monday 14/09/2020.
Hassenart Mohammed bamalli