Showing 15001 words to 18000 words out of 25578 words

Chapter 6 - Bagidajiya Book 2 Complete hausa novel by Haseena Muhammad .txt

01 Dec 2024

1194

tsakar falon suka baje sunaci
Mamane ta d'ago labulai na d'akin
“Subhannallah ,tsarki ya tabbata ga Allah,'yan biyu wata bak'uwar balarabiyace Ku kazo da ita?”tafada cikeda tsokana, da gudu Aisha taje tafad'a jikinta,sai hawaye bul²


“Mama wai baki gane autar kiba?”


“Hmm koda naji,Ashe autace to ke d'in ne duk kin canza ga kyau,ga natsuwa lamarinki da ban mamaki”


“Hhhh,Abunki da kin haifo kyakywa ,kema na canza maki ko?...kodayike wallahi namayi fushi,ko kita6a zuwa ki dubani,nayi kewarki kamar mene....keko ko ajikinki”


“Waya fad'a maki indodo ta”


“A'ah fa,point of correction, Aysha ba indodo ba...”


“Oho,nafa manta Autan ta zama er gayu...kinkozo a daidai ana shirin bikin rahanen ki”


“Ciftsi,mama sai yanzu lallai tayi badago a k'auyen nan,na aza zan jita da yara biyu”


“Allah shi yasa naga mai magana tayi...To aiko kamar yanda kika canza haka itama,don yanzuma cancellor zuntu zata aura,wai itama andaina cemata rahane,waisai ko rihana,ko raihane”


“Kaimama raihana”


“Yawwa muje nayi maku girki”


Sosai Aisha taji dadin hutun ,sun zazzaga dangi kafin suka komo zaria.





*A year later*
Su Indo na hango zaune cikin hall ana rubuta final paper na ssce d'in su.


Wanda da sungama zasu yi graduation,sai su dawo in the next day ayi masu walima Wanda duk zasusa graduation gown.


Sosai malaman sunji kewar 'yan set dinsu Indo, ga rashin ji ,ga k'ok'ari.


Sun samu prizes sosai ,kafin daga baya aka kira head girl tayi bayanin ban kwana


Hassana nakuka sosai ,tayi tak'aitaccen godiya takoma wajenta tareda amsar kyautarta na matsayin head girl data bawa makaranta gudunmawa tareda cigaba masu dama.


Haka akazo kan labour,habawa nan students suka rikice da fadin ifirituu,ifiritu!!


Dariya ne yakamata,bata ta6a yarda ana kiranta ifiritu ba sai yau


da confidence d'inta ta kar6i mike d'in,waigawa tashiga yi tana k'arewa students din kallo


“Doka da dokokinmu, kibi mu zauna lafiya,ki kibi ki ga taron dangi...”


Dokokin data gabatar aranar su tafarkone a matsayin prefect ta maimaita, sannan tajiya wajen wacce ke rike da muk'amin ta a yanzu


“Allah yasa kiyi Wanda yafi nawa....”


“Ba amunba....”gabadaya aka k'are hargitsewa,waving tashiga yi.


“Alright,alright... Nasan akwai Wanda na 6atamawa,a makarantan nan,yau ga Aisha,ifiritunku tazo tana rokon afuwarku,don Allah kuyafeni....kusani duk sonku ne yajawo haka...”


kukane me k'arfi ya k'wace mata sosai jikin kowa yayi la'asar sai yanzu suka fara jin kewarta.a haka ta amshi nata kyautan farouk nacan wajen audience yana aiko mata da confidential look.




Log book sukayi,cike da jimami suke daukan numbern friends dinsu da contact address dadai sauransu.


A washegari sukazo yin walima,Aisha kam dai² da k'aramin yaro saida tabashi kayan surveillance nata Wanda rabi da kwata duk farouk yayi mata su.


Kuka wiwi haka suka ringa yi ,aka d'auke su hotuna da malamansu prefect din da suka maye gurbinsu da 'yan ajinsu


Daganan taro yawatse,kowa ya kama gabansa da 'yan uwansa,sai fatan samun kyakyawar sakamako.






Manage please
~*Hassenate*~
*★★BAGIDAJIYACE★★*
•★
By Hassenart bamalli
•★


09065990265


*One of the five Za6a66u of 2020*





~Bagidajiyace,Isn't for free.kibiya #200 na katin MTN ,inkuma VIP ne #300…Bazanyi tsinuwa irin na sauran marubuta ba,gamasu karanta littafi ba tareda sun biyaba,Saidai kowa yasan daidai ai,so we are all matured enough~








_____________________________


38-39


Cikin farinciki su Aisha suka dawo gida ,Maryam ma qanwar farouk tashigo tayi masu congrat, tareda su dadyn farouk ,duk da itama dawowarta kenan daga makarantan su,dayike ita boarding ne na nan Queen ameena ,gida kam yacika kowa na tayasu murna.


“Yaya wai bamu gane bane,kowa ya wani saki hannu rabbana ,andawo gida an zauna ,mu bazaku yi mana party bane ko yaya ?”


“Wane mu Anty Ashmer, kin tari numfashin mune ,amma dama akwai get together dazamuyi na school friends d'inmu,kunga sai mu Had'a da naku,ko yakace chief Aesh of mar?”


Balla mai harara umar yayi ,yana nuna masa iyayen su dake zaune a falon.


“Hm, I see”


“Oho maku dai,ko yayane dai muna nan muna jira....Ku Ku tashi muje daga ciki”


Su Hassana ne suka mik'e tsaye, itama Aisha tamike ta kamo hannun maryam suka shige d'akinsu.


“Kunsan menene babes ,yanzu fa mun shiga freedom shadow, bamu ba uniform so,mun zama manyan babes sai mu chanza ma kanmu sunaye na mata masu aji and mu fara kula bf amma banda 'yan yungu² wa'inda bama a dad'e da share masu hanciba”


Dariya gaba d'ayansu suka saki,suka tafa


“Wohoho,Anty Aisha shi yasa muke sonki wallahi ”


“Kunga irin taba,wai anty Aisha salan Ku koremun customer a aza ni d'in tsohuwa ce ko...”


“To aike an rigada an sallama ki,ke d'in ta yayanmu ne ,mu dai ne zamu he searching ”


“Maryam ina ganin ki kamar mumina...aifa kinci sunan ki mero kunama,to ai kema dai gab muke jira mu warwashe musha bikinku da gadanga ikon Allah ”


Zaro ido tayi waje,ta dafa k'irjinta da sauri


“Serious,bama wannan wasan yaya haidar yayanmune fah”


Sai anan Hussaina tasaka masu baki


“ke wai bakisan yaya haidar na sonki ba...Ashe naku abun na munafukaine ,to ki rubuta kuma ki aje soon zai furta,much more inkina tareda mu anty Aisha zatana d'auraki a way”


“To nadai ji kumubar maganar, yanzu wani suna zamu sawa kanmu ne...nidai na za6i memxy”


“To ni kuma eashah kodai abar Aeshmar d'in, Hussaina hussy...”


Hassana ce tayi saurin katseta “karki samun sunan da bazai fad'u ba,ni kuma Hassenart ”


“Hm oho ma mutum komai sai ya nuna shi d'in bagidajene,yanzu dai mu ringa kiran kanmu da wa'innan sunayen yakukaga abun?”


Zasu bata amsa kenan, suka kutso kansu d'akin
“Hello,Topah,gija²n 'yan mata naji hayaniyar Ku tundaga falo, firan me kuma akeyi ne?”


“...Hiran yaushe gamo mana”


“Hmm,aifah to ataimaki d'an marayan nan mu Had'e a meeting point dinmu please ”


“worry don't ,on my way”


Mikewa tayi taje gaban dressing mirror tadan k'ara tulare sannan tajuyo “To babes bara inje in d'an zo”


“A'ah ai maza aje akula mana da yayanmu”


“Humhumhum,I reserve my comment memxy”


**************************************
Mashaallah get together ya amsa kar6uwan abokansu sosai ciki harda su munnir da yasir ,Aikam munnir Mr. Frank yana ganin Hassana ya k'yankyasawa farouk shifa yaga mata,yaseer nema ya d'an tsaya nok'e² don shi da farko ma Aisha yace yanaso unfortunate yasamu farouk da maganar nan ,yaga yak'in k'uhudu.ba shiri ya chanza shek'a zuwa Hussaina don haka yakasa taran abokanshi da maganar, wata dakakiyar zuciya ce tabashi 'kwarin guiwar ya tunkareta.


Hussaina ne a tsaye karkashin bishiya brankace na compound din hall din dasuke taron , receiving call din kawarta takeyi tana jiran isowarta gurin.


“wai where where you been since...anya kuwa zakizo dagaske anfakusa tashi...”


Sallama dataji a bayan ta ne yasata saurin juyowa.


“Laa ya yaseer,Kaine da kanka ?maimakon ka aiko a kirani in wani sako kakeso...”


“No at all,infact ni yafi kamata ,na zo nan din kinsan ance mai nema shi kebi,kamar yanda garin masoyi bayinisa...”


“Yaya bangane ba,wata kakeso ne a garin namu?”


“Hussy ,letz sit first?”


Nan yayi ta mata zuban plus ,sosai take kwasan dariya,tasaki jiki dashi sosai,a hankali ya gama yana ta ,bai kuma sha wani wuya ba ta faller gaba d'aya sai dai muyi fatan Allah yasa ya kaisu da aure amin.


Soyayyan farouk da Aisha kam kowa yarigada yasani a dangi shi kuma na haidar ne da maryam ake wai² don haka ,farouk bai koma port court ba saida yaje zuntu da rakiyar haidar dasu nan ya je gaida surukai😜


Had'a kai haidar da farouk sukayi kan result d'in su Aisha nafutowa zasuyi wuf dasu.dawannan plan d'in suka koma garuruwan aikin su.








_Don Allah kusani cikin addu'oinku wallahi am seriously ill though nafara samun sauk'i tunda yanzu hakama ina receiving drip...kuma naji k'arfin jikina ba laifi, but still I will manage ma self to post you a day even late...hope yhou will understand me better_
*★★BAGIDAJIYACE★★*
•★
By Hassenart bamalli
•★


09065990265


*One of the five Za6a66u of 2020*





~Bagidajiyace,Isn't for free.kibiya #200 na katin MTN ,inkuma VIP ne #300…Bazanyi tsinuwa irin na sauran marubuta ba,gamasu karanta littafi ba tareda sun biyaba,Saidai kowa yasan daidai ai,so we are all matured enough~








_____________________________


40-41


Sakamakon ssce nasu Aisha kam saidai alhamdulillah ,jamb ma yayi kyau saidai ba'a barsu sunyi applying wani makaranta ba ,akayi engagement dinsu with short date saboda ba'ason ya matsu shekaran karatun su,kar suyi missing admission a shekaran...munnir ma ya harraqo da nasa magana don haka dad uban Ango da amare, jama'u yayi yasa date din bikin su uku harda Hussaina duk da, da mum ta tambayeshi dalilinshi nayin hakan,tunda Hussaina ba tsayayye garetaba sai cewa yayi ai kafin lokacin itama Allah zai fito mata da natan.


Shikam haidar sai yaja k'afa nasu tukuna acewarsa agama da kwamacalan su Hassana tukunna,inyaso zaiyi ma maryam applying A.b.u ita tafara karatun ta .


Hm. Ta6angaren farouk kuwa acan pourt court.
dama tun tuni kafinma su shiga office akwai Wani training ne dasuka so zuwa a Hong kong na shekaru biyu da haidar da farouk sunjima da applying but shiru,ba tsamani ganin shiru kawai sai suka fara aiki


Shinefa sunanshi yasoma fita saidai sati biyu jal aka basa yaje yagama shirin sa yatafi




Baiwani ji murna ba due to damuwoyi biyu da suka zo masa,na d'aya bikinsa dazai prolonging, na biyu haidar da bai samuba,shiru kawai yayi kowa bai fadamawa ba gashi baida certainty din wajen su za'a yarda masa ma yaje.


Bai fara samun appeasement ba saida haidar yakira sa yace yasamu amma ta hanyar na munnir don haka Germany ne,kuma ma bazashiba tunda farouk bai samuba,shine yake fad'a masa ai shima yasamu ta hongkong din yaki sanar ma kowa ne because of that reasons.


Sosai sukayi murna sai fatan yardan manyansu


Office din shugaban su yaje da request dinshi,reluctantly don yasan ba lallai a amince ba


Saidai alhdulillah baisha wani wuya ba a wajen dayake aikin duk da kasancewarsa na sabon fara aiki.


Forms akabasa yayi filling yaje yafara clearing komai wajen manyan su


Daganan yasamu akaba sa releasing letter, daga depot din nasu a yau, zaiyi kamar inservice kenan with his full salary.


don haka zumud'inshi ya kasa 6oyuwa a ranar ya taho gida don fesawa iyayen su shima tasa albishir din.




Aunticulovanty shopping mall yafara biyawa,yaje ya dank'arowa Aisharsa English wears,agoguna da fashion bangles kowanne kagani designers ne.kundaisan kaya irin na port court .


Daganan yabiya oriyopose junc ya saya masu wayoyi dukkan su suhud'un iri daya saidai kowa colour din nata ya banbanta.yasaimata mini laptop tunda yasan bata dashi.sosai dai yayi tsaraba.yabi flight dondai baya iya endouring speedy driving.


Cikin kakinsa yazo looking very giant, gajiki yayi fresh Hutu da naira sun fara hudasa,dama kowa bai sanarma zuwansaba he's trying to surprise all of them ne,shi baimasan haidar was already yana a garin ba.


*Aviation*
Jirgin nagama tsayawa a filin jirgin fasunjojin ciki suka shiga fir fitowa,


Farouk nahanga fuskarsa da dan annuri but atamke,sanye yake da farar T-shirt da wandon kakinsa,bakomai a hannunsa sai jakar laptop dinsa rataye abayansa ,fuskarsa manne cikin shadow goggle ,kunnensa mak'ale da Bluetooth .don haka kallon farko bazaka kawo masa saukin kai ba kwata².


Sakkowa yayi daga matakalar jirgin yaje can reception yasama waje yazauna,har kayansa aka fito masa dasu,yayi hayan taxi ya wuto gida.




Taxi din daya dauko sa daga airport din na zuwa yayi parking a k'ofar gidan,yaje yayi knocking gate din ,saida aka jima kafin wani soja yazo yabude, arude ya k'ame yana furta


“Sorry sir,sorry for our delay”


“No at all...kindly open the gate please ”


Jiki na 6ari ya hau tura gate din ,shi kuma yajuya wajen taxi drivern yace su shiga dashi daga ciki.


Shock yad'an yi bai maga girman gidan yakai har hakaba saida yace yashiga.


Tunanin yanda zai arta yakeyi saidai kuma ga zaratan sojoji bisa kansa...“.oh ni ayuba kowa da inda ajalinsa yake nikuma Ashe sanadiyyar taxi zan halaka...amma gaskiya da in shiga wannan mansion gida ,gabadaya glasses wannan yana reflecting ta jikin wannan ga green flowers kota ina kowanne tidy yasha aski,anya!billahillazi gara in kwatanta sa'ata Allah ma yace tashi sai in taimakeka...inmadai sun kamani daga karshe anyi fawana ,bazance na tsaya kamar kisan 6era ba....”


“kai you waste my time...will you common key the car and go....mtseww”


Tsawan da farouk ya d'ad'amasa ne yadawo dashi hayyacinsa


“Alhaji...uhmmmm malam kaiwa darajan tsoho da tsohuwa ni Ku k'yaleni ,wallahi ko kun yanka ni namana baxai maku gard'i ba,a wahalce na tashi rogo mukeci sai su kwaki bawani sinadari mai Gina lafiyar jiki da zaku samu a wajena”


Takaicine ya k'ume farouk Sam shi ko jin mema yake cewa beyiba,don haka yamutsa fuska yayi sannan ya gyara zaman gilashin fuskarsa


“Kai me kake nufi?...wai you mean can't go inside as I instruct you?”


Daddalaro ido yayi waje kamar na kyanwa ,don dai shi beji me yaceba,d'ago kai yayi yaga fuskarsa kem a kansa,da sauri ya gyada masa kai


“Eh offisa haka nake nufi”


“Hiye bala'i.... Ko a barrack an isa ayi mun haka....yanzunnan nasaka kayiwa kwaltan nan cakulkuli...wuce kashiga dani...”


Salati yashiga yi ,wani dabarace ta fad'o masa


“To shiga mu shiga ”


Ai yana shiga yayi fit,ya fyalla a guje yabar motar anan da key din ajiki.


Dariya ne yaji ya tunnuk'e shi haka yashiga dariya yana kiran sa ina ko walk'iyarsa bai ganiba yabar street d'inma


Shiga yayi ciki suma masu gadin da basu San meke faruwa ba,suna nasu dariyar


D'aure fuska yayi
A futar mun da kayana nacikin boot d'in taxi d'innan, sai kuje anema mai motan nan


“I seem naga I.d card nasa... So sai ku tafi wajen en union dadai duk inda zai zama joint na taxi drivers,then if you find the client you give him this... ”


Yaciro kudi mai yawa ya basu subashi,sannan yawuce yana cigaba da dariya.


Yana sallama a falon disko kawai yaji ya haye masa kai mai d'auke da amon wa'kar rihanna




Aisha, Hussaina da maryam duk suna kwasan rawa cikin vest da gajerun wanduna.Hassana Miss m.c


Ko jin shigowar sa basu yiba,maryam ce taji kamar k'arar bud'e k'ofa, da sauri ta waigo ai tana ganin sa ta tsaya tana tsuru² da ido.


Aisha kam,zillo tayi tana fad'in


“Hassana off it,bara kiji nayi maki rawar da wa'kar a had'e kiyi count zanyi wak'okinta kala goma kowanne da kalar rawarsa.....now ”


Ba musu ta kashe suka koma suka zazzauna harda maryam dake masu alama ko ganin ta batayi ,shi kuma can kujerun dinning yasamu yazauna yana kallon ikon Allah


“....shine bright like diamond....(oh wait bara kuji inda yafi birgeni though kunga ai wa'kar diamond is old)....I too see you ,when ease very well,hmmm very well....every sky light form energy when sure that....”


Sosai take rawa ,exact like na rihanna,tana wani k'ankamewa kamar bata da k'ashi a jiki


Maimaitawa yake a ransa yaushe yaran nan suka zama hakan...amsar dayadawo dashi cikin hankalinsa shine Hutu da zaman waje daya ba school ba kwa6o


Gyaran murya yayi
“Foolish girls,yanzu masu shirin shiga wai jami'ah ne suke wannan... Imergine wai Ayshahh na mimicking wak'a an ma gaba daya bama daidai take yiba,dama Ashe abunda rihanna ke cewa kenan....Ku kuma kunsaki falafalan kunnuwa kunajinta with full of expression.... Zanyi maganinku ne dani kukeyi....”


Kuka suka saka masa irin na ta6ararrun en mata


“Yaya ba ruwan mu Ayshmer ce kad'ai ”


“...Heyeye wato Ashmer bola to wallahi karya ne dukkanmune...musamman ku memxy da hussy...kune ma kuke koyamun rawanfa...Ku fad'i gaskiya”


“A'ah Anty aisha karki jamana wahala fa”


“Dayalla kuyi mun shiru,kuna Neman fasamun kunne uwa kaji....tsai² ni bansan rawar gwana bane.....inasu mum suka barku kuna wa'innan abubuwan ....I think bazaku rasa zuwa night party ba”


Yafad'a gabansa na dukan tara² wani zazzafan kishi yaji yana Neman shak'e mai numfashi


Farfar da ido Aisha ta hauyi tana murguda baki
“Farouk karkaga muna baka hak'uri kayi mana sharri fa kowa Allah yana rufa masa asirine ,gwanda mu rawa kadai kaganmu munayi,wani fah?....”


“.....ke dayalla meye haka ,aha k'ok'arin lalla6awa mu rabu lafiya kuma....yaya wallahi kaji mun rantse bamu ta6a zuwa wani party bama indai ba na birthday ba kuma shima duk inda yamma tayi driver zai dawo damu gida,so please we are seeking for pardon Albarka cin kakinka”


Murmushi yayi,kawai dondai dama ba abunda zai iya masu ,asalima wani special feelings yakeji akan Aishansa har every thing is cute and adorable ”


Lumshe ido yayi “oya aje akira mun mummy ”


Had'a baki sukayi
“Suna gidan mu,relatives din yassar d'in hussy sunzo za'ayi masu...”


“ohkk,yanzu nagani,wato celebrating kukayi ko...'yan fici² Ku daku?”yanayi yana k'arewa Aisha kallo,tareda kashe mata ido ,baisan duk sun ganiba.


K'unkunai maryam tashiga yi

“Kajima yayan nan d'an San kai yanaso shi kuma baison wani shima yashiga layi”


“Ehye me kikace?”


“Laah yaya bance komai ba ...kawai nacene ,great yaya highly welcome ”


“ku tafi da gulmarku” yawuce hanyar belcony dinshi dake a left hand side,inda zai sadaka da part din sa.


Yana wucewa sukayi maza suka tattare drinks da snarks din suka gyara wajen ,sukayi hanyar matakalar dake hannun dama part din mum da maryam kenan


A gado suka watse suna dariya
“waik yau da ya caule mu da belt...to waima me yadawo dasune zasu fara takuramana kenan fah...Allah yasa ba dad'ewa zasuyiba”






Farouk kam wanka yayi yashayo wankan sa,cikin simple kaftan sky blue na yadi filtex maras nauyin,ya taje ya taje gashinsa,ya saka mayukan gashin ,ya fesa turarukan sa.shar yayi dakaganshi kaga matshi da komai ke kaimasa.


Wayar Aisha yayi dialing,suna can suna zuba buhun shiririta saiga ki ransa,tunda taji ringing tayi mu'kus tunda tasan ringing d'insa




A hankali taje tayi picking.
“what is available a dinning ”


“Uhm,uhmmmm ...yaya saidai dambun nama da snacks iya me girki d'azu jikanta ta haihu ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login