Showing 3001 words to 6000 words out of 25578 words

Chapter 2 - Bagidajiya Book 2 Complete hausa novel by Haseena Muhammad .txt

01 Dec 2024

1200

taje wajen kujeran ta tadaka dak'arfi da k'afanta ,tusssh takimu a k'asa uwa buhun flour


Tajanye kujeran tayi zamanta tana k'unk'unai "Wato Ku Baku iya tarban bak'ibako....to kujeran ki nakeso"


Wage baki tayi tasaka kuka


"Ehehehh,what is all these? Isn't she a new comer?"


"Sir wannan ba new comer aka kawo manaba aktuwace" gaba daya ajin suka bashi amsa


"To dan uwarku basai Ku koreniba..."
Tafad'a tana hura hanci


Fita ajin malamin yayi ya wuce office din p.c yakaimata k'arar sabuwar zuwan "


Dakanta tazo ajin dasauran staff sukaja kunnenta ,sukace sun d'aga mata k'afane saboda ita sabuwace .




Ai kam tunda wannan abun yafaru ,inyamuran ajin suke tsoron ta,abinka da inyamuri sarkin tsoro,suna na musamman suka samata wai *Oga senior*


Tana kuma alfahari da sunan ,tuni sunan indo yafara 6acewa acikin makarantan kowa babba da yaro kagani a makarantan bakinsa ya rik'e oga senior .


Ita kanta tanada basawa masu tayata cin k'aniyar yaran mutane kuma su kansu badon Allah suke biye mata ba tsorone kawai.


Tunda kaf tsoron ta akeji ,tundaga yanayin ta ma dashigarta,da kalar hausanta zakasan wannan she's badly barbaric tafita dabam cikin d'alibai.










Haukanta kam kullum zuwa ma 'yan ajinsu sabo yakeyi,kuma Sam bata gogewa,makarantan fa dai yana bama indo pepe to in aka kama mutum yayi Hausa akwai taran kud'i ,arana sai aci taranta kaf kudin break dinta sannan abita bashi ,goben ad'aura akai.


Tayi jaraba tadaki 'yan ajin masu alhakin anti vanacular din,har tagaji don kanta.


Don Dole tafara koyon magana da turanci.


Wata rana sun fito break kenan ,rep.din vanacular tazo wajen indon "oga senior,ana binki #80 na vanacular"


"Ke dan uwarki ban dashi dagani sai wannan naira Ashirin d'innan..... To ko bazan Baku inci shiru ba, don haka ,kuyi yungu yungu da naman jikina kukasa kawai,nonnnnseeee kawai"


Fakam² tawuce school canteen d'in kusa da wajen. ta nunama matar eggroll ta cikin glass d'in dake ta waje²n Shagon.


"Madam cincin,ina buk'atar ta Ashirin"


Matar ne tataso tana k'arewa kudin hannunta kallo


"Student, bana saida chinchin"bayerbiyan tafad'a da gur6ataccen hausan ta


" ha'ah ya ina kallon chinchin gashi,kice babu ?"


"Eyyah, wannan ba cincin bane eggroll ne ,kuma naira d'arine ba Ashirin ba"


Rik'e baki tayi tana jinjina kudin,sannan ta kwantar da murya kamar saliha


"Madam ki taimakeni don Allah, kibani bashin k'wara biyu,kwarankwatsa fareti yanzu haka akemun aciki,jinake uwa ana watsan tiyagas ahanjayen cikina....ki ceton rai billahilllazi gobe ina zuwa zankawo maki.....
Cutan makarantan nan zai haifarmun da laluran k'onewar hanji...
Kullum sai an yimaka k'wacen kud'i gashi sai yamma lik'is muke komawa gida ....
Kiyi tunani baiwar Allah"




"Allahu sarki ,kinban tausayi yarinya...kin dai yi alkawarin ko?"


"Wallahi nayarda nakuma sa6a laya,zanbada gobe...badai d'ari biyu kenan ba kawai?...zan biya"


Egg roll din taciro tabata takar6a tana k'wafa




Tun daganan indo ta d'auke k'afarta tama hanyar shagon mata,mata taji shiru²indo bata kawo kud'iba ,sai ranan taga wulk'awarsu dawasu gungun students kafa bututu takalmi,a hannu da k'atuwar k'wallo wai sun dawo match


Dasauri ta aika yarinyar ta dabazata wuce shekaru gomaba taje ta amso mata


Tunda ta hango zuwan yarinyar ranta ke tafasa
'Ya bata saniba tagama ingausan Hausa da turancinta agaban indo ,bataji tace komai ba,d'agowa tayitasake maimaita mata maganar amsar bashinsu


Wani wasu fararen wuta tagani mai tartsatsi cikin idonta tagani daganan kuma taji d'if duhu ya gauraye ganin ta,


Wani kururuwa yarinyar tasaka tsabagen gigicewar Marin da indo ta falla mata


Kururuwan yarinyar ya ankarar da uwar kanta wajen su


Afusace indo taba basawan ta umurni
"Sama da ita"


Cak,cika cicci6eta suka d'aga ta zasu danfarata ak'asa


Matar hannu tasa aka takurma ihu"jama'a zasu kashe mun yerinya seboda Dari biyu"


Ina har sun wullota k'asa !caraf farouk yarike ta yana maida numfashi tsabagen gudun dayasha.




"Indo nanma laluwan kika zama masu?!....jiku kukuma tik'atik'anku daku kuna daka ta wannan BAGIDAJIYAr ,ballagazan....dawayewarku da iliminku ....To inma bakusani ba kusani kuma duk kallon da ake maku kenan.....haba da iliminku kuna bin JAHILAR 'YAR K'AUYEn nan, karku sake kulata kota maidaku gidadawa irinta!




" Ummaru nikake ciwa zarafi,agaban 'yan cikina,ai ko dai zan nuna maka halin BAGIDAJIYA....bakaga cin fuskar da yarinyar tayi munba kenan ...don mutane na sun Nemi k'watar mun 'yanci shine laifi....? To muzuba ni dakai maga masha wuya"


Kuka wiwi tawuce tanayi kullum ana kiranta bagidajiya,bata ta6a jin haushin hakanba sai ayau


"To kodai nid'in BAGIDAJIYACE ba sharri suke munba?"




Wani tausayinta ne ya d'arsu a ransa nan take,dafari yaji zafin cin fuskar da tayi masa a gaban yara saidai kuma,hawayen da yagani a idon ta ba k'aramin dukkan zuciyar sa tayiba...


A Iya zaman shi da ita yaune rana ta farko dayaga hawaye a fuskarta, duk da har jibgarta ya shayi,to mai ya tunzura tane haka?




Jan k'afarsa yayi zai bar wajen, da sauri bayarabiyan ta dakatar dashi


"Sir,naga kamar kai yayantane,plz adinga yi mata fad'a ....bari kaji abunda fa ya had'amu da ita daga taimako....


Nan tazayyane masa duk yanda sukayi da indo akan eggroll dahanata kud'in da tayi




Hak'uri yabata yaciro kud'i 'yan hamsin² sababbi katakal acikin rafarsu ya 6allo dadama yabata .


Bai tsaya jin storyn godiyarta ba,yayi tafiyarsa.


Office din p.c yatafi inda yabar haidar yafito siyan recharge card


Anan ma k'orafin indo sukaita amsa,amma a maimakon farouk ya zak'e yayi ta masifa ,shiru yayi yana saura ran haidar yana basu hak'uri, sukuma suna kara hutsewa adole zasu d'auki mataki




Tunzura farouk yayi yahau bambami




" waikai haidar meye kake wani loveying d'insu ,bakasan human rights din ka bane?....


....bassu suyi duk abunda zasuyi Aysha haka take,responsibility dinmu ne mukula da gyaran tarbiyyan ta bakuba....


.....Sannan dole kulalla6amun k'anwa tunda kunsan dai ba inda doka tabaku hurumin ko dukan d'alibi bare cin zarafi....


In tayi badaidaiba mu zaku kira ba Ku Ku d'auki matakiba....


Gameda anti vanacular asaurara mata kar Wanda yakuma kar6an mata kud'i ....failure to follow my instruction wallahi sainayi k'aranku,kuma bazan janyeba ,sai naga an kulle makarantan nan...


So inkunga baza Ku iyaba kuyi magana,you're not the only private school here in Zaria sai acanza mata wata"




Tsumi haidar yayi shaye da mamaki,anya farouk dinne kuwa?....farouk dinda yatsani indone zai dinga bala'i akanta?...




Hakuri management din suka koma bashi tareda alkawarin kiyaye dokokin daya kafa masu


D'age kafad'a kawai yayi masu,alamu ko a jikinsa tashi yayi yafita .yacema haidar inya gama zaman yasameshi a mota




Indofah tana 'yan wanne?




*KARKU MANTA FA!*
*Littafin nan yana cikin gwarazan zab'ab'b'u biyar .na kungiyar hikima writer's association,Wanda siyanshi zaisa ki zama cikin zab'ab'b'u fans,sauran littafan sun Had'a da:-*
*ANYA KUWA! Na ummy 2018,YAKIN MATA Na fateeyzah, YOUSUF Na zulaikhat Aliyu misau,da RIBAR HAK'URI Na Aisha y.hanwa.*


*My friend karki bari wannan damar ta zababbu tawuceki,littafin nan gadad'i ga saka nishad'i, namu ba irin gasu bace akwai sauk'i daidai misali.*


*In zababbu guda biyar d'in duka kikeso zaki biya #500, guda hud'u kuma #450,zab'ab'b'u 3 #400 ,zab'ab'b'u 2 #350 , Idan kuma d'aya kikeso #200 ne kacal👌*






Zaki biya tawannan account number
Fatima sani Muhammad
Access bank
0796627818




Idan kuma ta katin waya zaki biya ta mtn ko airtel ,to zaki biya ta wannan number 07032266778.




*Comment and share please!*






*Hassenart*✍🏻


Typing〰️〰️〰️〰️💻📲










*♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️BAGIDAJIYA♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️*






___________________________________________
*©️HIKIMA WRITERs ASSO.*
*(Home of peace, joint entertainment to educate and enlighten our readers)*
___________________________________________






Story and written by✍🏻
Hassenart Mohammed😍
☎️090 -659 -902 -65.






*MARUBUCIYAR*
*RAYUWAR AFREDARH*💔💯
*QASAITATTUN MATA*👸👸
*RAMUWAR GAYYA*🩸😫
*and now*
*BAGIDAJIYA*😂😁




*Bagidajiya 2020,* isn't for free ,pay only #200 of MTN and enjoy your reading safely
Then if it is VIP that one is #300.


~*Dedicated to my fans*~




...........Kar kiyi share plz..........




21-22




'Yan ajinsu indo kam kowa ,zuciyarsa na a k'umbane,d'ari² suke da ita,don a iya zaman su da indo yaune rana tafarko da suka ganta tana kuka haka wiwiyy.


'Yan biyu da kansu ,sukazo seat d'in ta suna rarrashinta, suna tambayarta ko lafiya?...
Basu amsa kawai tayida bata jin dad'i ne.
"Sorry indo taho muje dispensary,kisha magani"
"A'ah ki barshi kawai innaje gida nasha"
Ganin ta tubure yasa sukaje suka kira health prefect
Da lallami da ban baki suka shawo kanta ,taje aka bata paracetamol jin dumin da jikinta yayi,ga fuskarta da yayi jajur ya kuma kumbura ,tsabagen kuka,abunka da fari ya sha daunin datti ne😁


Ana kad'a k'ararrawar tashi tazargawa karenta igiya tuni ta rigasu shiga mota
suna zuwa,suka nufi gida.d'akinta tatafi tana shiga dakin gadonta tafada,ko takalmi bata tsaya cirewaba, takuma rushewa da wani saban babin kukan.


mom faty ne tashigo d'akin hankali tashe ,jin taji shigowar kowa banda nata , shine da tatambayi 'yan biyu suke shaida mata wai tace bata da lafiya ,kuma sai kuka take


A ko wannan yanayin tameta ,da sauri ta karasa kan gadon ta jawota ta rungume
"auta waya ta6a minke?....ki fad'a mun auta,kinji inna barki banji damuwarkiba kamar naci amanar su mamane
...ki taimakeni kinji 'Yar k'anwata"


Sauke ajiyar zuciya ta ringa yi a jejjere,kamar numfashinta zai d'auke ,saida tajima a haka sannan tahau Koro mata bayanin tozarcin da farouk yayi mata a bainar nasi tana fada mata murya cike da shashek'a ta d'aura da cewa
"Anty cikin jama'a fa yanuna ni yakira ni da ballagaza,bagidajiya,waye waye....anty dagaske ni d'in bagidajiyace,kuma na cancanci aringa hantarata yanda farouk da Hussaina sukeyi mun?.... Anty wai me Nike yi yasa ake kyarata?"


"Ki kwantar da hankali nki,auta ke d'in ba BAGIDAJIYACE ba ,hasalima shar kike bakida ko k'irar Allah ya isah,abunda nikeso kisani shine,wannan rashin natsuwar bataji bace,idan kinaso ki canja ki soma kwaikwayen yanda kikaga Hassana keyi,zaki bawa kowa mamaki...ki zauna Ku tattauna da su nasan zasu so kizama kamar su ,suma"


Nannauyan numfashi ta sauke,daganan tace"anty turo mun Hassana muyi magana "


"To auta tashi kicire uniform d'in ki,zan aiko maki da abincin ki nan"
Jinjina Mata kai tayi kawai


Haidar da farouk suna shigowa falon inda indo take zama yasoma kalla ,yaga wayam!
Afirgice ya juyo yana kallon Hussaina "kardai yarinyar nan takoma garin sune ,dako tabbas zanabita har can nabata hakuri,bazanso ko zata bar gidan nan ta bari a sanadiyya ta ba." Da wannan zancen zucin, ya jefo ma Hussaina tambaya


"Ke ina bagidayar gidan nan na wai?"


"Yaya tanafa ciki bata da lafiya"
Zaro ido yayi tareda fad'uwar gaba
"Me yasameta?"
"Ya mumafa bamu saniba...tun a makaranta dai take kuka"


"What ?...muje ki kaini in ganta"


"A'ah fa farouk kunasa ma k'anwata tsama...to tace Kaine nan kayi mata laifi...afa kiyaye ma auta shiru²ba tsoro bane ,ina lura dakai da Hussaina yanda kuke mata cin mashi...zanko fara tare mata tun daga yau"


Mom ne take mayar masa da martani cikeda ba'a.


Sosa k'eya yayi cikeda jin nauyin mom d'in
"Afuwan mom,inshaallah we will change a new leaves"


Yajawo hannun Hussaina ,suka wuce d'akin indon,tunda yasaka k'afarsa a d'akin cikin sa ya wani hautsina jikake "gurrrurr", wani tsamin kayan wanki da wani k'arni , ya soku mashi ,dasauri ya toshe hanci ,cikin in'inar magana da baisan ya iyaba ,yake cewa Hussaina ta rarrasota su had'u a falon k'asa kawai.yana kaiwa nan ya fita da sauri.


" hajiya indo ,yaya yace kifito zakuyi magana, so don Allah karki mai tozarcin da kika saba don kinsan shima d'in ba kanwan shafa bane "


Bani da lokacin ki Hussaina daga ke har farukun kuje da halinku Allah ya isah...amma yanzu dai inaso nima inzama cikakkiyar mace...abun alfaharin kowa"


"Toooo,lallai su indo an musulunta wannan abu haka...sha zamanki ki kwashi warinki har ki godewa Allah, bawanda zai cigaba da biye maki acikin d'akin nan inba Wanda yakeso ciwon hanta yazama ajalinsa bane...."


Juya wa tayi cikeda gatsali ta kama hanyar fita,sufa tayi ta cafko wuyar ta,shak'eta tayi tamanne ajikin garu kakari ta shigayi ,idonta duk sunyo waje....


Ihu Hassana ta tsandara ta zube kan guiwoyinta tana kuka,tana rokon ta saketa


Ihunta ya jawo hankalin kafatanin 'yan gidan ,shigowar su yayi daidai da cilli da ita da indo tayi ,sakamakon jin magiyar Hassana


Watsewa tayi a wajen tana sauke numfashi na azaba


"Kad'an ma kika gani ....hegiya wato kinga giwa ta hwad'i dole zabbi suyi hwareti akanta ko....to kwarankwatsa tallatsa kika kuma yimun rashin kunya sai naga baki numfashi...."


Kota kanta Hassana batayi ba ,bare taji mai take cewa har ta fakimta,dasauri ta rarrafa jikin Hussaina ta fada jikinta yaraf tana kuka.


"Twiny nafad'a maki kidaina tsokanar indo kink'i jiki....ranar da ta kashe ki shikenan nima sai in hadiye zuciya nabiyoki....don haka don a llah ki rabu da ita plz"


Itadai Hussaina babaka sai kunne, kwakwaran motsi takasa yi.


"Lallai kin burgeni Indo duk shegiyar da tamaki ki maujeta nabaki go ahead.....zasu gane akwai banbanci tsakanin maciya tuwon dawa Dana semo


" Nagode gadanga...kukuma lafiya akai mun fird'i²a d'aki... Kowa yaje uzurinsa mana"


"Da farko indo INA mai baki hakurin duk abunda mukayi maki ,musamman ni da Hussaina... Koma inaso yan cikin dakin nan Ku shaida cewa nayi ladama...and inshaallah hakan baxai kuma faruwa ba"


"Ciftsi nannagi ashe fa!?to kenan kanaso kacemun yanzu kazama na Allah ne bayan kwance mun zani d'azu dakayi a kasuwa?"


"Ayshahh...kiyi hakuri kuma wallahi ba saboda rikicinki da Hussaina bane yasa jikina ba yayi la'asar ba....ki tambaya haidar shidin zai iya zame Mani hujjah... Wallahi har concrete warning saida nayi wa kaf management din makarantanku,inkuma na fahimci matsalar ki da kyau training kike bukata ba kyaraba...kuma da ikon Allah zan yi iya iyawata har sai kin gyaru"


"Nako gode farouk Allah ya kuma shige mana gaba" momce ta kar6e maganar cikeda gamsuwa.


Komawa indo tayi ta zauna da6as akan gadon ta,jin sun cigaba da damun ta yasa ta kwanta a gadon tahau baccin karya,dole kowa yayi takan shi


Farouk ne har sun fita yad'an dawo,daidai fuskarta ya tsaya


"Inkin gama abunda kikayi ,inada maganar DA zamuyi dake....so, kisameni a garden nanan gidan."bai jira Cewar ta ba yafice
*********************************
*Garden*


Umar na hanga zaune nesa kadan da Aisha da alamar dai wani abu take fada masa muhimmi,tundaga natsuwan da yayi with rapt attention,tarkato takarduna nayi dagudu inacewa'oh ni Hassenart ko me sha tattauna kafin inzo oho'






"Kanaji nako...
A garinmu ne,akwai wani mai shigen halinka,amma fa shi nashi yafika don be tsaya kallon hotunan banzaba harda yi a aikace...shi ma hojane...amma irin masu yin gadin nan a gidajen bunni.....


hikenan ,hikenan watarana naje gidansu zan anso dashie d'ina a gidansu wajen suyud'i....


...indodo da lek'e lek'e nako shige d'akin zauren danaji kamshin indomie yana tashi,indo da kwadayi baki na yoyo kafana nakuma cusa jikina ciki,dakatawa nayi ganin mutum dawata busashiyar yarinya mai suna hamamatu nayi tim6ir suna iskanci,a lokacin anko samusu rana daita.....


Cikin gidan nashiga dagudu naje nasama uwarsa atsakar gida cikin taron matan gidan ,ina haki nafad'a mata komai,dukko 'yan gida aka tafi yuuu d'akin, rangad'a salati sukayi Niko nasulale nagudu...


Haba tuni magana yawatsu cikin gari wai shamo soja yana lalata da hama...kuma wai ko abunni haka yakeyo hayan iyayen karya ,inyanason yarinya wata har sai anyi masu baiko ,sai yayi lalata da ita ya hwatse....


aiko watarana naje shagon ya'u d'an tireda,na hadu da k'awata rahane a shagon nan nahau fesa mata labarin dukda naji gameda shamo dakuma kamasu da hama danayi dumu²


Ashe bansaniba abokin shamon yana cikin 'yan siyayar k'ofar shagon


aiko dare beyiba sai ga shamo a zauren gidanmu,kantara sallama yashiga yi da iya k'aran makoshinsa...


Habawa karkashin gado me rumfar mama nashige,yayane kishiyar mamanmu tafara fita ,jin yakawo k'ara nane dakuma ganin shi tik'ek'en kurtu cikin kaki yasa baki narawa taringa masa magana


"Wohoho,soji agidanmu,lallai indodo ta ta6o wa Audu ubanta bala'i, bawan Allah kahimili shegiya karka ragamata,inba hakaba zaka shiga jerin sullu6ayen mazan garin nan,kaiko yanda kake jinka turgujejen banasaren nan,zare mata ido kadai kayi zaisa ta tashiga taitayinta....hhhh hmmm...kasan abinka da Wanda yasaba da cin naman aladu...ai yasha banban damu, masu cin nabunsuru...."


Wani ihu yayi kamar inyamuri ,bai tsaya sanyan jikiba yakifa mata mari,dare baki tayi uwa na k'adduwa....aguje mamanmu tafito


Tsola yaya taganshi yanayi uwa ya samu ball yanayin soccer soccer,bai kyaleta ba saida yasadata da k'ofar gida


Hakuri mama tashiga bashi ,amma baisa ya sauraretaba....


Ai yana cimma bakin zaurenmu mama tayi ciki dagudu


Hankad'a murya yayi ya k'wala mata kira
"Baba come...I said come here,stupid brat...."


Dayike mama tana danjin turanci dawowa tayi ta tsaya daga d'an nesa


"Waye innan indo acikinku?"


"Nine officer"


"To kijama yarinyar ki kunne,daga yau har zuwa sati biyu masu zuwa ina nan a garin nan....indai naga wa'innan sillanlun kafar nata a waje saina karairayasu.....


Musamman nashiga kasuwa Naasa aka yan yanka mun bulalan Inji,duk wani kwata da kika sani a unguwar nan nayi ajiyar bulala na....don haka Ina ganin tafito kwata mafi kusa zan nufa in Ciro ajiyata inmata ragaraga da tsokan jikina ba fataba...


Dariya sosai farouk keyi,har tafi na sarkeshi
" uhm sai akayi yaya ya cafje kin..zanso hakan"


"Wa?...waini ai ban son ata6i lafiyar jinjina...takaban dole nashiga , har ya tafi .nima kuma ba'a dadeba na gudo nan....


" hmmm kice kinsha da kyar".


"Kaidai bari kawai ummari...muhiga daga hiki kar anty fatsima taji mu hiru "


"Hmmm indona kenan"
Azabure tajiyo
"Me kace?...naji kamar iska ya huro mun maganan ka wai kace indona!"


"Nikuwa...may be dai iskokin kanki ne suka daya maki hakan.....yawa wait indo wai dagaske ne kinada jinnu masu duka?"


"Ehman....kabari watakaron zan baka labari"


"Yawwa point of correction my dear ki fara gyara hausan ki, yakuma stylish irin nawa...kinji?"


"Ciftsi ,kana nufin yanda nikeda murya me dad'i d'innan immaisheshi irin naka,na gardawa fa kenan....balagaggun maza"


"Bahaka Nike nufi ba ayshah...even me I like your voice,salon maganar ki nakeso ki gyara,take for instant,in zakice sshhhhh,sai nice hihhhh, like shikenan sai kice hikenan... Kingane ba!?"


"Wayyo halshena kenan, ko a makaranta ,ana yawan tsokanana,takan magana ta...bayanda zanyi ne"


"Akwai yanda zakiyi mana practice koyan tunanin me zaki fada ,kafin ki furta....you will marvel belief me"


"Hikenan...farouku zan kwatanta ingani.... namanta shikenan ko?"


"Da kyau ...yaushe zamu kuma haduwa anan din?"


"Ha'ah kai kafada mana...."


"To gobe in Allah ya kaimu,please don't keep me waiting"
"Mene kenan?" ta fad'a tana duru² da ido


"A'ah cewa nayi ukuna prompt yayi mana anan OK?"


Gyad'a kai tayi masa kawai tatafi


Oh ni farouk meyasa nake daka ta bagidayr yarinyar nan ne?....kayi hakan mana don saboda makarantan su da ka cika masu baki....


Tofah yaya take ne dai farouk ?see me next






*KARKU MANTA FA!*
*Littafin nan yana cikin gwarazan zab'ab'b'u biyar .na kungiyar hikima writer's association,Wanda siyanshi zaisa ki zama cikin zab'ab'b'u fans,sauran littafan sun Had'a da:-*
*ANYA KUWA! Na ummy 2018,YAKIN MATA Na fateeyzah, YOUSUF Na zulaikhat Aliyu misau,da RIBAR HAK'URI Na Aisha y.hanwa.*


*My friend karki bari wannan damar ta zababbu tawuceki,littafin nan gadad'i ga saka nishad'i, namu ba irin gasu bace akwai sauk'i daidai misali.*


*In zababbu guda biyar d'in duka kikeso zaki biya #500, guda hud'u kuma #450,zab'ab'b'u 3 #400 ,zab'ab'b'u 2 #350 , Idan kuma d'aya kikeso #200 ne kacal👌*






Zaki biya tawannan account number
Fatima sani Muhammad
Access bank
0796627818




Idan kuma ta katin waya zaki biya ta mtn ko airtel ,to zaki biya ta wannan number 07032266778.




*Comment and share please!*






*Hassenart*✍🏻


*BAGIDAJIYA*
By hassenart bamalli
09065990265






*One of the five Za6a66u of august 2020*




Bagidajiya isn't for free,ki biya kudinki, don ki karanta ,littafin ki hankali kwance ,batareda kinci hakkin wasuba.🤗


Page 24-25


Sosai indo tafara gogewa,zama

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login