Showing 1 words to 3000 words out of 25578 words
Chapter 1 - Bagidajiya Book 2 Complete hausa novel by Haseena Muhammad .txt
Typing〰️〰️〰️〰️💻📲
*♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️BAGIDAJIYACE♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️*
___________________________________________
*©️HIKIMA WRITERs ASSO.*
*(Home of peace, joint entertainment to educate and enlighten our readers)*
___________________________________________
Story and written by✍🏻
Hassenart Mohammed😍
☎️090 -659 -902 -65.
*MARUBUCIYAR*
*RAYUWAR AFREDARH*💔💯
*QASAITATTUN MATA*👸👸
*RAMUWAR GAYYA*🩸😫
*and now*
*BAGIDAJIYACE*😂😁
Bagidajiyace isn't for free ,pay only #200 of MTN and enjoy your reading safely
Then if it is VIP that one is #300.
~*Dedicated to my fans*~
...........Kiyi share plz..........
Page 1️⃣7️⃣~1️⃣8️⃣
Gaza sukunin zuciya farouk yayi ai ba shiri ,ya zari makullin mota ya shiga kasuwa Neman dunk'ulallen k'uli da kwalayen sugar cubes .dole parking yayi a gefen hanya ya kutsa ciki da k'afa.
'Yan k'uli yafara shiga,cikeda k'yankyami ,yake jefa k'afarsa cikin surk'uk'in wajen ,kota ina ja6e ja6e da ruwan da 'yan kasuwar sukayi alwala.
Dakyar yaidasa gurun masu saidawa,ahanzarce ya Ciro 1k yaba wata mai saida k'ullin
"hmmm kima wa'innan almajiran sadaka please"
Yafad'a mata yana nunamata gungun almajiran da yatsansa.....haba nan yaga tsiyan da bai shirya ganiba ,buuuuu almajiran wajen suka yayya6eshi duk suka tattake masa takalmin sa dayasha polish.
Dak'yar ya 'kwaci kansa,yafito kasuwar,afujajan cikeda takaici.abunka gamai zuciya fasa sayo sauran sak'on indon yayi
Nan yayi dawowarsa gida
**************************************
Itakam indo d'akinta tashige zuciyar ta kwal kamar ranar sallah.
Daka tsaminta taje tadafko ,ta fente fuskarta tsaf da powder jajazir dashi,tajajja jagira har kusan kunne,ta dan6ara bak'i a le66anta nasama tazo ta jar6a jan jambaki ala66en k'asa
Nanfa fuskar yahad'e yadame,powder kam tsabagen jibgashi da akayi ,haka duk yabi ya daddank'are ajikin kwantaccen gashin goshinta Wanda har yaso had'ewa da gira,ga sajenta dasuka yi k'uda k'uda,kamar mutum zaiyi amai.
Dagani ba tambaya kasan zatayi gashi amma kana ganin yayya6in gashin fuskarta kasan yana alamta maka gashin baita6a samun alfarman relaxer ba.
Cukurkud'ad'd'un kayanta tasaka ,taje main falon gidan ta hakimce akan cushion k'afa d'aya kan d'aya,tana hura hanci adole nasha kyau.
Hankali kwance su Hassana dake kallon movies suka watse don sunsan minti biyu ,suka k'ara za'a iya jinsu da ita.
Dasallamarsa yashigo falon ,da fuskar indo yafara arangama,baya yayi dagudu yana duk addu'ar da yazo bakinsa
"Wa'innahu sulaimanu la'ilaha illalahu....
shaf ya sha'afa da hakan ne irin kwalliyar indon.
duk zatonshi ,aljanun kanta ne suka soma mashi siddabaru.
Shek'ewa tayi da dariya " honiiii! Hegiya indo,inci uwar maza in kwana gidanmu lakadan,saini mai ifiritai masu kawuna k'wal uku,yabaga baga yak'iluuu...."
Da azamarsa yabar gidan hankali tashe ,yana daf da fita gidanne shi kuma baba maigyara fulawas na kokarin shigowa.
Jin abune yayi masa kiki kaka agaba,aibai watawataba ya tokaras! Cilli yayi da baban nan kwankwason sa ya k'umu da get.
Wani salati yasaka mai had'e dakuka "wayyo shatuna,azara'ilu rok'onka nake kazare cikin sauki,allahu akbar ashe mutuwar saukine gareta....aljannah fiyy"
watsewa a wajen yayi war was!.kamar gawa yana fincikan numfashi da karfi adole shidin ya mutune
Waigowa yayi yana kallonshi yashe ak'asa
Amma ko tausaya masa baiyiba,asalima haushin jahilcinsa ya karana farouk tsantsar jin haushin sa
,cikin tsawa yasoma masa magana
"Alhaji inzaka tashi ne,katashi inkuma kwanciyar kakeso kayi,banida lokacin shiriritarka"
Dagana. ko takan sa bai kuma bi ba ya tsallakesa yayi waje harda k'arawa da d'an gudu,don karma su k'araso bai cika masu umrninsuba.acewarsa
Madara peak yaje yanemo mata da sugar kwalin kamar yadda ta buk'ata
Sannan yasamu k'arfina dawowa gidan.
*******************************
Gaba d'aya gidan fitowa waje sukayi ,cikeda tararrabi ,suka nufi wajen get din harda indon.
"Allahu akubaru,yanzu baba ummarune yayi maka wannan yankan kaunar...aradun Allah nine daidai shi dan k'wal k'aniyarsa bari yadawo zan muku maganin sa,kad'an yasoma gani daga kaidin indo...." Koro masu labarin abunda yafaru itada iliya a kauye da zana dayasha aga6as!
Tsuru tsuru kowa yashiga yi da idanuwa bawanda ya iyacemata cikanki
Tunda baba yaji zancen bulalai ,wani karfine yaji tashige shi,cikeda zafin nama ya mik'e yabar su nan .
Kodasu Hussaina suka koma d'aki tattauna matsalar suka shigayi.
"Hassana wallahi iskancin indone fa kawai na dauki zancen aljanun nan,amma bawasu aljanu....don haka bara ya farouk din yadawo nida kaina zan warware masa komai....batasan kantsiya ba"
Murmushi Hassana tayi "uhmuhm sis ina gujema fitinafa kinsan ni ,don haka ni nafi ganin ki kyaleta in halintane ai dubunta zai cikane"
"Ke matsoraciyace...saina fad'a d'in inyaso aljanun suyi k'ulin kubura dani"
Tanaji tahak'ura ta kyaleta,
Corridor d'in da zai linking d'inta da d'akinsu ta zauna awajen tana jiran dawowarsa.
Farouk kam yana shigowa kota section din su baibiba.ya haura sama d'akin indo zaune take dirshan da roban youghurt a hannunta, da katon kwalin biscuit agabanta,saita karairaya biscuit din ta watsa ciki ta cud'a da spoon tana sha .
A hankali ya turo k'ofar yashigo ,cikeda ladabi yasamu can gefe ya zauna yad'an turamata ledan hannunsan.
"Ranki yadad'e ga sak'on"
Fuskewa tayi tana wani irin muzurai,tajawo ledan tafarke kwalin sugar tad'ebi sugar wajen biyar ta watsa abaki tashiga taunawa ,rugugum rugugum.baki cikeda tarkace ,tahankad'e bakin
"Jeka abunka,saina nemeka"
Dama kamar akan k'aya yake,fit yafita
**********************************
Yagangaro kenan yayi hanyar d'akinsu yaci karoda Hussaina, tamke fuska yayi kam.
"Yaya bara muyi magana please" cikin rashin kula yace
"Uhum inajinki,lafiya?"
"Yaya kaci uwar indo ne ,nafad'a maka wallahi bawani iska she's extremely playing game with you.....kwashe duk abunda taji indo tana fad'a tayi tafad'a masa,sannan tad'aura dacewa
" yaya with full of brags fah,gaskiya you have to take note"
Wani gingering d'insa tashiga yi ,take idonsa yakad'a yayi jajir,alluran sojansane yatashi aibaiyi watawataba yajuya d'akinta steps hurhud'u ya ringa had'awa Allah ne kad'ai yakaisa d'akinta.....
Kwance take daidai akasan tiles d'in ta tasa tunbinta akasan tiles d'in d'akin.cikinta yayi tulele tama rasa ya zatayi dashi ,da k'yar take iya nishi.
Zare belt d'in wandonsa yayi yashiga sauke Mata iya k'arfinsa kamar yasamu jakkah.nishi kawai takeyi ko ihu takasa yi tsabagen k'oshin da tayi.sannan batason plan d'in ta ya ruguje.
Hakan ba k'aramar bashi mamaki yayiba ,ba arziki yafita yana maida numfashi.bai saurari kowaba yatafi gidansu.
Yana fita su Hussaina suka shiga d'akinta, lek'awa suka shiga yi taji kin labulai,suna kyakyata dariya.
Kukan kura tayi , ta datse k'ofar,had'asu taringa yi tana gwara kawukansu waje d'aya ,ihu suka dauka gaba daya .bata saurara masu ba saida taga goshinsu yayi malulai.sannan tabud'o k'ofa tawatso su waje ta maida k'ofa tarufe.
**********************************
Dadynsu ne yazo wucewa ya gansu watse a wajen ,cikeda zolaya yake masu magana
" A'ah 'yan biyuna yanaganku a kofar d'akin aminiyar taku,kotak'i bud'e maku ne? "
Hussaina ne tasoma d'agowa ,ido fal da 'kwalla ,fuska duk malolai.
Ri'ke baki yayi dariya taf cikinsa
"Topah wasu tawagar dokunane sukayi sukuwar sallah afuskarku haka?"
"Abbah daukan kisa tayi mana ai" tafad'a hawaye na gangaro mata.
"Eyyah to kuko laifin me kukayi mata har haka?"
Hassana nane data kasa motsi tace "dad kaimu asibiti kawai"
***********************************
Aliyu haidar tunda yafito daga section din dad dinsa section dinsa ,tunda yaga baiga farouk ba yasan gidansu yatafi ,ilai kuwa yana zuwa gidansu farouk,yagansa yana cika yana hutsewa.saida ya sha fama da tambayarsa.sannan ne
Anan farouk ya shaida masa dramarshi da indo,saida yayi dariya mai isarsa sannan ya rarrasoshi ,suka shiga gari yawo sai yamma lis suka shigo gidan.
Varendarn gidan suka fito ,suka sa seat na roba guda biyuda table d'in seat din a tsakiya, suka aje Hollandia milk akan table din.
Mp dinsa ya kunna,suna shan wakarsu cikeda nishad'i.
Gardamace ta kaure tsakanin su,haidar na opposing Hausa films da wakokinsu ,shi kuma farouk yana supporting
"See malam baganewa zakayi ba,wallahi since i realized that gaba daya Hausa films basirarsu yak'arene a aure sai saki,inkuma wakane kaji sunce ina sonki wance.....ya fad'a yana mimicking maganar su.
" mtesw to ai haka halin hausawan suke dole ana masu komai based on how they are if not ai bazaki suyi kasuwaba....
Letz play this,wata tsohuwar waqar adamu zango yasaka mai taken 'Aisha indo'
6ilim sukaga indo agabansu tana tik'an rawa tana mimicking din wa'kar da tsatsamar hausar ta ,kamar tana studio d'in akayi wa'kar
Juyi taringa yi tana pointing farouk kamar abokin wasanta "Nazama wata kaiko Zara ciwona ganinka zasu warke....inada beautiful face,zankaika beautiful place don nasanko zakazam fes I love you baby kace dani yes!...Aisha aisha a'i na iya kwalliya indo.....mata kutaka rawa yayye gayu kutaka rawa...."
Tafi haidar yashiga yi raf raf"wow enmata kina wuta muna binki da fetur dama kin iya rawa ne har haka?"
"Cab gadanga munefa ake zuwa damu gasan 'yan rawa a school dinmu....nalaso Kofi ba adadi"
Farouk daya cika yayi fom ,wai shine indo ke pointing dinshi tana cewa wai I love you baby ,wai tace yaes!
"Hey idiot da wannan busashen jikin naki kamar kara?"
"Ciftsi malam ummari bari kaga wata irin "
Tsayawa tayi daga tsaye tafara twisting iya k'ugunta kad'ai ,haka d'an kwankwasonta ke sama da k'asa sukad'ai batareda ta motsa komaiba
Shaye da mamaki suke kallonta ,baki sake
"Ke da k'ashi kuwa a jikinki?"
"Hmmm sosaima gadaugau nake inkana ganin ba'ane kawo hannunka"
Lankwashe hannunsa tabaya yayi kamar zata finciki hannun ta k'arfin tsiya
"A'ah malam ummari meye na 6oye hannu,sai lace zankwata ta karfi .....
" kenifa ba sa'ar ki bace ,I don't care kujirani da yaya but call me with my beautiful name faroukk!"
Dariya kamar ya kashe haidar gaba daya farouk yana Neman ya zare saboda indo?! Such a comedy.....Zuru kawai yayi masu da ido inya kalli fuskar wannan ya kalli wannan
Ca6e fuska tayi
"Hu'um sorri madam no Engilish yi mun yarena.....
Au nama mantako da sak'onki gimbiya.....ummari 'Yar Mairo tace ka jira sak'onka da biyun Daren yau"
Tawuce shi tana kakkantara jiki kamar me jin kashi
Tsam farouk yayi da ransa,tokodai da gaskene inbahakaba ya za'ayi ,yayi mata wannan jibgar har tasake tunkararsa da maganar?,gata digirgir kamar lafiyama aka k'aramata
"Nashiga ukuna nidai.....aboki kanada application d'in complete Qur'an na sudais ko minshawi." Shiru yaji waigowa wajen haidar yayi gyangyad'i yaga yanayi,har ga Allah ya aza da gaskene "aboki kajini kuwa?"
"Eyyah sorry friend, baccine yaso kwashe ni,me kace?"
Maimaitawa yayi
"Ohk muje d'akina bazan rasaba"
"Hmm kasan Allah yauba gobeba ,zan goge duk wasu bf videos na cikin system dina kai harms da nude pix"
"Haba wai yakake son zama raggon sojane?...be strong mana duk akan indon?"
"Bawata indo kawai nagane gaskiya ne"
"To ai shikenan ....muje"
Su Hassana gaba sukeyi k'akas da indo itakam ,indo ko ajikinta.
Ana haka su Hassana suka fara shirin jsce ,dady bai shawara dakowaba yaje ya biya ma indo kudin jarabawan dakomai dakomai.sunyi bak'incikn hakan amma haka nan suka hakura Haj.faty tana jin dadin yanda mai gidanta ke nuna kulawarsa ma k'anwarta fiyeda 'yan biyu 'yayan cikinsa.
Cikin sa'a sukayi jsce su Hassana anfitoda result mai kyau ,itakam indo sai godiyar Allah donko duk pass akajera mata.tuni su haidar sun koma makarantan su suma.
***********************************
Dady mutum ne simple ,kullum cikin barkwanci yake acikin iyalensa,duk wata akwai kudin da yake ware masu Hassana harda junior Wanda zasuje suyi sayyayar abubuwan da basudashi driver kekaisu,amma tunda indo tazo dakansa yake kaita shopping yasaimata duk abunda yake ganin su Hussaina dashi amma fir bata sawa,kullum tana cikin danki dasu,Sam tak'i wayewa
Ahaka akabiya masu registration na ss1 anfara zama 'yanmata,dad saida yaje yanemi izinin rikonta wajen su mama binta sannan yayi mata registration itama duk makaranta d'aya yasasu,'yan biyu sunso su fahimtar da dadynsu halin indo ,dacima mutane mutunci dazata ringa yi ,kuma duk in return su zata jawa raini,amma fafur yaki yarda ,saima samu su gasa dayayi.
Wai duk wanda yayi wani abu na wayewa har yaja ra'ayin indo tayi imitating topah tanada kyauta mai tsoka
Sosai competition din yaja ra'ayinsu har ya mance dasu gaaban dasukeyi da ita,dama dai ita indon bagaban ta iyaba,hargagin bakinne kawai
To yake nan anya ko indo zata kile tazama wayis d'in kuwa,bara dai mugani
Follow🏇🚴♀️🚵♀️
Vote💌
Commment✍🏻📩
*ZAB'AB'B'U BIYAR NA HIKMA WRITERS NA KUD'INE:-*
*GUDA D'AYA NAIRA----- #200*
*BIYU KUMA -----#350*
*IN UKU KIKESO ------#400*
*INKUMA GUDA HUD'U KIKESO-------#450*
*INKUMA BIYAR DINNE DUKA ------#500 Ne kacal biya kudinki ,ki littafin ki batareda kinci hakkin kowa ba*
*Munama masoyan mu na kwarai barka inkin shirya biya tananne kawai👇🏻*
Zaki iya biya tawannan account number
Fatima sani Muhammad
Access bank
0796627818
Idan kuma ta katin waya zaki biya ta mtn ko airtel ,to zaki biya ta wannan number 07032266778.
*Comment and share please!*
*Hassenart*✍🏻
Typing〰️〰️〰️〰️💻📲
*♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️BAGIDAJIYACE♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️*
___________________________________________
*©️HIKIMA WRITERs ASSO.*
*(Home of peace, joint entertainment to educate and enlighten our readers)*
___________________________________________
Story and written by✍🏻
Hassenart Mohammed😍
☎️090 -659 -902 -65.
*MARUBUCIYAR*
*RAYUWAR AFREDARH*💔💯
*QASAITATTUN MATA*👸👸
*RAMUWAR GAYYA*🩸😫
*and now*
*BAGIDAJIYACE*😂😁
Bagidajiyace isn't for free ,pay only #200 of MTN and enjoy your reading safely
Then if it is VIP that one is #300.
~*Dedicated to my fans*~
...........Kar kiyi share plz..........
Page 1️⃣9️⃣~2️⃣0️⃣
Yau monday su Indo za'a fara shiga makaranta ,Hassana da Hussaina ne suka fara shiryawa cikin uniform dinsu mai d'an guntun skirt,saida suka kintsa tas ,sannan suka d'auki kayan indo suka shiga mata dashi d'akinta,share² take barcinta hankali kwance
Cikeda takaici Hussaina tadaga hannu ta kalli agogon hannunta 7.15
"Twiny zafa mu makara idan muka dakata kasan nan,jibi fa yanxu lokaci,muda muke fara assembly 7.30am,nidai gaskiya zantafi ko okada ne gara nabi kwazo daga baya"
"Haba sis ai baza ayi mana komai ba tunda yau muka fara zuwa,kawai mutasheta sai muje muyi break kafin nan sai tayi sauri ta shirya mutafin ko?"
"Oho kekika jiyo wannan tasheta inzata tashi mugani tadad'i" tana kaiwa nan tasakai tayi ficewarta.Hassana ce tatasheta daga barcin a hankali ,da bud'e idon indo tayi tozali da Hassana cikin uniform, da azama ta durko agadon ,tsayawa tayi mata k'erere aka
"Jimana,Hassana kike ko Hussaina ina zaki da wannan kayar kamar Wanda zataje kamun kifi,kin wani d'irka wannan faifan hulan kamar mod'a...ga wannan takalmin na k'afarki kamar zaki kwambe"
Cikin saukin murya tace"Anty Indo bajiya dad yafad'a maki yau zamu fara zuwa makaranta ba,to wannan shine uniform din kowani cikakken dalibi haka akeso yazama...kema ganakinan cikin jaka....ki maza ki shirya karmu ,makara"
"Yanzu Ku su Hassana har bad'alar taku takai kuna irin shigar nan?Ku ringa tafiya gantsare²....lallai borin namjine....to badaniba kinji na fad'a maki tun wuri kufita idona....ina laifima asaka hijabi"
"Kiyi hakuri antyna lallurace,ko bakiso ki iya yaren nan dakika ji munayi da ya umar....me makikace sunan yaran?"
"Ohooo,Wanda ranan kukayi ta cewa musss Miss's misss ,yaren magiyoyi nace kobashiba...eh inaso "
Kwalla mata kira Hussaina tashiga yi ,daga can dining area
"To yawwa maza shirya mu tafi kinga iyayen wutan cikin can tana kiran mu"
Bata musa mata ba ta shaiga toilet tayi alwala tazo tayi sallah ta shafa mai ,tana cikin shafanne Hassana takuma shigowa,lokacin takwas har tagota
Zuwa tayi taga ta dadumo Jan powder ta da6a a fuskarta,salati Hassana tasaki
"Indo kanki k'alau kuwa!,na aza kwalliyar motsasstun nan da kikeyi saboda fashion ne,bansaniba Ashe ke d'in cuta yazamar maki...eh mana cuta inbahakaba makaranta fa zamu ko an fad'a maki makarantan mahaukata zamune ga wani uban tsamin hammata daki keyi baki dagaje dagaje da yamun bacci ido duk kwantsa...please na had'aki da girman Allah kije ki wanka indo ilu driver inya dawo kaimu cefane zai tafi kai larai kuma fa, kar mu dinga 6ata masu lokaci don Allah..."
"Ke karki nemi gayamun bak'a kinji na gayamaki,kina nufin wai duk kokarin nan ma danayi baki ganiba ?,meye to aibun kwalliyar tawa nagadai hoda kawai na gurza shima kad'an to Yaseen saidai afasa zuwan kawai ni dama barcin bai isheniba"
Tamike ta saka wani bujen wando har k'asa, takawo gajeren skirt din makarantan asama tasaka,tasaka rigar ta,ta kifa Barret d'in uwa kwano.
Tagumi kawai Hassana tayi tana daga kan gadonta tana k'arema shirin indon kallo,ta kya6e fuska kamar zata saka kuka.
Tunanika kala² yazo kanta kodai k'walwarta dama a motse yake suke mata kallon cikakkiyar mutum?koko iskancine?....karad'inta yadawo da ita daga duniyar da tatafi a furgice tad'ago tana k'are mata kallo
"To 'Yar na iya ,inkin gama kalle² d'in tashi mu tafi nashirya "
Mikewa tayi tafita dakin ahaka tasauka wajen su ,kamar kwai ya fashe mata aciki
"Indo kanki guda?...Hassana bazaki iya gyara indo ba ahaka zata makarantan?"
Momce ke masu wannan tambayan wacce zuwan ta kenan gurin da nufin tayi break fast itada dad,dayike yau su Hussaina duk sun rigasu farkawa ,saboda zumudin fara zuwa makaranta .
saiga Hussaina ta rafka tagumi cikeda takaici duk murnanta yakoma ciki
"Mom bazan iyama indoba tabbas lamarinta mai girmane... Dad kawai kacanza ma indo makaranta kasata ko public school ne don Allah"
Dad kam dariya fal ransa haka ya daure yasoma masu magana
"Waiku meyasa kuke son takurawa 'Yar zuntu ne?....kinji Aisha jeki ki cire wandon cikin nan ,amma ras kwalliyar ki yayi kyau babu mai saki ki share,har uwargidan....shima kinsan meyasa zance ki cire saboda masu makarantan kahurai ne basusan addiniba da badalilin da zaki cire..."
"Alhaji muna 'Yar kunya dakai ...karmu fara 'Yar haka..."
"Nasani antyn yara maza jekicire...d'an yaune kahaife shi baka haifi halinshiba ,baccin haka meye aibun shigan ki?a musuluncedai ai kin kwatanta....kinajiko banni dasu zan maki maganin su har ita fatsiman"
Murmushi tayi takoma bukum² ciki.
Cin serious dady yayi yakallesu gaba d'aya cikin d'an fushi²yasoma magana
"Ashe bance kuringa binta da hankula ba...da kyaran da kuke nunamata ne zai sa tasaki ra'ayinta tak'ama naku?...gaskiya banson haka,musamman ke Hussaina tunda bazaki iya kula sabgarta ba to kadaina sa masu baki kawai.....Hassana keep it up kyautan ki nanan tafe yau, don ko ayanzu mun soma ganin canji"
Dariya hajiya Fatima tayi
"A hakan ne kaga wani canji lallai akwai aiki....ke kam Hassana kamar ki ta yanke sak'a"
Cikeda takaici Hussaina ta tashi tafita itama Hassana bayanta tabi,motar sukaje suka zauna basu d'ibi wani lokaci ba tashigo suka tafi.
Idi driver kam yanayin driving yana k'arema fuskar indo kallo,duk tayi zufa tundaga saman hanci har saman bakinta.
Daganinta kaga jarababba mai kiran kyet
Bawanda yakuma bi takanta har suka isa makarantan duk inda sukabi su ake bi dakallo har suka shiga office din v.p suka bada komai aka kaisu aji
Da confidence dinta tashiga class din kamar wata muguwar guruwa.
Ajin da malami aciki duk an natsu ana jin karatu ,ai suna shigowa,atmosphere din ajin yasauya
Tuni aji yakaure da hayaniya, kowa natofa albarkacinbakinsa,su Hassana can wasu seats suka samo suka zauna itakam ,k'arewa ajin kallo tashiga yi ,ita bata zaunaba kuma bata fitaba
Malamin ne ya6ara yace tazauna mana
Haba dawa Allah yahad'ata badashiba"kajimun k'aton banasare,kana tunanin yanda kazanzaren nan da zanzaro ka tallabo tik'ek'en cikin nan da ace kyauta akace mu zauna kakoyar damu zakayi ne,to d'an lafafa mun innemi kujerun da zai d'auki nauyina tukunna,yanda zan watanda na,in bajajjage in more na kud'inmu....6araye kawai gab kuke dafara k'wace...."
Daddalo ido 'yan ajin sukayi ,suka d'auki ihu cikeda al'ajabi
"Heeeeee!!!Nawawo!!🙆♀️🙊"
Sunkuyarda kai su Hussaina sukayi saurin yi ,tuni Hassana tahau ruwan hawaye
Cikin rashin fahimta malamin ke kallonta yana yamutsa fuska,shidai yaga kamar fad'a takeyi
"Am not communicated ,the Hausa is partially strong for me....class can you please interpret what she just said to me?"
Shiru ajin akayi ba Wanda ya iya cewa komai
Ganin duk ajin yayi tawai²,yabata damar k'arikema 'yan ajin kallo....wata jibgegiyar inyamura ta hango kaf tafi 'yan ajin k'iba.
Tayi zaune da6as a seat d'in ta tana raba ido ,alamar ma bata fahimci abunda ya hautsina ajin bama
Dagudun gaske